ANA BARIN HALAK

PG 3

by @khadybabeey

PG3

“ Good morning class."

“Morning sir"

“ Yau za mu yi karatu a kan homeostasis( homeostaza), wan da aka same shi daga kalmomi guda biyu, na farko shi ne helenanci homosis ma'ana daidai, sai kuma stasis wan da ya ke nufi dindindin.

Homeostaza ya na nufi yan da za'a kula da gabobin jiki na ciki. gabobi kaman su jini da duk wa ni cells da ya ke jikin ɗan adam.

Gabobin jiki wan da suke alakanci da homeostaza sune, ƙoda, ƙwaƙwalwa, hanta da fata da dai duk wa ni abu da ake aiki a cikin jikin ɗan adam, koda na..."

Gillin, Gillin Gillin.

" Period ina ne ya ƙare?"

" Eh"

" To ba matsala zamu tsaya a nan, amma kafin nan ga aikin gida, kowa yaje ya yi research individually akan gabobin jiki da suke alakanci da homeostaza, kuma kuyi takaitatcen rubutu akan sa, za kuyi present a ajin mu na gaba kuma 20mrks."

" To malam." Muka amsa sanman ya fita daga ajin.

" Uhmmm gaskiya malamin nan ya iya koyarwa sosai fa, na fahimci duk a bun da ya koyar."

" Uhmmm wallahi Kursum ban fahimci komai ba."

" Gaskiya Nabila baki kyautawa kanki ba dai, na biye su kuna hauka a aji dan Allah me amfani rashin mayar da hankali malami na koyarwa."

" Kai dan Allah ba na son maganar banza harkan ki da ban nawa da ban."

" To shi ke nan sai ki ta yi."

" Uhmmm kanki ake ji."

" Yanzu lokacin sallah ne ko??"

" Eh yayanmu"

" Ok kuma Kursum yanzu za ki tafi Ko?"

" Eh yanzu"

" To ba laifi bari in je in yi sallah ga jaka na Nabila."

" To sai ka dawo." Ya kaɗa kai sannan ya fita daga ajin ya yi ƙasa, da ya ke muna sama ne hawa na farko.

Nima tashi na yi na tattare littafina na yi hanyar gida.

Washe gari da nazo makarantan sam sam ban gane kan ajin ba, saboda duk an yi group ana ta jayeya nikam ban bi takan su ba na samu wuri na zauna na zuba wa sarautan Allah ido? a rai ina jiran isowan Nabila saboda no matter how ta na da masaniya akan me suke magana akai. ILaiye kuwa sai gata ta shigo, ajiye jakan ta kawai ta yi a sit in mu sanman ta yi joining in su suka cigaba da mu'awaran sai da akayi ringing bell alamun fara karatu sannan ta dawo, sit ta zauna nan ma sun cigaba ne da sauran ɗalibai, ban iya jure tambaya na ba na ce mata. " Wai ni Nabila me ke faruwa a ajin nan?.”

“ Uhmmm ke dai Ƙawata bari, wallahi jiya ne fa bayan tafiyan ki an dawo daga sallah Yazeed da Yasir suka ci dambe."

“ Subhanallahi dambe kuma me ya had’a su?"

“ Kin san dukan su suna son salima Ko?"

“ Eh na sani."

“ To ashe wai jiyan da aka je sallah a wurin alwala, sai Yasir yazo ya na mata magana a lokacin da shi Yazeed in kai mata magana, to shi ne fa a bun da ya kawo faɗan. Kuma sanadiyar hakan aka yi cancelling competition in football da za'ayi kwanan nan."

" To fa har abun ya kai haka?"

" Wallahi kuwa"

" Wallahi Nabila bazan iya soyayya da ban ajin mu ba, na gama hauka na a gaban ka, kuma ka zo kuma kace kana sona na yarda."

" Kai ki kai gani haka Kursum, wallahi nikam zan yarda musamam idan kana da ƴaƴan banki wallahi."

" Wallahi nikam bazan taɓa yi ba wannan hauka ne."

" To kai ki ke gani haka wallahi, Uhmmm wallahi Kursum kar muzo tambayane baki fa."

" Allah ya tsari gatari da saran suka, hanyar jirgi daban na mota daban."

" Sai da first double period ya ƙare, Ashraf da waɗansu ɗan ajin mu suka shigo aji suma suna dan maganganu tsakanin su."

“ Yayanmu me ya faru kayi missing class?"

“ Wallahi munje mun roki mr Ayomide akan cancelling sports in da ya yi da kuma suspending in su da ya yi."

“ To yanzu ya kuka yi?"

“ To ya yarda za'ayi competition kuma ya janye suspension in, amma on one condition."

“ Na me ke nan??"

“ Zamu je competition in, amma Idan bamu ci ba zasu tafi suspension na sati uku, wan da zai shafe academic in su saboda kun san duka satin muna da pratical wan da za'a haɗa da exams in mu, ayi wa waec submitting."

Shiru mu kayi cikin zulumi yiwan hakan, dan a competition dole akwai winner akwai losser.

" Yayanmu Allah ya bawa mai rabo sa'a."

“ Amin…