Dangin juna

3

by @asmybaliyu

DANGIN JUNA

Asmy b Aliyu

3..

10Years leap....

Moha ne ya shigo dauke da rufaida wacce numfashi da kyar yake fitar mata sabida axabar tsananin ciwon marar dake adabbar ta.

Amma ce ya tarar a falo fuskarta dauke da damuwa.

kwantar daita yyi akan tree star yana share xufan dake keto masa ,da farin hankicif.

Amma wannan ciwon na rufaida ya wuce tunanin ki"...ciwon nan na Mara har sumar da ita yake fah."

Principle din makarantar su tasa aka dawo daita nan gidan daddy na Kaduna ,kwanan ta biyu bbuci bbu sha " shiyasa Abba yace yau naje na dauko masa ita."

Dan haka ma yace karna sanar maki" tom Allah ya kyauta makanrantarta fah?"Amma tayi maganar fuska dauke da damuwa." sai tasamu sauqi saita koma tunda sun sani ,,,nidan haka bason bording school din nan nake ba."

Dan banxan yaron nan Ahamd yayi cuku-cuka yasa aka kaisu Allah kawae ne yasan irin wahalar da suke sha idan suna ciwo."

Shidai moha baice uffan ba ,dan yasan Amma idan tafara korafi bbu sassautawa "saima hannunsa da yasa ya dauki rufaida xuwa bedroom din Amma haka yana mamakin rashin kibar rufaida ,,a haka ma assha tafita kiba" da mamu ,duk da kasancewar sun fara girma shekara goma sha shidda sai uban tsawo."

Allura moha ya hada yyi mata kasancewar sa babban likita.

Yanxu yaushe allurar xai saketa?"Amma ta tambaya dauke da matsanaciyar damuwa."

Nan da ya'n wasu a wanni."nixan tafi na watsa ruwa.

Anan yasa kai ya fita.

Amma ta maida hankalinta kan rufaida wacce take barci abunta ,,sai dai ta rame tayi wani haske .Addu'a Amma ke tofa mata ,,aranta tana addu'ar Allah ya dauke mata wannan ciwon marar ta huta Dan bakaramin axabtar daita yakeyi ba.

*

saukarsa kenan A kasar ta Ghana yana sanye cikin kananan kaya da jibgegiyar rigar sanyi ruwan anta.

Kai tsaye hotel yaje yyi booking kafin ya isa makarantar su raudha " Dan rabon sa daita shekara daya kenan tunda tagama secondary school baya ma kasar tawuce karo karatu a Ghana sai dai yaji lbr." Wandda a xahirin Gaskiyya baiji ddin xuwan sahibar tasa xuwa wata kasa karo karatu ba."

Yaso ace ta tsaya Nigeria kasancewar Ahmad mutun ne mai shegen kishi mussaman akan abunda yakeso.

Dan sun fara soyayya da raudha ,tun tana ss2 wandda ita tafara nuna masa zallar so".

saida ta wahala kafin tasamu soyayyar Buddy din nata."

Ga raudha da shegen iyayi da nuna ita wace kusa duka ya'n group nasu way'ndda suka gama queen ameena a tare kasar ghana ,suka nemi admission.. su ukku ne kacal a group dinsu daga raudha din sai friends dinta biyu duka diyan manyya ne.

Zaheeda dai a Abuja take suhaila suke gari daya, tare da raudha "kusan friends din nata sun San soyayyar dake tsakanin Ahamd da raudha.

Amma ko a ghanar ba wani karatun kirki sukeyi ba"kullum suna cikin xuwa club da party...

Abba basheer yaji xafin abunda daddy yyi na tura raudha wata, kasa karatu tana matsayin ya'h macce abunda hanan ta so kenan ayi mata.

Abba yace Sam baxai yuyuba".. Intana tsayawa b.u.k.tayi karatu tayi idan baxata tsayaba, tafiatar da miji yyi mata aure..

Aunty balki taji xafin abunda Abba basheer yyi sai dai bbu yarda suka iya sunsan abban kaifi dayane."

Abba shikuma akwae abunda ya shirya Dan acewarsa raudha baxata yi shekara biyu a Ghana ba."

Xata tattaro ta dawo Nigeria inyaso ayi aurenta da ahamd sai taci gaba da karatun ta a dakinta."

yasan Ahmad ko giyar wake yasha baxai bari raudha taci gaba da karatu a Ghana ba."

Dan haka Abba ya yanke shawarar shida mama Aysha akan ahamd yaje yaxo da raudha "..

basuyi shawara da kanin nasu ba." Dan sun San mahaukacin son da yake, ma ya'rtasa.

xa'a hade bikinsa ne da Muhammad wata mai xuwa shima Ahmad tuni yagama karatunsa yasamu aiki anan garin Kaduna a wani babban company .

#

Hey guys!!" Ku sassauta murya buddy na kirana a wya tace da friends nata . da kuma wani sabon friend da tayi waishi saleem.

Suna xaune a wani club suna sheke ayar su.

Hello buddy dama kuma bai faɗamata xaixo ba."

Wat!!

Ta fada gamida kwalalo idonta waje,, tashiga ukku buddy na a kasar nan jikinta nan take yakama bari sabida tsananin tsoro.

Kinyi shiru babyna" ko bakiji ddin xuwana ba "cikin rawar murya take fadin " nop buddy kawae dai nayi mmki ne, shine kaki kirana ka shaidamin, ta karasa maganar a shagwabe.

Ni gani nan ma hotel ,xuwa anjima xan shigo...da sauri tace no buddy katuro min adress din hotel din xan zo"

Da mamaki Ahamd yace meyasa?

Ni buddy bana son kaxo ya'n mata suyi ta kallamin kai "takarasa a shagwabe,,murmushi Ahmad yyi Dan yasan gimbiyar tasa da kishi bbu sauqi.

ita kuma tana da dalilin yin hka Dan tayi wani sabon boy friend

mai kashe mata kudi matashi wandda baxai wuce shekara 25 ba a dunia" shima school din su daya dashi

Ameer shegen kishi yake dashi bayason yaga kowa ya rabi raudha asalinsa s Dan zamfara gusau ne shima karatu yakawo sa Ghana"

yana gaban raudha da shekara daya.

*

Wanka yyi ya kwanta ya huta misalin karfe biyar dai-dai na yamma kamar yarda agogon kasar Ghana ya nuna lokacin ahamd na xaune a gefen bed yana wya yana sanye cikin body hook na shan iska" yana wya da yah moha haka hankalinsa na jikin kofa .

yana mmkin meya hana raudha xuwa har wannan lokacin..

Knocking din kofa yaji a hankali ,,nan yyi sallama da yah moha yaje ya bude kofar matashiya ce ya'r kimanin shekara ashirin adunia kananan kayane ajikinta ,,Riga da wando wandda bakaramin kamata sukayi ba

Kallonta kurum yake ko mayafi bbu asaman kanta sai bakin Veil, din da ta daure kanta dashi..

Ta kara girma ta kara cika yanayin shigarta da ya gani yasa yyi balain bata rai tamkar ba musulma ba."

Wani irin kishi yaji ya lullubesa.

Itakam da gudu taje ta fada akan fadeden kirjinsa tayi hugging nasa sosae.

Baya-baya yyi ransa a bace ya buga kofar gamida Dan tureta ajikinsa yana binta da mugun kallo.

Sosae jikinta yyi sanyi kan bed ya koma ya xauna a fusace ya fara mgana "raudha meye hka?" Dama irin wannan rayuwar kikeyi a kasar ta Ghana?"

Sai kace ba diyar musulma ba?" Hawaye raudha ta fara yi shar -shar idan akwae abunda ta tsana bai wuce fadan buddy ba."

Cikin kuka take fadin to menayi buddy daga xuwanka ka hauni da masifa meye aibun wannan shigar saboda Allah?"

Wani matsiyacin Kallo ya jefa mata "waton ma tambayar aibun shigar da tayi takeyi."

Xaunawa tayi akan cinyarsa tana shafa kyakkyawar fuskarsa haka taci gaba da kukan kissa."

Nan take Ahmad yaji hankalinsa ya tashi , raudha meye hka?"

Kinfa girma janyeta yyi daga jikinsa,,,....

Raudha !!

Ya kira sunan ta cikin sanyi muryarsa ,,farin hankicif ya mika mata ta amsa ta goge hawayenta.

"Dan na nuna kishi akan shigar da kikeyi shine xaki fasamin kuka" shin bakyaso nane ,yanxu da Sauri ta girgixa kai "to meyasa kike irin wannan shigar bancin kinsan tsananin kishin da nake maki.

" kayi hkuri buddy na daina ta fada a yangace.

Ya school?"

Ya tambaya yana kallonta

Alhmdulillahi."

Gobe ma xaki Bini Nigeria ansaka date din auren mu!

"Raudha jin mganar tayi tamkar saukar runduna" sabida tsananin rudewa buddy aure yanxu da kurciyata haba mana!

Tayi mganar cike da bacin rai haka tayi folding din hnnunta akan kirjinta.

Da mugun mmki Ahmad ke kallonta."

#Dangin Juna

#Ahmad Bashir

#Raudha

#Asmy b Aliyu