Chapter 25
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*Page 25*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Hajiya Zainab tana zaune a ƙaton katafaren falonta ita da ƙawarta mai suna Nabila wacce suka taso tun yarinta,amma ita tana aure a Abuja ta zo ganin gidane da kuma ta ya Zainab murnar asibitin da ta buɗe.
Lantana ce ta shigo saboda tsabar gulma jikinta har kyarma yake yi.
Duk da ganin tana tare da baƙuwa amma sai ta kasa haƙuri har baƙuwar ta tafi, matsawa kusa da ita ta yi ta fara magana don tsabar gulma da yake cinta.
"Hajiya don Allah in ba za ki damu ba ina son na yi magana da ke kuma mai mahimmanci."
Zainab ta kalle ta sheƙeƙe tare da jan tsaki ta na tauna jingam a bakinta.
"Ni fa Lantana na fara gajiya da halinki yadda kika san ke kika kawo babu duniya,na san yau ma bai wuce ki ce na baki kuɗin aiki kafin wata ya ƙare ba,kuma na rantse ko me za ki ce ba zan bayar ba."
Ta faɗa hankalinta na kan waya ta na hira da matar da ta addabeta take ta tura mata da sallama kullum,ba ta daina ba har sai da ta yi nasara ta fara magana da ita suna gaisawa.
Lantana ta kalleta a ranta ta ce."Banza mara mutunci kawai ai wallahi don kawai iskanci suke yi da ita da na so ma ya aureta na ga ƙaryar iya shege."
Amma a fili sai ta ce." Ba wannan ya kawo ni ba idanuwana sun yi mummunan gani kuma in kika ji,wallahi hankalinki zai tashi matuƙa ba na son abin da zai cutar da ke ne kasancewar ki na taimaka min.
" Ke dakata karki dame ni da shegen surutunki."
Ta ce bayan ta ije wayarta sannan ta kalleta ta ci gaba da cewa." Za ki iya magana ba ni da matsala ƙawata ce tun na yarinta."
Lantana ba haka ta so ba amma tun da ta faɗi haka gashi gulma na iban ta sai ta kwashe abin da ta gani,harma da ƙara magi da gishiri don ya yi zaƙi cakwai ta fara gaya mata.
Ba ta kai ga ƙarshen labarin ba in da take tunanin zai fi ɗaga hankalinta.
Zainab ta miƙe kamar wata mahaukaciya ta kai mata raruma.
Wani irin shaƙa ta kai mata cikin ihu ta zare idanunta kamar mahaukaciya.
" Ke baki da hankali mijina kike maganar kin gan shi da wata in ma da wata kika gan shi,bai kamata ki haɗa shi da wata ƙazamiya kucaka yar matsiyata ba."
Sai kawai ta rufeta da duka da mari take kai mata.
Lantana ta hau ihu da ƙarfi ganin dukan da take mata ta ƙara sakin ƙara ganin ta wawuro wani gilas za ta maka mata.
" Don Allah ki taimake ni wallahi abin da na faɗa miki gaskiya ne,ba zan shirya irin wannan ƙaryar na gaya miki kawai don na ɓata miki."
Ta faɗa yayin da ta ruga ta ɓoye a bayan Nabila da ta miƙe cikin tashin hankali ganin za ta yi kisa.
" Zainab be patient kar fa kishi ya sa ki aikata dana sani,ya kamata ki yi ma maganarta kyakykyawar fahimta,ita ba ƙaramar yarinya ba ce da za ta yi miki gulma don son ranta."
" Ke Nabila dakata wallahi yanzu za ki fita da fashashshen kai mundin kika yadda da abin da take faɗi,mijina mai aji da kyau za ta haɗa shi da mai aikina.Na yadda da A.m ba zai taɓa kula wata ƴa mace ba,don ban taɓa ganin ya kula mata masu aji ba bare ita ƙazama mara gata da aji."
Ta ce da ita tare da ƙara rarumar abu ta yo kanta da shi.
Nabila ba ta damu da abin da ta ce ba ta tunkare ta tana ƙoƙarin ƙwace makamin da ta ɗauka.
Da ƙyar ta samu ta zauna tare da dafe kanta ta ce."Na yi baƙin cikin da ki na nan ta kawo min wannan baƙin labari,da bakya nan sai na nuna mata haukana."
Sai kuma ta kai mata shaƙa da ƙarfi saboda gani take kamar ta raina ta ne ta kawo mata wannnan labari.
Lantana idanunta suka kaɗa suka yi jajur ta na ƙaƙari saboda ta shaƙe ta sosai,sai zaro idanu take ta na dana sanin gaya mata gashi za ta baƙunci lahira ba ta shirya ba.
Lantana ta sadaƙar mutuwa za ta yi ta tabbata da ita kaɗai ne da Zainab a gidan, sai ta kasheta dama haka take da kishi akan mijinta take barin shi ya na garari.
Da ƙyar Nabila ta ƙwaci Lantana da take fitar da numfashi sama-sama.
Ta samu ta tura ta cikin ɗaki tare da rufe ta a ɗakin ta dawo gurin Lantana da take murza wuyanta.
" Kin tabbata abin da kika gani gaskiya ne?"
" Wallahi da gaske ne Hajiya da idona na gansu."Ta faɗa cikin kalar tausayi.
" Ok ga wannan ki riƙe na gode da kika gaya mana ki ci gaba da saka ido a kansu."
Lantana da ta ga an miƙa mata farare gal da su sai ta washe baki,ta karɓe ta soke sannan ta kalle ta ta ce.
" Hajiya na gode dama tuntuni nake lura da ita yadda take mishi kallo kamar mayya,zan ci gaba da bibiyar su amma fa sai dai ki bani numbar ki ba zan gaya ma Hajiya Zainab ba kashe ni za ta yi."
Bayan ta gama da Lantana ta buɗe ɗakin ta shiga ta na zaune akan gado,ko kaɗan ba ta nuna damuwarta akan maganar ba,saboda ta saka a ranta A.m ba zai taɓa dubi ga wata ƴa mace ba.
Nabila ta zauna a gefen ta suna fuskan tar juna.
Zainab na yi matuƙar mamakin irin yadda kika yadda da mijnki duk da ba ina zargin sa ba ne, amma Lantana ba za ta taɓa gaya miki ƙarya ba musamman in kika dube ta za ki ga alamun gaskiya a fuskarta,na tabbata a kwai ƙamshin gaskiya a maganarta ko da kuwa ba haka maganar take ba.
Duk da cewa A.m mutumin kirki ne wanda bai damu da irin wannan rayuwar ba,ni kai na ba na tunanin zan iya tarayya da mai aiki duba ga yadda ya tsani duk wani talaka,amma ki tsaya ki yi karatun ta natsu ki saka ido domin namiji ba shi da tabbas!"
Zainab ta kalli Nabila a wukaƙance tare da miƙewa ranta a ɓace ta ce.
" Ba na son wulaƙanci Nabila mijina za ki din ga haɗa shi da wata.A kwai yadda a tsakaninmu da shi,muddin kika ce za ki faɗi wani abu na rashin kirki a garesa wallahi yanzu za mu raba jaha da ke."
Ta buɗe baki za ta ƙara magana ta ɗaga mata hannu tare da nuna mata ƙofa."Ki fitar min daga gida na yanke duk wata alaƙar da ke tsaƙaninmu."
Miƙewa ta yi ta ɗauki jakarta ta na kallonta.
" Bazan yi fushi da ke ba ƙawata zan yi miki uzuri har zuwa lokacin da za ki gane gaskiya,ni na san dole wata rana za ki neme ni bayan kin gane cin amanarki yake yi."
Har ta fara taku bayan ta gama magana sai kuma ta dawo,ta tsaya gaban Zainab tare da riƙe hannunta ta na hawaye ta ci gaba da magana.
" Ba wai ina son na tona miki rayuwar aurena ba ne a'a sai don na gaya miki don ki ɗauki darasi a ciki.Kamar yadda kika ba wa A.m amana haka na ɗauki yaddata na ɗora akan Al'amin,ba ni da haufi akan sa na yadda da shi fiye da yadda na yadda da kaina.Kwasam na kama shi da kwandom a aljihun sa wanda hakan ya ɗaga hankalina matuƙar gaske har sai da na kwanta jinya.Na yi kuka sosai rikici sosai muka yi sai daga baya na haƙura bayan duk mutuncin sa ya zube a idanuna."
Fara tafiya ta yi bayan ta gama gaya mata ta na kuka.
Jikinta ya yi sanyi da sauri ta kama hannunta ta riƙe tare da faɗawa jikinta ta fashe da kuka sosai.
"Don Allah Nabila karki saka zuciyata ta gasganta abin da kike faɗa min domin zuciyata ba za ta iya jure ganin A.m da wata mace ba!Kin ji na rantse miki duk ranar da A.m ya yi gigin kallon wata ƴa mace to ni ce ajalinmu baki ɗaya,nufin sa zai iya ganin ɗansa a duniya bayan ni na lalata rayuwata saboda shi?"
Ta ce ta na kuka tamkar wata wacce aka yi wa mutuwa sai kuma ta janye jikinta tare da share fuska.
" Kai ina! Zuciyata kasa karɓar zargin da kike masa A.m ya yi min alƙawarin ba zai kula ko wace ƴa mace ba kuma na yadda da shi,in kuwa zargin da kike masa ya zamo gaskiya wallahi sai na canza kamannin ko wace ya mace da ta haɗa jiki da shi, ke bama Juwairiya wulaƙantacciya ba ko yar gidan uban waye acid zan wasa ma shegiya ta mutu kowa ya huta."
Cikin matsancin kuka take magana gabaki ɗaya hankalinta ya tashi,sosai duk da ta yi ƙoƙarin ta saka zargin da take ma A.m,amma in ta tuna ko kallon fuskarta ba ya yi bare ya riƙe sunanta sai ta ji sanyi ta kauda zarginta.
" Haba Zainab kamar ba ki waye ba ina bokon na ki yaje? Ai yanzu karki nuna komai ki nuna tamkar ba ki san da wannan maganar ba,sannan ki saka matakan tsaro ki sa ido sosai a tsakanin su duk wata hanya da zai saka ki fahimci ko da wani abu ki kula da ita sa..."
" Kai."
Zainab ta ce sannan ta kalle ta taci gaba da magana." Ta ya ya za'ai na kauda kishina na saka ido don in gano abin da suke yi,ba zan iya ba ni kawai zan tambaye shi ne in ya gaya mini ƙona su duka zan yi,in ya so duk abin da zai faru ya faru!" Ta furta cikin tashin hankali yayin da take ji sam ba za ta iya ba.
"Na san ba zai iya auren ƴar aiki ba,amma yanzu sun cika ɗora kwaɗayin su ba sa iya ɗauke idanun su.
Ki ɗan danne kishinki ki gano wani abu in har kika gane ya na tare da ita, ni zan siyo miki acid ki watsa mata,ko ki bani kwangilar watsa mata babu uban da zai ɗaure ni yar manya ce ni mijina kuma canal."
Da ƙyar Nabila ta yi nasarar kwantar mata da hankali,duk da har yanzu ta kasa amincewa,don haka ta saka a ranta ya na dawowa za ta tambaye shi dole ya gaya mata komai.
A tare suka fito daga ɗakin suka nufi kicin in da Lantana take aiki,ganinZainab da gudu ta ruga ta na faɗin.
"Wallahi Hajiya na gan...."
Da sauri Zainab ta ɗora ɗan yatsa a bakinta kan ta yi shiru,don ta na jin kamar ta ƙara mata wani dukan.Kuɗi ta ƙara ma Lantana da take ta murna sosai ga duka ga samun kuɗi ita kam yau gulma ta yi riba.
Zainab na zaune a gaban madubi ta na tsantsara kwallliya zuciyarta cunkushe da tunani kala-kala.
Ji ta yi an rungume ta ta baya sannan ya ɗora kan sa a bayanta,ba ta juya ba kasancewar tun kafin ya shigo ƙamshin turaren sa ya bayyanar masa da shigowar sa.
Fuskarta a ɗaure ta juyo ta kalle shi sama da ƙasa haka kawai sai ta ji wani mugun haushin sa da tsanar haɗa jiki da shi.
Sakar mata murmushi ya yi tare da kamo hannunta.
" Gibbiyar mata sarauniyar mata a cikin birnin zuciyar Abdurrahman mai na yi ake fushi da ni? Ko don rashin dawowata da wuri ne am so so sorry babyna wallahi wani uzuri ya tsare ni na kira wayarki ba ta shiga."
Ya faɗa da muryar sa mai sanyi da take kwantar mata da hankali ya kuma san ya na sace zuciyarta da ita.
Ganin ta ƙi kula shi sai ya kamata suka faɗa gado ya na shaƙan kamshin turarenta ya na faɗin.
" Wane irin turare kika sa yau kamar yafi wanda kike shafawa daɗi,don ban taɓa jin ƙamshi mai kwantar da zuciya da saka nishaɗi a rai ba..
Gaskiya kuma kwalliyar ta yi na kuma yaba bari kiga in siye ta koma nawa ne babu tayi."
Ƙoƙarin warware tawul ɗin dake jikinta yake yi ya na gaya mata kalamai masu daɗi da kwantar da hankali.
Da sauri ta ƙwace jikinta ta harare shi ta saki tsaki ta saka kayanta ta fice daga ɗakin ba tare da ta kalli in da yake ba.
Tsayawa ya yi yana kallonta ran sa ya ɓace saboda ya tsani tsaki ita ma ta san haka,don haka bai ƙara kula ta ba ya tuɓe kayan sa ya watsa ruwa,bai nemi abincin ba saboda sai da ya tsaya gidan A.k ya ci abinci tun da ya san Juwairiya ba ta nan gashi ya kasa iya cin abincin Lantana.
Kwanciyar sa ya yi ba tare da ya ƙara kula ta ba,wanda hakan ya sa ta fara yadda da abin da Lantana ta faɗa mata,tun da har zai iya ƙyaleta ganin ta yi fushi ba tare da ya rarrashe ta ba ko ya tambayi ba'asi.
Tun tana saka ran zai zo ya rarrrasheta amma sai ta ji shiru,ta kalli agogon hannunta ƙarfe ɗaya na dare sai ta sauka a chert ta shige ɗakin sa tare da buga ƙofar da ƙarfin gaske.
Tsayawa ta yi a kan sa ta na huci kamar wata mesa ganin bacci yake yi,filo ta ɗauka tare da maka masa ya buɗe ido cikin razana ganin ta tsaye a kan sa sai ran sa ya ɓace,ya kalle ta bai ce mata komai ba amma idanun sa suna masa kallon gargaɗi.
" Kaga Malam ka tashi magana nake son mu yi da kai."Ta ce dashi tana girgiza ƙugu idanunta a bushe kamar ba dare ba.
" Zainab."
A cikin wata irin murya ya yi magana sannan ya ɗora da ce wa." Don Allah bacci nake ji ki bari sai da safe."
Ya rungume filo tare da mirginawa ya ci gaba da bacci,komai ya tuna sai ya juyo ya na kallonta ya miƙo mata hannu yana nufin ta zo su kwanta.
Wani irin kallo ta watsa mishi." Ka ga Malam wallahi sai ka tashi ba za ka barni da baƙin ciki na kasa bacci ba don ba zan iya bari gari ya waye ba."
Sai ta fara tsiya ta na mishi wasu irin maganganu da ya kasa gane mai take ce wa,sannan kuma ta hana shi bacci da ga ƙarshe dole ya tashi saboda magana take da murya mai ƙarfi,kuma abin da take faɗi ya yi mugun ɗaga masa hankali duk da bai wani fahimce ta ba.
Tashi ya yi zaune ya na mata wani mugun kallo.
" Wallahi baki da mutunci ga shi na tashi gaya mini damuwarki,amma ki sani in na ji maganar ba ta da mahimmanci kin san sauran."
Ya faɗa da muryar gargaɗi ganin ta hana shi bacci.
Hararar shi ta yi tana faɗin" Oh koma me za ka ce kai ka sani tun da ka zama munafuki, ka bani mamaki fir'auna a zuci Annabi Musa a baki." Ta faɗi hakan ne don ta gane ko ƙarya Lantana take mata don har yanzu ta kasa yadda da abin da ta faɗa mata.
Bai ce mata komai ba ya ƙara watsa mata mugun kallo na na gargaɗin ta iya bakinta.
Cikin tsanani mamaki A.m ya ji ta watso mishi tambayar da ya girgiaza shi ta ce.
" Mene ne alaƙar ka da Juwairiya?"
Ya shiga cikin tsanani tashin hankali ya ruɗe matuƙa ya kuma razana domin jikin shi rawa yake ayi,jin tambayar da ta watso mishi ya shiga damuwa Baba Sani ya faɗo mishi a rai yana tunanin ko shi ya faɗa mata,ya san zai iya don ya na shakkar sa ba shi da mutunci na ƙarshe.
Allah ya so babu wadatacciyar haske a ɗakin sai fitila mara haske na bacci dake kunne mai kama da babu,domin da a kwai ya tabbata babu abin da zai hana ba ta gano gaskiya ba,saboda jikin sa ya jiƙe sharab da gumi sai zufa yake karyo mishi,ya na ji a ran sa in Allah ya haɗa shi da Baba Sani sai dai Allah zai raba su.
Shirun da ya yi sai zuciyarta ta karye ta fara tunanin to ko gaskiya ne.
A.m da yaga zai tona a sirin kanshi da kanshi sai ya dake cikin wata irin murya ya ce." Mai ya sa kike min wannan banzar tambayar waye ita kuma meye haɗa ni da ita? Ƴar aikin ki fa kike danganta ni da ita kin cuce ni,mai zan yi da ƴar matsiyata jinin talauci kin taɓa ganin na kula wata mace duk da damuna da suke yi balle ita.
Wani irin sanyi ta ji ya kamata jin abin da ya faɗa dama ta san ce wa babu yadda za ayi ya kulata,amma don kar ta yi saurin sauko wa ta ce." Ba wani nan munafiki ai ni ka bani mamaki ka rasa wacce za ka kula sai ita,to bari ka ji na rantse maka ba ita ba ko wace mace ka kalla nine ajalinta saina illata rayuwarta,yadda ko waɗanda suka kawo ta duniya ba za su so su ganta ba balle kai kana tunanin zaka haihu ne ni bana haihuwa."
A.m da ya koma ya kwanta jikin sa a mace hankalin sa ya tashi sosai,ya ɗan ji daɗi da ya fahimci ba Baba Sani ya gaya mata ba,don in da shine duka zai ɓata lamarin ya tabbata sai ya kunna mata wannan recording da ya yi,amma a ran sa ya na mamakin wane munafukin ne ya gaya mata,ya san ce wa A.k ba zai taɓa gaya ma matar sa ba."
Domin ya cire mata shakku sai ya miƙe cikin ɗaga murya ya ce.
" Look Zainab na lura baki da hankali ko kuma kin sha wani abu ko kin fara ɗaukar zigin ƙawaye,in baki yadda da ita ba mai zai hana ki daina yawo ki zauna ki kula da ni,wanda ni kaina zan fi buƙatar haka,bawai ki tsaya kina zargina da wata kucaka ba,kamana kike tunanin zan iya kula ta mai take dashi kuma waye ubanta a duniya."
Ya yi ƙuta ya ci gaba da magana da ƙarfi ganin maganganun sa suna tasiri a kanta saboda ta yi shiru ta na sauraren sa.
Janyo ta ya yi zuwa jikin sa." Zainab please trust me."
Ya ƙara marairaice murya ya na shafa bayanta da ta yi lamo a jikin sa kamar wata mage ta na ƙara jin madarar son sa na ƙwaranya a zuciyarta.
A.m da ya ji ta yi lamo a jikin sa ya saki gwauron numfashi,ya na tunanin yadda zai yi ta amshi yaron da Juwairiya za ta haifa masa,amma ya saka a ran shi dole ta karɓa ko ana ha mata ana ha maza.
" Bai kamata ki yadda da zugin maƙiya a kanmu ba ki tuna na yi miki halacci har yau babu wanda ya san ke ce bakya haihuwa,kuma na kasa haɗa wata mace da ke na riƙe alƙawarin da ba yi miki duk da ina son naga ƙwaina a duniya fiye da rayuwata,hakan ba zai sa ki yadda da ni ba?"
Zainab jikinta ya mutu murus duk da ta yadda da shi,amma ta ɗauki aniyar cusgunawa rayuwarta da wulaƙanta ta agaban shi,domin ta cire ɗan shakkun da take yi a zuciyarta kuma in ta gane gaskiya Lantana ta kuka da rayuwarta.
" Ka yi haƙuri zauji zuciyata ce ta kasa gasganta hakan bayan na san halinka fiye da kaina,amma in sha Allahu ba zan ƙara maka irin wannan tuhumar ba, kuma ni ma na fahimci maƙiya ne suke son su raba mu sai dai su mutu don ni da kai mutu ka raba."
Rungumota ya yi ya ce." Wannan dalilin ya sa nake matuƙar son ki auren mu da ke sai mutuwa za ta raba ni da likitar likitoci.
Yauwa bari na siya kwalliyar da aka hana ni siye bayan daga kallo ɗaya na siya babu ta yi gashi yanzu har ta yi arha."Dariya ta saki suka manta komi .
A.m bai tambayi wanda ya gaya mata ba amma ya zama dole ya ƙara saka tsaro saboda someone is behind ko kaɗan bai yi tunanin Lantana ba ce.
Cikin tsananin mamaki Baba Sani ya tsaya a ƙofar gidan sa ya na kallon Maama da ke tsaye da ƴan sanda guda biyu a bayanta.
" Yauwa ranka ya daɗe ga shi nan ku kama shi."Ta faɗa fuskarta babu walwala.
" Ranka ya daɗe don Allah kar ku kama ni na rantse gobe Juwairiya za ta dawo na gaya mata,amma ta ƙi ji duka yau sati biyu da shekara ta yi kuma wannan bawon Allah ya taimaki rayuwarta."Ya faɗa ya na zare ido.
" Ok kin ji abin da ya ce ki yi haƙuri in har ba ta dawo ba sai mu ɗauki mataki."Ɗaya daga cikin ɗan sandan ya faɗi.
" Ba komai Allah ya kaimu goben in kuma ba ta dawo ba zan kai gaba,ko da kuwa baku ƙwato min haƙƙina ba."
Ta ce ta kalle Baba Sani cikin ɓacin rai ranta ya na faɗa mata a kwai abin da Juwairiya da Baba Sani suke ɓoye mata.
A daren da suka yi maganar da misalin ƙarfe biyu na dare Mama na zaune a sallaya ta na karatun kur'ani bayan ta idar da sallar nafila.
Sai ta ji kamar ana buɗe get ɗin gidan tsoro ya hana ta motsi zuwa can ta ji an shigo.
Wasu ƙattin maza majiya ƙarfi guda uku suka shigo.
Da sauri ta miƙe ta na salati kafin ta furta komai sun shaƙa mata wani abu a fuska ta zube luuu a ƙasa.
TO FA MASU KARATU NA IJE BIRONA SABODA TSORON WAƊANNAN MUTANE INA TUNANIN SU WAYE.
KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.
BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI