ZUCIYAR MUTUM

Chapter 42

by @khairatup01

Zuciyar Mutum.
Khairatup.
Wattpad:khairi_Muhd.
Arewabooks:khairatup01
42.

Tuni ɗakin ya ɗauki sowa da ihun murna.Duk yadda na yi na ƙwaci kaina daga wurin Hamma amma abu ya ci tura na kasa. Hasalima ƙara rungume ni ya yi tsam saukar hawayen shi na ji a gadon bayana. 

Vedio aka dinga yi mana.

Cika ni ya yi ya riƙo hannaye na biyu ya haɗa da na sa ya ce "Alƙawarin ki na rike. Daga yau ga Haidar ki yi yadda kike so da ni."

"Aa Hamma ba haka za a yi ba Hamma wanka za ki yi mata ta soyayya."

"Haba? In dai tana so zan yi mata." Ya faɗa yana kallona. Na sunkuyar da kaina ƙasa ya sa hannunsa biyu ya tallafi kumatuna ya kalli cikin idona yace "Na miki waƙa za ki yi rawa? Rawa ta nuna godiyar ki da farincikin kasancewa matata  a yau?"

"Wayyo Allahna! Soyayya da akwai daɗi Hamma Haidar ka kashe ni."

Harararta ya yi yace "In dai waƙa ce zan miki." 

Kowa ya koma ya zauna ban da su biyu. 

Ya riƙe hannunta ya soma juya ta irin yadda turawa suke yi yana mata waƙa jama'ar wurin suna tafi.

"Babban burina in kasance daf da ni. In za ki ƙirga masoyana ki sanyo dani. Duba kan ki ana kallona majnuni,ni kuma na ce in dai kai na ki ne ban faɗi ba. Saƙo ya bayyana ne ne tun daga zuciya sannan ƙaunar ki tana kaman zuciya,kin kama mini kuruwa ta tun jiya har ya kai matsayin bana samun lafiya. Kin shiga raina kin zauna don kin samu wuri..." 

Tsabar kunya haka ta kwantar da kan ta a kan ƙirjinsa.

Aka kuma sakin sowa a ɗakin. Ba ƙaramin burge mutane Haidar da Ummu suka yi ba. 

"Wai dama kai ka iya soyayya munafuki kake ta wahalar da ƴan matan  da suka mato kan ka?" Taheer ya faɗa yana dariya.

"Ba su suka dace na nunawa soyayar ba shi ya sa na kame kaina. Yuu kuma alƙawarin Allah Ya cika na samu muradin raina kun ga kar ku ga laifina ni na faɗa da babban murya ni nan mijin Hajiya ne."

Kowa ya saka dariya.

Ya kalli Ummu ya yi mata raɗa a kunne "Tafiya fa zamu yi ni da ke don ni ban ga dalilin da zai saka na bar ki a nan ba."

Bata iya cewa uffan ba kawai tayi zuru tana kallonsa ta san zai aikata kuma ba shayin kowa yake ba. 

"Hamma ka bari mana su faɗi lokacin da zamu tafi ba zamu zo mu same ka ba?"

"Amma dai kin san cewa an ɗaura aure yau ko?"

kai ta gyaɗa masa.

"Yauwa to daga yau ni ne kowan ki.Cewa ta ce ƙarshen magana."

"To." Kawai ta ce da shi don ta san ba za a bari ba.

"Kamar kun manta muna wurin?"


Kai Adda kina da sa ido gaskiya. Ni ɗauke matata zan yi mu wuce ai an gama biki.

Tabɗi ai Wallahi baka isa ba akwai biki a gaba za a kawo maka matar ka daga baya.

Wallahi ba a isa ba. Kin san ba a isa ba ko. Ƙafata ƙafar ta. 

Ikon Allah! Yau ina ganin fitsara. 

Juyawa tayi zata bar falon ya yi wuf ya kamo hannun ta. "Ina za ki je?"

"Wurin Mami za ni."

"Ai yau sai kin saki Mami."

"Kai Hamma..."

"Kin san kuwa irin karar da na yi a kan ki? Ba ki sani ba to ki yi shiru ba yarda zan ba ato."

"Na shiga uku Hamma ana kallon mu fa."

"To ni meye ruwana da su? Akwai wadda nake kunya cikinsu ne? Ke ni ko gaban Baffa riƙe ki zan yi. Duk wanda ya ji yaji ya fita kawai."

Adda Hassana ta miƙe tace "Ku tashi mu fita wannan ba mutunci ne da shi ba zai aikata koma meye zai aikata."

"Tuntuni nace muku mu tafi ai." Adda Rukkaya ta faɗa.  

Dayan bayan daya suka dinga fita daga ɗakin. Aka bar su daga su sai su.

Janyota ya yi yace "wa na kama yau?"

"Ummu."

"Ummun wa?"

"Ummun Hamma."

"Waye haka?"

"Mijina."

"Iyi ashe kina da miji?"

"Eh ina da miji mara ta ido."

Hhhh "Yarinya ta girma."

Bata kuma ce mai komai ba. 

Ya sunkuyar da fuskarsa dai-dai saitin kumatunta ya sakar mata sumba a hankali.

Lumshe idanuwanta tayi ta ɗan ja da baya tace "Hammana..."

"Hukuncin hana zuciyata sakat ne." 

"A yaushe na hana ka sakat ɗin."

"Koyaushe." 

Ya ja hannun ta suka zauna kan kujera. Sai ga shi sun manta a ina suke suka dinga hira gabaɗaya ya takura mata ya hana ta sakat bata san haka yake ba sai yau da aka ɗaura musu aure, bata taɓa zaton yana da bakin magana haka ba sai yau.  Shin da gaske ne Hamma Haidar ya jima yana dakon son ta ?  Ta jima tana gani wani abu a idanuwansa game da ita sai dai bata iya fassara kallon ba ko abinda take gani ba amma yau ta gane soyayarta da ƙaunarta ce ta lulluɓe masa ido.

Ɗankwalinta ya zame ya soma shafa gashinta da ke a tsefe. 

Hamma kar a shigo fa.

Sai me in an shigo? 

Akwai kunya ai.

A wurinki dai.

To ka bari na samo mana abinci mu ci.

Ke kaɗai ma kin wadatar,ni fa iya wannan zaman da kika yi nake kallon ki nake jin muryar ki ya ishe ni ya cika min ciki ma in gaya miki.

*

Mami ta dinga bin bakunansu da kallo suna maida mata fitsrar Haidar. Sai da suka gama tace "To ai sai ku ɗauke kai kawai kun dai san Haidar ba kunyar kowa yake ji ba. Ya ɗau matarsa su tafi ni babu ruwana ai ikon shi ce. Tunda ya ce a gaban Baffa ma zai iya kamata to Wallahi sai ya aikata. Ku raba kan ku da wahala."

Kowa ya yi shiru ya rasa abin cewa.

A ka ci gaba da yinin biki. 

Haidar be fito ba sai da aka kira sallar la'asar don tunda ya shiga bai fita ba kuma bai bari Ummu ta fita daga ciki ba. Duk yadda aka so a ga amarya haƙura aka yi. Haidar ya saida kunyar sa a kasuwar marasa kunya. Ya rufe idanuwansa da kwallin fitsara.

Wannan fitar da ya yi bai dawo ba sai isha. Dole ya haƙura da tafiya Gombe ranar sai da safe. Hotel suka kama shi da Taheer suka kwana a can. A can ɗin ma raba dare ya yi yana waya da ita. Taheer ne ya kwace wayar yace "Haba farin shiga meye haka zaka wani dame mu an gaya maka mu bamu da matan ne? Dallah saurara min na huta shege maye."

"Hhhh tuƙwaƙwaƙwa! Kai ƙaramin shege ne dalla ban wayata in yi waya da masoyiyata."

Na rantse da Allah baka isa ba bacci zan yi duk na gaji. Kai ne angon amma ni na sha gajiyar amsa wayoyi da fatan alkairi.

Ai amfanin ka kenan.

Diramar Haidar da Taheer bata ƙarewa haka na ce bara na wuce su na koma wurin Uwargida mai capacity.

AFEEYA!

Umma don Allah ki gaya min wasa ne. Ki gaya min wannan ƙarya ne. Wannan ya aura?

Ita ce.

Na shiga uku.

Ba ki shiga ba tukunna. Da sauran ki.

Umma na yarda zan yi abinda Okafor ya ce in dai zan ruguza farincikin Haidar. Ba zan bari ya zauna lafiya ba.

Haka nake son ji. Ni kuma yau na yarda za ki iya komai don samun nasara. Zan haɗa mana tafiya da ke.Zamu je mu ga elder.

Umma na yarda.

Yau na yarda ke ƴata ce.

Toh muna biye Afeeya mu ga naki kalar kishin.

*


Washegari.

Bayan na fito daga wanka na ji wayata na sowa. Haka na ajiye tawul ɗin na ɗauki wayar.Hamma ne. Har na ƙosa da amsa kiran sa saboda daga wayewar gari zuwa yanzu ya kirani ya kai sau goma ni na san yanzu ma Mtn sun gane lambarsa da tawa. 

Ɗaga kiran nayi tun kafin na yi magana ya riga ni.

"Ina kika ajiye wayar ki?"

"Yanzu na fito daga banɗaki."

"Ok. Kin shirya yanzu?"

"Aa. Daga wanka na fito."

"Vedio call."

"Aa."

"Why?"

"Ni dai aa."

"Uhm. Duk wayon amarya dai."

"Eh na ji."

Bara na bari ki kimtsa. In kin gama ki kira ni.

To.

Sauran ki ƙi kira ki shiga wata sabgar.

Zan kira.

Bye love you.

Love you too.

Suka ajiye waya.

Hamma kenan.

Atampa ta saka ɗinkin zani da riga. Ta yi ɗaurin zahra buhari ta saka ɗan kunne mai barima. Flat ɗin takalmi ta saka baƙi.  Ta fita tsakar gida. Kowa na zaune kan tabarma suna ta hira haka ta zauna tsakiyarsu Mami ta kwanta kan ƙafar Hajiya ta kwanta.

"Wash Hajiya na gaji."

"Ai dole ina jin kuna ta waya da wannan fitinannen."

"Kai Hajiya ni ban yi waya ba."

"Muna fa jin ku ƙus-ƙus ɗin naku ai ana ji ato."

Aka koma tsokanarta. Da gaya ta bar wayar a ɗaki. 

A nan ta karya. Suna zazaune har ƙarfe biyun rana. 

Mami ce ta dubi wayarta ta kalli Ummu.

Ni na san wannan kiran ba nawa ba ne na ki ne ina wayar taki ke?

Tana ɗaki. 

Ni ba za a ƙarar min da caji ba ki ɗauko wayar ki.

To Mami.
Tashi tayi a hankali cikin sanyi ta shiga ɗakin. Adadin miss calls ɗinsa da ta gani sai da ta tsorata kusan ashirin.

Zata kira ya riga ta kira.

Balbaleta da faɗa ya yi.

"Ashe kin raina ni? Ashe ban gaya miki ki riƙe waya ba? In ba kya son na kira ki kawai ki gaya min kiga in na kuma kiran ki."

"ka yi haƙuri ina tsakar gida wayar na ɗaki."

"Saboda ba ni da muhinmmanci a rayuwarki shi ya sa za ki bar wayar a ɗaki ke ki fita an gaya miki waya ta ajiyewa a gefe ce."

"To ka yi haƙuri?"

Tsaki ya yi ya ajiye wayar.

Ita dai ta bi waya da kallo. Daga ƙarshe kuma ta taɓe bakinta ta ajiye wayar.

Haidar.