Tushen Jarin Kowane Ɗan Kasuwa

6 GUN UBANGIDA

by @115395593230860196762

BONUS!!!

A yau mutane da dama suna aiki ne ƙarƙashin wasu a matsayin iyayen gidan su.

Mafi yawan lokuta za ka ci gaba da aiki ne ƙarƙashin ubangidan ka har na tsawon wasu shekaru inda a ƙarshe zai salame ka ko ya yaye ka.

Sau da dama ba zai bar ka hannu rabbana ba, wani ubangidan zai baka jari domin kaima ka fara naka kasuwancin.

Idan ka yi dace da wani ubangidan, zai siya maka fili kuma ya ɗau hidimar auren ka.

Ama mafi ƙarancin abun da zaka samu a gun ubangida shine jarin fara naka kaduwancin. Wanda shine alƙiblar wanan littafin.

DARASI:

Za ka ɗau tsawon lokaci kana aiki ƙarƙashin wani kafin ka samu ƴancin fara naka kasuwancin.

Tsawon shekaru kana aiki ƙarƙashin wani na nufin yawan ƙwarewar da zaka samu a wanan kasuwancin.