chapter 41
by @khairatup01
Zuciyar Mutum.
Khairat.
Wattpad:Khairi_Muhd.
41.
"Hammana ina mai baka haƙuri bisa ga laifin da na yi maka. Ka yi haƙuri kar ka yi fushi ni."
Saƙon da ta aika masa kenan ,kuma yana ta dubawa amma kibiru ya hana ya bata amasa. Haushinta yake ji sosai baya jin nan kusa ma zai koma Billiri don in ya koma Billiri ma ba ƙaramin tashin hankali zai yi ba don zai aikata ba daidai ba.
Saƙon ne ya kuma shigowa.
"Hamma! Ni ce fa ƙanwar ka Ummu."
Koda ya karanta sai da ya murmusa a fili kuwa cewa ya yi "Ummuna." Ajiye wayar ya yi a gafe ya gyara kwanciyarsa ya kwanta.
*
Wayar ta bi da kallo amma babu amsar Hamam Haidar duk sai ta ji zuciyarta babu daɗi tsaki kuwa ta yi shi ya fi ba adadi. Bacci dai ɓarawo ne kawai ya sace ta.
Washegari ƙarar wayarsa ce ta tashe shi daga bacci a hankali ya buɗe idanuwansa ya kalli wayar tar ya buɗe idanuwansa bayan ya ga sunan Abi. Kiran ya katse ya tashi da azama ya zura slippers ɗinsa ,singileten sa kawai ya zura ya fita falonsa.
Wayar ya jona ta kuma harba masa caji percent biyu da ke iphone ce jiya rigima ba ta saka ya jona cajin ba. Kiran Baffa ya gani wannan karon da sauri ya ɗaga.
"Salamu alaikum Baffa."
"Baccin ne dai Haidar? Maza yanzu ka zo ga Abin naka ya zo zaku yi magana."
"Gani nan zuwa Baffa."
Haidar Haidar ne a haka ya fita daga ɓangaren na sa ya fita da gudu ,slipperas ɗin ma bai saka ba.
Kawai ganin sa suka yi kamar an jefo shi.
Dariya suka saka masa daga shi sai singileti da gajeran wando. Kan sa ya kalla sai ya ba wa kan sa dariya da kan sa ya shafi ƙeyarsa yana murmushi.
A hankali ya zauna kusa da Abi yace "Abi barka da zuwa bacci nake ta yi ban yi bacci ba jiya ina ta taƙaicin ganin Ummuna da wancan yaron marar kunyar. Abi amma tun jiya ka taho ko?"
Abi ya ko dara da rigimar Aliyu. Yace "Aliyu ba ka yi bacci ba? Yanzu ya naga kamar ka yi baccin?"
"Abi ɗauke ni ya yi fa baccin amma har mafarki na yi. Kai haukacewa zan yi Abi ni dai a duba lamari na."
Abi ya ce "Bar su ni nan ni ne Abban ka kuma na zo maka da albishir."
"Abi gaya min don Allah!."
"Tashi zaka yi ka shirya ka zo mu tafi Billiri."
Zabura ya yi ya tashi tsaye ya yi hanyar fita. Hajiya tace "Ina zaka je kuma?"
"Kash Hajiya ba ki ji Abi ya ce na shirya mu tafi Billiri aurena za ayi."
Hajiya ta kama baki. Mami tace "Aliyu ne fa bai san kunya ba."
Baffa ko dariya ya yi kawai yace "Wallahi Abin yara ni na bar maka Haidar ba zan iya da lamarin yaron nan ba. Sam ba ya kunyar mu kaitsaye yake dukanin lamuransa."
"Ai wato jiya bayan mun yi waya da kai kiran Baban Kamalu ya shigo mini ya gaya min komai sai na ƙara jinjina lamarin yaron. Da na ji yana nemawar wa ɗan sa izini ne sai na dakatar da abin na ce ai an ba wa Haidar marigayi Baba ya bar wassiya kuma Aliyun na so ni na sani tun da can ma Baba ya bar wa Ummun to yanzu in aka kuma tauye shi zai iya yin komai. Irin su Haidar lallamasu ake yi ba wuta-wuta ake bin su ba. Ni na gaya musu can su shirya in an sauko massalaci za a ɗaura auren kawai in ya so koma me zai faru ya faru ba zan iya da raba faɗa ba. A ce Aliyu da dambe ya yi wa ɗan mutane jina-jina. Ita ma ya yaryarfa mata maruka a fuska ai akwai matsala."
Mami tace "Hmm! Ai Yaya wannan yaron ba shi da hankali wani bin. Ni ban san ma ya aka yi kuka yarda zaku ba shi ita ba jiya ya mareta gobe me zai mata?"
"Ya yi cikin fushi da kishi ne. Ke kan ki kin san Haidar ya yi sanyi sosai. Ku dinga tuna zamanin da sai ayi watanni ba a san duniyar da yake ba yana can yana afa ƙwaya ga ɗauko rigima zuciyar ce ta daina tsoro ta kangare."
"Allah dai Ya shirya mana."
"Amin."Suka amsa dukan su.
Ya labarin Ango?
Yana shiga ciki, ya faɗa banɗaki. Sai kuma ya fito da gudu ya ɗauki wayarsa ya kira amininsa Taheer.
"Ya shegen kaya?"
"Maza mu haɗu a Billiri ɗaurin aure na za ayi."
Wayar Taheer ya cire daga kunnensa ya kuma kallan lambar ya maida wayar kunnen yace "Me ka sha Aliyu? Ba ka yi alƙawari ka daina ba?"
"Mtsw! Wallahi da gaske nake maka mu haɗu a can. Ina son ka kasance a wurina."
"Don girman Allah wacce wannan ta yarda da auren ka?"
"Kai kutu....."
"Allah taimaki ɗan iska na gamsu auren za kai yi yau. Gani nan bara na ga ya za ayi."
Ya ajiye wayar ya koma banɗakin.
*
Ai ni Haidar ka jiƙa min aiki. Ta Abuja zan bi dole. Da ke sabga ce ta kuɗi nan da nan ya sayi tikit ya yi Abuja. Daga can ya hau Azman air zuwa can Gombe.
*
Aliyu Haidar fes ya fito cikin wata dakakkiyar shadda fara tas sai ƙamshi take yi. Bai manta da shaddar ba ita ma Habib ne ya ba shi ita bai saka ba ya ajiye ta yace masa "Habib zan saka amma sai ran da zan sake aure." Tunda ya ajiye ta a cikin drower bai kuma kallonta ba. Shaddar filtex ce mai laushi daga switzaland aka kawo ta. Hular Garkuwa ya saka mai dauke da zanen lu'ulu'u (crystal) ya saka.Creed Aventus ya fesa nan da nan ko ina ya ɗau ƙamshi. Ya ɗauko dai takalmin Gucci leather loafers ya saka.Ango ya fito fes wanka ya bi jiki an ƙure wanka in ka kalle shi sai ka ƙara.
Tabarau ɗin sa ya zaro daga ma'ajiyarsa ray-ban ya saka. Kallon kan sa ya yi a madubi ya kuma kalla yace "Ma sha Allah! Gaskiya Ummuna ni kai na na san kin yi sa'a."ya faɗa yana dariya.
Tunda ya fito yake ta zuba faɗi yana tafiya cikin isa da izza. Ba ƙaramin kyau ya yi ma yan wurin ba.
Ita kan ta Mami sai da ta jinjina ado da kyau na ɗan nata. Addu'a take a ranta Allah Ya sa abokiyar zaman sa ce ta alkairi. Har ga Allah tana son haɗin Haidar da Ummu.
Abi yace "Kaga gwarzo na Ummu."
Sunkuyi yayi da kansa yana murmushi haƙoransa sun kasa boyuwa. Haidar dai yau hakoransa ba sa rufuwa ras ake ganinsu saboda tsananin farincikin da yake ciki.
Abi ya kalle shi yace "My son yau ka ke ango shi ya saka yau tafiyar ban girma zamu yi. Abin hawan ma na Ummu ne amma kai nake so ka kai mata kyautar ta a matsayin kyautar aure."Motar ya bi da kallo Mercedez Benz-A class ce.
"Abi ta yi kyau.Muna godiya."
Kowa ya shiga mota aka yi convoy.
Ana buɗe musu gate motar da ta kawo Taheer na shigowa. Sallamar mai motan ya yi ya fito.
"Taya za ayi tafiyar nan ban iso ba?"
Ta taga ya leƙa yace "Taho mu tafi sha ɗaya ta kusa."
"To rasa kunya."
*
Billiri.
Tun asuba wayar Hajiya ta riske ta. Duk da gaban ta ya faɗi hakan bai hana ta ɗaga kiran ba.
Hajiya ta tambayeta abinda ya faru tsakanin Kamal da Haidar. Bata ɓoye mata komai ba ta gaya mata duk abinda ya faru. Bata yi tsammani ba kawai ta ji muryar Abi a cikin wayar yana tambayar ta shin zata iya aurar Haidar? Sai da ta ji komai ya ɗauke mata na wucin gadi. A kwance take amma sai da ta miƙe ƙafafuwanta kamar zasu kasa ɗaukar ta.
"Hello! Ƴa ta ba kya ji na ne?"
"Abi duk yadda kuka yanke ni mai yi muku biyayya ce."
"Na sani. Amma ina son ji daga bakin ki gaskiya nake son ki faɗa min bana son kara ko jin kunya. Ki gaya min gaskiya."
"Abi zan iy...a." Tana gama faɗar haka ta kashe wayar ta kulle ido kamar ana ganinta.
Sai tashi ta yi ta ga gida ya ɗauki harama ana ta abubuwa.Mamaki bai gama kashe ta ba sai da ta ji Dada na cewa "Gwara da kika tashi je ki yo wanka , ki shirya ga kayan nan Hajiyar ta aiko da su."
"Dada me ake yi? kayan me wannan?"
"Ɗaurin auren ki da Aliyu."
Da mamaki ta saki baki tana kallon Dada. Dada aure?
Ke ban san gulma. Ai kin sani tunda Abi ya ce ya kira ki. Ke ni gwara da za ayi ba zan iya da Haidar ba can ku je ku ƙarata.
Kai Dada.
Ke kika sani dai.
Dole ta saka hijab ta ɗauki wayarta ta fito gidan Yafendo zata je ba zata iya da wannan hayaniyar ba. Wai Hamma Haidar mijin ta? Ita kan ta abin dariya yake bata.
Tana fita ta haɗu da jama'arta Meenal da Nana.
Aiko suka rangaɗa mata guɗa. Hannu ta sa ta toshe kunnenta.
"Meye haka?"
"Amarya ce! amarya ce! amarya. Amaryar Hamma Haidar gadanga ƙusar yaƙi mazan jiya mazan yau. Wato jiya ya gama bawa hammata iska shi ne ya ce bara ya yi maganinki ya ɗaure ki kawai da igiyoyi uku iye akwai kallo a gidanku fa."
"Kai kun banu."
Suka kwaikwayi maganar ta. Gaba tayi ta bar su. Suna biye da ita a baya.
Bata biye musu ba don kunya ma suke bata ganin sai kallonsu ake yi ana nuna su.
"Kai haba ku nutsu mana sai ka ce ba matan aure ba?"
"Ahaye!Sannu farin shiga."
"Wuce nan Wallahi!" Ta faɗa tana harararsu.
Haka suka je gidan Yafendo.
Nan ta ga Rukkaya da su Adda Hassana. Tsabar farinciki ta faɗa kan Adda Hussaina ta rungume ta haɗe da sakin kuka.
"Lah meye haka? Amarya da kuka salon Haidar yace na miki wani abun."