ZINARE🔥

4

by @nafisatusasaal01

🔥ZINARE🔥

      


        SASAAL

        
         04

Bayyanar Salman a Fadar Sarki Hammam a matsayin mai koyar da Sana'o'i ya yi matuƙar faranta ran Mutanen Yankin, saboda ya zo akan gaɓar da suke tsananin buƙatar ire-iren shi.

Ɗayyib ne ya kawo shawarar maizai hana a kai Salman Gidan Abduh Dhahab da tun bayan Mutuwarshi yake a garƙame a matsayin Masauki. Ba bu jaa kowa ya yi na'am da shawarar Ɗayyib tunda Salman ya ce shi Maƙeri ne.

Da tsananin Farin ciki da wani ƙauna mara iyaka Ɗayyib ya nufi Salman bayan ya gama kallon irin Tukwanen da Salman ƙera. Rungumeshi ya yi kafin ya sumbaci gefe da gefen kunchinshi.
"A ina ka koyi ƙera irin Tukwanen da Aminana Abduh Dhahab yake ƙerawa. Tun bayan mutuwar Abduh muka shiga wani yanayin na ƙangin rayuwa, saboda mutuwar Kasuwar Tukwanen Zinaren da yasha wahala kafin kafuwarshi, ba bu wanda ya yi hikimar koya a cikin mu daga Abduh Dhahab sai Ɗanshi Sulaim ne kawai suka iya ƙerawa. A baya munfidda rai da ƙarasamun rayuwa mai daɗi sai gashi Allah Ya Kawo mana kai. Alhamdulillah!" Ɗayyib yaƙara faɗa ƙwalla na kwanciya a ƙasan fararen manyan idanuwanshi.

Salman bai ce komai ba sai murmushin shi daya faɗaɗa yana komawa wajen Tukwanen daya ƙera.

Bisa Umarnin Sarki Hammam Fadawanshi suka dinga bi layi-layi suna shelar Bayyanar Salman a matsayin mai koyar da Tukwanen Zinare sak irinna Marigayi Abduh Dhahab. 
Nan da nan farin ciki ya mamaye zuƙatansu, maimakon su godewa Allah su ƙara sanin amfanin Marigayi Abduh Dhahab a Yankinsu sai suka hau Sukarshi da ce wa "Allah Ya sa wannan ba irin Abduh Dhahab ba ne mai mugun zuciyar da zai yi sihirin da Kasuwar Tukwanen Zinaren zai ƙara rushewa idan bayanan"  da ire-iren waɗannan kalaman suke ta sukar Marigayi Abduh.

Ba su tsagaitaba har sai da labari ya jewa Sarki Hammam. Da kakkausar Murya ya yi gargaɗin duk wanda yaƙara sukar Abduh Dhahab abisa son zuciyarshi to zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Ba bu kunya mutanen Yankin suka cika gidan Abduh Dhahab, Yara da Manya, Maza da Mata.

Da wani irin takaici Ɗayyib yake kallon Sufyan, ba don kalamanshi suna yimasa daɗi ba ya cigaba da saurararshi.

"Baaba tayaya zan koyi ƙera Tukwane da wannan kyan nawa? Baabah ba ƙera Tukwane ne ya dace da Matashi kyakkyawa irina ba. Ni burina shine naje Babban Birni nayi Karatu mai zurfin da  zai kawowa Yankina cigaba, amma ba koyan ƙera Tukwane ba gaskiya" Yaƙarasa faɗa yana yin ƙasa da kanshi da suma baƙi mai laushi ke kwance luf.

Tabbas! Ɗanshi Sufyan kyakkyawane amma idan aka haɗa kyanshi da na Sulaim daya ƙare rayuwarshi wajen bautar ƙera Tukwane to tabbas Sufyan ɗin ba komai bane.
Da taushin Muryar da yake burin Sufyan ɗin zai fuskanceshi har yagane abinda yake yimai kwaɗayi ya ce;
"Sufyan Idan har Sulaim da Allah Ya yi baiwar kyau ninkin baninkin naka zai ƙare rayuwarshi wajen ƙera Tukwane bisa umarnin Mahaifinsa, to banga dalilin da zai hanaka bin nawa umarnin ba. Sana'a baya hana karatu sai dai ma ya taimaka wajen ragewa Iyayenka ɗawainiya kuma kai kanka sai ka fi jindaɗin kayiwa kanka abu batare da ka jira an ɓata maka lokaci ba. Kaje kayi shawara da Mahaifiyarka amma kasani idan har ka saɓawa umarnina to babu ko sisina a harkar neman Iliminka."

Sufyan ba a iya Cikin zuciyarshi yake jin raɗaɗi ba har a kan fuskarshi.
Yaushe labarin kyan Sulaim zai gushe a zuƙantan mutanen Yankin. Ya na son ace yana da kyau duk da yayi imanin shi ɗin kyakkyawane, don matan Yankinsu da na maƙotan Yankinsu har so suke yi yayi musu magana. Amma duk wannan yabon kyan na shi da sukeyi da zarar hirar Sulaim ya ratso sai su hau ƙodashi da faɗin da Sulaim ya girma a raye to da babu wani Matashi da zai kamoshi a kyau a kaf faɗin Yanki a wasu lokutan ma sai su ce har da maƙotan Yankunansu, duk ranar da irin haka ya ratso a gabanshi ko labari yazo kunnenshi yini yakeyi yana kallon ƙaton madubin Gidansu. Mahaifiyarshi mai taya ɓera ɓari tana ƙara zugashi da cewa "ba wai su na zuzuta kyan Sulaim ba ne don dagaske ya na kyan ba, sai don Tukwanen Zinaren da Mahaifinshi ya ƙirƙirowa Yankin, idan shima yaje Babban Birni Ya yi karatu mai zurfin da kaf Yankin ba bu mai kwatankwacinshi to ba shakka shima zai zama abin kambabawa, kar ya kuskura ya yarda da batun Sana'ar da Mahaifinshi ya jima yana burin ya yi, idan ba haka ba Sulaim shi zai cigaba da zama Saurayi mafi kyau a Yankin duk da baya raye, idan ma ya lura sun mayar da labarin kyan Sulaim kamar wani Tarihin da suke kambawawa. musamman ga waɗanda ba su sanshi ba" har alƙawarin auren gata tayimai da wacce zata bauta mai kamar Sarki idan har ya cikamata burinta na zuwa Babban Birni karatu.

 Waɗanan huɗubobin da su Sufyan yake kwana kuma yake tashi.

A ɓangaren Mutanen Yankin ma su koyan ƙera Tukwane a wajen Salman sosai suka nuna jajircewarsu da farko amma da tafiya tai tafiya sai suka fara nuna gajiyawarsu har sai da Salman ya zaburar da su da kalaman asalin wanda ya ƙirƙiri Tukwanen " Ba a lokacin da muka shuka iri, zamu girbi amfaninshi ba dole sai munjira kuma munyi haƙuri tare da yin aiki tuƙuru" waɗannan kalamai na Salman baƙaramin tsoratar da Mutanen Yankin ya yi ba, musamman ga waɗanda sukayiwa Abduh Dhahab farin sani. Tsoron kar su wayi gari wata rana suka babu Salman don sun fi alaƙanta shi da aljali saboda kalamansa masu kamaceceniya da Abduh Dhahab yasa suka ƙara zage damtse.

Labarin kamaceceniya kalaman Salman da Abduh Dhahab dayake yawo a gari har kunnen Naila da Kakarta. Naila data kasa samun sukuni a sace ta tafi Gidan ba tare da sanin Kakarta ba. 

A ranar zuwan Naila na uku Salman ya kamata.
"Maiyasa kullum kike zuwa ki maƙale kina kallona, mai kike nema?"
Salman ya tambayeta yana kallon cikin idonta.

Murya na rawa Naila ta ce "inaso nasan labarinka, inaji a jikina kamar Kanada alaƙa da su Sulaim, shin dagaske Sulaim yaƙone bazai ƙara dawowa?" 

Kamar  wanda ya ke son haddace halittun fuskarta haka Salman yake kallonta kafin ya ce
" Ki je nan da Sati biyu ki dawo zan baki labari" ya ƙarasa faɗa ya na turata waje haɗe da kullo ƙofar Gidan.

Daga wannan rana Naila ta fara lissafin kwanakin da Salman ya ɗebarmata ba tare da sanin Kakarta ba.

A ɓangaren Mahaifiyar Naila tun bayan komawarta Yankinsu ita take kula da Mairam Matar Abduh Dhahab, kullum su na tare sai dare take dawowa gida. Mairam tana samun sauƙi amma kullum a cikin kuka take ba magana. Ranar da ta buɗi baki ta tambayi Ruwa, gidan ruɗewa sukayi da farin ciki ba iya su kaɗai ba har mutanen Yankin da labari ya je wa. Murnar fara maganar Mairam kaɗan-kaɗan yasa Mahaifiyar Naila yanke shawarar kwana, acewarta "kwana zamu yi muna hira" ta ƙarasa faɗa tana dariya.

A daren ranar aka kawo mummunar harin da ya faɗa kan Mahaifiyar Naila. 

★washe gari kuka Kakannin Naila suka ƙanƙame juna sunayi mai raɗaɗi da ciwon gaske lokacin da sukayi ido biyu da gawar ƴarsu. Ga shi Mairam da Mahaifanta sun gudu tun Asubahi.

Gangami Kakan Naila ya yi da Mutanen Yankinsa har Fadar Sarki Hammam, don suna kyautata zaton fara maganar Mairam ne yasa suka zo kasheta don karta faɗi abinda ta sani tsautsayi ya faɗa kan ta su ƴar. 
Maganganun ma su nauyi a harshe da raɗaɗi a zuciya Kakan Naila da mutanen Yankinsa suka zazzage a Fadar Sarki Hammam. Zafin kalamansu dayake nuna cin fuska ƙarara ga Sarki Hammam yasa Fadawanshi nufarsu da manyan bulalai.

Sarki Hammam dakatar da su ya yi, sannan ya yi wa Kakan Naila alƙawarin yin adalci matsawar ya bincika ya gano dagaske da hannun Mutanen Yankin shi akan kisan gillar da akayiwa Ƴarsu to zai hukuntasu dai-dai da abinda suka aikata. 

Da wannan yarjejeniyar Kakan Naila da mutanensa suka bar Yankin, ko kallon Naila dake kuka kamar ranta zai fita basu yi ba.

Naila da taje da Kakarta Yankin Mahaifiyarta ko wajen zama ba'a basu ba, a cikin bainar jama'a suka ce sun yafe ta, babu su babu ita, kuma karsu ƙara ganin ƙafarta a Yankinsu.

A yammacin ranar sai da Sarkin su yaje har Yankin Tudu duk dai akan kisan gillar Mahaifiyar Naila, alƙawarin da Sarki Hammam ya yiwa Kakan Naila shi yaƙara yiwa Sarkin su. Bayan Sarkin su ya dawo ya tattauna da Kakan Naila. A take Kakan Naila ya yafewa Iyayen Mairam tunda tafiyar tasu shine nutsuwar su da na Mutanen Yankin gaba ɗaya.

Naila bayan sun koma Gida zazzaɓi mai zafin gaske ne ya rufe ta har bata gani da kyau. A haka tasha jinyar da tayi sati Uku a kwance. Bayan ta wartsake ta tuna alƙawarinta da Salman sai dai babu damar zuwa saboda a ranar ake bikin sake buɗe Kasuwar Tukwanen ZINARE.

Kowa na Yankin bakinshi a washe yake, saboda dawowar Kasuwar Tukwanen Zinare babban nasara ne gare su baki ɗaya.

Haniyar kowa da murnar kowa ya tsaya cak ne lokacin da Salman yake ƙoƙarin sanar da Shugaban Kasuwar Tukwanen ZINARE. Kowa burinshi ace shine ko wani nashi.

A bisa tattaunawar da Salman ya yi da Sarki Hammam bayan sun gama cin liyafar daya gayyaceshi ana saura kwana ɗaya a buɗe kasuwar ya sanar da ƊAYYIB a matsayin shugaba DATTIJO JUNAID kuma mataimakinshi. 

Hayaniya ne ya ɓarke wasu suna ganin Dittijo  Junaid da baya iya magana bai cancanci ya zama Mataimakin Ɗayyib ba, wa su kuma daga Ɗayyib har Dattijo Junaid ɗin duk basa so. A haka taro ya watse wasu sun rai a ƙuntace da alwashi kala-kala.

Salman tare da Dattijo Junaid da Ɗayyib gidan Abduh Dhahab dayake a matsayin Masauƙin Salman suka wuce don yin bankwana saboda washe gari zai koma garin su.

Sun shafe awanni suna tattaunawa kafin dukkan su su miƙe suna ƙarayin musabaha. Dai-dai lokacin da suke yunƙurin fitowa sukaji ana kwaɗa sallama haɗe da ɗan bubbuga Gidan....✍🏻

***