ANA BARIN HALAK

PG 16

by @khadybabeey

PG 16

Washe gari

Gari duk ya dauki ƙirƙirar labari ce wa wae an kama Yazeed da lefin kashe iyalin sa saboda ya na safaran sassan jikin ɗan adam wan da tun kafin a yan ke masa hukunci zuciyar sa ya duga.

"To sanadiyar haka kuma Mansura ta haukace. Ashraf ne kawe wan da ya yi saura.

Sanan a dukan ɗangi babu wan da ya taimaka mu su da wurin zama a cewan su ba zasu iya zama da mahukaciya ba to a ɗaya daga cikin yayun ta ne ya siya musu wannan gidan da suke ciki."

Komawa zuwa yanzu.

Aunty salam ne ta bi kowa da kallo sannan ta ce"

"Dukkan labarin da na baku na san shi ne a gurin mahifina malam Salihu.

Sanadiyar haka Ashraf ya shiga mugun sana'a na siyar da giya a nightclub saboda ya dinga kula da mahifiyar sa musamman wurin lafiyan ta.

Na tabbata ranar da ku ka gan sa ya na tafiya a duge mistakely ne ya sha amma wannan ba ɗabi'an sa bane.

A hankali kursum ta ce"

"Amma Aunty an ce Ashraf ya yi hatsari ya na emergency. "

"Eh tabbas ya yi hatsari amma ya na farkawa ya bar asibitin saboda mahifiyar sa idan ki ka duba da kayu da san da ya ke tafiya."

Kursum ne ta tashi ta je gaban Ashraf ta ɗurkusa.

Idanuwansa ya cenza kalla ya kuma jan launi sosai.

"Ashraf......"

Hawayen da suka maƙale a idanuwan sa ne suka zubo.

Ita ma hawayen take. Cikin kukan tace"

"Ashraf zan zauna da kai a ko wani irin hali ka ke ciki amma zaka iya ciyar da iyalin ka da haram??.

Me ya sa ba ka yi min bayani ba??

Ka lulube min gaskiyan halin da ka ke ciki??."

"Kursum tsoro ne."

"Wallahi kursum ina tsoron rasa ki saboda ina matukar ƙaunan ki.

Na rasa yan da zan yi ne, na......."

Kuka ne ya ci ƙarfen sa ya ha na she magana.

Tashi ta yi daga gaban sa sanan ta je gaban Baba Jabir."

"Baba ina so aure na dan Allah kar ku kashe min aure na.

A jiyan zuciya Babba Jabir ya sake sannan ya ce."

"Wallahi kursum ko baki ce ba ni ma niyya na ke nan amma Ashraf ta fika gaskiya dole ka cenza sana'a. Zan baka jari sai ka fara wani sana'a."

"To baba na gode sosai."

"Ka je ka fara shiri nan da sati ɗaya zan a kawo maka matar ka.

Ku tashi mu tafi." Ya/na faɗan haka ya ta shi ya fita daga gidan.

Miƙewa su Kursum su suka yi suka mara masa baya.