ANA BARIN HALAK

PG 20

by @khadybabeey

PG 20

Biki ya yi biki bangi maza da mata yara da manya sun halarta bikin ya yin da dukan classmate in su sun zo bikin kuma masha Allah biki ya yi kayu sosai abun sai son barka.

Gidan su na mahuta ba ƙaramin kayu da saruwa ya yi ba.

Gida ne me ɗauke da ɗaki hudu, uku a ciki ɗaya a waje kuma dukan su ɗauke da bayi fallo daya da kitchen sai tsakar gida me fili so wan da ya sha interlock.

Abokanan ango sun rako ango ɗakin amaryan sa.

Tun daga bakin ƙofa a fallo kawayen amarya suka hana sa shida ɗakin amaryansa wai sai an siya bakin amarya.

Usman nai kai ta ciniki da su Nabila akan kudin da za su babsu."

"Haba Nabila bai kamata ace dara ta ci gida ba sanin kan ki ne abun duk na gida ne dan haka ai bai kamata ace muna wannan jayaya ba ko."

"Uhmmm Usman ke nan ba wani na gida ne kawe ku yi a bun da ya kamata ka wai."

"To shi ke nan muyi maganar gaskiya mun da dubu talatin."

"A a arbain dai."

Kalla Nabila wallahi daga dubu talati in ba zamu kara ba.

Raɗa ɗaya daga cikin ƴan matan tayi wa Nabila a kunne sanan ta kali Usman ta ce."

"To kawo dubu talatin in."

Murmushi Usman ya yi sannan ya fito da kudin daga cikin aljihun sa ya mikawa Nabila.

Guɗa suka sake sannan Fauziya ta ce".

"Tabbas a yanzu babu shamaki Kursum ta zama na Ashraf har abada."

Yazeed ne ya ce".

"Salati goma ga annabi."

"Ameen, Ameen, Ameen al-fatiha"

"Anas ka rufe mana ko."

"Aa Yazeed Ameen, Ameen Ameen dai."

Dariya Yazeed ya yi sannan ya karasa addu'an."

"To ango mu zamu huce amma kafin mu tafi ga dan tunatarwa aure ba abun wa/sa bani ka ga dai yan da Allah ya sara lamari sa babu wan da ya yi zato.

Hausawa suka ce daga wa sa ƙaramin magana ta zamo babba to dan Allah ka dinga haƙuri kai ne a sama kuma ka yi ƙoƙari kar a ji kan ku ka ji ko."

"Na gode sosai abokina kuma insha Allah zan iya bakin ƙoƙari na sai kuma ku taya ni da addu'a."

"Insha Allah."

Miƙewa su kayi sannan Yazeed ya ce".

"To mu zamu tafi ango Allah ya bada zaman lafiya."

Miƙewa shi ma ya yi sannan ya fita raka su. Miti talati da fitan su ya dawo tana ciki taji karan yana kule ƙofan fallo.

A hankali ya duɗe ƙofan ɗakin.

Lulube take ya kaykkyawan mayafi me launi kore wan da aka tsare da shi da ganyen.

A hankali ya zauna a gefan ta ya yin da ya kasa magana har tsawan miti ishirin sannan cen ya ce"

"Ina godiya wa Allah (S.W.T) da ya nuna mana wannan ranar me cike da inbun tarihi."

A hankali ya sa hanu ya bude fiskan ta wan da ya sumar da shi na hucin gadi.

Murmushi ta sake mishi."

"Wallahi Kursum da na rasa ki da ban san wani hali zan shiga ba.

Kursum kai ce rayuwata kai ce farin ciki na.

Alhamdulillah Allah da ka nuna mun wannan ranar da zan dube idanuna na gan ki a gefe na."

To sai mu gode masa."

"Tabbas kam dole na gode masa tashi kiyi alwala ni da alwala na."

"Nima in da alwala.

To masha Allah kashi muyi sallah.

A hankali Ashraf ya tada sallah sannan ya ja su sallah.

Sun daɗe sosai suna addu'a sannan suka shafa.