2
by @asmybaliyu
DANGIN JUNA
Asmy b Aliyu
2
Yayi iya kokarin sa dan yaga laptop din ta kawo wuta amma bata kawo ba ,A fusace yyi wurgi daita kasa takarasa tarwatsewa ,,sai lokacin ya maida hankalinsa kan rufaida .
Iya karfinsa ya daddage ya naɗamata duka amma ga mamkin sa ko motsi batayi . gabansa yaji ya fadi hannunsa ya kara dai-dai hancinta nan ma bata numfashi.
Dagota yyi yana girgixata da karfin gaske hey ! Rufy ,kitashi mana Allah idan Baki tashiba xan xaneki ne."
Ya karasa maganar a fusace shuru yaji ware manyan idonsa yyi akanta kodae ta mutu yashiga ukku !
Nan take ya rude gefen bed dinsa ya ajeta ya nufi fridge din dake gefen sofa....ya Ciro gorar ruwa da sauri ya bude gorar ya tsiyaye mata su kakaf akai cike da mugunta. Doguwar ajiayar xuciya ta sauke cike da jero atishawa ,,dan ruwan sanyi ne masu kankara aciki ya zazzage mata su ajiki gaya kuma tana mura..
Ruwa kadan xai tabata sai mura ,idonta tar akansa shima din ita yake kallo ga mmkinsa sai yaga kamannin sa sak na rufaida ya haɗe rai tareda binta da harara ta mike xaune da sauri haka tana tsallenta na yara tana kokarin cire Pampers din dake like daita ,,ganin yyi ta fisge pampers din wani irin wari ya ziyarci hancin Ahmad da sauri ya rufe hancinsa gamida jada baya da sauri yah amad cicina kemin ciwo janyi kashi.
Xata wurgar da pampers din a kasa sai a fuskar Ahmad wani irin ihu na ban mamaki ya saka Wanda ni (Asmy ) a tsorace naja gefe
Ihu Ahmad yake kwarara wa tamkar Dan shekara bakwai ihun da ya raxana rufaida kenan itama ta fashe da kuka hayaniyar su ya jawo hankalin ya'n gidan duka ,,har lokacin Abba basheer na gida Dan shi ya dauko Ahmad da khaleel daga school. "
Khaleel ne ya fara shigowa a rikice yana fadin yah Ahmad lpi......baikarasa ba ya hango rufaida dame-dame da kashi ga kuma fuskar yah Ahmad itama da kashi lokacin shi khaleel bbu ma uniform a jikinsa farar singlet ce da guntun wando sabanin Ahmad dake cikin kayan makaranta ..
Dariya keson xowa khaleel amma sai yyi saurin maidata Dan yasan halin yah Ahmad yana iya masa bugun mutuwa..dai-dai nan Abba ,amma suka karaso dakuma Aunty balki ..
Suma din tsuru-tsuru sukayi ,,sabanin Amma datayi gurin rufaida takamo ta. Abba basheer ke tambayar Ahmad ya akayi idonsa a rufe ya nufi toilet,khaleel ne ya taimaka masa amma a hkan sai xagin khaleel yake yana ta zabga masa ruwa akai inbaya iyawa yyi tafiyansa.
A hkaa ya samu ya wanke fuskarsa ya fito a fusace nan ya tarar da Abba yana jiransa da kuma aunty balki amarya "wani kallon rainin hankali yashiga aika mata dashi ,ni kifitar min a daki mallama!!
Yyi mganar a fusace sum-sum ta wuce Abba basheer yabisa da wata uwar harara.
Waye sa'anka anan?" Abba basheer ya fada cikin fushi sunkuyar da Kansa yyi tamkar xaiyi kuka ya fadawa Abba komai,sae kuma Abba yaji tausayin dan nasa,musamman hasarar da rufaida ta masa Dan yasan son da Ahmad keyiwa laptop din."
Dan ranar da yah moha ya zomasu dashi daga Russia inda yake karatu shida khaleel kowa daya-daya ranar Ahmad yini yyi akanta a rayuwar Ahmad kuwa yana balain son ,laptop.
Yah isa!!
Xan canja maka wani kira Johseef "ya gyara maka dakin yana gama fadin hka ya juya yabar dakin .
Shima Ahmad da sauri ya cire kayan jikinsa, ya nufi dakin Amma a fusace....
Yana tura kofar dakin ga mamaki ya hango rufaida zaune akan sofa tana shan chaculate abinta wandda xuwa lokacin anyi mata wanka .an canja mata kaya xuwa wata gown ta yara marar hannu mai shegen kyau".mai manyan flower's haka itama red ce."sai uban gashinta da akayi mata parking dinsa da ribbom red koshi da kyar sabida tsabar yawansa da sartsinsa.
Rufaida jin tayi anja kunnenta da karfin tsiya .wani ihun axaba tasaka Amma dake a toilet da sauri tafito Ahmad baikula da Amma ba ya kalli rufaida ,a fusace Dan uwarki
Idan nakara ganin kafarki a dakina ko a kofar dakina ,sai na maki illar gaske."
Nice nan ,uwartata nagode da xagin." A tsorace ya saki kunnen rufaida gamida jada bayam
Ehhhh lallae Ahmad wuyanka yyi kwari zagin da mutane kesha a gurinka yau takawo har dani."to maxa ficemin a daki kafin nayi maka rashin mutunci haka kuma daga yau kafita a harkar rufaidah ."
Ganin yadda ran Amma ya baci yasa yabar dakin a fusace..
*
Alh.Aliyu karaye yana xaune a garin Kaduna acan yake aikinsa na banki.yyi aurensa da wata cikakkiyar kanuri hajia zulaihart wanda Allah yabasu albarkar haihuwa a tsakanin su ya'r su ta farko raudah wandda daga raudha basu kara samun y'a macce ba duka maxane kanninta Dan haka suka dauki son dunia suka axa mata ,,hka sun sangartata sosai masu bima raudha twins ne maxa sageer da sadam saimai bima su Muhammad basheer wandda suke kira jeniour tun raudha nada shekara biyu a dunia Allah ya daurama Ahmad kaunar yarinyar ,,Dan hka bbu wuya yaje Kaduna haka jininsu yyi balain haduwa daita ...
Haka xai riqa Tara kudinsa na break yana sayawa raudha kayan wasa ,,a haka raudha tata so Ahmad na kula daita Dan haka duka zuri'ar su sunsan irin tsananin shakuwar dake tsakanin raudha ,dakuma Ahmad a bangaren Ahmad kuwa shi yana nuna mata sone kawae na ya'n uwantaka. haka din Dan yagansu ((DANGIN JUNA NE))...Dan hasalima shi a lokacin baisan wani Abu soyayya ba."raudha kusan sa'annin junane itada hanan hka halinsu yaxo daya, rawar kai da shegen kicififin tsiya."
Ahamd na xana jarabawar N&W.nasa yyinda aka hada masa da jamb."ba da jimawa ba result ya fito "inda yasamu good result kasancewar Ahmad mutunen mai kokarin gaske ,haka bayason mutum marar son karatu fannin Arab&boko."
Da haka mahaifinsa ya shirya masa tafia xuwa new York" Dan yin degree sa na farko a lokacin yana da shekara goma sha takwas a dunia"inda xai karantar (Architecture) "wato ilimin zane-zanen gini."
Haka yyi bankwana da mutanen Nigeria ya daga new York"...
Shekarar sa biyu acan ya dawo Hutu gida wandda a gidan daddy na Kaduna ya sauka Dan kawae yanaso yaga raudhan sa da irin girman da tayi kasancewar raudha akwae girman jiki"yanxu xata tafi j.s.s.one lokacin baxata fi shekara goma shabiyu ba a dunia anan mami kesanar masa yyima ya'r lelan tasa fada Dan batason karatu nan ta dauko masa school bag nata anan ya dinga cin karo.da manya-manyan zero da raudha kesamu"...
Haka yaga position nata gurin na ashirin tasamu Dan su talatin ne a class nasu.
Sosai Ahmad ya bata ransa haka ya nuna mata baiji ddiba." Zuciya ma yayi yabar Kaduna ya nufi kano ko tsarabar da yayo mata trolley daya na body hook ,English West ,da skull bags na makarnta da shoes masu shegen kyau" wucewa yyi da abinsa.".
Haka raudha ta rika ihu tana kuka akan mami takira buddy "wato (friend) tabasa hakuri Dan sunan da take kiransa dashi kenan har sunan yabi sa." Dan gabadai kakaf kannensa haka suke kiransa dashi tun..
Tun daga ranar raudha ta daina wasa karatu kurum takeyi."wandda koda Ahmad ya karasa hutunsa ta kano ya koma" baije yayiwa raudha ban kwana ba."
Ya kama ranar lahadi misalin karfe goma sha daya na safe sun gama break fast duka yaran gidan sunyi wanka "xasuje gidan kitso ,sabida gobe Monday.
Rufaidah da raudha bakar jallabiyya ce ajikinsu sai mayafinta baki da sukayi rolling din Kansu dashi.
Sabanin hanan da mamu da suke sanye cikin English west " kasancewar hanan girma ya fara xomata hijab tanema ta saka shima dai karamine mamu kuma karamin gyalen doguwar riga ta saka akanta .
Ahamd dake xaune a main falo din ammah yana break fast " saiga Abba ya shigo falon kai ahamd kagama break fast kaje ka sauke yaran nan a zoo road." Gidan kitso."
Abba hanyar Kaduna xan kama yanxu." Auhhhh xuwa kadunan ne xai hanaka kakai su gidan kitso"..Abba ya karasa mganar a fusace shikenan karka kaisu" din kaji marar kunya!
Bbu abunda ahamd ya tsana a rayuwarsa irin fadan Abba basheer fadansa yana balain gigitasa 'shida wannan fadan gara ya rufesa da duka."
Kayi hkuri Abba "yafada a ladafce."
Car key ya dauka yyi waje."
Assha ce kefamar kwalawa rufaida kira ....rufaida! Kifito da sauri "buddy ne xai kaimu.
Rufaida ce karshen fitowa Ahmad sai famar binta yake da mugun kallo" Dan uwarki!
Ni sa'anki ne?"
Kayi hakuri buddy "tayi mganar cikin sanyi muryarta da karfi Ahmad yaja mota haka yaran kowa ya kama kansa a mota zaman kurame sukeyi " Dan sun San halin yayan nasu motsi kadan xaisa ya hau mutum da masifa har suka kai ko dogon motsi yana ajesu yaba kowace 5 hundred na kitso"..godia sukayi yaja mota .....
Da yamma kuma khaleel ne yaxo daukarsu da yake yagama secondary school "yana shirye shiryen xuwa malesia."..
*
Ya'n Kaduna sai murnar xuwan buddy suke musamman raudha da ya dagata sama yana xagaye falon daita ..sai kyalkyalar daria take abinta suna xaune yana lunch ya kalli raudha.". Wai raudhata me mami ke baki haka?" Irin wannan kibar daria raudha tayi kajika dai buddy .ta fada a shagwabe gamida turo bakinta.
Dai-dainan daddy ya shigo falon da alamar fita xaiyi ya kalli Ahamd yana fadin kaga mutunniyar taka nan wai baxata je boarding skull ba."
Ahamd ya kalli raudha "cike da mmki ehhhh my raudha yaushe xaki girma ne?" Yanxu fah s.s. one xakije shekara goma sha biyar ba wasaba.!
Ni buddy ba hka ba fah."wai daddy f.g.c.gusau xai kaini ni nafison yabarni a Kaduna kusa dasu."tunda ga queen ameena "
Dan Allah buddy kama daddy magana plzzzzzzz ta fada a shagwabe Ahamd ya langabar da kansa yana kallon daddy Dan Allah daddy kabarmu A Queen Ameena."
Daddy ya hararesa batareda yace komai ba."ya nufi bakin kofa gobe xan turo maka kudi a Account dinka kayi hakuri bbu yawa."tunda kace gobe xaka koma ,nagode daddy Allah ya qara budi ameen Allah ya kiyaye hanya ban da wrong driving.
Buddy dama ba anan zaka kwana ba?" Tayi mganar a shagwabe to yana iya my raudha gobe zan koma new York.
Yanxu kuma sai yaushe?"
Ohhhh raudha ko Dan jarida albarka ."sai kingama secondary school ta tabe bakinta kadan ai bbu yawa..........xuwa la'asar yyi sallama dasu ya kama hanyar komawa kano..
***********
"Ohhhh rufaidah ina kuma eyeglasses naki " cewar khaleel dake rike da car key a hannunsa da alamr school xaikai yara."
Yah khaleel bana son eyeglasses din nan ya'n class namu suyi tamin daria suna tsokana na .waini makauniya ce.
Ohhhhhh rufaida dear!!
To zaki iya gani bbu eyeglasses ki kyalesu duk mai maki daria ,xaiyi ya barine.
Idan naxama dector xan gyara maki idonki tayarda bbu ke bbu saka eyeglasses "wangale bakinta tayi cike da murna ..shigowar Ahmad ya katsesu yana sanye cikin farin yadin captani Riga da wando .Ya kalli khaleel mln kana batamin lokaci ko baxaka kaini air port ba?"
Buddy xan aje yara a school sai na dawo nakai ka.". Ina drivern su ne?"
Yyi tafiya ya'r karamar tsuka yaja batareda ya koma kallonsa ba ya nufi part din ammah."
Yana jin rufaida na fadin "yah khaleel yau buddy xai koma ne?" Baiji mai khaleel din yace ba.ya nufi bedroom din ammah.
#Dangin Juna
#Ahmad Bashir
#Rufaida
#Raudah
#love/Romantic
#Asmy b Aliyu