PG 24
by @khadybabeey
PG 24
Hauswa sun ce daga wasa ƙaramin magana ya zamo baba to haka ya kasance tsakanin su Ashraf da su Yasir sun dage kan cewa dole sai su Ashraf sun rabu.
Rigima sosai ya farƙe tsakanin su har ta kai ta dawo duk idan Kursum zata je bata taba tafiya ita kaɗe Ashraf ne ke kai ta dan gudun kar Yasir ya cutar da ita kaman yan da ya faɗa.
Kaman kullin yau ma Ashraf ya zo daukan ta a in da ya saba parking ya yi parking yana jiran fitowan ta amma kuma sai yu ta daɗe hakan bai dame sa ba a tunanin sa ta tsaya kammala wani abu ne a aji dan haka sai ya cigaba da zuba ido dan ya ga bil-lowan ta."
Zarah ya gani ita kaɗe ta nifo in da ya ke, da ta karaso gasuwa kawai su ka yi ta sa kai zata huce da sauri ya ce ma ta."
"Zarah ina Kursum take bata gama bane??.
Jiyowa tayi ta zuba ma sa idanun ta na mishi kallon mamaki."
"Lafiya Zarah da irin wanan kallon.?"
"Haba ƴallabe ai kai ya kamata ka fi ni sanin in da take."
"Kaman ya ban gane ba."
"Ba kai bane dazu ka yi ma ta text kan cewa idan mun fito daga lectures ƙarfe goma ta tare napep ta sane ka a milaliyon city ba.
Da sauri ya ce".
"Zarah ni kuma."
"Eh kai har ta ce maka bata da kudi a wurin ta, ka ce mata ta zo zaka biya."
Wallahi Zarah Allah bani bane ni kwata-kwata ban kira ta ba yau kuma karin daɗawa wayata a gurin charge ta huni."
"Wallahi Allah yaya Ashraf kai ka kira ta akan cewa ta fito ta same ka a milaliyon city kuma kaman ma baba mai shayi me ya kai ta a napep in sa."
"Yauwa dan Allah muje mu same sa.
Zaune yake yana sauraran radion da ke gefensa."
"Salamu alaykum baban mai shayi ina wuni."
"Lafiya kalu Ashraf ya gida yauwa dama jiran zuwan ka nake yi."
"Da me ya faru baba?"
"Kudin napep ina zaka bani da na ke matarka milaliyon city."
"Ni kuma baba a yau she mu kayi haka da ke.?"
'Dazu ta kawo min waya ka faɗa mn in kai ta idan kazo zaka bani kudin."
"Innalillahi waina illaihi rajiun wallahi Allah baba ban kira ta ba."
"Ka kira ta ne yanzun?".
"A a ban kira ta ba."
"To kira ta muji ko tana in da na kai ta.
Da sauri Ashraf ya fito da wayan sa ya kira ta amma wayan switch off.
Hantan cikin sa ne ya yi wani irin kaɗawa ya yin da miyon bakin sa ke neman kafewa."
"Ya ya Ashraf bata dauka bane?
Daƙer ya ce".
"Baba wayanta switch off."
"Tofa to ka san me ne ka je gidan ƴan uwan ku mana ka buda ko tana cen."
"To baba bari in duba Ashraf ya faɗa a san da ya ke kuna mashin in sa ya bar haraban makarantan.
Duk in da ya ke tunani zai gan ta ya je amma bata nan sai ya koma gida ko ta kuma.
Gate in gidan a buɗe amma hakan bai dame sa ba shi dai burin sa ya ganta.
Ciki ya shiga har ɗaki amma ba kuwa kuma abun ban mamakin shi ne ko ina a buɗe ɗakin Ammynsa ya duba amma kuma ita ma bata nan.
Cikin tashin hankali ya fito daga gidan ko zai samu wan da zai tambaya in da mahifiyar sa take.
Ya yi sa a kuwa ya ga makocinsa malam Sada.
Gaisawa su kayi sanan yace".
Dan Allah baba kaga fitan Matara tare da mamana ne."
"Eh to dazu naganta ta fita tayi sama da dugu tana kuka munyi ƙoƙari mu tsayar da ita amma muka kasa.
"Dama Ashraf maman na ka bata da lafiya ne?.
Ashraf bai amsa wa malam Sada ba illa me me ta salati da yake ta yi ya yin da wani jiri ya dauke sa.
Har ya kusa faɗi malam Sada ya riƙo sa sannan ya zaunan da shi a kan dakali.
Sai bayan dan mitina ya dawo hayacin sa sosai sannan ya tashi ya kara bazama neman su."
Duk yan da Ashraf ke tunanin sauki a kan alamarin abun ya ki dan har dare bai same ko mutum ɗaya ba.
Bai yi niyar neman taimakon kowa ba amma haka ya kira kawunsa dan abun yafi ƙarfinsa.
Dukan daren Ashraf da kawun sa sun karar da shi ne wurin neman su Kursum daga karshe suka kai kara wurin ƴan sanda.
An dauki statement in su aka ce su dawo nan da kwana biyu.
Da Ashraf bai so a gaya wa Baba Jabir ba amma kawun sa ya ki.
Ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba a san da labarin batan su Kursum ya isar musu.