Zuciya Mai Rauni

BABI NA BIYAR – Wasikar da Ta Fara Tonon Asiri

by @deeyerhwrites1

Idan aka fara da ƙarya, sai gaskiya ta tona kai.”


A cikin dare, bayan kowa ya yi shiru, na zauna da fitilar waya na rubuta wasika. Ba wai don in fitar da ita ba, sai don in fitar da abinda ke cike da zuciyata.


Na kira sunanta:


“Umma…”


“Na fi son ki sani cewa ban taba jin cewa ke ce uwar da na fi so kamar yau ba. Amma kuma, zuciyata tana bukatar gaskiya. Waye mahaifina? Me ya faru da shi? Me ya sa kika ɓoye min rayuwata na gaskiya? Kuma me yasa Alhaji ke ƙin duk abinda ke sa ni farin ciki?”


“Umma, kina tunanin zan iya mantawa da Usman? Kina tunanin zan iya zama da wanda bai ji zuciyata ba, saboda suna ko dukiya?”


“Ki gaya min gaskiya. Ko zai ci min rai. Domin zuciya ta na rauni—amma tana neman warkewa a cikin gaskiya.”


Na nade takarda cikin hijab na, na boye ta a cikin jakar makaranta. A dare, ban runtsa ba.



🕌 Hajiya Nafisa Ta Karanta Wasika


Da safe, bayan na fita Islamiyya, Amina ta taimaka aka bar wa Hajiya wasikar. Lokacin da ta karanta, ta zube a gado. Hawaye suka dinga zubo mata kamar ruwan sama da bai da tsayawa.


Tana karanta kalmomin Maryam kamar ana kiran zuciyarta da sunan mahaifin Maryam.


“Yunusa…” ta furta da kyar, sunan da shekaru ashirin suka shafe cikin shiru.


Sai ta zame jakar leda daga cikin daki. Ta zaro tsohuwar takarda da hoto.


Hoto ne na wani saurayi mai kamala, mai murmushi, mai idon da suka cika da so.


“Ke da gaske… ‘yar Yunusa ce,” ta ce a hankali, hawaye na shara gefen fuskarta.



🧕🏽 Zama Tsakanin Iyaye


Wannan dare, Hajiya Nafisa ta tara karfin zuciya, ta shiga dakin Alhaji Bashir.


“Alhaji, lokaci ya yi da zan fada maka gaskiya.”


“Wani gaskiya kuma?” ya tambaya yana duba wayarsa.


“Maryam… ba ‘yar ka bace. Ita ce ‘yar Yunusa. Saurayina kafin ka zo rayuwata. Kuma wallahi, ka karbe ni da ita da gaskiya, amma zuciyata bata taɓa jin dama in fada ba.”


Alhaji ya juyo da idanu masu cike da mamaki da ƙiyayya. “Na dauki ‘yar wani kamar tawa, amma yanzu ita ce ke ƙin biyayya? Ba ke kika zame min abin ƙyama ba, Nafisa, ba ita ba.”


Yayi shiru. Amma cikin ransa, da akwai rudani fiye da fushi.