ZINARE🔥

3

by @nafisatusasaal01

🔥ZINARE🔥

     SASAAL

         03

A fadar Sarkin Hammam aka sallaci gawarwakin da shi kanshi Sarki Hammam ɗin ya jagoranta. Kafatanin Mazan Yankin ne sukayiwa gawarwakin rakiya zuwa makwancin su. Kafin dawowar su Dangin Mahaifin Mairam (matar Abduh Dhahab) sun zo sun ɗauketa saboda gudun abinda zai biyo baya.

Bayan awannin da binne su Abduh Dhahab, sai gaba ɗaya mutanen Yankin suka koma zancen asarar da suka tafka, ba tare da sun ƙarabi takan abinda ya yi makasudin ajalin Abduh Dhahab da Ɗan shi har ma da Mallam ba. Wannan lamari ya yi matuƙar sosa ran Dajjito Junaid. Junaid ɗaya daga cikin Dattawan Yankin ne, kuma na hannun daman Sarki Hammam.

★washe gari Dattijo Junaid ya yi tattaki har ƙauyen su Sarah Matar Mallam. Ya sameta a mawuyacin hali mai ban tausayi, iyayenta sun karramashi tare da bashi abin sha don jiƙa maƙoshi. Tambayar duniya Sarah taƙi faɗar waɗanda suka zo gidanta neman Mallam, ƙarshe da Dajjito Junaid ya matsa mata kuka ta fashe da shi raɗaɗin kisan gillar da akayiwa Mijinta na cigaba da sukarta. Ta yaya zata faɗa bayan tasan za su bibiyeta. 

Har yammaci Dattijo Junaid bai bar Gidan su Sarah ba. A kan idonshi Iyayen Sarah da ita kanta da ƴaƴanta suka fito da kayayyakin su don yi balaguro tunda sun san dole a bibiyi ƴarsu gudun kar ta faɗi gaskiyar abinda ta sani.

 Hawaye Dajjito Junaid ya share ya na bin bayan su. Cikin taushin harshe da amon dake bayyana irin raɗaɗin dayake ji a ƙasar zuciyarshi ya ce

 "Sarah tunda bazaki bani ƙarin haske akan abinda ya faru ba, ki taimaka ki faɗamin inda Mallam yake samun taimakon inganta babban Asibitin mu, da kuma Makarantun ƴaƴamu na roƙeƙi" ya ƙarasa faɗa yana haɗa fararen hannayenshi waje ɗaya alamar roƙo. Tsayawa Sarah ta yi zuciyarta na karyewa tsananin tausayin Abduh Dhahab da Sulaim na bijiromata. Sai da ta tattaro dukka jarumtar daya bata dama shanye kukan dake neman cin ƙarfin maganganun da takeson faɗa sannan ta ce "Abduh Dhahab shi ne wanda ya gina makarantu da Asibitin daya bawa Mallam amana bayan ya roƙi Mallam ya yi mishi alfarmar kar ya bari kowa ya sani har sai idan shi ya buƙaci hakan da kanshi. Ya ƙare rayuwarshi da Ɗan shi wajen bauta muku da son ganin cigaban Yankinku, amma duk da haka sai da kukayi sanadiyar ajalinshi. Tir! da wannan Yanki na ku" ta ƙarasa faɗa tana fashewa da kuka haɗe da barin Dajjito Junaid tsaye da sakekken baki. 

Tafiya yakeyi da iya ƙarfinshi amma sai yake ganin kamar baya sauri, burinshi ya isa Yankinshi ya ba su labarin da zai dawo da su hayyacinsu su binkico shaiɗanin dayayi sanadiyar rushewar Yankin su. 

Lokacin da Dattijo Junaid ya iso Yankinsu da labarin alkhairin Abduh Dhahab ba bu wanda ya saurareshi balle ya yarda da shi

"ta yaya Abduh Dhahab dayake mayen kuɗi, zai yarda ya bautawa Yankinshi da dukiya mai yawa irin wannan? Kawai ƙage da rashin son zaman lafiya Dajjito Junaid yake son kawowa Yankin su" wannan shine surutan da sukai tayi har da masu kwashemai albarka. 

Duk da haka Dajjito Junaid bai gajiya ba washe gari ya ƙara ɗaukar harama ya na shela layi-layi.  "Ya ku mutanen Yankin Tudu! Ina jiyemuku ranar nadamar da zakuyi nan gaba da kuma talauci mai raɗaɗi da azabar da zai riskeku matsawar kukayi butulci baku tsaya tsayin daka wajen ganin an binciko waɗanda suka kashe Abduh Dhahab da Iyalinshi ba, lallai sakayya mai raɗaɗi yana nan zuwa garemu, matsawar kuka yofintar da zance na, to kowa a cikinmu zai ɗanɗana kuɗarsa wata rana. Wannan rana nake jiyemana mutanen Yankina" 

leƙoshi sukeyi  wa sun su na dariya tare da yin Allah wadai da kalamanshi.

"ai mu Abduh Dhahab ya cuta, tunda dama sihiri ya yi wa Kasuwar Zinaren da idan ya mutu Kasuwar da ya gina shima zai mutu baza mu moraba" wannan shine kalaman ɓatancin da suke jifan Abduh da shi bayan saurarar maganganun Dattijo Junaid. 

Har a fadar Sarki Hammam sai da Dajjito Junaid ya yi magana, a nan aka samu waɗanda hankalin su yafara karkata kan anya labarin da Dattijo Junaid ya zo dashi ba gaskiya ba ne ba kuwa? Haka a ɓangaren Sarki Hammam ɗari bisa ɗari ya yarda da zancen Dajjito Junaid har ya bada tabbacin ƙara ƙarfafa binciken waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin. Dama ya daɗe yana kokwanton wanda Mallam ya faɗa suke ɗaukar nauyin dukka ayyukan tun farkon buɗe Makarantun da Asibiti, da yanda ake biyan ma'aikatan jinya da malaman Makaranta albashi akan lokaci, da yanayin kulawar da ma'aikatan suke samu duk ba iri ɗaya bane da wanda gomnati take ɗaukar nauyi. 

 Ragamar binciken komai Sarki Hammam ya miƙa a hannun Dattijo Junaid. A wannan ranar da tsananin farin ciki Dajjito Junaid ya nufi Gida.  

Dattijo Junaid bai runtsa ba har sai da ya fara kamo bakin zaren abinda yake zargi.

A Yammacin wata Laraba ya shirya kaiwa Sarkin Hammam ziyara, don gabatar da shaidun da zai ƙara buɗe idon mutanen Yankin har su bashi goyon baya wanda ya yi dai-dai da cikar su Abduh Dhahab sati biyu a kaburburan su. Kafin ya buɗe gidanshi anrigashi buɗewa.

★washe gari, har rana ta fito Ba bu wanda yaji ɗuriyar Dajjito Junaid da Matarshi dama kuma Allah bai ba su haihuwa. Wannan dalilin ya sa aka ɓalla Gidan tunda ana da tabbacin su na ciki. Cikin jinin daya bushe aka samu Dattijo Junaid da wuƙa soke a gefen cikinshi bakinshi ma jini duk a bushe ko da suka duba bakin anyanke mai harshe. Tsohuwar Matarshi kuwa tana Ɗaki a kulle tsoro da tashin hankali ya daɗe da sumar da ita. Mamaki da tsoron ne ya dirarwa mutanen Yankin Tudu, amma dayake yawancin su ma su ƙaranci tunani da kuma hangen nesa ne, sai suka fara surutun

 "ai shi ya jawowa kanshi, tunda ya ce shi bazai kama bakinshi ba"

 Ba bu wani cikakken damuwa ko alhini a zuƙatan mafi akasarin su wannan ya sa suka cigaba da harkokin gabansu, tare da alƙawartawa kansu jan bakunansu su yi shiru tunda ba su shiryawa mutuwa ba, don babu wanda yaji ko da ihun naiman taimakon su Dattijo Junaid da Matarshi balle su sa ran idan sunyi ihu za su yi iya samun taimako.

Cikin hikimar Ubangiji numfashin Dattijo Junaid ya dawo cikin tsananin azabar rayuwa ko mutuwa tunda Allah bai ƙaddara ajalinsa a hannunsu ba. Itama iyalinshi ta farfaɗo banda kuka babu abinda take yi. Keɓantaccen wajen da babu mai shiga sai Sarki Hammam da  likitan da zai dinga duba lafiyarshi Sarki Hamman ya tanada tare da kashe maganar bincike akan kisan su Abduh Dhahab. Ba bu wanda ya gamsu da maganar Sarki Hammam saboda sun san dole yayi bincike ta ƙarƙashin ƙasa. Don haka waɗanda suke da alhakin kisan suka shiga tararrabi tare da fara tunanin ƙirƙiro abinda zai kawar da hankalin mutanen Yankin da shi kanshi Sarki Hammam ɗin.

Naila tun tana sa ran wata rana Sulaim zai dawo har ta gaji da cire rai, sai dai Gidan su ya koma dandali taruwa Yara abokannan wasanta tana ba su tahirin rayuwarta da Sulaim, har da tatsuniyoyi ta ƙirƙira  na labarinta da Sulaim. Ba ta fita wasa kullum tana Gida kamar ba Naila mai son wasa da neman tsokana ba.

A cikin watanni biyu da mutuwar Abduh Dhahab wani gagarumin Talauci yafara kunnowa Yankin kai. Rana ɗaya suka wayi gari babu Malaman Makaruntun su, Asibitin Mallam da Sarki Hammam yasa aka gyara dukka ma'aikatan jinyar sun gudu. A cikin yini biyu Mutane biyar suka rasa ransu saboda rashin ma'aikatan jinya. Ba bu wani Ɗan Yankin Tudu da hankalinshi bai tashi ba, ciki har da Ɗayyib da bai jima da samun sauƙi ba.

 A rana ta uku Mahaifin Naila da ya tashi da tsananin ciwon ciki shima ya rasa ranshi zuwa yammaci duk da maganin gargajiyan da akayita ɗirkamai don sun je Asibitin Gwamnati ba ma'aikata. Asibitin Mallam dama tuni aka rufeshi tunda dukka ma'aikatan sun gudu. Rasuwar Mahmoud Maihaifin Naila wani babban gibi ne mai girman gasken da basu da abin maye gurbinshi, har abada.  A cikin watannin da suka biyo baya wani irin Talauci ya yi wa Yankin mamaya mai ƙarfin gaske, ga shi babu wadataccen ilimi ba bu Ma'aikatan lafiya masu sanin makamar aiki. Zuwa Lokacin Dattijo Junaid ya samu lafiya amma babu damar yin magana. 

Suna cikin wannan yanayin Abdullah ya bayyana  a matsayin ƙwararren Likitan da Gmannati ta turo. Cikin iko Allah marasa lafiya suka fara samun kulawa ta musamman. Mutanen Yankin sun sakin jiki da Abdullah tare da wani irin so da sukeyimai saboda sauƙin kanshi da iya mu'amalar shi. Wannan dalilin yasa ya buɗe aji koyawa Matasan da suka kai shekaru 18 mata da Maza dabarun kula da mara lafiya da karɓar haihuwa cikin Hikima a keɓantaccen Gidan da Sarki Hammam ya bashi. Da kayan aikin dayazo yake koyawa mu su. Kafin rufuwar wata biyu wasun su har sun ƙware, a hankali labarin alkhairin Abdullah ya fita ko ina na Yankin sai ya zamana har a maƙotan Yankin su ana zuwa ɗaukar Matasa wala Namiji ko Mace don duba majinyaci ko karɓar haihuwa. Cikin lokaci ƙanƙani talauci Yankin ya fara raguwa walwalarsu ya fara dawowa.  

A cikin watanni shida Abdullah ya yaye Ɗalibansa haɗe da ƙara ɗiban wa su. Sarki Hammam da Dattijo Junaid baƙaramin alfahari sukeyi da Abdullah ba, girmamashin da suke yi ma na daban ne. 

A na cikin haka aka tsinci ƙaramar Yarinya anyi mata fyaɗe mara kyan gani a bayan Ofishin Abdullah. 

Duka na rashin imani da manta halacci sukayiwa Abdullah. kafin sanarwar ya isa fadar Sarki Hamman har sun sumar da shi. "Wani irin ƙwaƙwalwa ne a cikin kan Mutanen Yankin Tudu, kuma wacce irin zuciya gare su mai tsanin butulci da manta alkhairi? Ta ya ya Abdullah zai iya yiwa Yarinya ƙarama fyaɗe na rashin imani irin wannan? shin ina hankalin su yake? Maiyasa ake amfani da toshewar basirar su wajen sa su su dakushe cigaban Yankin su da kansu batare da sun sani ba?" Dattajo Junaid ya tambayi kanshi zuciyarshi na Suya. Asibiti Abduh Dhahab daya jima a rufe aka nufa da Abdullah rai a hannu Allah. Duk da haka Mutanen Yankin basu haƙura ba gangami sukayi har Asibitin suna faɗin abi mu su haƙƙinsu, a cikin su har da waɗanda Abdullah ya koyar kuma suke samun alheri. A cewar su "dama sun san dole akwai wanda ya turoshi don cin mutuncin Yankin su" Daƙyar fadawan Sarki Hammam suka fatattakesu da bulalai.

★washe gari aka tashi da labarin guduwar Abdullah daga Asibiti bayan ya farfaɗo, wanda fadawan Sarki Hammam suka bada shedar wani ne yazo da sunan dubanshi shikuma Abdullah ya yi mishi rakiya a daddafe zuwa  motar daya zo dashi  gabannin Asubahi daganan kuma basu ƙarajin ɗuriyarshi ba. 

Labarin sam bai yiwa Wa su marasa goyon bayan lamarin daɗi ba musanman Sarki Hammam da mutanenshi. Dattijo Junaid kuwa har da kukanshi.

Labarin Tafiyar Abdullah har wajen Yankin wannan sai ya sa musu baƙin jini tare da kafa tsoron su da ƙyaƙyamin kulla alaƙa da su a zuƙantan maƙotan Yankin su.

A wannan yanayin Mahaifan Maman Naila suka zo ɗaukarta tunda ta gama Takaba. ko da aka buƙaci su tafi da Naila tunda Yarinyarce, ƙin amincewa sukayi bayan baƙaƙen maganganun da suka gasawa  Mahaifiyar Mahmud kakar Naila tare da yin Allah wadai su tafi Yankinsu da jinin mutanen Yankin Tudu.

Dole Naila ta koma wajen Kakarta da zama bayan kukan da ta sha har da zazzaɓi.

Cikin watannin da suka biyo baya suka ƙara komawa Talaucin da yafi na baya muni da raɗaɗi. Ga ƙyama da suke fuskanta daga dukka ƙabilun dake kewaye da su, ko Aure ɗan Yankin Tudu yaje nema ba'a ba shi.

Rana ɗaya dukka matasan Yankin suka yi zuciya suka koma Gona har da Ƴaƴa mata saboda raɗaɗin Talauci da rashin abin yi. Don ko aure Mazan Yankin suka fita nema a mokatan Yankin su ba'a ba su, balle su yarda Ɗan su ya auro mu su Ƴar Yankin Tudu. Wannan dalilin yasa suka fara auren Junansu cikin tsananin Taulauci.

Bayan amfanin Gona ya yi, suka fara fita dashi kasuwanni Yanki-Yanki. Abin mamaki duk Yankin da suka kai ba'a siya sai su ce "Allah Ya raba su da cin kayan amfanin gonar mutanen Yankin Tudu" kamar waɗanda sukayi bar ruwa da guba haka Kayansu ya koma a idon Mutane. Ko wani bare daga wani ɓangaren da bai sansu ba ya yi niyyar siya sai aja kunnenshi da kar ya kuskura idan ba haka ba kuwa, tamkar ya kirawa kanshi mutuwa ne.

Mutanen Yankin Tudu suna ji suna gani suka ƙara komawa Talaucin dayafi na da raɗaɗi da azaba

Suna cikin wannan yanayin Salman ya shigo Yankin a matsayin mai koyar da sana'o'i...✍🏻

***