ANA BARIN HALAK

PG 7

by @khadybabeey

PG7

Washe gari bayan mun shigo makaranta gaba na sai faɗuwa ya ke zulumi da tashin hankali duk ya cika ni duk da an ban labari da ga ma jiya me ƙarfi cewan ba a yi faɗan ba, saboda Technical drawing teacher ya hana su amma kuma yau bai zo makarantan ba kuma hakan ya da me ni sosai wan da ko fara'an kirki na gagara yi.

" Wai Kursum ina mai gidan ki?."

" Waye kenan??"

" Ashraf mana."

" Uhmmm wallahi ni na ce ya kwanta yau ya huta saboda jiya da ciwon kai ya kwana saboda kaceniyar ku na jiya."

" Eyya lalle kam wife material ke man, gaskiya kinyi ƙoƙari. Amma fa ni banci goron daurin auren ba kuma ban sheda ba."

" To ai sai ka siyo sweet da goro ka sake dauran auren."

" Amma kursum......"

" Usman ai a inda ba kasa a ke gardaman kokuwa ko. Kursum za'a siya goro da sweet a raba sannan a sake ɗaura aure da kyau in da za a samu cikakkum shedu."

" Uhmmm iska na wahalar da me kayan kara wallahi, kuma koda kun siyo goro da sweet ai sai an biya sadaki ko?."

" Eh ba komai ni zan biya dama yau na amsa adashi na 3k sai in biya sadakin." Dariya na fashe dashi sanan na ce. " Kuje ku ɗaura wallahi ku ban sadakin na cin ye a banza ne wallahi."

" Haka ki ka ce??"

" Eh haka na ce."

" To shi ke nan."

Fita su kayi waje ya yin da ni kuma na fitar da iska me zafi cikin hushin surutun bazan da suka cika ni da shi abbun da ya dame ni ma ya dame ni. Sosai kai na ke ciwo ya yin da wani zazzabi ki neman ya suƙa min.

Usman, Jabir, Yazeed, kamal tare da wasu ƴan ajin suka shigo da ihu suna wakan an daura"

An daura ,an daura ta zamo matan Ashraf Allah ta gode ma, amma fa gaskiya kun ɗace sosai.

" Amarya ga sadakin ki."

Miƙewa na yi zan tafi gida da ya ke an yi ringing bell.

" Kin rantse za ki amsa sadakin fa."

Fizgewa na yi na fita daga ajin rai na a ɓaci na shusa kudin cikin jaka na da niyar Allah ya kai mu gobe zan karta musu rashin mutumci dan naga rashin hankalin su ya yi yawa.