Chapter 21
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*Page 21*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
A.m ya tsaya cikin tsananin mamaki ya na kallon Baba Sani da ya ci magani fuskar sa babu walwala ko kaɗan, alamun da rashin mutunci ya zo koma fiye da haka don a wulaƙance yake kallon A.m da yake jin kamar ya kai mishi bugu.
" Uban me ya kawo wannan mara mutuncin gidana ya akai har ya san gidana."
Irin tarin tambayoyin da A.m yake yi ma kan sa wanda ya kasa amsa ko da guda ɗaya ne.
" Kai Malam na ga ka na kallona kamar ba ka gane ni ba."
Baba Sani ya ce cikin ɗaurewar fuska ya na ƙarasowa gurin A.m da ya harɗe hannun sa a ƙirji ya na kallon sa a wulaƙance burin sa ya ji mai yake tafe da shi.
"Ba zan kalle ka ba ka san halina ba ni da mutunci mai ya sa ka zo gidana,bayan ka san duk abin da muka yi sirri ne a tsakaninmu,shi ne za ka biyo ni har gida saboda kai tantiri ne."
A.m ya faɗa fuskar sa babu sauran fara'a ji yake kamar ya shaƙe sa,domin baƙin cikin dake cikin zuciyar sa.
"Ban sani ba na ce ban sani ba wallahi kamar yadda kake faɗin ba ka da mutunci na fika,don ni yawo nake a tasha da gidan karuwai kai ko ina tunanin iskancin na ka haye ka yi,in ban da iskanci ƴar ɗan uwana a gidan ka kake tambayata abin da ya kawo ni gidan ka.Ai tushiya mafarin dawa."
A.m ya zare idanun sa ya na kallon shi ganin yadda yake ɗaga murya ya na son kowa ya ji,duk da unguwar ta su ta manya ce kowa ya na cikin gidan sa,amma A.m hankalin sa ya tashi ƙwarai sai ya shiga waige-waige ba yan ya galla ma maigadi harara dake tsaye ya na kallon su.
Sum sum ya wuce sannnan A.m ya taso ma Baba Sani cikin hargowa zai make shi,don yadda yake jin zuciyar sa na tafasa kai dukan shi ne samun sauƙi.
Ganin da gaske dukan shi zai yi sai ya masa da sauri,amma yaƙi wucewa a gurin faɗa yake ya na hargowa tare da nuna A.m,da yake jin zuciyar sa kamar za ta yi bindiga.
A.m ya ƙara kai ma Baba Sani duka daidai lokacin da motar A.k ta sawo kai,da sauri ya yi parking tare da fitowa ya riƙe A.m da yake hargowar dukan Baba Sani.
" Ba ka da hankali ne A.m ka san me kake shirin yi ƙanin mahaifin Juwairiya za ka daka karka manta shi ya ba ka aurenta?"
A.k ya faɗa don ya kwantar ma A.m hankali ganin yadda ya zuciya.
"Allah ya sa mahaifinta ne yazo ba shi ba,tunna yaƙi kama kan sa wallahi zan kulle shi igiya ta yi rara."
A.m ya ce cikin zafi yayin da yake jin kamar ya shaƙe shi,shi baƙin cikin sa yadda akai har ya gane gidan sa.
" Bar shi A.k ka bar shi ya yi min rashin mutunci dama na lura ba shi da mutunci,amma tsoratar war sa ba za ta yi tasiri a cikin zuciyata ba.
"Ka gaya mishi in ya na son lafiyar sa, to ya bar nan kar kuma ya ƙara gangancin wucewa ta hanyar gidan,nan ballantana ya yi tunanin ƙwanƙwasa min gida,ka san ba shi da mutunci da ba ni ya samu ba haka zai fasa ƙwan kowa ya ji."
A.m ya ce ya na kallon sa da yake ta karkaɗa jikin sa alamun irin da rashin mutunci na zo ko fiye da haka.
" Ka kwantar da hankalin ka bai kyauta ba duba ga irin halaccin da muka yi masa,amma ka tsaya mu ji mai yake tafe da shi."
Ya ce da A.m sannan ya juya ya kalli Baba Sani ya ce."Mai ya sa ka yi haka ba yan mun yi waya da kai na ce maka zan zo."
Baba Sani ya kalle shi tare da kaɗa kan sa ya na ce wa."To dussa ne ni da za ka shanya ni kwana biyu na jira ka ba ka zo ba,shi ya sa na yanke shawarar na je gurin wannan ɗan mara mutuncin komai zai tafi daidai."
Tsaki A.m ya yi ya ce da shi." Ai ko in ka ƙara gangancin zuwa ƙofar gidan nan ni ne ajalin ka,don na tsane ka tsana mai tsanani mugu kawai wanda ya kasa riƙe ƴaran wan sa."
A.k ya kalli Baba Sani ya ce." To wai tsaya don Allah mene ne ba mu yi maka ba,za ka zo ka dami rayuwar mu?Kuma na gaya maka zan zo har gida aiki ne ya yi min yawa kai kuma mara haƙuri."
"Oho koma me zaku ce kuce amma ni ba ruwana gara ku tsaya ku ji mai yake tafe da ni ba wai ku tsaya ɓaɓatu ba."
Ya ce ya na girgiza jikin shi har da ƴar waƙar shi irin na cikakkun ƴan bariki.
A.m ya watsa mishi mugun kallo ya na jin wani irin tsanar shi mai tsanani ta na zagaye duk ilahirin jikin sa ya ce.
" Ko ma me ya kawo ka ka ɓace min a ƙofar gidana ko na kira ƴan sadda su tafi da kai."
"Sojoji za ka kira ba ƴan sanda ba kuma abin kunya a gare ka take,ka kulle surukin ka don ko banza na gama da kai tun da ƴar wana kake aure shi ya sha nono ya saki na kama."
Ya ba A.m amsa jin abin da ya faɗa babu ko ɗigon damuwa a zuciyar sa.
A.m ya yi ƙuta ya ce." Allah ya tsare ni na haɗa zuriya da kai dangin matsiyata,ai ko ba mata a duniya gara na zauna ban yi aure ba da na auri zuriyar ka jinin matsiyata dangin talauci."
Ya faɗa cikin ɓacin rai ya na jin kamar ya shaƙo shi ya gama masa aiki,don ya ƙara masa baƙin cikin da ke cikin zuciyar sa.
" Ok to haka kace ko ɗan ƙaruna to sako min ƴar ɗan'uwana wacce kuka yi auren kwangila da ita,dama na zo na tuna maka da yau saura wata biyu da kwana shirin da takwas da yini ɗaya,amma fa ban da kwana auren kwangila ya ƙare ma'ana kuɗin ka sun ƙare shekara ɗaya ka iba,kuma waɗannan watanni biyu da kwanaki suka rage sai a shirya sako min ƴata,don Juwairiya ba ta da uban da ya fini."
A tare suka buɗe baki tsananin mamaki ya kama su ko kaɗan ba su taɓa tunanin haka zai faru ba,lallai Baba Sani ya cika tantiri ɗan duniya ne wanda ya zama lamba ɗaya.
A.m cikin fushi ya taso kan sa ya na faɗin." Baka da hankali matar ta wa kake maganar kwanakin rabuwarmu,kai za ka sake ta ni nake da ikon sakinta,kuma babu ɗan iskan da ya isa ya sakin min mata.
Ya numfasa ya na jin wani irin tashin hankali da mamakin sa ya ci gaba da ce wa."Kuma da kake maganar haka auren ta na yi don ta haifa min yaro,ammma ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba shi ne har za ka zo ka ce wa'adi ya cika?To na ga uban da ya isa ya sakin min mata."
" Allah ko ɗan zamani hauka kake yi ka yi abu da ƙuruciya ni kuma zan nuna maka da wanda ya riga ka shan iskar duniya,ya girme ka ko da da sakan ne.Bari kaji lokacin da ka zo nai man auren Juwairiya na bi dindigi na gane kai ko ɗan waye da duk wani labarin ka,har da asalin matarka da komai na ta na sani zan iya zuwa gurin aikin ta na kai mata recording ɗin da na yi,lokacin da ka zo neman auren Juwairiya har ma da na ɗaurin auren ku."
Sai suka zare ido jikin A.m ya yi sanyi matuƙa har ya kasa magana don ya cika tantiri na gaske!
Ganin yadda maganar sa ta razana su sai ya yi dariya ya ciro wayar sa ya kunna recording ɗin suna ji,babu wanda ya iya ko tari a cikin su sai tsantsar razana da A.m ya ji musamman a ce ya kai ma Daddy kamar yadda ya yi ninya.
A.k ya gyara tsayuwar sa ya na jin wani wani irin tashin hankali ya na ziyartar sa,wani irin gumi yake jiƙa shi don ko kaɗan bai yi tunanin Baba Sani ya na da wannan wayon ba,lallai sun yi boko mai zurfi amma shi ya nuna musu aiki da shi.
" To kun shirya saurara ta ko na tafi don ni ba na son ɓata lokaci."
A.m shiru ya yi ya ɗauke kan sa ji yake kamar ya fisgo shi ya danƙara wayar da ƙasa.
A.k ya kalli A.m da ya kasa ce wa komai ya ce da shi." Ka shirya zama da Juwairiya a matsayin yadda ko wace mace take a gidan aurenta ko har yanzu ka na kan bakan ka ku...?"
" Allah ya kyauta na zauna na har abada da gaiyar tsiya ai in wannan mara mutuncin ya na raye ba zan taɓa haɗa zuriya da su ba,kuma mai zan yi da gayyar matsiyata ba na son Juwairiya yaro nake son ta haifa min na saketa,sannan ba zan yi asarar kuɗina ba dole sai ta haifa min baby,wallahi ko dashe ne sai am mata don ba zan yi asarar kuɗina ba."
A.m ya katse A.k da yake magana cikin zafi da kakkausar murya mai hargowa.
" Kuɗin ka ne zai tafi a banza ka maida matsiyata masu kuɗi,dama ta hanyar wani Allah yake azurtawa ɗan ƙaruna,yanzu sai ka ƙaro kuɗi na shekarar ne ko shekara biyu,amma fa ka sani ba zan yadda Juwairiya ta zauna a cikin wannan daular ba,don haka sai ka shirya kawai ka je a farke mahaifarta ayi mata da she ta haihu kowa ma ya huta."
Ya ce ya na kallon A.m da jikin sa ya yi sanyi don yanzu yake nadama ashe tunanin halin sa ya wuce wannan.
Sannan ya ɗora da ce wa "Mahaifiyar Juwairiya ta taso ni kan sauran lokacin da ya rage Juwairiya ta dawo aure za ta yi mata,sosai ta yi min bore har ta na barazanar kai ni kutu ƙila tare za a kai mu ko kuma ka ba ni kuɗin da zan san yadda zan yi na kawar da idanunta kafin wa'adin ya cika."
Har zuwa lokacin shiru suka yi suna kallon juna da mamakon sa.
"A.m ka na jin abin da ya faɗa na fara shakku an ya mutum ne shi ko aljani? Allah ba shi da imani karfa ya zo ya ruguza komai,zan ji kunya sosai domin ni Daddy zai fi ba ma laifi don ban kasance aboki na ƙwarai ba."
A.k ya ce ran shi a ɓace ganin abin da suka yi cikin sirri ya na son ya fasu.
" Kyale matsiyaci ka ba shi kuɗi kawai don ba zan iya sakin Juwairiya ba matuƙar ba ta haifa min yaro ba,don ina son jinina ya fito ta tsatson ta tabbas ubanta mutumim kirki ne don ya ba ƴar sa tarbiya na ƙwarai,amma na san kai yaranka sai dai su ɗauki halin dabbobi don ba su yi dacen uba na ƙwarai ba."
Dariyar jin daɗi ya saki ganin ya ci galaba a kan sa ya ce." Allah ya sa karuwai za ka kira su ni na san halin su,kuma na san irin tarbiyar da na basu in dai kawai na ji bayani wato kuɗi abokan harka.In baka accourt numba ne ko cash za a bani."
Takaici ya hana A.m magana sai A.k ne ya kalli A.m ya dafa kafaɗar sa ya na faɗin "Ka koma ciki kawai zan ji da shi."
Kamar ƙaramin yaro ya juya ya shiga ciki da ƙyar yake ɗaga ƙafafun sa ya na shiga falo ya zauna shaɓar, ya na jin wani ƙunci a ran sa abu ya haɗu ya tarun masa goma da ashirin.
Juwairiya ta fito daga kicin jin shigowar sa wanda ta ɗan ji hayaniya sama-sama,amma ba ta sheda abin da yake faruwa ba,asalima komawa kicin ta yi ta ci gaba da aikin ta don babu kyau laɓe.
Hannu ya miƙa mata ta iso gare shi janyo ta ya yi ta faɗa ƙirjin shi tare da matse ta da ƙarfi har sai da ta yi ƙara ya ce." Juwairiya ina cikin damuwa sosai abu ya yi min yawa.Zainab ba ta son farin cikina wai dama haka ne abin da kake so shi yake wahalar da kai?Tana amfani da son da nake mata ta na azabtar da zuciyata,ga Baba Sani ya zo ya ƙara min zafi."
" Baba Sani ya zo gidan nan na shiga uku."
Ta ce tare da zare jikinta daga gare shi ta zare idanunta don ta san zuwan shi ba alkhairi ba ne.
Kan sa ya ɗaga masa ya riƙe hannunta sosai." Yanzu ta tafi."Ya kwashe duk yadda suka yi ya gaya mata cikin rauni yake maganar.
Juwairiya ta yi shiru ta na kallon sa sai ya ba ta tausayi sosai juya mishi baya ta yi da nufin ta ce mishi ya bayyana auren su kawai,don ta gama kamar ya fara son ta da irin kashe ta da shaukin kala-kala da yake yi,amma sai ta ji muryar sa ya na faɗin.
"Juwairiya don kawai ina kwaɗayin na ga ƙwaina a duniya kuma ke ce mace ta biyu bayan Zainab da na ji zan iya rayuwar auren wucin gadi da ita,da ace zan iya zama da wata ba yan ke da zan rabu dake ne kawai saboda tantirin ƙanin mahaifin ki sam ba shi da mutunci,sai dai kamar yadda ba zan iya rabuwa da Zainab ba domin an halicci zuciyata don ita haka ba zan iya rayuwar auren wucin gadi da wata mace ba in ba ke ba."
Tasowa ya yi ya rungume ta ta baya kamar yadada Juwairiya take hawayen jin ya na faɗin zai iya rabuwa da ita hak shi ma ya fara hawayen rashin ɗa.
Juyo da ita ya yi suka fuskanci juna dukkannin su hawaye na zuba fuskar su ya ce."Kin san na yi miki ƙoƙari Juwairaah don Allah ko da nine ba na haihuwa ki yadda na zuba kuɗaɗena ayi miki dashen mahaifa kin ga Zainab ita an yanke mata mahaifar."
Da yadda yake magana ya ba ta matuƙar tausayi sosai ta ƙara sautin kukan ta ta na ganin an ya ta yi masa halacci kuwa,duba ga irin abin da ya yi mata kuma sai da ta yi masa alƙawari karo na farko ta ji ba ta kyauta masa ba,don har ciki ta zubar wanda bayan ta sha lemun tsamin,amma har wata biyu bai zoba sai da zai zo ta ji ciwo sosai,sai dai shima bai yi ma zuciyarta adalci ba saboda ta na son shi ko idanunta ya isa ya isar mishi da tsaƙon hakan,amma ya yi biris da ita ko tunanin shi bai gane son shi take ba."
A tare suka fara tafiya kowannen su ya shige ɗaki domin samawa junan su maslaha daga halin ƙuncin da suke ciki.
A.k da Baba Sani ya sasha fama kafin Baba Sani ya amince ya karɓi kuɗin da ya ba shi,amma ya rantse in har lokaci ya ƙare zai zo ya ƙara karɓar wani kuɗi,kuma A.m ya sa a ran shi dole ya saki Juwairiya ko da ba ya so.
A.k ya yi shiru kawai ya na kallon sa har ya gama zuba mishi rashin mutunci ya tafi,a ran sa takaicin A.m yake yi sosai don shi ya jawo musi wannnan tashin hankalin,haba!A ce kana auren mace wani yazo ya yi maka iko da ita sai ka ce ya na zaman dadiro.
Ai dama duk abin da aka yi tare da son zuciya a kwai nadama a cikin sa dole mutum ya yi nadama, yanzu in da duniya ta san matar sa ne har wani banza ya zo ya maida su A.t.m ɗin sa,to koma mene ne ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ka doka.
Sati biyu da Zainab ba ta nan Juwairiya ta yi amfani da damar ta koya mishi wani kalar kulawarta,wanda shi kan shi mamakin ta yake don yanzu ta cire kunya ta na son ta saka mishi soyayyarta a ciki zuciyar shi,don haka duk abin da ta san zai faranta mishi rai kuma matar sa ta kasa da shi Juwairiya ta cika gurbin sa,shi kan sa mamakin yadda ya saki da ita yake yi.
Sai dai ya kan tuna Juwairiya ba macen da namiji zai iya wulaƙantawa ba ne ko da kuwa ba ya son ta,don Allah ya yi mata abubuwa da dama ga tsananin kula da ibada sosai,sam ba ta wasa da ibada wanda hakan ya na matuƙar ƙara masa ƙimarta a idanun sa.
In ka gan su a gidan zaka ɗauka wasu masoya ne ko da yake ya sha gaya mata shi kan sa bai san ya aikai ya sake da ita da yawa ba,amma kawai su rayu tamkar ma'auratan da suka yi auren soyayaya domin ya na jin zai iya mata komai a zaman su in dai zai faranta mata.
A.m ya kai da komai ba ya iya yi sai dai ta yi masa hatta abinci a baki take ba, gabaki ɗaya ya shagwabe ya koma kamar wani ƙaramin yaro ya na fatan ina ma ace Zainab ɗin shi take da wannan hali na kula da shi lailai da ya more.
Juwairiya ta dage sosai ta saka wata irin shaƙuwa a zuciyar A.m ba tare da ya san haka ba,shi ya na danganta hakan da irin kular da take ba shi shi ya sa in ya ji kewarta sai ya ɗauka jikinta da yake matuƙar so yake sa shi jin kewarta.
Amma take zai nemi waya ya kirata su shi hira sosai,ya kuma ɓata lokacin sa ya na waya da ita.
Duk irin kular da take ba shi ta mai da kanta tamkar baiwa a gare shi ta na jiran ta ji ranar da zai rungumeta ya ce mata ina son ki!
Amma bai taɓa faɗin haka ba sai kalaman da suke sakata kuka yake faɗi irin su,kina da wata irin baiwa da ba ko wace mace take da shi ba,in kika riƙe alƙur'ani ki na karatu wani irin ƙarin ƙima kike samu a idanuna,domin Allah ya jarabce ni da son mace mai kula da ibada.
"Juwairiya duk ranar da muka rabu zan yi fama da kewar ki ina kishin mijin da zaki aura nan gaba domin ya yi dacen mace ta gari da baiwar kyau da sura.
Alokacin da nake kallon ki cikin hijabi sai nake jin tsanar ki kamar ba ki waye ba,ashe Juwairaah mata masu saka hijabi wata baiwa suke da shi na kyawun sura kike ɓoyewa.Surar ki abin sha'awa ce ga kowa.
Har lau ina faɗa miki zuciya ta da gangar jikina za su yi kewar ki,amma ba komai zan mai da kula ta akan ɗan ki sai ya zama wani abu a rayuwa,Allah ya sa ki haifa min baby mai kamar ki."
Duk lokacin da ya faɗi haka Juwairiya ringume shi take ta saka kuka iya ƙarfin ta shi kuma ya ɓuge ya yi ta aikin rararrashi.
A haka dai suke zaman su cikin kulawa da juna da girmama juna don in Juwairiya na mishi magana,gabaki ɗaya hankalin sa yake ba ta ko tari ba ya yi sai ta gama ya na matuƙar girmama lamarin ta,don ita ma ta na ba shi kulawa har ya na kawai ya ƙyale Zainab ta tafi duk in da yake so tun da ya na da wanda take kusam makwafin ta kawai Juwairiya ce baya jin ta a zuciyar ta amma komai na ta ya yi masa.
Ranar wata alhamis Juwairiya ta dage ta shirya ma A.m abincin da yafi so wanda duk sai da ta zauna ta tambaye shi,ta kuma saka su a cikin ranta don kullum sai ta tambaye shi abin da yafi ƙauna a cikin rayuwar sa,kuma duk ya gaya mata.
Ƙarar shigowar mota ta ji da sauri ta miƙe daga sallayar da take zaune bayan ta idar da salla,ta na karatun alkur'ani ta rage zaman jiran dhi don ta ƙagu ya dawo musamman da ya kirata ya ce mata a kwai labari mai daɗi.
A ranta tunani take ko zai zo ya faɗa mata ya na sonta shi ya sa ta ɗauko kur'ani ta na karantawa,saboda ta zaƙu matuƙa da ya shigo.
Ɗaga labulen ke da wuya ta leƙa kawai sai ta ga Zainab ta fito janye da akwati,wani irin tashin hankali ya ziyarce ta ta saki wata ƴar ƙara na rashin jin daɗin dawowar ta ta zauna jaɓar!
Sai kuma ta yi zubbur ta miƙe da ta kalli kanta a madubi sai da gabanta ya buga ta yi kyau matuƙa ga ƙarin haske da ta yi,da jikinta bai da haske amma yanzu wani irin ja ta yi sosai jikinta kamar ka losa jini ya fito.
Falo ta fito amma lokacin har Zainab ta shige ciki sai ta koma ɗaki ta yi kiran A.m tare da yi mishi albishir da Zainab ta dawo.
Zubbur ya miƙe ya tattara komai ya taho gida don ya ganta saboda ya yi mising ɗinta sosai.
Ya na shigowa ɗakin ya same ta a zaune ta na ɗaki waya take yi ganin sa sai ta kashe wayar ta miƙe ta na zare ido,tare da dafe ƙuncinta a tunanin ta mari zai kai mata kamar na farko.
Amma sai ya ba ta mamaki sosai ya ganin ya harare ta ya saki tsaki ya nemi guri kusa da ita ya zauna.
Abin sai ya ba ta mamaki ta kalle shi ta ce." Habibi i miss you zuc.."
Wata uwar harar ya daka mata tare da taɓe bakin sa.
"Rufe min baki shashasha kawai ni za ki yaudara duk abin da kika ga dama ki je ki yi ta yi na zuba miki ido duniya ce,tunna ƴan'uwan ki dabbobi ne ba su san a kwai Allah ba bare annabi ya faku."
Ya miƙe ya sauko ƙasa don ya ci abinci ita ma sai ta biyo shi dama wanka ta yi ta na son ta sauko ƙasa ta ci abinci,sai aka kira ta ganin kiran na kuɗi ne don wata Hajiya ce take son ta yi mata oder kayan ɗaki za ta aurar da yara biyu.
Biyo shi ta yi da sauri suka sauko ƙasa duk yadda take ta mishi hira bai tanka ba don ya so ace Juwairiya na gefen sa yake cin abincin ya yi ta mata sanni ,ita kuma ta yi ta murmushi dimple ɗinta ya na lotsawa shi kuma ya yi ta saka hannu a gurin don ya na burge shi,sai ya ciro wayar sa ya tura mata da tsaƙon godiyar abincin har da steaker na kis akai ma abinci.
Rungume wayar ta ta yi tare da sakin ma hoton sa da ta ɗauke shi ba tare da ya sani aba suna zaune a falo,saboda bai taɓa ce wa zai ɗauke ta hoto ba duk da in ta yi kwalliya ya yi ta yabawa shi ya sa ita ma ta ɗauke shi ba tare da ya sani ba.
Kuma ya yi kyau sosai kamar wani balarabe ta saka pasword a gurin hoton kafin ta buɗe sai ta rubuta sunan ta da full sunan shi.
Da sauri ta saka ƙaton hijabin ta har ƙasa saboda tsoron fita kiran da Zainab ta yi mata,sai da gabanta ya buga don gani take hijabin ƙara mata kyau kawai ya yi,amma dai ya rufe surar jikinta da A.m kullum sai ya yi ta yabon shi ya na zuzuta wa.
A hankali ta taku har zuwa in da suke duk da dukan da gabanta yake yi.
Zainab haka kawai ta tsinci gabanta ya faɗi ganin yadda Juwairiya ta canza har sai da ta miƙe, gabaki ɗaya ta zama kamar wata matar gidan yadda fuskar ta ya canza ta ƙara haske sai abin ya ba ta mamaki ƙwarai ta kalle ta tare da sakin ƙara ta ce.
TO MASU KARATU ABIN DA ZAINAB ZA TA CE YA TSORA TA NI NA MIƘE DA SAURI HAR BIRO NA YA FAƊI GASHI NA NEME SHI BAN GAN SHI BA KUCI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.
BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI
SAKACINA KO HALIN MAZA
TAKU
JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba ***_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.