ZINARE🔥

5

by @nafisatusasaal01

🔥 ZINARE 🔥

      


        SASAAL


         05

Kafatanin Mutanen Yankin Tudu ne suka yiwa Gidan Marigayi Abduh Dhahab zobe, kowannen su zuciyarshi cike da tsoro da wani fargaba mai girma gaske. Yunƙurin faɗar gaskiya a Yankinsu ko kawo wani cigaba ya zama babban musibar da Mutum zai iya rasa ransa a kai.

A cikin Gidan Gawar Salman ne da ya yi kacha-kacha cikin jini, sai Dattijo Junaid da shima idonsa ɗaya yake a tsiyaye bayan raunuka marasa kyan ganin dayake jikinshi. Haka Ɗayyib shima wuƙa ne soke a gefen cikinshi sai raunukan da ba'a rasa ba.

Sarki Hammam kanshi ya ɗaga sama, sai da ya tabbatar ya shanye ƙwallar da ya yiwa ganinshi yana sannan ya ɗurkusa a gaban Gawar Salman. 
Baƙin cikin da yake ji bai tsaya a iya cikin zuciyarshi ba har saman fuskarshi, yana son Salman sama da son da ya yi wa Abduh, saboda ya taimaki Mutanenshi a lokacin da suke da tsananin bukata, amma wannan baisa sun rangwantamai ba har sai da suka kaishi ƙasa kamar yanda su ka kai Abduh. Fari ƙal ɗin hannunshi da ya ɗan fara yamushewar tsufa yasa ya shafi fuskar Salman, kafin ya miƙe don a samu damar fitar da su daga Gidan.

Fito da Salman a luluɓe har kaa, saɓanin ragowar yasa zuciyar kowa ƙara karyewa. Banda koke-koken muryoyi daban-daban ba bu abin yake tashi a ƙofar Gidan.
To ko dai Tukwanen Zinaren ne ba'a so a Yankinsu tunda shine sana'ar da yafi kowawa Yankinsu kuɗin shiga? Wanene yake musu wannan Ta'addacin a Yanki? Daga Abduh Dhahab har Salman dukkan su maƙera ne, ma su kamaceceniya a ɗabi'u har ma da wasu maganganun su. kenan anfiso su cigaba da rayuwa cikin azaba da ƙangin Talauci? 

Kamar shekarun baya da suka shuɗe, Daular Sarki Hammam aka wuce da Gawar Salman anan aka Sallaceshi bayan an miƙa su Dattijo Junaid da Ɗayyib Asibiti. Fargaba mai gusar da nutsuwa ne ya dabaibaye zuciya Sarki Hammam, dalilin haka yasa Jininshi ya hau dole aka buƙaci Likita daga Babbar Birnin Abyad.

Kafatanin Mazan Yankin Yaransu da Manyansu ne suka tafi kai Salman makwancinshi cikin su har da Manya masu faɗa aji a fadar Sarki Hammam.

Daf da zasu shiga Maƙabarta harbin bindigar da yasa mutane dayawa darewa aka saki. Ma su ɗauke da Gawar Salman ma ajjiyeshi su ka yi sai dai su ba su gudu ba, su na dai tsaitsaye. Ƙarar Harbin da'asaki sau biyu a jere ne yasa suma suka tarwatse aka bar Iya Gawar Salman.

Mota mai tudu baƙi mai tsananin sheƙin dake bayyana girman dukiyar da'a zuba kafin mallakarshine ya yi parking a gefen Gawar Salman.

Maza majiya ƙarfine suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya har su uku a jere kafin fitowar na huɗunsu. 
Fitowar na huɗunsu ne yasa Bashar daya laɓe a ɓoyarsa shi kaɗai kuma ya sawa zuciyarshi dole sai ya ga duk abinda zai faru zare dukka girman fararen manyan idanuwanshi na Usul ɗin Mutanen Yankin Tudu. Fitsari mai ɗumin gaske na biyo jikinshi, a take ya ji idanunsa na ƙyaƙyayin azaba. Amma duk da haka taurin zuciya, da kafawa duk abinda yasa a gaba ƙahon zuƙa yasa ya ƙi kulle idanuwansa kamar yadda ragowar su ka yi a maɓoyarsu.

Ba bu rahama a fuskar na huɗunsu da yafi su girma da tsaho, hannu ya sa ya ɗauke Salman a makara, yanayin yanda ya ɗagashi na bayyana rauninsa. dasauri  ragowar ukun suka buɗemai bayan mota ya shimfiɗeshi. 

Harbi suka ƙara saki amma duk da haka fararen idanuwan Bashar da suka koma jajaye na tsaye ƙyam a kansu. Yunƙurin shigar su Mota yasa ya ɗan lumshe idanuwansa na seconni ko zai samu sassaucin zugin azabar da idon yake mai. 
Ɓude idanuwan da Bashar zai yi ya tsinci Mutum biyu a gabanshi, dama ba bu wani tazara a tsakaninsu. Ya kasa ihu saboda duniyar fargabar daya tsinci kanshi a ciki. Kamar Kayan wanki haka suka ɗebeshi har Gaban mutumin da Kallonshi daga nesa kaɗai ya sa shi sakin fitsari. Ƙasa Bashar ya yi da kanshi jikin da dama can lallaɓawa yake yi saboda yawan shekaru ya fara karkarwa. Ɗago shi ya yi suna kallon tsakiyar idanuwan juna, idon Bashar kamar an tsiyaya jini tsabar jan da sukayi. Ƙasa Bashar yaƙarayi da kanshi saboda gudawan daya tahowa mai, ba ya kuma burin ya ƙara kallon ko da fuskarshi ne balle cikin idanuwansa saboda tsoro. Bashar bai gama saƙe-saƙen da yake yi ba yaji ya ƙara ɗago Kanshi. Da ƙarfi ragowar suka buɗemai baki. Gurnanin azabar gaske Bashar ya saki lokacin da na huɗunsu ya ciremai harshe kwatankwacin yadda aka yanke na Dattijo Junaid. Watsar da shi su kayi suka faɗa Mota kamar iska haka suka bar wajen da Yankin Tudu gaba ɗaya. Gurnanin azabar da Bashar yake yi babu wanda bai jiyosa ba a maɓoyarshi, amma tsoro ya hana kowa fitowa duk da Matsayin da Bashar ya ke da shi a Daular Masarautarsu. 

A can wajen Sarki Hammam duk bai san wainar da'ake toyawa ba saboda barcin daya ɗaukeshi, suma waɗanda suka rage a Masarautar laƙwas su kayi kamar basusan abinda yake faruwa ba, tunda wanda zai tilasta mu su fita kai agajin bai san ma anayi ba.

Sai da kowa ya yi hour biyu da ɗoriya a maɓoyarshi sannan duk su ka firfito, zuwa lokacin tuni Bashar ya yi suman azaba. Ko takan inda harshen da suka yanke yake basu bi ba suka saɓashi a guje sai Asibiti. Daga Asibiti kowa ya silale ya yi Gida haɗe da kulle ko ina.

Har aka kwana aka wuni Yankin Tudu tsit kamar babu kowa.

A ɓangaren Naila tayi kukan daya saukar mata da ciwon kai mai nauyin gaske, gashi babu damar fita kaita Asibiti saboda tsoro. Haka Kakarta tayi ta yimata jiƙe-jiƙe har zuwa washe garin da ta ji ɗan dama-dama.

★washe gari da Sarki Hammam ya farfaɗo ya samu labarin abin ya faru. A gaggauce ya yace a shirya mishi zuwa ganin Bashar.

Lokacin da Sarki Hammam ya isa Asibiti kafin ya shiga Ɗakin da Bashar yake saƙon Dattijo Junaid ya riskeshi na;" idan Sarki Hammam ya shigo ina raye, ku faɗamai yazo gareni inada saƙo." fasa shiga Ɗakin Bashar ya yi ya wuce na Dattijo Junaid bayan ya dakatar da kowa daga bin bayan shi.

Kallon yadda Dattijo Junaid ya koma kaɗai wani abin fargaba ne. Bayan ya yi mai ya ya jiki ya naimi waje ya zauna.
Alama da salon maganar kuramen da ya saba Dattijo Junaid yakeyiwa Sarki Hammam bayani, cikin ikon Allah Ubangiji ya ba shi ikon yin bayani kamar da bakin shi yake magana tsabar yanda Sarki Hammam ya fahimceshi. Hannunshi Sarki Hammam ya kamo. Junaid Amininshi ne tun suna Yara amma banbancin Gidan da suka fito ya nisanta Amintakarsu dole, Bayan ya zama Sarki Junaid ya dawo ƙarƙashinshi Bashar ya maye gurbinshi na Amini. Ya na cikin wannan tunanin Allah Ya amshi ran Dattijo Junaid. Kuka ya zauna yi kamar ƙaramin Yaro. Ya yarda Bawa baya mutuwa har sai idan lokacin da Ubangiji ya ɗebarmai sun cika, banda haka tayaya Dattijo Junaid zai yi ƙarfin zuciyar rayuwa bayan yana kallon ajalinsa a kusa dashi ko da yaushe kuma ya ja bakinshi ya yi shiru. 
Mutuwar Dattijo Junaid da hasken da Sarki Hammam ya samu dangane da badaƙalar dayake addabar Yankinshi a ɓoye bai tsaya a iya hawan jininshi ba har jinya ya kwantar da shi, don dole aka fitar dashi Babban Birni Abyad.

Mutuwar Dattijo Junaid da abinda ya samu Bashar ya kasa hankalin mutane kashi-kashi. Wa su sun yarda waɗanda suka zo a Baƙin Mota sune suke yiwa Yankinsu aika-aika wa su kuma suna ganin sam ba haka bane idan hakane aiba Bashar zasuyiwa haka ba kawai Ƴan Uwan Salman ne suka zo ɗaukar fansa, tunda babu komai na Salman da ba'a bincika ba amma sun kasa gano daga ina yake.
Wannan dalilin yasa baƙin jininsu raguwa a zuƙatan Maƙotan Yankinsu saboda da yawa sunfi yarda masu Baƙin Mota ne suke yiwa Yankinsu ta'asa tuntuni.

Kwana biyu da dawowa Sarki Hammam daga Babban Birni Abyad Bashar ya samu sauƙi.

A Fadar Sarki Hammam aka gayyato ƙwararrun ma su zane  don su zana wanda Bashar ya haukace yana ta kwatance har da kaisu gidan Abduh Dhahab, duk wannan kwatancen na shi ba bu wanda ya ɗauki hasken komai Sai Sarki Hammam dashi ƙadai yasan wanda Bashar yake nufi. Shara da tsaho yake ta kwatantawa, banda wannan ya kasa siffanta komai. Sai da ƙyar ya fara zayyano siffar wanda sam babu ko mai kamanninshi a Yankin. Dole yana ji yana gani masu zane sukayi tafiyarsu. 

Kwanaki bayannan Sarki Hammam yasa atara mishi mutanen Yankin don zaɓar sabon Shugaban Kasuwar ZINARE da Mataimakinshi tun da har lokacin Ɗayyib bai samu sauƙi ba....✍🏻

Anya muna tare??😊
***