SAKACINA KO HALIN MAZA

Chapter 23

by @jamilalawalzangojamcy




*SAKACINA KO HALIN MAZA?*    



  *RUBUTAWA:-*
 *JAMILA LAWAL ZANGO*

                   *SADAUKARWA GA:-*

 *SUMMY M NA'IGE*
              _(Aminiya)_             

      
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

                          *Page 23*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM



Cikin tashin hankali ta kama shi ta riƙe ta na kuka sosai kamar ranta zai fita ganin hankalin sa ba shi a jikin sa.
"Na shiga uku A.m so kake ka yi kisa?".
Ta faɗa cikin muryar kuka ta na girgiza shi gabaki ɗaya ta ruɗe gani take kamar zai ƙara yankar ta.

Wani mugun kallo ya watsa mata ya sake ta ya na huci."Allah ya sa ki ƙara gigin aibata aurena sai na zama ajalinki."

Binta da ta ji maƙura da gudu ta ruga ɗaki tare da kulle kanta ko kaɗan ba taɓa tunanin mahaukaci ba ne ganin zai illata ta.

A ranta ya zama dole tabar gidan domin ba za ta zauna ba ya kashe ta.

Ta shiga cikin tsananin mamaki da ya ce Juwairiya matar shi ce,to mai hakan yake nufi bayan Anty Zainab ta gaya mata yar aiki ne.

Sam ba ta kawo cewar zai iya ije matar shi a gidan ta zama ƴar aiki ba,shi ya sa ta ɗauka kawai ya gaya mata hakan ne don ya kawar da tunaninta aka suna zina.

Haɗa kayanta ta shiga yi domin dole in Anty Zainab ta dawo za ta bar gidan ba yan ta tsegun ta mata.

Juwairiya kuwa kuka ta saki ta ƙara faɗawa jikin sa." A.m ka na cutar da zuciyata mai kake tunanin zai faru in har ta faɗa ma Anty Zainab abin da yake faruwa,kawai gidan nan zan bari ayau in ya so duk abin da zai faru ya faru,amm na gaji da wahalar da rayuwata da kake yi.

Da ƙarfi ya janyo ta jikin shi ya na huci.
"Juwairaah ki saurare ni ba ni da nufin na cutar dake kawai ki fahimci abin ɗaya.."

Juwairiya ta katse shi ta na faɗin cikin kuka da murya mai ƙarfi.
" A.m ya ishe ka ba ka sona ka tsane ni wannan dalilin ya sa kake wahalar da zuciyata da gangar jikina,kullum sai dai ka yi min maganar ka na son jikina halina da kyawuna shin ni bani da zuciyar da za.."
                    "Juwairiya."

Ya faɗa da ƙarfi tare da girgizata ya na zare idanunsa.
"Karki kawo min maganar banza kin san dalilin aurenki so ban ga dadilin da za ki kawo min maganar banza ba."

Fisge hannunta ta yi ta na kallon sa ta na ja da baya har ta kai bakin ƙofa da gudu ta fice.

Ko da ta shiga ɗaki halin da ta ga Binta sai ta ba ta tausayi karɓar tsummar da ta ga yaga cikin kayanta ta na ƙoƙarin ɗaure gurin yankar.

Hannu ta saka ta karɓi tsummar ta ɗaure mata hannun yayin da hawaye yake kwaranya a fuskokin su duka.

" Ki yi haƙuri haka rayuwa take tafiya a ko da yaushe talaka shi ne a ƙasa ko da shi yake da haskiya."

Ta faɗa ta na kallonta idanunta na ƙara zubar hawaye.
Binta ba ta ce komai ba sai share hawaye da yake gangarowa a ƙuncinta da ta yi.

A ranta ta saka ba za ta ƙara kallon kowa daga cikin su ba balle ta yi magana ta tono ma kanta tsuliyar dodo,ganin abin da ya yi mata ya sa ta fara tunanin ko bashi da imani ne amma har yanzu ba ta amince da faɗin cewar Juwairiya matar shi ce,sai dai in za su yi mata badda kama don kar ta gaya wa Zainab.

Kallonta ta ƙara yi ta na jin tausayinta matuƙa ganin yankan da ya yi mata ya shiga ciki sosai.

             "Anya A.m ya na da hankali?"

Tambayar da ta yi ma kanta kenan amma ta rasa amsa sai ta ɗago ta ƙara kallon Binta a karo na biyu.
"Wannan dalilin ya sa na ce miki ba za ki fahimci komai ba."

Ta faɗa tare da juya mata baya sai dai ta ji a jikinta kamar babu kowa a ɗakin ko da ta juyo wayam ba Binta ta fice daga ɗakin.

Duk yadda ta so ta yi magana amma Binta taƙi tanka mata sai in ta ga za ta takura mata ta saka mata kuka,hankalinta ya tashi matuƙa ta yi zuru ta na kallonta.

Binta ta saka a ranta ba za ta ƙara mata magana ba balle ta tanka a kan cin amanar da suke yi ita da shi,Allah Allah ta ke gobe ya yi Zainab ta dawo ta saka mata kukan ta kaita gida.

A.m bai shigo gidan ba sai misalin bakwai bayan ya dawo daga masallaci kamar yadda bai neme ta ba,haka ita ma domin ko kiranta ba ta son ya yi saboda hankalinta ya tashi jin ya faɗi za a yi mata dashen ƙwan haihuwa.

Sai ta fara nadama matuƙa ta na ji kamar ta gudu daga gidan don ta san mundin ta faɗa mishi to ita ma yanka ta zai yi ko ya kasheta,saboda ya gaya mata duk abin da ke tsakanin su ba da wata manufa yake yi ba burin sa ya samu baby shi ya sa yake mata haka don haka ta saka a ranta abin da ya fi na Binta zai yi mata.

Kwanciya ta yi ba wani karsashi a tare da ita saboda duk yadda ta so ta zo su kwanta amma taƙi sai ta samu guri a ɗakin da Baba take zama ta kwanta.

A.m da ya gama shirin baccin sa shiru ba ta zo ba dama bai saka ran za ta zo ba kuma shima ransa babu daɗi don sun yi ɗan tanka-tanka da A.k akan nemar shawarar sa da ya yi na dashen da yake so ayi mata,amama sai ya nuna rashin amincewar sa akan ya ƙara haƙuri har Allah ya kawo.

A.m ya ji ba daɗi don ya gaji da jiran gawon shanu don haka ya nuna ma A.k rashin amincewar shi in da har ya ji zafi ya gaya masa magana,yayin da ya saka a ranshi kawai za su tafi ai shi ba uban shi ba ne da duk a bin da zai yi sai ya nemi shawarar sa.

Ɗakin da take kwance ya nufa tare da saka cocilar wayarsa ya haska fuskarta,ba bacci take ba amma ta yi maza ta rufe idanunta jin shigowarsa.

Ta yi mamakin da bai tashe ta ba ya juya ya fita.

Hankalin shi ya ɗan tashi ya shiga tunannin ko ta gudu ne don bai ganta ba,sai kuma ya duba ɗakin da ya san Baba ta na zama ilai kuwa ta na ɗakin ta takure a guri taya ta na baccin wahala, don ko numfashi ba ta saukar wa ta daɗi ganin yadda ta takure kanta.

Sai dai ya yi mamaki ƙwarai ko da ya matsa kusa da ita sai ya ga ta miƙe zubbur ta na salati,wanda ya saka a ranshi mafarkin shi take yi.

"Inna lillahi na bani don Allah karka cutar da ni mahaifiyata ba ta da rai."

Ta faɗa da muryar kuka ta na roƙonsa amma bai kula ta ba sai ya saka hannu a aljihun wandon sa ya zaro bindiga ya ɗora mata a goshinta.

Ta buɗe baki za ta yi ihu amma sai ya saita daidai bakinta ya ce da murya mai sanyi."In kika yi ihu sai na kashe ki.".
Ya faɗa da wata irin murya da ta ƙara tsorata ta wanda ya sa ta yi sauri ta rufe baki ta tare da mai da kukan.

Ganin ta yi shuru ta na kallon sa har fitsari ta yi a wando.

A.m ya kalleta tare da watsa mata harara ya fara magana da ce wa."Gobe Zainab za ta dawo Allah ya sa ki faɗi wani abu a tsakanina da Juwairiya kashe ki zan yi."

Wani irin kartawa cikinta ya yi ta ƙara toshe bakinta ta na tunanin yau Allah ya kawo ta gurin jidali gashi mai gida na son ya kasheta.
"Wallahi ba zan ce komai ba babu ruwana ka taimake ni karka kashe ni."

Ganin ta tsorata ya sauke bindigar ya na shafawa ya ce."Good in kunni ya ji gangar jiki ya tsira ina fatan kin gane."
Da da sauri ta ɗaga masa kai sannan ya fara taku zai fita wanda Binta ta fara addu'a Allah ya raba ta da shi lafiya.

Ganin ya kuma jiyo sai hankalinta ya ƙunduma ya tashi ta ƙara firgicewa ta na tunanin mai ya saka ya dawo."
"In Zainab ta dawo ina son ki yi ƙaryar aljanu a mai dake in da ka ɗauko ki in kuma ba haka ba wannan zan saka na kashe ki."

Ya faɗa ya na nuna ta da bakin bindiga sannan ya juya ya fice daga ɗakin.
A ranar kasa bacci ta yi ta na ta kuka daga ƙarshe dole ta koma ɗakin da suke kwana don gani take kamar zai dawo ya kasheta.

Washegari gidan ya kacame sai gyara ake yi kasancewa da misalin sha ɗaya Zainab za ta iso shi kan shi gogan bai je ko ina ba ya na zaune a falo ta iso.

Tun da suka shiga ɗaki ba'a ƙara jin ɗuriyar suba sai da aka kira sallar azahar sannan A.m ya yi wanka ya fito yayin da Zainab take biye a bayan sa don ta fito ta ba ma cikinta haƙƙin sa.

Binta da take jiran fito ba ta jima da jin fitowarta ba lokacin ta na waya ta fito da gudu ta ruga zuwa waje sai ta dawo ta kalli Zainab ta ƙara rugawa waje,tun Zainab ba ta damu ba sai ta ɗan firgita tare da daka mata tsawa amma ba ta dai na ba ƙarshe fashewa da kuka ta yi ta kama suratai.

Zainab da ta matsa ne sa da ita ta na faɗin."Na shiga uku ke Juwairiya fito ki ga abin da take yi dama Anty Fati ta san ba ta da hankali ta kawo min ita?"

Ko da ta fito ta ga halin da take ciki sai hankalinta ya tashi matuƙa yayin da tsoro ya shigeta gani take kamar ta yi hakan ne don ta tona asirin su.

"Gida za ni amai da ni gida a kwai dokin da nake hawa ni Sarkin ljanu a can in kuma yau ba hau ba duk saina yi maganin ku."

Ta faɗa da tsamin murya ta na girgiza jikinta kamar ta na da aljanun da gaske.
" Na shiga uku kin ji mai take ce wa?"
Ta ce da Juwairiya da ta tsaya ta na mamakinta yayin da tausayinta ya cika ranta don ta san ta yi hakan ne don ta koma gida ita ba ta san A.m ya tsoratar da ita bayan wannan.

Kama ta yi ganin ta na jijjiga sai hawaye ya wanke mata fuska.

Zainab da ba ta taɓa ganin wai mai aljanu ba sai ta tsorata ainun take ta kira Anty Fati jikinta na ɓari ta sanar mata halin da Binta take ciki nan take ta ce bari ta turo direba da mai aikinta su taho da ita don sam iyayen ta ba su yi mata bayani ba.

Zainab ta tsorata sosai a ranta Allah Allah take direban Anty fati ya iso,abincin da take ci kasa ci ta yi ta tsaya ta na kallon ikon Allah yayin da jikinta ke ɓari.

Suna cikin wannan halin ya shigo da sauri ta ƙarasa gun shi ta yi masa bayani.

Ya kalli Binta da take kaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa ta na zare ido,sai hakan ya so ya bashi dariya amma ya cije.

Wata uwar tsawa ya daka mata ganin ta gan shi sai ta razana kamar za ta gudu don Allah ya saka mata matuƙar tsoron shi.
Ɗan natsuwa ta yi amma ba ta daina zare ido ba ita a dole ga mai aljanu.

A.m ya kalleta sai ya kauda kansa tare da taɓe baki ya ce da Zainab da ta yi tsuru-tsuru ta na kallon Binta.

" Maganin ki kenan da shegen kwashe-kwashen ki ta yi maza ya bar gidan nan ai ga yi nan kin je kin jawo ma kan ki mai almatsutsai."

Ya yi maza ya haye sama ya na dariyar yadda Binta take yi sai ka ce wata ƙadangaruwa,saboda in ya tsaya dariya zai kubce masa.

Direba na zuwa Zainab ta saka aka kwashe kayanta tare da yi mata ihisani aka wuce da ita.

Ta na shiga ɗaki kuka ta fashe da shi na tausayin Binta haka kawai ya yi mata sanadin rabuwa da aikin ta bayan ya san ita marainiyace an ya ya kyauta kuwa.

Ta na kallon shi akan mutum wanda ya fiye son kan sa bai damu ba in dai zai faranta ma kansa da masoyiyar sa bai damu don ya cutar da kowa ba.

Don haka ko wayar da yake yi da ita in ya fita duk lokacin da Zainab take nan ta ƙi daga ƙarshe kashe wayar ta yi saboda haushin sa da take ji matuƙar gaske,don ya faye son kan sa akan komai.

Zainab ba ta haƙura da neman mai aiki ba don har ta yi maganar a kawo mata wata.

Makarantar da ta fara sai hakan ya yi maata daɗi sosai ikon Allah kenan duk da ta cire rai sai gashi Allah ya saka ta na da rabon yi.Abin da iyayen gidan ta suka zaɓa mata ya sa ta ƙara yadda da cewar nufin su rayuwarta ba ta da wani amfani sai dai don ta yi musu hidima saboda girki suka zaɓa mata,ita ta na ganin wani kalar girki ne ba ta iya ba,amma kuma da ta fara karatu sai ta raina kanta don gani ta yi kamar da can ba ta iya komai ba.

Ganin hakan sai ya dage damtse burinta ta iya girki ta yadda za ta siye zuciyar A.m,da take jin kamar ana mata wahayin son shi.

Duk da cewa makarantar sau uku take fita a sati amma ta na jin daɗin karatun,sosai fiye da komai ba kamar da da ita kaɗai take rayuwarta in dai matar gidan ta na nan.

Juwairiya ta yi ƙawa ɗaya a makaranta wacce suka shaƙu sosai duk da ba su daɗe ba,sai dai ita matar aure ce har da yaranta biyu.

Suna matuƙar shiri sosai komai ma su tare suke yi ga halin su ya zo ɗaya ba ruwan su da hayaniya,musamman ita da take kullum cikin bege da ƙaunar masoyin ta.

Kimanini wata uku da fara karatun Juwairiya wanda Zainab ta ɗauko ƴan aiki har guda uku sai A.m ya yi tsalle ya kawo ƙauli da ba'adi.

Ganin haka sai ta kori Baba in da aka kawo mata mai jini a jika ta na koya mata girkin amma ba ta kwana don ta na da miji sai dai tun safe in ta zo sai magariba take komawa gida.

Ranar wata Juma'a Juwairiya ta tashi da ciwon kai mai zafi da zazzaɓi ko tashi ta yi sallah ta kasa ga wani irin sanyi da yake shiga cikin ƙashin jikinta ya na nuƙurƙusanta.

Abin takaici gashi suna da test don ana gabda yi masu jarrabawa.

Ganin ba zata iya zuwa ba gashi matar gidan ba ta nan kuma yau A.m zai dawo daga tafiyar da ya yi,wayarta ta ɗauka tare da duba numbar ta kiran numbar Hauwa Tukur amma wayar ba ta shiga ba sai ta yi tsaki ta jefar da wayar ta kwanta.

Ta na kwance jikinta na ƙara zafi sosai kamar wuta misalin tara sai ga kiran Hauwa Tukur ya shigo,da ƙyar ta janyo wayar da ke kusa da ita ta kanga a kunninta ta na nishi a wahalce.
"Hello Juwairiya ba za ki zo makaranta ba ne lafiya kin san muna da test ga shi Malam D.d ba shi da mutunci."Hauwa Tukur ta faɗa a ranta ta na tunanin mai ya hanata zuwa,kasancewar ba ta wasa da karatu.

" Wallahi ba na jin daɗi ne kin san sai da lafiya ake komai.Don Allah ki yi min test ɗin in zai yi wu."Ta ba ta amsa ta na kyarmar jiki.

Bayan ta yi mata sallama tare da mata alƙawarin in dai ya yadda za ta yi mata ta kashe wayar ta koma ta kwanta.

Sai misalin shidda na yamma A.m ya shigo babu abin da ta yi masa na abinci.
Ganin halin da take ciki ya ruɗe sosai kamar zai yi hauka a tunanin sa ciki ta samu,don haka jiki na rawa ya ɗaga waya ya kira likita ya zo ya duba ta.

Juwairiya ta ji hankalinta ya yi ƙololuwar tashi jin ya kira likita ita yadda take jin ciwon gani take kamar ciki ne.

Kawai sai ta ji hawaye ya fara sauka a ƙuncinta don ta san lokacin rabuwar su ya yi daga ranar za su fara irga kwanaki.

Bayan likita ya zo ya yi mata gwaje-gwaje ya sa ta yi fitsari ta kawo masa.

A.m da ya yi zugum duk ya ƙosa ya ji abin da likitar zai faɗa,ya na ta addu'ar Allah ya sa likita ya yi mishi kyakykywan albishir.
"Ga wannan maganin za ka siyo maleria ce ke damunta in sha Allahu tasha magani za ta warke."

Hankalin sa ne ya tashi matuƙa kawai sai ya ji hawaye na son ya zubo a ƙuncin sa yayin da zuciyar sa ta karye da tunanin zai samu ɗa.

Jikin sa a sanyaye ya karɓi takaddar ya fice tare da likitan don ya siyo magani ko kallon ta da take zaune bai yi ba.

Wani wawan ajiyar zuciya ta saki wani irin sanyi ya ziyarce ta jin ba ciki ta samu ba.

A ƙalla sai da ta yi kwana uku sannan ta warke sarai ta shirya ta tafi makaranta.

Suna zaune da Hauwa Tukur ba yan sun fito daga lakca Hauwa Tukur da hankalinta yake kan danna wayarta ta kalle ta da ta zuba uban tagumi ta yi nisa gurin karanta wasiƙar jaki.

"Yawan tunani ba shi da amfani ga lafiya kuma ban ga dalilin da zai saka ki zo makaranta ki zuba uban tagumi,ba yan kin baro gwarzon ki a gida nifa da kika ce baki da lafiya na ɗauka ciki ne da ke."

Wani irin tashin hankali ya ziyarce ta ta zare idanunta ta na kallonta.
"Subuhanallahi ciki kuma ni fa ba matar aure ba ce."

Ta faɗa tare da gwalalo idanu jin abin da ta faɗa yayin da take mamakin mai ya saka ta faɗi haka.

Sakin dariya mai sauti ta yi ta ɗauki lemun robar da Juwairiya ke sha ta zuƙa tare da kwashewa da dariya.

"To don Allah meye na tsorata haka sai ka ce na ce kin yi kisa."

Ta faɗa ta na mamakin yadda ta razana haka saboda ta haƙiƙance ma kanta ita matar aure ce,sai dai in ba ta son ta ga ya mata amma ko wa ya kalle ta ya san ta na da aure.

"Haba Juwairiya ko wane mutum ya kalle ki ya san kina da aure kin san a kwai matan da dole a gane matan aure,duba ga yanayin jikinta ki kalle kanki kema kin san bakya son ki gaya mini ne,to ki mai da wuƙar ni ban ce zan gan shi ba bare ki yi tunanin ko zan bashi ƙanwata ne."

Ta ce da tsigar wasa saboda ta na son ta kwantar da hankalinta ganin yadda ta birkice lokaci guda.

Jin abin da ta faɗa sai hankalinta ya tashi sosai duk da gargaɗin da zuciyarta take mata na kar ta faɗa mata halin da take ciki,amma ta na jin lokaci ya yi da za ta daina shanye damuwarta ita kaɗai ta sanar da ita ko don ta samu shawarar yadda za ta cire son maso wani a ranta.

Kama hannunta ta yi ta haɗe da na ta ta kalli ta cikin muryar son kuka ta ce."Tabbas tunanin ki haka ne amma ina buƙatar mu samu in da babu mutane ina da damuwa ina son ki ba ni shawara."

Ganin ta fara kuka sai ta riƙe hannunta suka koma in da babu mutane.
"Tabbas tunanin ki gaskiya ne ina da aure amma auren sirri na yi da mijina na shekara ɗaya."

Sai ta din ga kallonta irin kin zare kenan ko kuma baki san mai kike faɗa ba ta kasa magana sai kallonta take yi.
Ganin ta kasa yadda da abin da ta faɗa mata sai ta ƙara fashewa da kuka ta na jin wani irin zafi a zuciyara ta.


Hauwa Tukur da ta yi shiru ta na jinjina wannan lamarin mai kama da shirin fim ko hikaya a gare ta!A ranta ta na mamakin ta ya ya za'ai wannan aure ba tare da sanin mahaifiyarta ba!Ita ko wani irin so take mishi?An ya ta yi tunani kuwa mai ya kai ta namiji ba ɗan goyo ba ne ɗan masara ne ana goyon shi ya na kayan gemu."

Maganar zuci take amma ba ta san maganar zuci ya fito fili ba.
Ta riƙe hannunta ta na kuka sosai ta ce ba yan ta yi murmushi mai ciwo."
Dole ki jero min waɗannan tarin tambayoin ni ma na san na yi kuskure,kullum cikin dana sani da kukan zuci nake yi."

Ta saki hannunta ta miƙe tare da juya mata baya ta ƙara ce wa da ita."Allah ya jarabce ni da tsananin son shi sosai,amma A.m ya tsane ni baya sona ni ce mace ta farko da ya tsana saboda a koda yaushe cutarwa ce a tsakanin mu ya na ƙara saka min son shi a raina.

Na san ce wa ban yi ma mahaifiyata adalci ba amma babu yadda zan yi ne Baba Sani yaƙi taimakonmu,gashi ba na son na rasa ta,kuma ko banza auren sa ya ceci rayuwata daga auren Alhaji Tanimu,amma kuma yanzu ina tsoron ranar da A.m zai rabu da ni na san ranar ita ce ranar da fitar numfashina zai yi bankwana da gangar jikina."

Hauwa Tukur da take jin tashin hankali ita mamaki take ba ta da har ta yadda za ta iya saida ɗanta,amma sai ta danganta shi da don ba ta san son da yake tsananin uwa da ɗanta ba ne shi ya sa ta aikata wannan aiki,da kuma zafin talaucin da take ciki uwa uba Baba Sani da ya ke mugu azzalimi.

Ta nisa sannan ta fara magana cikin mamakin mugun hali irin na Baba Sani.

"Gaskiya na ga wauta da ƙuruciyar ki duk da kin yi hakan ne saboda ki taimaki rayuwarku,amma a kwai kuskure a ciki haba ta ya ya zan amince na auri mutum kuma na zauna a matsayin mai aikin matarsa har na iya wanke mata ƙazantarta wallahi hakan ba zai yi wu ba,na tabbata da kin ƙi amincewa in dai idon A.m a rufe yake ya na son yaro dole ya naimi wata hanyar k..."

"Don Allah ki fahimce ni na san na yi kuskure amma kuma abin da ya faru ya riga ya faru!Ki ba ni shawarar yadda zan saka soyayyata a cikin zuciyar sa,yadda dake ya sa na bayyana miki damuwata saboda friend in need is a friend indeed."

Ta katseta jin ta na ta maimaita maganar da wautar da ta yi bayan ta san hannun agogo ba zai taɓa dawowa baya ba.
"Wane shawara zan baki ni fa ina son naga ranar da wannan lamari zai fasu har na zaƙu da na ga kin yi ciki don a kwai turka-turka kina ganin Zainab za ta yadda ta karɓi yaron ne?shi kan sa bai yi tunani ba domin ya ibo ruwan dafa kan sa ala'mura canzawa za su yi saboda man propose but Allah dispose. Sannan babban kuskuren da ya yi na kawo ki gidan sa Zainab ta sanki ina tausaya masa lokacin da maganar ciki za ta fito fili,don Zainab ba ƙaramin hauka za ta yi masa ba.

Ni yanzu shawarar da zan ba ki shi ne ki ƙoƙarta a ki samu ciki za ki ga yadda komai zai canza."

Saka kuka ta yi ta ce."Shawarar da za ki ba ni kenan?ba ki san waye A.m ba kuma ba ki san Zainab ba shi ya sa kike ganin kamar inna samu ciki zai soni wayar ta ta ciro ta nuna mata hoton A.m da Zainab wanda ta ɗauke shi na falon su da suka manna..

A duk lokacin da ciwon son shi ya kamata sai ta ciro hoton ta na gani saboda zuciyarta ta sare da soyayyar A.m ganin irin zuƙeƙiyar matar da yake aure,amma haka ba ya canza komai ta na ganin son shi kamar wahayi ake mata.

"Duk da wahalar da shi da Zainab take mata har ƙasashe take fita kasuwancinta amma kullum ya na gaya min ita ce matar so ni matar wucin gadi ne,amma abin takaicina sai ya zo ya din ga more ni ya na gaya min irin baiwar da Allah ya yi min bai taɓa kuskuren faɗin ya na sona ba."

Hauwa Tukur ta yi matuƙar tsorata da ganin su kamar wasu larabawa yanzu ta gane dole jikinta ya canza saboda irin daular da take ciki.
Hannunta ta ƙara riƙewa ta ce."A.m ya haɗu irin mazan nan ne masu wayo da dubara sam ba za ki taɓa gane in da ya dosa ba,amma na yi mamakin in da kika samo wannan gayen saboda maƙura ne gurin kyau."

Murmush mai kama da kuka ta saki."Don Allah ki ba ni shawara yadda zan jawo hankalin sa."

Numfashi mai ƙarfi ta."Ikon Allah ita Zainab wata irin banzar mace ce ina tausaya mata ranar nadamarta saboda na ga sakacinta sosai mace sai kace mahaukaciya abubuwan da take yi sam babu tsari aciki kuma ni na fi ganin laifin A.m da ya barta take mishi wannan iskanci.Gaskiya ba na goyon bayanki da kike kare kanki daga ɗaukar ciki, wanda ko ba a faɗa ba na san irin kuskuren da matar sa ta yi kenan kuma na tabbata ta na nadama.Ga kuma in da son duniya ya kaita haba ai ya raina mata wayo ya kawo matar sa cikin gidan ta ya na more abar sa ya maida ita shashasha.

Duk da ita ta na tunanin ba zai taɓa duba gareki ba saboda ba ku dace da juna ba tunaninta bazai kawo mata zai iya ɗaga ido ya kalle ki ba duba ga matsayin sa,ba ta san namiji ba haka yake ba abin da kake ganin yafi ƙarfin sa sai kiga ya mutu akan abin."
Sai ta kwashe da dariya ta duk da ganin halin da take amma rainin wayon ya yi yawa gani take kamar ya na raina musu wayo ne daga ita har Zainab ɗin.

" Matsalar ka bayyana damuwarka ga mutumin da ka yadda da shi kenan na yi tunanin za ki ba ni shawara,amma ba ki duba halin da nake ciki ba kin tsaya ki na min dariya."

Ta faɗa a zuciye tare da ɗaukar wayarta za ta tafi.

Da sauri ta ɗauki jakarta ita ma ta kama hannunta."Afuwa lamarin ne a kwai rikitarwa ni dai ina baki shawarar ki kasance a shirye, saboda duk ranar da Zainab ta san abin da ke tsakanin ku Allah kaɗai zai raba ku lafiya yanzu ki ɗaga waya ki kira A.m ki sanar mishi da kina son shi mijinki ne fa,wanda yake dawowa ba yan ki ya kwanta mai zai hana ki sanar da shi."

Ta ce mata ta na kallonta a ranta jinjina lamarin take yi."Ba zan iya gaya masa ba kuma ba zai bani damar haka ba haba ya kamata ya ce ya gane irin son da nake masa ko ƙwayar idanuna ya kalla ya kamata ya gane."

"Ai ko dole ki sanar masa meye amfanin dakon son mutumin da bai sani ba kuma ko banza,daga ranar da kika gaya masa irin son da kike masa wallahi ko baya sonki ya kalle ki a matsayin kina son sa zai din ga kallon ki kuma ko banza masoyinka yafi maƙiyinƙa sannan a tunanina a haka wani abu mai girma zai shiga tsakani ba tare da ya sani ba."

Juwairiya jikinta ya yi sanyi matuƙar gaske zuciyarta ta halasto mata irin tarin son da take dakon sa ta ji ya na tasowa nan take ta faɗa kogin zuma har ta ji za ta iya kiran sa ya zo ta sanar mata da damuwar zuciyarta duk da kafin su yi aure sai da suka yi sharaɗin babu wannan wayarta ta zaro domin ta kira shi.


WANI IRIN FIRGITA NA YI SABODA BUGUN ZUCIYAR JUWAIRIYA DA NAKE JI YA SA CIKINA YA MURƊA NA TASHI DA NUFIN NA JE BAYI,AMMA KODA NA DAWO TSABAR TASHIN HANKALI BAI SA NA GANE MAI KE FARUWA BA SABODA SAUKAR BUGUN ZUCIYARTA JI NAKE KAMAR ANA BUGAMIN GUDUMA.
TOFA KO YA ZA TA KAYA A M ZAI AMINCE DA SOYAYYARTA?

KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

   BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



           SAKACINA KO HALIN MAZA 


                              TAKU 

                 JAMILA LAWAL ZANGO
                             JAMCY





  Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba ***_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.