ANA BARIN HALAK

PG 12

by @khadybabeey

PG12

“ Duk da ban ga me ke cikin litafin ba amma na san cewa kuma ina da tabbaci babu amsan, abunda ki ke zargi a zuciyar ki, dan zaki iya hakuri da dik tarin tambayoyin ki to ki zo muje inda zaki samu amsan ki.” Kallan matan kawu Jabiru nayi a sanyaye, sanan na miƙa na ɗauko mayafina na fita waje inda kawu Jabiru shi ma yake jingine da motan sa.

Mitin talatin ta fito sanan ta ce. " Riƙe Ma'arof in ja motan, da ba lalle ka gane wurin ba."

Ba musu ya miƙa mata makulin, sannan muka shiga muka hau hanya kowa zuciyar sa cike da sake sake.

Hanya cike da rame kwata ramin bololi ya yin da duk in da ka gefta idan kai me ƙyanƙyani ne ko miyo ba zaka iya haɗewa ba.

Parking mu ka yi, sannan muka sauƙa daga motan, muka fara takawa da ƙafa, sai da muka ƙara ƙare wa wurin kallo. Mun dan yi tafiya me tsawo sannan muka tsaya a wani ke bantatacen wurin wan da aka yi miki katanga da itace turawa, sannan muka shiga bakin mu ɗauke da sallama.

Wata mata ne zaune a wani rumfa cen gefe da ƙofan ɗakin da ke kallon ƙofan. Bata amsa ba sai de bin mu da kallo da take, sai kuma cen ta fara kuka tana cewa. " Gidaɗo Gidaɗo yunwa, yunwa Gabd'o."

Bread in da muka siya a hanya Aunty Salama ta ɗauko a mota tun sanda zamu saƙo, budewa ta yi ta cire shi gaba daya a ledan sa sannan ta mika mata. Fizge bread in tayi sannan ta fara ci.

" Shin kun san dalilin da har yanzu ƙasar mu ta kasa cigaba? Shin kun san dalilin da ya wai tan yan ta'adda su kayi waya a ƙasar mu? Shin kun san dalilin da karuwai su kayi yawa ya yin da ƴaƴan shegu suka yawaita?. duk na san amsa ɗaya zaku bani rashin aiki da samari basu da shi da wan da akai gani gwamnati da lefi, kuma rashin wadatan zuciya ko? Ba ma wannan ba dan ba zan baku amsan ba, ku da kan ku zaku bawa kanku amsa, amma kafin nan a tunani ku me zaku iya cewa akan wannan baiwar Allah? Tana da cutar tabin hankali amma kuma bata yawo kwararo kwararo sannan tana samun kulawa, To a ganin ku wa zai kula da ita? Allah a'alamun."

“ Haka ne to, ƙarfe nawa yanzu?"

“ Biyar da minti hamsin da shida."

“ Nan da miti shida wan da ke kula da ita zai shigo.”

“ Shiru mu kayi muka zuba wa ƙofa idanun dan ganin wa zai shigo.”

Sallama ya yi sannan ya tura ƙofan ya shigo hannun sa riƙe da leda. Dukan mu mun daskare da ganin juna.

Juyawa ya yi da zum'mar komawa sai ta ce. “ Gidaɗo tsaya nu fuskanci juna lokacin ya yi da za’a daina sanar mun akan da ba namu ba. Akan kaddaran da Allah ya hukunta mana…