7
🔥ZINARE🔥
SASAAL
Arewabooks@sasaal
07
Su na zuwa su ka tarar da rumfarsu a rushe, yanayin shafewar wajen ma kamar ba'ataɓa kafa Rumfa ba. Kafin Mahaifin Kabeer ya dawo daga ɗimuwar da ya shiga, tuni Kabeer ya nufi kewayayyen rumfar da yake a matsayin ofishin Ɗayyib.
Abin mamaki kamar wanda ake jira tun kafin ya kaiga inda ya nufa, matasa masu irin Shekarunshi suka rufe shi da duka ta ko ina.
Ihun naiman taimakon Kabeer ne ya fito da Ɗayyib haka Mahaifinsa daya ƙaraso a guje ya na haki.
Dakatawa su kayi da dukanshi saboda ihun da Mahaifinsa ya kurma, kowannensu na numfarfashi saɓanin Kabeer daya goge jinin bakinsa ya yinƙura ya miƙe yana kallon inda Ɗayyib yake tsaye. Da zafin da yake ji a cikin zuciyarshi da gangar jikinshi ya fara magana;
" da a haka Abduh Dhahab da muka mayar abin aibatawa ya gina Kasuwar Tukwanen Zinare da bai kai ko ina ba zai mutu, ban nufo ofishinka don naci zarafinka a matsayinka na Shugaba garemu ba, sai don na kawo maka ƙorafin rushewa Mahaifina Rumfa da akayi. Menene laifina? Idan gaskiyar da na faɗa waccen watanne ina neman yafiyarka ka dawowa da Mahaifina Rumfarshi. Ni na haƙura da zuwa Kasuwar gaba ɗaya, don matsawar ina zuwa dole wata rana zan kasa jurewa nayi yunƙurin dakushe duk wani abinda zai kawowa Yankina koma baya ko akan waye kuw.." bai ƙarasa ba saukar naushin da yasa shi zubewa ƙasa warwas ya dakatar shi. Da gudu Mahaifinshi ya nufoshi yana kuka haɗe da kiran sunanshi. Ɗayyib ma tsawa ya dakawa Matasan da ko shakka bayayi Sufyan ne ya turosu.
Rige-rigen ɗaukar Kabeer kowa yake yi don kaishi Asibitin Mahaifinsa ya hana yace a barshi ya kaishi Gida yana da maganin da zai bashi.
Abinda ya faru da Kabeer yaƙara zama zanannen layin da kowa zai ji tsoron ƙetarawa, har ya yi azarɓaɓin faɗar gaskiyar a kan duk wani abu ba dai-dai ba da ake aikatawa. Jiki a sanyaye kowa yaci Kasuwarsa ta wannan rana.
Cikin tsananin Azaba Kabeer ya farka gabannin sallar magriba bayan ɗure-ɗuren maganin gargajiyan da suka yini suna yimai. Daga Mahaifinsa har Mahaifiyarsa hannunshi suka kamo suna rige-rigen yimai sannu da jiki.
Cikin taushin harshe Mahaifinshi ya fara magana " Kabeer lamarin Yankin nan sai addu'a faɗar gaskiya duk ƙanƙatarshi ya zama abin tsoro, amma naje Fadar Sarki Hammam da Shugaba Ɗayyib ya yi alƙawarin kawo ƙarshen gidan rawar da abokin kasuwancinshi ya ƙirƙiro kuma ya bani haƙuri, Kabeer ko da wata ɓarakar za ta kuma kunno kai ba na so na ƙara jin bakinka idan ba so kakeyi su kashemin kai a banza ba na roƙeka!." ya ƙarasa faɗa da kuka mai sosa zuciya.
Kai Kabeer ya ɗagamai alamar ya ji. Fara kiraye-kirayen Sallah ne yasa Mahaifinsa yin alola ya bar Gidan. Itama Mahaifiyarsa miƙewa tayi don yin alola kafin ta taimakamai shima ya yi. Ta na yunƙurin zuba ruwa a buta taji ana bubbuga Gidan a hankali. Fasa zuban ruwan tayi ta ɗauki mayafi ta lulluɓe jikinta.
Bai jira izininta ba ya yi gaba ya barta da buɗaɗɗen baki, zuciyarta na bugawa da ƙarfi ta nufo cikin Gidan ƙafarta na harɗewa. Mayafin fuskarsa ya yaye.
A take fuskarshi da yake abin tsoro a wajen duk wani Mutumin Yankin Tudu a tun shekarun baya da'a yankewa Bashar harshe ya bayyana. Da sauri ta dafe bakinta hawaye na ɓulɓulowa wani kan wani. Kai MALIK ya girgiza mata kafin ya ce " mai kike yiwa kuka?" Bata kaiga ba shi amsa ba Mahaifin Kabeer ya shigo don yakasa zaman Masallacin daya saba saboda fargaba.
Shima ruɗu da tashin hankali ya shiga sai dai shi ya yi ƙarfin halin zube gwiwoyinsa dukka biyu a gaban Malik ya na roƙonshi " ka tausayamin, haƙiƙa ni bani da wata masaniya a kan yanke harshen ɗan uwana Junaid, haka Iyalina. Ka yi haƙuri ka barmin ɗana ya rayu da mu saboda shi ya rage a kusa da mu, na roƙeƙa" Kai Malik ya ɗaga sama yana kallon ƙofar Ɗakin da Kabeer yake tsaye yana Kallonsu kafin ya ce " na zo ku bani Kabeer na tafi dashi, wata rana nayi alƙawarin dawo muku da shi a yanayin da zakuyi alfahari da shi, ba lallai naushin Sihirin da su ka yimai ya barshi ya rayu ba, kuma ko da ya rayu wata rana dole zasu rabaka da shi" yana ƙarasa faɗa ya matsa inda Kabeer yake a kafaɗa ya saɓashi duk girmanshi, batare jiran amincewar su ba. fuskarshi ya ƙara lullɓewa ya nufi hanyar barin Gidan. Da ya juya baya, Kabeer hannayenshi duka biyu ya ɗaga a hankali ya na yiwa Iyayenshi sallama, tausayinsu na mamaye ilahirin zuciyarshi. Suma kuka suka saki bayan fitarsu suna ƙanƙame juna.
Ba su yi tunanin zasu iya runtsawa bayan Malik ya tafi da Kabeer ba. Domin Malik tamkar mala'ikan ɗaukar rai haka yake a wajen Mutanen Yankin Tudu.
Haka kawai suke jin nutsuwa a ransu tare da gasgata alƙawarin da Malik ya yi musu na zai dawo mu su da Kabeer wata rana a yanayin da zasuyi alfahari da shi.
★washe gari Mahaifin Kabeer ya fitar da labarin ɓacewar Ɗanshi, don ko mai zai faru bai isa ya ce Malik ne ya zo ya tafi da Kabeer ba, indai ba so yakeyi shima yabi Ɗan uwanshi Junaid ba.
Babu wanda bai ƙara shiga taitayinsa ba.
Ta ɓangaren Mutanen Yankin da basu da masaniya a kan komai, tsoron faɗar gaskiya da alwashin ɗauke ido akan komai suka ƙara sawa ransu.
Ta ɓangaren waɗanda suke da hannu tsumu-tsumu da waɗanda suka san abinda yake faruwa amma basu da damar faɗa suma sun shiga ruɗun wanene ya ɗauke Kabeer?....
Kamar komai bai faru ba haka kowa ya cije ya cigaba da harkokin gabanshi, saboda ma su ƙarfin haline ma suke iya shiga yiwa Mahaifan Kabeer jaje, ragowar kuwa tsoron shiga Gidan ma sukeyi saboda gani sukeyi da zarar sun shiga jaje za'a biyo su Gida suma a sace su, ko a yanke musu harshe.
*****************************
A ɓangaren Hindu Mahaifiyar Sufyan taje Yankinsu, ta gana da Malaman tsibbunta har mutum Uku kuma amsar duk ɗaya ne;
"Naila itace tsanin matakin nasarar Sufyan. Duk tsananin duk abinda zai faru karta kuskura ta bari Aurenta ya suɓucewa Sufyan, saboda sana'ar kitsonta shine mafarin nasararsa, daganan kuma zai haifar da gagarumin abinda zai sa Sunanta da na Mijinta har da na shi kanshi Sufyan ɗin ya zama abin faɗe ga kowa ba a iya Yankin Tudu kaɗai ba har ma da duniya baki ɗaya. Canji mai girma gaske zai zowa Yankinku a wannan lokacin, amma fa dukka hakan bazai tabbata ba har sai Sufyan ya auri Naila ya samu matsuguni a Babban Birnin Abyad."
Kamar haɗin baki dukka amsa ɗaya ta samu daga bakin kowannen su sai dai sigar maganar da ya ke bambanta amma dukka ma'ana ɗaya yake bayarwa.
Mallakar matsuguni a Babban Birnin Abyad ko da na haya ne abune mai matuƙar tsadar da duk kuɗin da Ɗayyib yake taƙamar yana samu a Kasuwar Tukwanen Zinare bazai wadatar ba balle ta lallaɓashi ya amince. Da farko bata taɓa kawowa Sufyan yin Karatu a Babban Birnin Abyad ba, sai hasashen garuruwan da suke kusa da shi, don ko a Yankinsu Sarki Hammam ne kawai yake iya zuwa can ya yi kwanaki amma ba ire-iren su masu iya arziƙin Yankin Tudu ba. Ta ina zata samu kuɗi masu yawan da zasu isa Sufyan ya tafi Makaranta har ya kama mu su matsuguni a Babban Birnin Abyad?...
Mahaifiyarta da kusan dukka ɗabi'unta ta gada ta tunkara da batun. Cikin ƙwarin gwiwa ta bata shawarar mai zai hana su tara dukka kadarorinsu waje ɗaya su kasa shi kashi uku su siyar da kashi biyu.... Da farko Hindu ƙin amincewa tayi da shawarar Mahaifiyarta ta har na tsahon Kwana uku. Tuno da Sufyan zai samu gagarumin ɗaukakar da sunansu zai zama abin faɗe ba a iya Yankin Tudu kaɗai ba har da duniya baki ɗaya ya sa ta amince.
Hindu bata dawo Yankin Tudu ba sai da kuɗi masu yawan gasken da ta zubo a Akwatin ƙarfe garƙame da mukulli. A daren ranar ta tari Sufyan da zancen. Mayan idanuwanshi farare ƙal ya zaro, tsabar ruɗewa hannuwanshi har rawa sukeyi wajen kamo nata hannun. "Ummi ki ka ce me? rayuwa a Babban Birnin Abyad? Kina nufin nakai matsayin da zan tafi can nayi Karatu Ummi ki ƙara faɗa dan Allah ko nine banji da kyau ba"
Dariya, ruɗewarshi ya bata, don haka sai da ta ɗan dara kafin ta zayyanomishi duk abinda ya faru da shawarar da Kakarshi ta bata har ta samu ta dawo da kuɗi ma su yawan gasken da zasu isheshi ya naimi Makaranta, su kama Gida har na tsahon shekaru biyu.
Lokacin da ta sa ɗan mukulli ta buɗe Akwatin kuɗin zabura Sufyan ya yi har sai da ya miƙe tsaye yana nuna kuɗin, duk girman kanshi da jinkanshi kasa jurewa ya yi yasa kuka yana ƙanƙameta, haɗe da faɗin "Ummi ba Naila ba kowa kike so na aura na amince, na gode Ummi Allah Ya sa na cikamiki burinki kamar yanda kika cikamin Burina" Bayanshi take shafawa ranta fari ƙal.
Bayan Ɗayyib ya dawo ya huta ta sanar dashi duk abinda ya faru bata ɓoyemai ba. Da farko ya ɗanyi jim da bata laifin da ba taje wajen Malaman tsibbu ba, da bata tono abinda yafi ƙarfinsu da zai kaita ga siyar da kadarorinsu na manyan kuɗaɗe irin wannan ba. Ƙara marairaice murya tayi har sai da tasan yanda tayi ta yaudareshi ya yi alƙawarin nemo kuɗi ma su yawan gaske domin Sufyan ya ƙara, su biya kuɗin hayar shekaru uku maimakon biyu, kafinnan sun san komai zai bayyana kanshi. Hindu zata iya cewa bata taɓa kwanan farin ciki irin na wannan ranar ba.
Shima Sufyan a ɓangarenshi yakice batun Naila ta taɓa abota da Sulaim ya yi ya amincewa rungumar Aurenta hannu bibbiyu kafin ɗaukakarshi ta bayyana.
Kwana biyu bayannan Hindu ta bayyana a Gidansu Naila da sunan ta zo kitso. Ba iya Naila da Kakartane kaɗai ne sukayi mamaki ba, har da maƙotansu da waɗanda suka ga gilmawarta. A iya sanin da sukayiwa Iyalan Gidan ABDULYASAR MUSAA DHAHAB Magadan Sarautar Yankin Tudu kuma masu faɗa aji a Yankin Mutanene ma su girman kai, da kai Kansu inda Allah Bai kai su ba, kama daga kan asalin ƴan Gidan zuwa kan baren da'aka auro, idan ka cire Marigayi Abduh Dhahab. Don haka zuwan Hindu Iyali ga Ɗayyib uba ga Sufyan da yake ƙafafa da jin yafi kowa, saboda Shugabancin Kasuwar Tukwanen Zinaren dayake hannun Mahaifinsa suka san dole da manufa ba wai don zuwa wajen Naila kitso kaɗai ba.
Rasa wajen da zata bata ta zauna Kakar Naila ta yi, saboda nesa ba kusa ba Gidansu yafi na su Naila kyau da ababen more rayuwa, duk da suma nasu Gidan ba laifi da kyanshi dan yafi na dubban mutane a Yankin.
Cikin sanyi hali da na murya da kuma sanin girman na gaba Naila ta buɗe matsakaicinta bakinta mai ɗauke da siraran laɓɓa ta ce "Barka da Rana Ranki ya dade, da kin turo har gida zanzo nayi miki ba sai kinzo ba" murmushi mai kyau Hindu tayi tana dafa kafaɗarta saboda sanyi da daɗin muryarta da ya yi matuƙar birgeta sannan ta ce " Karki damu ɗiyata gaba idan zan ƙarayi sai kizo Gida kiyimin" Kai Naila da gyaɗa itama da kyakkyawar murmushi a saman fuskarta.
Da dabara take kallon duk wa su motsin Naila har aka fara yimata kitson da tace guda goma take so.
Kuɗi mai yawa kwatankwacin wanda Iyalan Sarki Hammam suke bawa Naila idan taje Gida yi musu ƙananan kitso ta bata. Daƙyar Naila ta karɓi kuɗin don sai da Kakarta ta saka baki.
Yanayin Naila da dabi'unta sun matuƙar burge Hindu, don da ba dan burin auren Mace ƴar Babban Birnin da takeyiwa Sufyan kwaɗayi ba da ta amince Naila ta zama Surukarta ta har abada....✍🏻
***