A zuciyata

Chapter 1

by @aishatu98

The night it all began…


Ruwan ake da daddare yana sauka a hankali kamar yana jin raɗa. A cikin dakin da ke kunshe da farin labule da qamshin turare, Safna zaune take a gefen gado, cikin shiru. Auren ta anyi da yamma, amma zuciyarta ba ta cikin wannan dakin  ba ta cikin wannan duniya ma. Tunaninta ya tafi  ya dawo ya koma, kamar guguwa a cikin zuciya mai rauni.

Zama take da dogon riga mai launin gold, an jera mata lefe kamar yadda aka saba, an kwana biyu ana shagali, amma yanzu, ita kaɗai ce da sabon mijinta. Khalil. Mijin da iyayenta suka zaba mata. Mijin da aka ce “yafi” amma zuciyarta tana fadin wani abu daban.


“Are you okay?” muryarsa ta fado mata kunne  muryar sanyi da nutsuwa. Ba muryar da take ciwo ba. Ba muryar da ke saka jikinta rawa da dadi ba. Muryar da take da kyau, amma ba tare da rauni ba.

Ta daga kai ta kalle shi. Khalil ya tsaya kusa da mirror, yana cire agogon hannunsa. Kyakkyawan namiji ne  clean shave, farin fata, mai kamewa. Yaron manya. Sai dai… ba shi bane. Ba Fahad ba.

“I’m fine,” Safna ta fadi da karamin murya, amma cikin zuciyarta, akwai wani ihu da ba wanda zai ji.

Zuciyarta tana da wani sirri da duniya ba ta sani ba. Zuciyarta ta taba soyayya – soyayyar da ta fi karfin kalma. Amma wannan soyayyar ta tafi, kamar gizo. Ko da yaushe da zata lumshe ido, Fahad ke bayyana da murmushinsa mai sa zuciya dukan daban.  tunanin shi ya cika kowane kusurwar zuciyarta.

Fahad  mai nutsuwa, mai juriya, mai furta kalmomi masu nishadi da tausayi. Suna haduwa a lokacin da take yi wa wata NGO aikin sa-kai a Kaduna. Shi ne NYSC coordinator dinsu. A wancan lokacin, ta san soyayya na nufin sama da kasa suna haduwa. Sai dai… wani abu ya faru. Wani abu da ta kasa fassara. Da farko, komai na tafiya daidai. Saƙonni, kiran waya, ganawa a karshen sati, dariya da hawaye. Sai kuma kwatsam ya bace. Ya daina kira. Ya daina turo sako. Ya daina bayyana. Kamar bai taɓa wanzuwa ba. Ta yi kuka. Ta nemi bayani. Sai dai babu amsa. Iyayenta suka lura da canjin halinta. Sai suka ce lokaci yayi  lokaci yayi da zata auri Khalil, dan abokin mahaifinta, wanda ya dawo daga UK yana neman a d’aura masa aure. Ta amince. Kamar wata mara zabi. Amma zuciyarta… ba ta taba hakura ba. “Safna?” Khalil ya matsa kusa da ita. “Do you want to rest now? Or should I give you some space?” Ya san ba ta jin dadi, sai dai ya dauka saboda gajiya ne. Ba zai taba sanin cewa ba gajiya ba ce  ƙaryewar zuciya ce. “Space is fine,” ta fadi, cikin sanyi da mutunci. Ya jinjina kai, ya fita daga dakin, ya bar ta ita kaɗai. Ta zube a kan gado, ta lumshe ido, hawaye suka fara sauka. Sai yanzu ta tuna da sakonsa na ƙarshe Zuciyarta ta karaya. Da gaske Fahad yayi "try”? Ko kuwa ya gudu? Ko iyayenta ne suka hanashi? Ko akwai wani sirri da ba ta sani ba? A yau, ta zama matar wani. Amma a zuciyarta, wani ne ke da gurbin da ba zai taɓa cikewa ba.

Wannan dare ba dare ba ne kawai. Wannan dare shine farkon sabuwar rayuwa. Kuma farkon bayyanar sirrin da zai girgiza komai.