6
🔥ZINARE🔥
SASAAL
Arewabooks@sasaal
06
Ɗaya bayan ɗaya mutanen Yankin su ka yi ta sulalewa, bayan sanar da su dalilin tarasu, kafin rufuwar Minti Talatin babu kowa duk sun gudu.
Ajiyar zuciya Sarki Hammam ya sauke lokacin da labarin ƙin amsar shugabancin Kasuwar Tukwanen Zinare ya riske shi. Tabbas! sunyi nasara akan Mutanenshi. Tsoro da gudun mutuwa, rayuwa cikin Talauci, ƙin faɗar gaskiya ko da za'a kashe na su a gabansu saboda su tsira da rayukansu shi suka zaɓa akan dai mutuwar da dole wata rana sai ta riskesu. Sun gwammace ko shekara nawa Ɗayyib zai yi a kwance zasu jirashi ya jagorance su idan ya ga zai iya idan kuma ba zai iya ba gara su haƙura da kasuwar gaba ɗaya.
Sarki Hammam kasa jurewa ya yi, ya ƙarasawa ayi shelan
"shin da wanda ya ke so ya zama Mataimakin Ɗayyib idan ya warke?" Nan ma babu wanda ya amsa tsit sukayi a cikin Gidajensu kamar ruwa ya cinyesu. Gaba ɗaya Sarki Hammam sai ya rasa abinda yakemai daɗi, ba shi da wanda ya yarda da shi a kusa da shi balle ya tattauna damuwar da shi, saboda masu aikata ɓarnar a kusa da shi suke ta yanda ba shi da yadda zaiyi ya yakicesu, kuma ko da ya faɗi ma su aikata ɓarnar kai tsaye babu wanda zai yarda da shi.
A ɓangaren Ɗayyib ba laifi yanata samun sauƙi saboda ƙwararrun likitocin da suke shigowa dubashi akai-akai, don da farko a Yankin Tudu ya fara jinya, sai dai rashin ƙwararrun likitoci ya sa aka fitar da shi wani gari da yake kusa da Babban Birni Abyad.
A cikin watanni ya warke tsaf kamar bai taɓa jinyaba. Da tsananin farin ciki shi da Iyalinshi suka ɗauki hanyar Yankin Tudu.
A ranar da ya dawo Gida bayan ya huta Gidan Bashar da yake a matsayin ƙanin Mahaifinshi uwa ɗaya uba ɗaya ya nufa.
Lokacin da Bashar ya yi ido biyu da Ɗayyib da sauri ya rungumeshi ya na yi mai kwataccen ya ya jiki? Ɗayyib ya amsa haɗe da jajantamai abinda ya sameshi. Bayan Ɗayyib ya huta, ya tambayi Bashar garin ya ya haka tafaru? Da kwatancen Gidan Abduh Dhahab Bashar ya fara.
Ɗayyib mutum ne mai kaifin Basira da saurin Fahimta, wannan dalilin ya sa kai tsaye ya fahimci dole wanda ya gutsewar Bashar harshe yana da alaƙa da Gidan Abduh Dhahab.
"Sulaim ka gani, ko Abduh ko Mairam?" Ɗayyib ya tambayeshi a nutse. Shiru Bashar ya yi takaicin Ɗayyib na kamashi tayaya zai iya faɗamai bayan ya ambaci sunayen su dukka a lokaci ɗaya? Ganin ya yi shiru kamar mai tunanin yasa Ɗayyib umartar a nemo mai zane.
An zana Abduh da kwatancen da Ɗayyib ya ke yiwa mai zane Bashar ya ce ba shi bane an zana Sulaim da Mairam suma ya ce dukka ba su bane. Tunanin har lokacin ba su fuskanceshi ba ne yasa ya miƙe yana kwatanta tsaho da shara. Ɗayyib ba shi da zaɓi don sam yakasa fahimtar wanda Ɗayyib yake nufi don haka dole ya sallami mai zane kafin yabar Gidan ranshi babu daɗi.
Bayan Ɗayyib ya koma Gida, Dare ya nutsa, kasa runtsawa ya yi har ƙarfe ukun dare. Babu irin tunanin da baiyi ba game da wanda Bashar yake nufi amma yakasa ganewa. Ba don yana jin barci ba ya kwanta haɗe da rintse idanuwanshi.
★da tsananin ciwon kan rashin samun isasshen barci ya ɗora alolar Sallar Asubahi, har lokacin da tunanin wanda Bashar yake nufi maƙale a cikin zuciyarshi.
Ɗayyib yana cikin sallah raka'ar ƙarshe ƙwaƙwalwarshi ta harba. Shaidan ya samu damar wasa da hankalinsa haɗe da tuna mishi abinda ya kasa tunawa shara? tsaho? Anya ba MALIK Bashar yake nufi ba?.
MALIK hadimin Gidan Abduh Dhahab ne, kullum shi yake sharar harabar Gida duk Safiya kuma Ɗa ne ga Aminin Abduh. Tun ranar da aka kai gawar su Abduh Dhahab makwanci aka naimi Malik da Iyayensa aka rasa sun gudu, babu wanda yakawo tunanin komai a ranshi, sai tunanin sun gudune don tsiratar da rayuwarsu, tunda Malik yasan wasu sirrikan na Abduh Dhahab sama da su da suke Abokananshi. Malik dogo ne na gaban kwatacce don dalilin tsahonsa yasa Abduh Dhahab yake tsananin sonsa saboda irin siffar Sulaim Ɗanshi dana Mahaifiyarshi yake da shi, ba irin Siffar Mutanen Yankin Tudu ba.
Cikin rashin nutsuwar zuci da na gangar jiki Ɗayyib ya sallame. Daƙyar ya taushi kanshi har ya bari gari ya yi haske. A Wannan karo da kanshi yaje ya taho da masu zane har mutum uku.
Tsaf ya kwatanta mu su Malik suka zanashi kamar zai yi magana. Bashar yana ganinshi ya miƙe jikinshi yana rawa haɗe da gyaɗa kai alamar shine. Ɗayyib bai ce komai ba har sai da ya tabbatar ma su Zanen sun tafi saura isu-isu ƴan Gida sannan ya matso kusa da Bashar yana kallon tsakiyar idanuwanshi kafin ya ce;
" Idan Malik da kowa yasan matsayinshi a Gidan Abduh Dhahab zai kamaka kai kaɗai akaf faɗin Yankinan ya yankemaka harshe to ba shakka kanada masaniya akan Kisan Abduh. Menene gaskiya?" Ɗayyib ya tambaya har lokacin idanuwansu a sarƙafe cikin na juna.
Wani irin yaushi idanuwan Bashar sukayi haka tattaurar zuciyarshi. Bai ce komai ba sai ƙasa da ya yi da kanshi don tambayar Ɗayyib alamu ne na shima ƙarshenshi yazo.
Jin shiru bai ɗago ba har na tsahon daƙiƙu yasa Ɗayyib dafashi, sharaf ya zube ƙasa daga zaunen dayake kamar Gini. Kafin su je Asibiti tuni rai ya yi halinsa.
Lokacin da labari ya riski Sarki Hammam bai ce komai ba banda hutun da yake ɓukata don haka ya Yanke shawarar da zarar anyi bakwai zai bar Yankin na wasu watanni kafin nashi shima lokacin ya yi.
Mutuwar Bashar ya sanya nutsuwa a zuƙatan mutanen Yankin don gani suke yi dama Bashar da Allah Ya tonawa Asirine kaɗai matsalar Yankinsu kuma gashi ya mutu, ba su yi tunanin ina magoya bayan Bashar ɗin suke ba, domin bai isa ya yi wannan ɓarnar shi kaɗai ba.
Tuni kowa ya saki jiki suka fara ƙera Tukwane ba ji ba gani don tunkarar Kasuwar Tukwanen Zinare da ƙafar dama.
Naila sana'ar Mahaifiyarta na ƙera kayan wasan Yara da dama can ta iya tafara ƙerawa Kakarta tana tayata. Gwanin sha'awa ta ƙera su Tukwane, randar ruwa, murhu harda talabijin duk na lakar ƙasa. Da wannan kuɗin sukeyin hidimomin komai na su ita da Kakarta
********************
Kwanaki sun miƙa, abubuwa sun sauya, yawanci daga sauƙi zuwa tsanani.
Sufyan ya zama ƙosasshen Saurayi, kyakkyawan da yake taƙama da kyanshi da kuma zamowar Mahaifinsa Shugaban Kasuwar Tukwanen ZINARE. ya yi niyyar ajiye burinshi na zuwa Babban Birni ya yi ilimi mai zurfi amma ranar da faɗa ya haɗasu da Kabeer ɗan Gidan ƙanin marigayi Dattijo Junaid har ya ce mai. "Taƙamar mai kakeyi? Babanka Shugaban Kasuwar Tukwanen Zinare ne? Hmm! Kasuwar Zinaren da Abduh Dhahab ne yasha wahalar kafashi, bayan ranshi kuke cin arziƙinshi shi kakeyiwa taƙama? idan ban da ajali waye ma yasan Babanka balle kai? Ko Sulaim da Mahaifinshi shine ya ƙirƙiri Kasuwar Tukwanen Zinare daga filin da ya gada a wajen Mahaifanshi ya kuma fika kyau da nasaba baya yi mana abinda kake yimana. Kabari duk ranar da ku ka ƙirƙiri wani cigaba na ƙashin kanku a wannan Yankin, ba na cin arziƙin wa su ba sai kazo ka ɗaga mana kai. Banza mai macacciyar zuciyar da banda son ace mai ya na kyau bai san komai ba!" waɗannan kalamai na Kabeer sun sosa ranshi tare da sashi kukan da zuciyarsa ce kawai bai haɗiya ba. tsanar Kabeer kuwa babu inda bai ratsaba a jikinshi. Ya fuskanci zamowar Mahaifinshi Shugaban Kasuwar Tukwanen Zinare kaɗai bai wadatar ba bai kuma zama wani abin kambabawa ko abin ayaba a wajen Mutanen Yankin ba, sai ma ƙara dawo musu da soyayyar Abduh Dhahab da Iyalinshi da ya yi a cikin zuƙatansu, shi kuma ba wannan ne burinshi ba. Burinshi kowa ya manta da Abduh Dhahab ne ya ƙirƙiri Kasuwar Tukwanen Zinare, su riƙi Mahaifinshi tamkar shi ya ƙirƙiri Kasuwar tun usul, su kuma girmamashi a matsayin na Ɗa Namiji ɗaya tilo a wajen Shugaban Kasuwarsu.
Cikin ɗacin zuciya ya bawa Mahaifiyarshi labari, maimakon ta tausheshi sai ta ƙara zugeshi tare da ƙara tadamai tsimin burinta na tafiya Babban Birnin ya yi ilimi boko mai zurfi.
Tabbacin amincewar Sufyan ya sa ta shirya tafiya Yankinsu wajen Malaman dubanta, don su duba mata Matar data dace Sufyan aura don tafiya da ita Babban Birni ta dinga yi mai Bauta kamar yadda ta tsara a baya.
*****************************
Naila ta zama kyakkyawar Budurwa kuma makitsiyar da mutanen Yankinta suke alfahari da ita. Ba ta daina sana'ar ƙera kayan wasannin Yara na laka ba, sai dai ta daina fita da su Kasuwar Tukwanen Zinare saboda harajin da ake tsawwalawa ma su ƙananun sana'o'i irinta. A ɓangaren kitso tana samun ciniki don ba Makitsiyar da ta iya kowani kalar kitso kamarta. Har Daular Sarki Hammam take zuwa yiwa Iyalinshi kitso su biyata da kuɗi mai tsoka.
Duk tsayin wannan shekarun fuskar Sulaim na manne a cikin zuciyarta don har kuɗi ta biya ƙwararren mai zanen Yankin ya zanata ita da Sulaim a waje ɗaya, ta kai Gidan hoto akq wanke mata ƙaraminshi, da shi take yawo duk inda zata je.
Tsawwalawar Haraji ya kawo koma baya ga masu ƙananun Sana'o'i a Yankin Tudu harma da ma su manyan jari. Ga ɓullowar Gidan rawar daya zamewa Yankin musiba.
Gidan rawa an ƙirƙirar shine ne a cikin Kasuwar Tukwanen Zinare, har da Masauƙin da aka kewaya da katakwaye da langa-langa kamar Ɗaki ga waɗanda dare ya yiwa. dalilin haka yasa Matasan Yankin sai su sha wahala su ƙera Tukwane da zarar sun siyar sai su wuce Gidan rawa da Kuɗin haka ɓaki ma su shigowa, wa su ma suna shigowa ne don kawai suyi sharholiyarsu su koma ba don su sayi komai ba. Wannan lamari yana ciwa Mutanen Yankin tuwo a ƙwarya amma tsoron rashin sanin wanda ya kafa Gidan rawan, tunda ga shi Shugaban Kasuwar Ɗayyib bai hana ba kuma bai kai ƙara wajen Sarki Hammam ba yasa suke Kwana da ɓakin ciki suna tashi da shi. Ƙewar Marigayi Abduh Dhahab da suka mayar abin zagi a baya na damun zuƙatansu, da maganganun Marigayi Dattijo Junaid.
Ƙara ta'azzarar komai ga shi kowa yakasa magana yasa Kabeer Abokin faɗan Sufyan yanƙurawa, don bazaiyiwu saboda tsoron mutuwa su kashe kan su da Kansu ba. Faɗan da ya tada hazo ne ya ɓarke a tsakanin Kabeer da mai gadin gidan rawar. Dayake Kabeer matashine mai garin jiki da zafin nama sak Siffar mutanen Yankin Tudu kuma baya shaye-shaye ya sa yasamu damar yiwa Matashin da ba su ma san asalin ɗan ina bane saboda duhun fatarsa dukkan tsiya.
Ba bu wanda baiji daɗin abinda Kabeer ya aikata ba, don wasun su sun cire tsoro sun fito sunata maganganun sam bai dace ace an gurɓata Kasuwar Tukwane da Gidan rawa ba...
Kabeer ko a jikinshi zuciyarshi sakayau ko ba komai, yasamu ya amayar da abinda yake sukar zuciyarshi da na Mutanen Yankinsa. saɓanin Mahaifinshi da zuciyar ke cike da tsoron abinda zai biyo baya
Bayan wata ɗaya, watan cin Kasuwar Tukwanen Zinare yaƙara zagayowa. A gaggauce Kabeer da Mahaifinshi suke kimtsa Tukwanen su don fita Kasuwa. Su na zuwa suka tarar da Rumfar su.....✍🏻
***