2
🔥ZINARE🔥
SASAAL
Arewabooks@sasaal
02
★washe gari da zafin nama Sulaim ya ke yunƙurin fito da kekenshi, kalaman Mahaifinshi na ƙara sukar zuciyarshi.
"Ba a ranar da mu ka shuka iri, za mu girbi amfaninsa ba, dole sai mun jira kuma mu yi haƙuri, tare da yin aiki tuƙuru. Ka je Makaranta yau ma ba ni da kuɗin da zan baka"
Waɗannan kalaman su Mahaifinsa yake yawan nanata mai, duk lokacin daya miƙamai hannu da sunan ya ba shi kuɗin da zai siyi abu a Makaranta ko yin wa su uzururrukan da ba su zama tilas ba. Duk da ga kuɗin ya na ganin su muraran amma sisi ba zai iya ba shi ba.
Kamar kullum da haushin hanashi kuɗin da ya yi ya yaƙarasa fito da kekenshi ya bar Gidan.
Yanayin yadda ya ke tsala gudu a kan keken kwatankwacin ranar da ya fara ɗaukarta ya sa ta ƙanƙameshi da siraran hanayenta da ko kusa ba su ratsa rabin cikinshi ba. A haka suka isa dogon ginin da ke kewaye da ajujuwan karatu. A hankali ya kwanto da keken duk da ba wani ƙato ba ne ta sauka. Idanuwanta ma su kalar tausayi ta ke kallon shi da shi, kafin ta ɗagamai ɗan ƙaramin hannunta. Kamar yanda ya saba bai ɗaga mata na shi hannun ba kuma bai ce mata komai ba, sai kanshi daya ɗan karkata gefe yana lumshe fararen idanuwanshi haɗe da jinjina mata kai. Murmushi da ya bayyana ƙananun haƙoranta ta saki, kafin ta nufi ajinsu da ɗan gudu tana ƙara waiwayarshi.
Shima murmushin da shi kaÉ—ai yasan yadda ya ke yin kayanshi da salo mai birgewa ya saki ya na juya kan kekenshi ya bar wajen.
Tarin Tukwane sababbun ƙerawa ma su kala mai kyan gani a ido da ƙwari a hannu ne jere a ƙaton filin. Lokaci ɗaya ido bazai iya ƙirga su ba saboda yawansu, Ƙira mabanbanta akayiwa tukwanen. Gefe guda kuma wani tsoho ne da kai tsaye duk wanda ya ganshi zai kirashi da mai rangwamen hankali, don ko a zahiri kasan ba wai tsufan shekaru ba ne, tsufar bautar da ya ke yi ne da kuma rashin tsaftace jiki. Fararen mutune ne a gefenshi su na cinikin Tkwanen da ya jera da harshen nasarar shi da ke fita fes.
A haka Sulaim ya dawo da kekenshi ya same su. Hannu ya É—aga musu haÉ—e rusunar da kanshi alamar gaisuwa kafin ya wuce aihinin cikin gidan su.
Yana ƙoƙarin sa ke fitowa cinikin su ya faɗa a kan idanuwanshi su ka zubewa Mahaifinshi kuɗi ma su yawan gaske. Mamaki sai ya kamashi maiyasa Mahaifinshi zai siyar da Tukwanen da jibi ne ranar cin kasuwar su? mai zai cewa mutanen da za su taso da ga maƙotan Yankunan su da mutanen Birni ma su zuwa sara? Dole yasan wata sabuwar wahalar zai ɗora mu su, su sake ƙera wa su Tukwanen, amma ta yaya hakan zai yiwu?
Ranshi a ɓace ya ƙara komawa cikin Gidan. Matar Mahaifinshi ya samu a ɗaki. Da hannu ya tambayeta ta san dalilin da ya sa Babanshi ya siyar da Tukwanen da za su fita kasuwa da shi jibi? Alamar ba ta sani ba ta yi mai kafin ta cigaba da aikinta. Agogon ɗakinta ya kalla ya na miƙe da sauri. Inda ya kalla itama ta kalla kafin ta bi bayanshi da kallo, tausayinshi na kamata.
Ƙwalla ne ya tararar idon Abduh Dhahab da su ka zama jajayen ƙarfi da yaji, saboda bautan da neman kuɗi da ya ke yi tsayin shekaru ba tare ya mora ko ya bari Iyalanshi sun mora ba, shi dai kawai burin shi cigaban Yankinshi. bayan tafiyar Baƙin shi ɗaki ya wuce da tarin kuɗin. Yanayin yadda ya samu fuskar Ɗayyib jiya na ƙara dawomai. Zuciyarshi da babu ɗigon rauni ko tsoro a baya sai burin kafuwar Yankinshi na yin yaushi, to amma ya ya zai yi? ba shi da zaɓi ko don ginuwar rayuwar Sulaim da shi kaɗai Allah Ya mallakamai.
A bakin makaranta Sulaim ya sa mu Naila da jakarta na buhu mai kyau saƙale a kafaɗarta. Bai ce mata komai ba ya kwanto da keken ta hau. Har suka ƙaraso ƙofar Gidan su da ya ke maƙota da na su Gidan bai ce mata komai ba. Ya na sauketa dasauri ta sa ɗan ƙaramin hannunta tana lalubar jakarta, kwandala biyu ta fito da shi ta na miƙamai,
"ga shi ka siya wani abun"
ta faɗa da ƙaramin muryarta na yaranta, ta na jiran amsar shi. Saboda sarai tasan ya na magana.
Ɗan mitsitsin hannunta ya kalla da kuɗin sannan ya girgiza kai alamar a'a ya na karkata kan kekenshi alamar tafiya zai yi. Ƙin matsawa ta yi daga gurin ta na kallonshi. Har ya fara tafiya ya kasa jurewa ya juyo.
Hannunshi ya miƙa mata alamar ta kawo kuɗin. Da sauri ta miƙamai ta na dariyar da ya bayyana jerarrun ƙananun haƙoranta. Shima murmushin bazata ne ya tahowa laɓɓanshi wannan dalilin ya sa yabar wajen da zafin nama.
Har ya rage saura kwana biyu aci kasuwa, bai ji mahaifinshi ya yi mishi zancen ƙera wa su tukwane ba, kuma bai ga alamun ya na da niyyar yin wasu ba, wannan dalilin yasa yafara zargin abubuwa dayawa har ya kasa runtsawa, musamman daya ga Mahaifinshi ya tattara duk uban dukiyar da ya ɗauki shekaru yana tarawa a cikin buhu ɗaya.
★Washe gari jikinshi sam ba ƙwari ya nufi ƙofar Gidan su Naila. Tana tsaye ta shirya tsaf cikin wankakkun uniform ɗinta. Ya na sauketa ya juya batare da ya kalleta ba. Sai taji sam ba daɗi a ranta, kafin ta haɗu da ƙawayenta ta manta da komai.
A na tashinsu ta taho da gudu, nan ma bai amsa mata gaisuwar da ya saba amsawa da gyaɗa kai ba, duk sai ta ƙarajin ba daɗi, jikinta ya yi sanyi.
Ya na sauketa ta fara lalubar jakarta, soyayyiyar Aya ta fito dashi mai yawa da ta siya kwandala biyu ta miƙamai. Bai karɓaba sai kallonta da ya tsaya yi.
"ga shi Yaya"
ta faɗa da tsoron yanayin fuskarshi. Murmushin yaƙe ya yi kafin ya ce
"Naila" da muryarshi mai tsada a wajen mutane da daɗin sauraro ga wanda ya samu ji. kanta da ɗago dasauri ta na washe ƙananun haƙoranta kafin ta ce "na'am"
"Idan kina so na karɓa to ki faɗi sunana na ji" ya faɗa yana kallon fuskarta. dariyar yaranta ta ƙyalkyale da shi, daɗi kamar ya sumar da ita, kafin ta ce. "Sulaim" ta ƙasara faɗa tana murmushi haɗe da rufe fuskarta. Shima murmushin fuskarshi ne ya faɗaɗa ya na kallon yadda take dariya kamar an bata aljanna. Hannunshi ya miƙamata, da sauri ta miƙamai Ayar ta na shigewa cikin Gidansu ranta fari fes saboda ya yi mata magana baki da baki, ba da kai ko hannu ba. Sannan ta matsu ta bawa ƴan gidan su labari.
Bayan ya zura Ayar da ta bashi a aljihunshi kasa tafiya ya yi sai da ya ɗan jima a zaune a kan kekenshi kafin ya bar ƙofar Gidan...
A daren ranar ma kasa runtsawa ya yi, saboda tunani da hasashen da bai san dalilin su ba. Ya na jin ƙewar Naila ba tare da yasan dalili ba ga fargaban dalilin da ya sa Mahaifinshi ya sayar da Tukwanen da zai fitar da su kasuwa washe gari ba tare da ya ƙera wa su ba.
Ƙarfe 2:00am ya ji alamar motsi, gefen Mahaifinshi da ya dawo kwana a ɗakinshi ya kalla ya ga alamar barcinshi ya yi nisa. Wani ƙaramin ƙarfe mai tsini da kaifi ya ɗauka ya soke a gefen ƙugunshi, kafin ya fara takowa tsakar gidan a hankali.
Yankan da ya sa shi buɗe dukka girman muryarshi aka yi mai a gefen kafaɗarshi na dama. Dole ya zube ƙasa zuciyarshi da gangar jikinshi na karɓar raɗaɗin azaba lokaci ɗaya.
"Au ashe iskanci ne dama ka iya magana?"
Wanda ya yankeshin ya faÉ—a ya na sakin dariyar mugunta. Tsaf ya É—auki muryarshi duk da ba ya cikin nutsuwarshi.
"Zan Barka a raye matsawar ka faɗamin ina Mahaukacin Ubanka ya ke" ya faɗa yana ɗagoshi. Shiru ya yi ya na kallon fuskarshi dake sakeye cikin baƙin ƙyalle. Ƙaramin wukar hannunshi yasa ya ƙara yankar gefen kunci Sulaim da ƙarfi haɗe da ƙara maimaita: " ina Mahaukacin Ubanka Abduh Dhahab ya ke, a ina ya zuba tarin dukiyar Tukwanen Zinaren da ya siyarwa Buzayen da su ka zo kwana uku da suka wuce? Su na ina!" A wannan karon Sulaim bai saki ƙara ba, sai zaburar dayayi ya soke shi da ƙarfen da ya soke a ƙugunshi a dai-dai saman kafaɗarshi tunda ya na da tsahon ƙafa.
"yaushe ya fara girban amfanin irin da ya sha wahala da azabar shekaru wajen shukawa, da har zakazo karɓan na ka kason!?" Sulaim ya tambayeshi da galabaitaccen muryarshi da azaba ta sa ya ƙara yaushi.
Sulaim Bai gama sauke hannunshi da haɗiye yawun kalamanshi ba ya ƙara yankarmai gefen kafaɗarshi na hagu haɗe da fesar da hucin haushin kalaman da Sulaim ɗin ya jefeshi da shi. Shima Sulaim bai zube ƙasa gaba ɗaya ba sai ya da ya zaro ƙarfen da ya sokamai a kafaɗa ya ƙara kafamai a tsakiyar cinyarshi da dukka ƙarfin daya rage mai. Kusan lokaci ɗaya su ka zube. Kowannen su na sauke numfarfashin azaba ga jinin da ya ke bin jikin kowanne su. Kasa jurewa Matar Mahaifinshi da ke laɓe ta yi ta fito ɗaga ɗakinta don tsaf ta haddace muryarshi itama . Da kuka ta fito ta na ba shi haƙuri. Ya na ganin fitowarta ya miƙe da sauri kamar ba shi ba, saboda hasashen mallakar dukiyar Tukwanen Zinaren da Abduh Dhahab ya ɗauki tsahon shekaru ya na bautar tarawa ba tare da ya bari ko shi kanshi ya mora ba.
Itama tambaya ya titsiyeta da shi ya na rintse idon azabar da ya ke ji, "a ina Abduh Dhahab ya ajjiye kuɗin Tukwanen Zinaren da ya siyarwa Buzayen da suka zo? kuma a ina ya ke ɓoye dukka dukiyarshi?" Shiru ta yi ba ta ce komai ba, sai kallon bayanshi da ya ga ta na yi. Bai kawo komai ba a ranshi ya ɗauka halin da Sulaim yake ciki ta ke kallo. Ganin bazata faɗa ba yasa ya kai mata hauri ta bugi bango da ɗaya ƙafarshi. Ya na juyowa yaga ba bu Sulaim da ya bari a wajen. Kenan Abduh Dhahab yan a gidan? maiyasa bai fara bincika ɗakunan Gidan ba tukunna?
"Abduh!!!!" ya faɗa da ɗan ƙarfi yana zare dukka girman idanuwanshi da su ka yi jajir
Fito ya yi, abokannan rakiyarshi da suka maƙale suna jiran umarninshi suka shigo. Biyu zama su ka yi ɗauremai ciwukan jikinshi bayan sun zare ƙarfen cinyarshi, ragowar kuma suka hau bincika gidan.
Sun samu ÆŠakin Abduh Dhahab da duk amintakarshi da Mutum ba ya bari ya shiga, amma babu ko sisi a ciki.
Hanyar da jini ya ɗiɗisa su ka dinga haskawa su na bi, har suka samu ta inda Abduh Dhahab da Ɗan shi suka fita, ta ƙofar da ba su san da shi ba. Zabura ya yi ya na haska ƙofar bayan da Abduh Dhahab ya bi har zuwa inda jinin ya tsaya. Dariya yaƙen azabar da ke nuƙurƙusarshi ya saki ya na kutsa kai cikin gidan bayan sun ɓalla ƙofar Moƙocinshi kuma Amininshi da suke kyautata zaton nan ya shiga.
Da matar gidan su ka cinkaro tana salla a tsakar gidan. Bai amsa tambayoyin da ta ke jero mu su na dalilin shigo mata gida kai tsaye ba ya ce:
"Sarah! Ina Mijinki ya ɓoye Abduh Dhahab da Ɗan shi? Asibiti ya kai shi, ko su na cikin Gidannan? kifaɗamin gaskiya ko na wulaƙantaki" ya ƙarasa faɗa ya na ƙare mata kallo ta hasken farin watan daya haske gidan. Da sunan Ubangijin da take ambata ta yi jarumtar furta "Mallam ba ya gari, ya tafi Fansar Litattafai, Asibitin kuma sati ɗaya kenan ba a yi aiki a ciki ba"
dariya su ka bushe da shi don ko a ranar sun ga mijinta. Ƙasan Gidan ya haska ya na kai dubanshi dai-dai wajen da Jinin da ya ɗiɗisa har zuwa inda ya tsaya. Dai-dai inda Mallam ya ke ajjiye keken hawarshi har guda biyu ne. Dariyar ƙeta ya sa kafin ya ce. "ashe Mallam mai Asibiti da zai fita da dukka kekunanshi ya fita Fansar Litattafai kenan? Ki faɗa min wanene ya tuƙa ɗaya keken?" Kai ta girgiza haɗe da yin duk addu'ar dayazo bakinta.
"Wallahi kinji na rantse idan baki faɗamin gaskiya ba zan ƙona gidanan da ke da ƴaƴanki gaba ɗaya." kuka tasa ta na roƙonshi da magiya kala-kala.
Ganin ta na ɓata mu su lokaci ya sa ya ce a ƙona Gidan tunda taurin kai ne da ita. Ta na jin haka ta ce Abduh Dhahab ya zo da Ɗan shi amma sun tafi Asibiti. Dasauri ya ce: "ya zo da kuɗi?"
"Bansaniba amma dai yazo da buhu mai girma da abu a cik.." bai bari taƙarasa ba su ka bar Gidan.
Ko da sukaje Asibitin Mallam, ba bu Abduh Dhahab da Sulaim kuma ba bu ko sisi sai Mallam da su ka samu yana ƙoƙarin dawowa Gida.
"A wani ɗakin ya ɓoye Abduh Dhahab da Ɗanshi da kuma dukiyar da ya ƙullo a buhu?"
Shiru Mallam ya yi kamar kurma. Sunfi minti 15 su na ta tambayar shi kafin ya basu amsar Abduh Dhahab yana cikin Asibitin da dukiyarshi. A wani sashe na Asibitin? kuma a wani ɗaki? Tunda Asibitin ba laifi ya na da girma. Shiru ya yi yaƙi ba su amsa kuma ba bu inda ba su duba ba babu Abduh Dhahab kuma sun kasa gano shaidar ɗakin da zasu sameshi ga dai keken Mallam daya tuƙo a gefe jini duk ya ɓatashi. Kuma Mallam ya kafe Abduh Dhahab na cikin Asibitin da ɗanshi da dukiyarshi. Ganin kamar raina mu su hankali haɗe da son tona mu su asiri ya ke son yi. Sai suka turashi cikin Asibitin su ka kulle.
Suna fita Matar Mallam ta tattara Æ´aÆ´anta su ka nausa hanyar Yankinsu a cikin daren kamar yanda Mallam ya umarceta kafin ya zo ya samesu.
Kashedi mai zafin da ya kai ga guntulewa Matar Abduh Dhahab Æ´an yatsu su ka yi mata bayan sun tabbatar da sawa Asibitin da mutanen ciki wuta, tare da yashe duk wasu dukiya da suka samu a É—akinta na tarin kuÉ—in la'adar da Abduh Mijinta yake biyanta idan ta tayasu aiki.
★washe gari labarin gobarar Asibitin Mallam, da Mutuwar Mallam da Abduh Dhahab da Ɗanshi Sulaim ya karaɗe Yankin gaba ɗaya.
Duk da a kwai waÉ—anda suka É—an ji abinda ya faru a cikin daren, amma sun kasa magana, kowa ya ja bakinshi ya tsuke, tunda matar Abduh Dhahab bata farfaÉ—o ba tun da ga daren zuwa wayewar gari balle ta faÉ—i sunan waÉ—anna su ka aikata a É—auki mataki a kansu, kamar yanda Sarki Hammam ya ba da shela.
A wannan ranar kasuwar da Abduh Dhahab ya sha gwagwarmaya shekaru kafin kafuwarshi na siyar da Tukwane ma su Taken Tukwanen ZINARE don cigaban Yankinshi ya yi faɗuwar tasa da ba'a taɓa tunani ba. Domin duk wanda ya zo ya ji mutuwar Abduh Dhahab ba ya iya tsayawa siyan komai ya ke juyawa inda ya fito. Dubban mutanen Yankin sun tafka asarar abincin siyarwa da su ka dafa da sauraran kayan amfanin da suka sarrafa don siyarwa baƙin da suke shigowa.
Anya mutuwar Abduh Dhahab bazai kawowa yankin su Talauci mai ƙarfi da koma baya ba kuwa? tunda sun a samun kuɗin shiga ta hanyar abubuwan da suke sarrafawa su siyarwa Baƙin da su ke shigowa ta hanya mai sauƙi, ga kuɗin hayar masauƙin da suke samu da ga wajen baƙin da suke zuwa daga nesa. Dukka wannan ya rushe kenan?
Ta fi minti Talatin a tsaye a harabar Gidan su Sulaim ta na jiran fitowarshi, bayan tasha kukan daya ɓata Baby face ɗinta da hawaye da majina. Don ita bata yarda Sulaim ya mutu ba. Daƙyar Babanta ya janyeta shima na shi ran na suya.
An samu Gawar Mutum huɗu da suka ƙone ƙurumus bakyan gani don babu fuskar wanda aka gane balle a banbance. Ɗayyib na kwance lulluɓe cikin abin rufa sai kuka da ihu ya ke yi jikinshi na rawa, haɗe da sabbatun su fito mai da Abokinshi Abduh Dhahab, wallahi bai yarda Abduh Dhahab ya mutu ba, wanene ya kashemai Abduh Dhahab Aminin ƙwarai?????....
***