PG 1
by @khadybabeey
PG1
Dam! dam!! dam!!! ƙaran buga tebur in da akayi ne ya sa ajin ya yi shiru daga surutun da ake a cikin ajin.
Miƙewa mu kayi dan mu gaisar da malamin da ya shigo cikin ajin, tare da wani ƙyaƙyawan saurayi wakan tarwaɗa mai sufar fulani saboda yan da gashin kansa ya kwanta har wuyansa, sanan ga fararan tabarun da ya ɗaura hancinsa dogo kaman kara, wan da ya yi daidai tsakanin dara daran idanunsa motsa ƙaramin bakinsa ya yi.
" Morning students have your sit, sannan ina farin cikin sanar da ku cewa kunyi sabon ɗan uwa, ina fatan zaku zauna lafiya."
" Insha Allah sir."
" Yuwa Masha Allah, kai monitor ka rubuta sunan sa a register, sannan kai kuma ka zuna a gaba kafin malamin da kai kula da wannan ajin yazo ya baka sit kaji ko."
Kaɗa kansa ya yi alaman ya ji sannan ya zuna a in da principal in mu ya nuna mishi, sannan shi kuma malamin ya fita daga ajin.
Principal na fita, ajin ya ɗauki surutun ƙanaun maganganu, kuma duk akan sabon zuwan ne, nikam cigaba da karatun Al-Qur'ani na na yi, saboda ina da hadda gashi kuma ran alhamis zan bayar da shafi goma kuma ko daya ban haddace ba.
Kaman yan da principal ya faɗa Mrs joy na shigowa ta bashi sit second to the last sit, wan da shi ne sit in gaban mu da ya ke, makarantan mix ne wato muslim da christan sannan da kabilu daban-daban.
" Ya sunan ka?." Mrs joy ta tambaye shi cikin harshen turanci.
" Ashfar Yazeed."
" Ok nice to meet you, sannan barka da zuwa Deligent College."
" Yauwa nagode sosai." Ya faɗa a sanda ya ke zama a sit in da aka bashi, sannan aka shiga karatu da yake subject dinta ne, kuma daga shi sai lokacin sallah wan da ake yi ƙarfe biyu.
" Don Allah zan iya bari jaka nan na bisu muyi sallah." Muryansa ne cikin harshen turanci naji ya mun amsakuwa a kunnuwana, dan haka da sauri na ɗago na kale shi cikin mamaki, kafin nayi magana Nabila ta yi saurin cewa.
" Kawo na riƙe maka tun da kaga ita tana karatu."
" To nagode." Ya faɗa sanan ya Miƙa mata jakan ya fita daga ajin, tare da su yazeed dan zuwa sallah.
Ihu suka saki cikin shewa da murna kan cewa sune mutane na farko da suka fara magana da shi, yabyin da ni kuma mamakin magana da ya yi ne ya tsaya mun a rai, amma kuma sai na wasar saboda na san dole sai ya yi mu'amala da dan ajin.
To bayan sun dawo sallah Nabila ta bashi jakan sa, sai ya koma cen gefe ya zauna ya yi shiru yabna kallon yan da ake ta hira, da ya ke yau laraba ne ɗalibai basu tafiya gida sai ƙarfe biyu, kuma nima ina daya daga cikin su.
Yazeed ne da abokansa tare da sauran Mazan ajin mu, har da ma matan suka fara gabatar da kansu a wurin sa, sanan Yazeed ya ɗaura da cewa.
" Muna maka barka da zuwa Deligent College class of rising aka SS 3 science."
" Ok thanks and nice to meet you to." Ya yi reply da murmushi akan fuskarsa.
Bell in da aka buga ne ya katsai hiran da ake, sai aka shiga club, sai ƙarfe 4 aka buga Bell gaba ɗaya aka tafi gida.
Muna tafiya a hankali yazo hucewa nan ma sai da su precious suka nuna haukan su, nikam babu a bun da ya shafe ni na kama kaina nayi gidanmu, a raina ina jinjina yan da ƴan ajin mu suke yi musaman ma matan, kawai daga rana ɗaya da suka fara ganin sa...