Chapter 1
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ZINARE*
NAFISA ALIYU SASAAL
Arewabooks@sasaal
*BISMILLAH*
✍️ 7:30pm 5-7-2025
*Labarin ZINARE ƙirƙirarren labari ne, idan wani sashe na labarin ya yi kamaceceniya da rayuwar wata/ni to akasine*
*CHAPTER 1*
*"BA A RANAR DA MUKA SHUKA IRI ZA MU GIRBI AMFANINSA BA, DOLE SAI MUN JIRA, MUN YI HAƘURI, TARE DA YIN AIKI TUƘURU."*
01
Yankin Tudu, Daular Sarki Hammam, sassanin wasannin ƙarshen mako.
Yara Matasa Maza da Mata ma su shekaru 15 zuwa ƙasa ne suka cika filin wasan.
Ɓangaren Maza daban na Mata ma daban.
A ɓangaren Maza, a tsakanin ƙungiyoyin biyu da suke gwabza wasan ƙwallon ƙafa kowa na ƙoƙarin nuna ƙwarewar shi, da zafin namanshi. Wannan yasa ihu da tafi yake ta tashi daga kowani ɓangare, bakunan wasun su kamar zan yage saboda dariya da ihu.
Kujerarshi ba ta kusa da na kowa, fuskarshi daban yake dana kowa, ba bu murmushi balle dariya. Ba ya tafawa kamar ragowar kamar ma dai bai san me ake yi a wajen ba, ko wanda aka tilastawa zuwa sansanin wasannin dole. Tsayayyen dogon hancinshi ya shafo ya na lumshe fararen idanuwanshi. Kamar ance ya waiyawayo gefen da Matan suke wasannin su. A daidai lokacin wata matashiya mai irin Shekarunshi ta kwaso ƙafar ƙaramar yarinyar da bata wuci shekaru 6 ba, mugun dariya ya kwashe da shi yana ƙara waiwayowa kansu dakyau, zaman ƴan borin da yarinya tayi ne yasa ya ƙara kwashewa da dariya.
Ya na son mugunta a rayuwarshi sai dai baya iya yiwa wani amma yana so yaga anyi a gabanshi, saboda daɗin da yake ji, musamman idan wanda aka kai ƙasan ba shi da gaskiya.
A hankali yarinyar ta miƙe fuskarta duk hawaye da majina, nan ma dariya ya ƙara kwashewa da shi, ya na jin daɗi a ranshi. Mai ya kaita cikin manyan da ba sa'anninta ba yin wasa banda ga ƙananu Yara Ƴan uwanta suna na su wasannin? Miƙewarta tana karkaɗe ƙasar jikinta haɗe da zare idanuwanta da hawaye ya ɓata ne ya ƙara sashi sakin dariya kafin ya ɗauke kanshi yana sauke ajiyar zuciya nishaɗin da ya samu.
A take asalin fuskarshi da ba fara'a sam ya dawowa yadda ya ke.
A can nesa da shi Sufyan yaron da bai wuce shekaru 11 ba ne ya zubamai ido, ya daɗe ya na kallon duk wani motsinshi har hankalinshi ya bar wajen wasan gaba ɗaya. Maiyasa ba ya dariya sai ya ga mugunta? Maiyasa ba ya magana sai da ƙwaƙwarar dalili? Ya na son ya matsa kusa da shi ya yi mai magana kamar yadda Mahaifinshi yake umartarshi duk ranar da zai fito irin waɗannan guraren da shi kaɗai yake iya sumun damar ganin shi kai tsaye, amma tsoro ya ke ji duk da ratar shekaru hudu ne kacal a tsakaninsu.
NAILA da aka kwashewa ƙafafu jikinta ta ƙarasa karkaɗewa har cikin ranta takejin takaicin abinda akayi mata, banda zafin da take ji a bayanta. Kalle-kallen wanda zata kaiwa ƙara ta fara yi har idanuwanta suka faɗa gurin dayake zaune shi kaɗai. Da gudunta na yaranta ta nufeshi rabin fuskarta duk ƙasar da hannunta ya kwasa.
Gabanshi ta zagayo ta tsaya batare jin tsoro ko shakka ba.
Da ƙaramin muryarta na yara ta fara koromai bayani ta na sauke ajiyar zuciya.
Ba ya wasa da yara, balle ya ce ya taɓa wasa da ita a wani wajen ne yasa ta zo har gabanshi ta tsaya. Tsaf yake sauraronta, a bayanin na ta da yanda take kame-kamen dole sai ya bi mata haƙƙinta yasan itace bata da gaskiya amma take so a rama mata, rabin fuskarta ya kalla tare da tuno yanda aka kwashe mata ƙafafuwa tayi zaman ƴan bori. dariyar mugunta ya ƙara kwashewa da shi. Ya kai wasu daƙiƙu ya na yi kafin ya gimtse fuskarshi yana ɗauke kallonshi daga kan fuskarta. Tsayawa Naila tayi ko zai ce mata ta zo su je ya rama mata amma sai taji shiru. Ƙasar fuskarta ta ƙarasa karkaɗewa da kyau. Sai a lokacin ta gane wajen wanda ta zo. SULAIM ne ɗan gidan ABDUH DHAHAB ɗin daya zama ƙashin bayan Yankin su. Dama tasan bazai kulata ba, dan da tasan ma shine da bazata zo ba.
Barin wajen ta yi tana tunano abinda zatayimai tunda yaƙi kulata dama kuma tasan kurma ne baya magana.
A haka wasannin ya ƙare kowa ya fara haɗa kayan wasanninshi don tafiya Gida.
Sanyin iskar da yake busa ta ne yake ƙaramata ƙaimin tunanin sharrin da zata haɗamai lokacin da take kallon takun sawayenshi shi kaɗai, saɓanin ragowar da suka jero da Abokannan su.
★ƙarfe bakwai a harabar gidan Abduh Dhahab ya yi wa Naila sanye cikin Uniform ma su tsafta, kafaɗarta rataye da jakar buhu shima a wanke ƙal. Baki Mai share harabar gidan ya saki, lokacin da ya yi ido biyu da Naila kafin ya tambayeta dalilin zuwanta. Dariya ta fara ƙyalkyalewa da shi kafin ta ce
"ina kwana, dama Sulaim ne yace na biyo ya kaini Makaranta a kekenshi"
kai ya girgiza mamaki da wayon ƙaramar yarinyar na kamashi, uwa uba ƙarfin halinta. Kafin yayi magana Sulaim ya fito da Kekenshi shirye cikin Uniform ɗin daya bambanta da nata color. kallon ɗaya ya yi wa Naila ya ganeta, duk ɓacin ran daya fito da shi sai ya nemi gushewa; "tana nufin zata iya ƙuntatamai kenan?" Ya tambayi kanshi.
Kai kawai ya jinjina ya na karkata Kekenshi mai kyau da tsada ta gefen da take tsaye. Dasauri ta ɗane tana sakin dariyar nishaɗi haɗe da ɗagawa mai Share harabar Gidan da ya saki baki hannu.
Gudun dayasa Naila sakin kuka da majina Sulaim ya ke yi da ita a kan kekenshi. Duk inda suka gifta sai an kalleta ma su dariya na yi. Kafin su isa Makaranta mazaunanta har ƙaiƙayi su ke mata. Bai ce mata komai ba bayan ta sauka ya bar wajen. Naila takai minti goma a tsaye tana kuka kafin ta shiga aji.
Sulaim ya ɗauka Naila zata gajiya amma sai ya ga kullum sai tazo. Tun hankalin mutanen Yankin ba ya kansu har kowa ya fara Ankara haka ma Mahaifinshi sai dai bai ce komai ba.
Tun ƙarfin halin Naila baya birge Sulaim har ya fara birgeshi, ya dawo kullum shi yake tsayawa a ƙofar Gidansu ya ɗauketa.
A ɗan kwanakin da suke zuwa Makaranta tare Naila ta fahimci Sulaim ba kurma ba ne Selective mutism ne. Tun yana yaro har ya kai shekaru huɗu bai iya maganar arziƙi ba, kuma a haka sai ya wuni baiyi magana ba musanman a cikin mutane. Ya na jin nauyin yin magana a wasu lokutan da ma wasu guraren. Da farko yawon kaishi Asibitocin wa su Yankunan Matar da Mahaifinshi ya aura tayi saboda son da takemai. amma duk inda taje amsa ɗaya ne ba sauyi.
Rayuwar neman kuɗi da kafawa zuciya ra'ayin riƙau na tsayuwa kan matsaya ɗaya tare da aikin ƙarfi tuƙurun da Mahaifinshi ya horar da shi a kai ne yaƙara duƙufar da maganarshi, saboda shima ba gwanin surutu ba ne kuma tare suke wuni su na aiki, idan ya dawo daga Makaranta. Sannan Abduh Dhahab ya keɓance shi daga Abota da kowa musamman da ya ga sunfara tsokanarshi da kurma. Tun Sulaim yana jin ƙiwiya da nauyin yin aikin ƙarfin ƙera Tukwanen da sukeyi har ya haƙura ya saba.
Sulaim ya fi jin daɗin saurarar maganganun mutane a kan ya yi. Daga Makaranta ba ya zuwa ko ina sai wajen sana'ar Mahaifinshi, sai zuwa filin wasannin ƙarshen Mako.
Sauraran hirarrakin mutane ba tare da ya tofa ba, ya taimaka ƙwarai wajen mayar da Sulaim Yaro na daban a cikin dubban Yara ƴan uwanshi saboda basirarshi.
Matsowar ƙarshen watan cin Kasuwar babban Yankin ne yasa ko ina ya ɗauki harama don kusan dukka mutanen Yankin kowa da abinda yake siyarwa don samun kuɗin shiga daga baƙin da suke shigowa.
Haka yake a Gidan su Sulaim da suke ginshiƙin Kasuwar gaba ɗaya. Ba ji ba gani suke ƙera Tukwanen dake ɗaukar idon duk wanda ya kallesu tare da kwaɗaituwar son mallakar su.
A gidan su Naila ma haka zancen yake. Mahaifiyarta kayan wasan Yara take ƙerawa na laka, irin su kwano, murhu, cokali, da randar ruwa ƙananu gwanin ban sha'awa, dukka na wasan Yara. Kuma da yawan gaske takeyin su amm baya kwantai duk sai an siyeshi.
Zuwan Naila Makaranta tare da Sulaim ya ƙara farfaɗo da zumunci a tsakanin Mahaifiyarta da Matar Mahaifinshi, tun da dama can akwai alaƙar jini amma Abduh Dhahab ya datseshi saboda hanata shiga wajen kowa da ya yi.
A tsakanin kwana huɗun da ya rage aci Kasuwar Zinare, Ɓakin fuska a manya motocin da ya zama abin kallo ga Mutanen Yankin su ka bayyana a Daular Sarki Hammam.
A ɓangaren Ɗayyib Ɗan uwa ga Abduh Dhahab kuma Aboki, Mahaifi ga Sufyan. Bai samu sakewa ba, har sai da aka bincikamai dalilin zuwan Baƙin kuma wajen wa suka zo? Ta hanyar Aminanshi waɗan da suke Bayi ne a Daular Sarki Hammam.
Bayan Sallar Magrib labarin Faɗuwar Ɗayyib ya riski Abduh Dhahab.
Ɗan jim Abduh ya yi, yana sauraran ɗaya daga cikin Aminan Ɗayyib da yasa su ka bincikamai zuwan ɓaki da kuma dalilin zuwansu da wajen wanda suka zo, bayannan kuma ya yanke jiki ya faɗi. Wanda ko shakka ba ya yi akwai abinda Ɗayyib ɗin ya shirya. A tsarin Abduh baiyi niyyar Aminta da ɓakin da suka zo ba, don ko ganinshi bai bari sunyi ba, tayaya zai kwashe dukka Tukwanen ZINAREN da mutane suke baro Yankunan su da jahohin su don siya, ya siyarwa da mutane ƙalilan bayan yasan bazai iya ƙera wa su Tukwanen ba kafin zuwan ranar? Bayason Darajar Yankin shi da Kasuwar da ya sha gwagwarmaya kafin kafuwarshi ya yi faɗuwar Tasa, amma yana ganin lokaci ya yi. Mai zai sa Ɗayyib ya yanki jiki ya faɗi mai hakan yake nufi.....✍🏻
***