JIRWAYE

CHAPTER 8

by @deejasmah

JIRWAYE........

Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah)

***

Wattpad Deejasmah15

Tiktok Deejasmah_writer

Young talented writers association (YOTA).

In dedication to women in tech 💻

CHAPTER 8

Washe gari da safe suna gama breakfast Amah ta tasa ta a gaba, aikin tarban baƙo suka fara sai kace irin yanzu zai zo ɗin nan. Small chops ta sa suka haɗa kala-kala suka yi traditional drinks aka saka a chillers yayi sanyi, kakkafta komai suka yi a inda ya kamace shi sannan suka yi girkin lunch a tare da ita. Ai ko ta yi ƙorafin gajiya kamar bakin ta zai tsage amma ita ko a jikinta don sai lokacin ta rabu da ita ta ɗan huta ba kuma wai ta ƙyale tan ba ne kamar yacce ta zata, wanka ta samu ta yi ta ko kwanta bacci ba tare da ko abincin sun ci ba koda suka haɗu a table babu wanda ya tambayi inda take cikin su biyun sai da ta yi baccin ta ta hantse kafin ta iya tashi after 3.

Ta samu jikinta ya warware amma sai da ta kuma watsa ruwa ta farfaɗo daga baccin da tayi, tana fitowa ta samu Amahn zaune a gefen gadon ta don ta shigo tada ta ganin time na tafiya ta tarar tana toilet. Baki ta tura tana mai jin ina ma tana school ya zo gidan don ta san wani abun da ba ta so za'a tursasa ta yi dama haka take mata tun tana gidan in ta ganta ɗakinta a sanda za ta yi wanka to sa ta sa kayan da ba tayi niyya ba zata yi.

Kamar ko yanda ta zata hakan ce ta faru don tana gama goge jikinta ta shafa man da shi kaɗai ne abinda take iya shafawa jikinta ta miƙo mata wata Egyptian Abaya dark green mara zane ko stones a jikinta don ta san ba wani son ƙyale-ƙyale take yi ba. Ba tare da tayi magana ba ta amshi kayan ta sanya tana mai jin ta a takure don a cikin kayakin ta babu Abaya bar ta dai da kimono. Shi ma mara ado ta fi son plain haka kuma dull colors wanda ba su da kyan kallo don ita dai inda mutane suka bi ta gefen zaɓen sutura ta saɓa wa hanyar, opposite za ta bi.

Wani ƙarin damuwar sai da Amah ta ɗauko enchantment powder ta shafa mata, har da taje mata gashin gira da ke nan cukus saboda ba ta wani gyarawa hula ta ba ta ta sanya ta rufe gashinta da ke nan da lock ɗin shi mayafin abayar ta sanya ta yane kan ta sai ko ga shi nan ta yi kyau sosai fiyeda yanda kake expecting. Murmushi Amah ta yi tana cewa '' yawwa yanzu kam DeeDee na ta fito cas, kamar ka sace ka gudu''.

Hmm kawai ta faɗi tana kuma cuna baki don ita dai ba ta ga wani kyan da tayi ba da an barta ta zaɓi kayan sawanta da ya fiye mata amma an haɗa ta da Abayar da ba ma ta san daga wani yankin aka ƙwaƙulo ta ba, ta dai daure ta ce '' thanks Amah, Allah ya ƙara buɗi''.

''Ameen Baby, now ki yi sallah sai ki sauka ƙasa kafin ya ƙaraso''.

''Tohm'' ta amsa tana nufar wurin sallahr ta da ta ajiye dadduma, shimfiɗawa tayi ta kabbarta sallah cike da natsuwa ko da ta idar wurin wayarta ta nufa da tun tana sallahn take vibrating. As expected Rhidwan Audi ne ke yawo kan screen ɗin, cikin sanyin murya ta ɗaga tana sallama.

Amsawa yayi cikeda zaƙuwa yana cewa '' yanzu haka gani a Kawo tunawa na yi da ba ki gaya min sunan layin ba that's why I called''.

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce '' oops I'm sorry, Ɗan-Kaduna close rigachikun new extension or rather lemme just drop my Live address to make it easy for you.

''Yawwa Mine, do so''.

Okay ta amsa tana yanke wayar, WhatsApp ta shiga a take tai masa sharing location ɗin ta, sai da ta tabbatar yayi viewing kafin ta kashe data kamar yadda Amah ta umarce ta hakan ta aikata ƙasan ta sauko. Ita kaɗai ta tarda zaune murmushi ta sauke tana zama gefen ta, duban ta tayi da kyau tana cewa '' ba zaki ci abinci ba?".

Kai ta girgiza tana mai cewa '' I'm okay, sai ɗan anjima zan ci Affah yana nan kuwa?".

''Ya na study shi da TeeTee ba ki leƙa su ba ne?".

''Nope i didn't know su na ciki ai da na shiga''.

Uhmm ta amsa mata.

Suna nan zaune suna hirar har sai ya kirata akan ya shigo wurin yana bakin gate an hana shi shiga, miƙewa tayi tana cewa '' bari ta fito ta shigo da shi''. Katsewa tayi tana shaida wa Amah bari ta shigo da shi, tana fita ko a bakin gate ɗin ta same shi cikin motar shi bai ko fito ba hasalima mamakin fitowar ta daga gidan ne ya kashe shi don duk da ita ta tura masa da location ɗin bai yi tunanin wai da gaske daga gidan za ta fito ba. Don ko kusa ba tayi kama da ƴan gidan ba komai na rayuwa ba wai saboda rashin kyau ko wani abu ba but by Allah halayyar ta ba su taɓa nuna daga wani babban gida irin wannan ta fito ba. Ya dai fi ba ta ƴar tsaka-tsaki haka duk da dai daga ranar dinner da ya ga TeeTee da mota sosai ya fara tunanin wani abu sai kuma ya bar hakan da cewa '' ƙila ita ta siya '' tunda ya san model ce babba, ko wayarta ma ya zaci ita ta sai kayanta tunda tana aiki amma ganin ta fito daga irin gida haka ya goge masa malu matuƙa gaya.

Da murmushi ta iso wajen tana knocking glass ɗin motar hakan ne ya dawo da shi hayyacin sa da murmushi shi ma ya tarbe ta yana cewa '' so Milady ga ni a gidanku''.

''Yeah ga ka gidan su Adeeyah, ka shigo da motar ciki they'd open the gate for you''.

''Ko ki shigo mu shiga tare dai''.

''Nope ka dai shigo '' tana faɗin haka ta shige gaba yana bin ta a baya.

A parlorn ƙasa inda Affah kan gana da baƙin shi ta sauke shi inda ta tarar har an tanadi kayan tarbar shi, kujera ta nuna masa ya zauna yana sakin ajiyar zuciya kana yace '' ban yi rashin kunya ba in na zauna? Kar fa Daddyn mu ya shigo ya gan ni kan kujera''.

Murmushi ta ɗan saki tana cewa '' wannan kuma ban san inda ka samo shi ba, so.....'' ta ƙarashe tana nuna masa table ɗin gaban shi. Bai ko kula ba yace '' Allah Baby I'm kinda nervous, ban san yanda ake zuwa gaban in-laws ba ƙirjina sai bugawa yake ko dai in kira Sahib ne ya taya ni?".

''Ai lokaci ya ƙure man, and don't worry ka ji ko? My Affah won't bite or scratch mutum ne fa calm down okay?".

''Okay dear since you said so ''.

Ya furta har lokacin yana jin ƙirjin shi na bugawa, haka nan ya ji yana shakkar haɗuwa da Affahn na ta duk rawar kan shi kuwa. Ko ita da kan ta sai da ta ji mugun mamakin shi don ta fi kowa sanin halin ƴan kayanta ba ta taɓa zaton akwai rana a duniya da za ta ga yana jin shakkar tunkarar wani ba, duk da ita da kanta tana tsoron haɗuwar su da Affahn saboda sanin halayyar shi da ƙaidojin shi amma in ta tuna cewa shi da kan shi ya buƙaci ganin shi ta kan ɗan ji sauƙi kaɗan.

Ruwa ya ɗauka ya sha shi ma bisa tursasawar ta sai da ta ga ya natsu sannan ta fita ta staircase ɗin da zai kaita parlorn shi na sama ta bi, ya na a zaune shi da TeeTee suna wata magana kamar yanda suka saba don kullum ka gan su su biyun nan sai ka ga suna magana. Itama sanye take da irin abayar ta wanda sosai ya fito da kamannin su bambancin hasken fata da na Tee ya ɗara ta sai kuma piercing ɗin fuskarta da suke guda uku na ƙasan ido (dermal), na tsakiyar lip ɗin ta na sama ( Medusa) sai kuma na gefen baki (Monroe) da ba ta taɓa sanin da akwai su ba sai yau na hancinta (septum) kawai ta sani. Kai ta jinjina tana mamakin ƴaruwar tata wato ita dai komai na ta daban da na mutane, in ba haka ba ya mutum zai bi jikin shi duk da yaga kamar wani mara saiti ko masu yi ma zaka ga bai fi su yi ɗaya ko biyu ba amma ita kowani gefen fuska an bishi da huji. Ko da yake ba damuwar ta ba ne tunda wainda suka haife su ma ba su hane ta ba, abinda ya kawo ta kawai ta yi wato sanarwa Affahn cewa Rhidwan yana ƙasa yana jiran shi.

Okay ya ce kana da sauri ya miƙe yana gyara babbar rigar shi ya nufi ƙasan, da kallon mamaki ta raka shi har sai da ya saukan kafin ta janye idanunta daga kan shi tana duban TeeTee da ke cewa '' Amarya'' murmushi ta saki ta san duk wannan abinda take yi saboda ta share ta ne abinda ba ta sani ba ita ma ba ƙaramin ƙoƙari take yi ba don ba ta iya fushi da ita ko na yini ne wannan ne karon farko da ta taɓa kwanaki tana a halin janye mata, ta riga da ta saba da ta ita ke binta tana sha mata ƙamshi not the other way round.

''Twinnie'' ta amsa tana kuma faɗaɗa murmushin ta, baki ta taɓe tana cewa '' uhmm'' daga haka ta cigaba da danna wayarta. Ko a jikinta don nufar hanyar kasa ta yi zuwa wajen Amah, da kallo ta raka ta sai da ta ga fitar ta kafin ta ja dogon tsaki tana cewa '' gwara a yi maza a fara maganar auren nan as I don't have the patience to wait long''.

Bai wani daɗe a ɗakin ba suka gama duk wata magana da zasu yi inda kai tsaye ya buƙaci ganin magabatan shi don a cewar shi yarinya tana makaranta bai kamata a ce wani yana neman ta ba tareda iyaye sun san da zaman shi ba, shiyasa ya buƙaci ganin shi baya ga haka ma so yake in an samu daidaito a tsakani kawai maganar aure ya shiga ciki a yi a wuce wurin. Ya ji daɗi sosai ya kuma yaba da dattakon Alhaji Hussaini Shamaki, ya kuma nuna masa dama shi ma da aure yake neman ta ya kuma ji daɗin kalar tarbar da ya samu in shaa Allahu ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen shaidawa iyayen shi kuma su da neman aure za su zo. Nan fa fara'ar Shamaki ta kuma daɗuwa don yana ganin kamar lokacin cikar burin shi ne ya kusa, ai ko ya saki jiki suka fara hira har da shaida masa maganar genotype ɗin yaran da suke AS shi kuma yace '' AA'' ne shi daɗi kamar zai kashe shi sai shi masa albarka yake yi shi ma dai Rhid ya ji daɗi har a ƙasan ran shi yana jin ya dace da suruki ɗan mutunci mai ɗaukar kowa na shi.

Affahnmu ashe dattijo ne?

Ko da DeeDee ta shigar da shi don su gaisa da Amah sosai ta yaba da yaron shi ma kam ya ji daɗin haɗuwar ta su da ita musamman yanda ta karɓe shi kamar ɗan cikinta, da suka fita waje kam bai ɓoyewa Deeyah ba ya shaida mata yayi dace da samun ta a matsayin mata don tabbas ya yaba da gidan da ta fito da tarbiyyar da aka mata da ma yanda iyayen ta suke haba-haba da shi babu wani nuna isa ko izza. Ta ji daɗin yanda suka masan itama ainun hakan ne ma ya kawar mata da tunanin ta kan Affah da abinda yake nufi da haɗuwar ta su ta yarda ta amince Alkhairinta ne ya matso kusa may be in ta yi dace bayan an yi auren nan ya koma yana treating ɗin ta yanda yake wa TeeTee don ba ta da burin da ya wuce hakan a duniyar ta hakan har saka ta fatan ayi auren nan kusa a wuce wurin. Har dai ya zo ya tafi bai haɗu da TeeTee ba kasancewar ya san ita ma a hostel take sai bai ko tambayeta ba itama dama addu'ar da take yi kenan don in ya tambayar ma ba ta san mai zata ce ba don ta san ko da me take yawo ba zata sauko ta zo su gaisa ba kai kace ba ita ta tado zancen ba.

Daren ranar yanda ka san wainda suka yi hitting jackpot musamman Affah da ya bawa kowa mamaki don zaƙuwar da yayi yacce ka san an zo tambayar auren Adeeyahn ne koma kace irin in kawo kuɗin gaisuwan nan don har yana cewa Amah ta yi lissafin kayan ɗaki zuwa ƙarshen wata zai bayar da kuɗin sai a siyo, ce mai tayi ya bi komai a sannu dai DAGA TAMBAYAR IZINI? Sai ya zo ya fi mai kora shafawa? Ai sai ya jira a ji motsin da iyayen yaron za su yi kafin a fara siyayya ko? Sai cewa yayi ita dai tayi abinda ya saka ta, don bai son a ja bikin da nisa ne in da hali ma suna zuwa a saka kamar 2 months haka a wuce wurin. Yanzu kam riƙe baki ta yi tana kallon shi ba tareda ta iya cewa uffan ba, ita dai TeeTee yanda yake ma ba ƙaramin baƙanta mata rai yake yi ba ai ko sai zumɓura baki take yi tana kallon shi a kaikaice ba don tana da dalili na son Deen tayi ta bar gidan ba da sai tace ta fara nadamar janyo maganar auren amma da yake abinda take son ya fi gaban me suke ciki sai kawai ta shanye tana kawar da fuskarta daga gare su.

Farincikin dai bai saki Affah ba har washegari da Adeeyah ta masa sallama akan zata koma school, har da ƴan addu'oin shi da ja mata kunne akan ta kula kar ta yarda ƙawaye su hure mata kunne akan maganar auren nan. Da in shaa Allahu ta bi shi ya ciro kuɗi ya ba ta yana ce mata in ba su isa ba ta gaya masa zai daɗa mata, da murmushi ta fita daga gidan tana mai jin kamar an tsoma ta a aljanna don tunda ta fara school bai taɓa bata kuɗi a hannunta ba komai take buƙata sai dai ta gayawa Amah in ko ta gaya masa ta hannun Ateeyah yake zuwa shiyasa ma akan hostel take ta baza wulaƙanci akan don me zata kama room of 4 tana gwama numfashi da wasu a ɗaki ɗaya ita dai bata biye mata don ta san me yake damunta ƙyashi ne ba wani abu ba sai kace ba haɗawa suka yi da Mufee ba duk da ita kuɗin ɗaya ta biya Deeyah kuma na guda uku wanda ko rabin kuɗin off-kn da ake biyawa TeeTeen bai kai ba kuma inda ma ace ita ɗaya take kwana ba zata damu ba kawai takaicin ta wasu su ƙaru da ita don a duniya Tee ba ta son ta ga wani ya ci arzikin ta tafi son komai ta samu to kan ta ne kawai.

Ahhh lallai ƴar gidan Shamaki.

AUCKLAND NZ.

Kwance yake a kan gadon shi sai juyi yake yi so yake yi yai bacci amma ya gaza yi, shi ba gwanin tunani ba ne kafin bacci infact yana ɗaya daga cikin mutanen da babu damuwar da take hana su bacci komai ko matsalar da suke ciki. Amma daren yau hakan ya kasa yiwuwa da zarar ya rintse idanu zancen TK ne suke faɗo masa rai, wainda sai yanzu ne suke tsikarin shi a ƙirji ya gina kan shi a duniyar fasahar na'ura ta yanda babu wani mai ji da tashe da zai iya kamo shi a hatsabibanci shiyasa yake cin karen shi babu babbaka bai taɓa tunanin akwai wani ƙaramin alhaki mace ma for that matter da za ta iya warware masa aikin shi sai ga shi cikin ƙiftawar idanu wata yarinya ƴar Nigeria ta sha shi misilla tana shirin rusa masa reputation ɗin da yake da shi a idanun duniya. Kai ba zai taɓa yarda ba dole ne ya hukunta ta irin hukuncin tauna tsakuwa domin a firgita aya, ba kuma zai taɓa barinta ba zai mata abinda sai ta rubuta littafai akan hatsarin da ke cikin taɓa jelar damisa dole ne ta san ta faɗa kwanin kunama mai mugun dafi.

Tashi yayi zaune yana ture duvet ɗin da ya rufa wayar shi ya ɗauko yana fara lalubar number Snake, ringing biyu ya ɗaga yana cewa '' Scor''.

''Kun gano wacece yarinyar nan?".

''Akan hakan mu ke yanzu haka''.

''This is not what I want to hear Snake, you told me you'd take care of it. Why are you slacking? Ko dai so kake in yi aikin nan da kaina ne?''.

''Ko ɗaya ita ɗin kamar tsuntsu mai wayau take ka kuma san ta wuya ake kama su so....''

''Cut that! Ka san dai ban da haƙurin jin tales ɗin ka just get to the deal, how many hours zan ƙara maka kafin ka gama binciken naka?".

''In the next two hours ma zan kawo maka even a hint about her''.

''I don't want a hint I need everything, and failure to do so zai sa in shiga ciki and you know what that means''.

''Don't tell me Shadow zaka saka aikin nan? Ba dai empire zaka yi risking a kan yarinya guda ɗaya ba?".

''I'm not risking my Empire Snake, you are the one risking it and it is something I can't take. Da kuma kake maganar Shadow ba ka san ya fi min ku amfani sau goma because he's really doing his job right while ku kuna can kuna cewa i should calm down''.

''Don't say this Scorpion ka fa san mu ma muna ƙoƙari, kawai matsala aka samu but Tail is already doing his very best wurin ganin an shawo matsalar''.

''Na ji, ku dai yi abinda ya dace and don't forget that your time starts now tick tock.........''

Ya na furta hakan ya yanke wayar yana jan dogon tsaki kamar yanda ya saba jifa ya yi da ita sannan ya miƙe don bai jin zai iya jiran su har nan da awa biyu, haka yake a duniyar shi babu haƙuri ba kuma jira komai ya fi son yin shi da kan shi a kaf Empiren su daga Snake sai Shadow kawai yake iya sawa su yi wasu abubuwan su ma irin wainda suke da tazarar da ba zai iya yin su remotely daga inda yake zaune ba ne. Ko Tail ba kasafai yake son aiki da shi ba duk da ma bai taɓa ba shi aiki directly ba yaron Snake ne, zai ma iya cewa ko sunan shi bai sani a bakin shi ba. Aikin nan ma dalilin shi na jiran su saboda shi Tail ɗin ne ya fara kawo musu information akan an warware saƙon da suka yi don son ɓoye duk wasu sirrikan tsohon sanata kuma Amb Hon. Taheer Kallah, wanda yanzu haka sakamakon aikin har an baza cigiyar shi a madakatan ƙasar nan inda Allah ya taimaka ma sanda suke neman ya riga da ya shallake har ma da iyalin shi da dama ba a ƙasar suke rayuwa ba.

Tsaki ya kuma saki yana buɗe operation room ɗin shi, ƙato ne sosai ɗakin mai ɗauke da manyan na'urori wainda ka taɓa gani da ma wanda tunanin ka bai taɓa kaiwa kai ba. Kunna switch yayi a take komai ya kawo haske suna welcoming na shi, a gaban ta farkon ya zauna yana sanya passkey duka suka yi booting danne-danne ya fara yi don son samu wani hint sai dai kamar almara ya gaza sai ma redirections da yake samu. Wata dariya ya saki mai ƙarfi a bayyane yace '' seems like they don't know who Scorpion is!!..........."

Da alamu kam ba su sani ba, Adeeyah Shamaki ba ki san waye Scorpion Stings ba ko?!

Deejasmah 🦂