ANA BARIN HALAK

PG 17

by @khadybabeey

PG 17

Ba ƙaramin gudu Baba Jabir ke yi akan titi ba.

Motan ya yi shiru ya yin da kowa ke saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa.

Kai tsaye kotu ya nufa ya yi parking bai ce musu kome ba ya fita daga cikin motan."

"Mu fito ne??"

Aunty Salma ta tambaye sa."

"Aa."

Ya amsa mata. Sannan ya fara tafiya

Tafiya ya ke sanu a hankali har ya bace wa ganin su.

Kai tsaye office in barrister Kamal ya nufa.

Zaune ya ke ya na duban wa su files da suke gaban sa."

"A engineer kai ne tafe??"

"Wallahi barrister ni ne a hanya."

"To masha Allah sanu da zuwa bismillah ga wuri zauna."

Zama Jabir ya yi a kujeran da ke fiskantan Kamal bayan ya fito da wayan sa ya kira matar sa."

"Hello Salma akwai key a jikin motan ki ja ku, ku tafi gida idan na gama a bun da naki yi zan taho."

Kashe wayan ya yi ya na kallon barrister Kamal wan da ya miko mishi kofin shayi."

"Ka san komai ya fi tafiya daidai idan da shi a kusa.

Murmushi ƙadan Jabir ya yi sannan ya amsa kofin shayin ya kai bakin sa ya zuka ƙadan sannan ya ce"

"Haka ne kam kuma an fi fahimta ba."

Dariya dukan su su ka yi a tare sannan Kamal ya ce"

"Eh Jabir wa'adin mu ya kusa cika ko?.

Ajiye kofin shayin Jabir ya yi akan tebur in bayan ya cire fararan tabarun idanuwansa ya ɗaura akan tebur in sannan ya ce"

"Haka ne dama a bun da ya kawo ni ke nan."

"Uhmmm yaron na da taurin kai ko.

Kar ku damu zan yi maganin sa."

"Kamal ina so a janye karan nan."

"Na'am me ka ce??"

"Eh ina so a janye."

"Me ya sa???

Shiru Jabri ya yi na dan mitina sannan ya baiwa barrister Kamal labarin Ashraf gaba ɗaya.

Shiru Kamal ya yi ya na tunani sannan cen ya ce"

"Gaskiya Jabir hukuncin da ka yanke ya yi daidai kuma haka ya kamata amma wani hanzari ba gudu ba ya za kayi da ƴan uwan ka da mahifiyar yariyan nan?

Ka san ba yan da alkali bai yi da su ba akan ayi sulhu tun da yaran sun nu na a fili suna son junan su amma suka ki kuma ka san cewa anyi haka ba so ɗaya ba ba so biyu ba a kayi haka ko?."

"Kamal na sa ni amma ana barin halak dan kunya ko?.

Wallahi Kamal a yanzu Ashraf ya fi buƙatan Kursum fiye da Salisu kuma wallahi Ashraf sai ya fi riƙon ta da amana da sanin darajan ta.

Iska Kamal ya fitar cikin hannayensa sannan ya ce"

"Tabbas Jabiru kana da gaskiya amma ka shriya fiskantan ko wani irin ƙalubale da tashin hankali dan wallahi akwai rigima ba ɗan ƙadan ba."

"Kamal wallahi komai zai faru ya faru amma wallahi sai Kursum ta zauna da Ashraf ai dama ni aka ba wa ragamar rayuwan ta duk da ni ne ƙaramin su amma suka ce ba za su iya kula da ita ba dan haka duk a bun da na yanki game da rayuwanta ya zaunu.

Sannan su fa auren dole suke so suyi mata ai tun ba yau ba na san cewa watan rigima na da su ya kusa kamawa dama lisafin su shi ne zasu aurar da ita wa ɗan iskan ɗan na su idan anyi magana suce wai akwai alkwari aure tsakanin su ko, to wallahi ba na ba zai yu ba."

"Uhmmmm to shi ke nan zan taya ka faɗan nan sannan ai muna da shaidan da zamu shigar da su kotu.

But mafiyar ta ba??."

'Mallami zan kai mata suyi mata wa'azi wallahi tun da naga alaman ta wannan hanyar ya kamata a bi da ita.'

Dariya Kamal ya fashe da shi sanan ya ce"

"A'a abun bai kai da haka ba akawai hanya ɗaya kuma shi ne warning zamuyi mu su dukan su akan a bun da suke shrin yi."

"Ta ya ya??"

"Alkali zamuyi wa magana ya yi mu su warning in.

Kaga ai dole su haƙura tun da alkali ne ya zartar da hukunci hakan ko."

"Gaskiya kuma kana da huja haka za'ayi."

"To shi ke nan ka bani nan da gobe insha Allah zan tsara komai."

"To abokina na gode sosai dan Allah ka yi ƙoƙari zauwa gode komai ya hadu saboda ina so nan da sati ɗaya na mika yarinyar nan ɗakin ta."

"Insha Allah engineer uban amarya."

Dariya Jabir ya yi sannan ya ce"

"To godiya na ke ni kam zan tafi."

"To engineer yau ba rakiya."

"Aa ba matasala zauna abun ka sai in Allah ya kai mu goden dai."

"To Allah ya kai mu."

"Ameen". Jabir ya amsa sannan ya fita daga office in.