PG 19
by @khadybabeey
PG 19
Sha biyar da watan mayu shekara dubu biyu da goma sha takwas.
Duk wan da ya kamata ace ya halarta dan zaman kotu ya karaso.
A babban office in kotun suka taru tun da zaman na siri ne .
Miti talatin bayan sun hadu gaba ɗaya alkali ya shigo.
Miƙewa dukan su sukayi dan min grimamawa sai da ya zauna sannan suma suka zauna.
Prosecutor ne ya tashi ya kara kiran karan.
Sannan alkalin ya yi gyran murya ya ce."
"Kotu na buƙatan ganin Kursum Yazeed Umar.
Prosecutor ya ce"
"Kursum Yazeed Umar ta baiyana a gaban kotu."
A hankali ta miƙe.
Sanye ta ke da maron hijab har kasa wan;da ya yi matukan yi mata kayu.
Prosecutor ya ce."
"Ke ce Kursum Yazeed Umar."
"Eh ni ce."
"Ki daga hanunn dama ki ki ce."
Daga hanun ta tayi tana kallon prosecutor. "
"Ki ce ni Kursum Yazeed Umar na yi alkawarin cewa zan faɗi gaskiya akan duk a bun da aka tambaye ni."
"Ni Kursum Yazeed Umar na yi alkawari zan faɗi gaskiya akan duk a bun da aka tambaye ni."
"To masha Allah.
Prosecutor ya zauna sannan alkali ya ɗaura da cewa."
"Kursum ki kalli wa in nan samarin biyu kin san su?
Kallon Ashraf da Salisu ta yi sannan ta ce."
"Eh na san su."
"Ko zaki iya faɗa mana dangantakan ki da su da kuma sunayen su."
"Bakin sunan sa Ashraf kuma shi in abokin karatuna ne.
"Farin kuma Salisu shi kuma ɗa ne ga wan mafiyana."
"Ok malama Kursum zaki iya tuna a bun da ya faru ran bakwai ga watan mayu shekara dubu biyu da goma sha bakwai."
"Eh zan iya tunawa."
"To bamu labari."
A hankali ta kara ba da labarin komai tun daga farko har karshe.
Shiru alakli ya yi ya na dan rubuce-rubucen sa sannan cen ya ce."
"Kursum kin san akan me muka taru a nan?"
"Eh na sani."
"To yanzu tsakanin ki da Allah ki tsaya ki zaba mutum ɗaya a cikin su kar ki bi ra'ayin wani sai na zuciyar ki kuma wan/da ki ka zaba shi za a baki.
Shiru ɗakin ya yi yayin da kowa ke suraran hukuncin ta.
Zuciyar Salisu da Ashraf ne ke matukar bugawa dan tsoron kar ta zaba wanin sa."
Kursum ke muke sauraro."
Na, na......
Na zabi Ashraf."
"Kina son sa ne. Alkali ya tambaya."
"Eh ina son sa."
"Uhmmmmm kafin a yanke hukunci ina so na dan ja hankalin mu akan wani abu.
Azamanin Annabi Muhammad(S.A.W) an samu wata budurwa da ta ke karan mahifinta wurin mazan Allah kan cewa zai yi mata auren dole.
Mazan Allah ya sa a ka kira sa ya tambaye sa gaskiyan zancen.
Mahaifin yarinyar ya amsa da hakane ciki hikima na mazan Allah ya sulhuta su har yarinyar ta ammince da auran sakamakon mahaifin na ta ya janye da ga auren dolen da yake so yi mata.
Ba ma wanan ba.
Me ya sa ake samu mata da laifen kashe mazajen su saboda aurar da su da ake ga wan da basu so idan har mace ta auri wan da take so zata zauna da shi komin talaucin sa amma wallahi idan har mace bata so ko shekara dubu za a yi ba zata taba son sa ba sai dai in har ta bar gidan wan da bata so.
Iyaye shawarace gare mu mu dai na aura wa ƴaƴan mu wa in da babsu so duk wanda suka kawo idan har anyi bincike a kan sa kuma ya cika dukan sharioin da muslinci ya tanada to aura masu.
A karshe hukunci kotu shine.
Babu magana kashe aure tsakani Ashraf da Kursum sannan kuma kotu bata ba da daman a ɗauƙaƙa kara ba sanan gargaɗi da duk wan da ya ki bin hukucin kotu za a ɗaure sa a gidan gyran hali na wata biyar tare da tara na dubu dari uku dan haka sai a kiyaye."
"Ya mai grima mai sharia ina da magana."
"To mallam muna sauraran ka amma kafin nan me sunan ka?."
"Sunana malam ayuba kuma ni wa ne da mahifin yarinyar nan."
"To malam Ayuba muna sauraran ka."
"Mu ammince da hukunci da kotu ta yanke amma ina so jama'an wurin nan su zama shaida duk randa Ashraf ya wulakanta ta to kotu zata raba auran."
"Kotu ta ammince da buƙatan ka.
Da wanan hukunci aka wase. An fito daga kotu zuciyar wa su cike fal da murna ya yin da kuma wa su abun bai yi musu dadi ba amma kuma babu yan da suka iya."
"Kursum ki zo mu tafi gida."
Karo na farko da mahifiyar Kursum ta yi mata magana cikin rahama tun san da aka faɗa mata cewa wae an ɗaura wa Kursum aure da Ashraf a makaranta amma yanzu dole ta zubar da makaman ta tun da kuwa uban giji ya tsara hakan kuma shi kaɗe ya bar wa kansa sani daidai hakan haka.