ZINARE🔥

8

by @nafisatusasaal01

🔥ZINARE🔥

     

      SASAAL
    Arewabooks@sasaal

   
  08

Harajin da zai kai iya adadin kuɗin gidan hayar da ya yi alƙawarin biyawa Sufyan na Shekara ɗaya a Babban Birnin Abyad Ɗayyib ya tsawwalawa Ƴan Kasuwar Tukwanen Zinare. Wasun su har da kuka su na magiya amma ba bu wanda aka saurarawa. Sai bayan an tattara kuɗin ya zo yake basu haƙurin In sha Allahu Kasuwa mai zuwa hakan bazai faru ba. Dubban mutane ne suka koma Gida ransu a ƙuntace.

Ko da ÆŠayyib ya tattara kuÉ—aÉ—en basu kai adadin abinda yake nema ba har sai da ya haÉ—a da wanda ya jima ya na tarawa.

Tun kafin zancen neman Auren Naila yaje ga kunnen Danginta da ita kanta da Mutanen gari Dangin ÆŠayyib suka nuna sam basu amince ba. Ta ya ya Naila Æ´ar Gidan Mahmoud da yake Madinki talakan fitik zata shigo zuri'arsu? Hakan zubar da Æ™ima da mutuncin  Masarautarsu ne don haka sam su basu yarda ba.
Da labari yajewa Yayan marigayi Bashar Mahaifi ga ÆŠayyib murmushi ya yi a zuciyarsa tare da bada Umarnin nemawa Sufyan Auren Naila ba tare da jinkirtawa ba.

A ɓangaren Mutanen gari, ba su yi mamaki ba saboda sunyi zargin haka tun zuwan Hindu Gidan. A ɓangaren ƴan uwan Mahmoud da suke Uba ɗaya jiki na rawa suka amince ba tare da sanin Kakar Naila ko amincewar ita kanta Nailan ba.

Da labari ya riske Kakar Naila tsabar zabura sai da miƙe bakinta yana rawa take ambaton Sunan Allah don tasan ruwa baya tsami banza kuma tun a zamanin Budurcin Babbar Ƴarta Yayar Mahaifin Naila tasan wacece Hindu da makircinta. Itace silar rushewar auren Ɗan uwanta da Yayar Mahaifin Naila saboda kawai ba su da kuɗi. Baƙin cikin rushewar auren ne ya yi sanadiyyar mutuwar Ƴarta.

To idan zata hana Yayanta auren Yayar Mahaifin Naila saboda talaucisu tun a waccen zamanin wani dalili ne zai sa yanzu ta amince ÆŠanta ya auri Naila tunda su dai sunanan a Talakawansu ba bu abinda ya sauya.

Naila da take gyara dogon gashin kanta mai cika da tsaho a gefe ba tace komai ba, sai Æ™wallar da yayiwa ganinta yana. Ba ta da abin cewa, tunda burinta macaccen burine a zahiri, amma a baÉ—ini rayayye ne a cikin  zuciyarta tunda da shi zata mutu.

Tasan ko da Sulaim ya na raye ba lallai ya so Mace irinta ba. Sai dai Mutuwarshi ya sa tanajin ƙwarin gwiwar da wataƙila ya na raye da zai iya aurarta suyi rayuwar farin cikin da take hasashe.

Tasan dole wata rana, irin wannan ranar zata zo domin bazata dawwama a haka ba tayi aure ba, shiyasa tayi alƙawarin sawa kanta jarumtar amsar duk Namijin daya zo mata a matsayin Mijin aure, tunda son Sulaim a cikin zuciyarta ba Ɗan adam ba ne irinta balle ta yaƙeshi.

Kusa da ita Kakarta ta zo ta zauna tana kamo dukka hannayenta daga tazar gashin da takeyi.

Cikin tausayin jarabawar da yake samun Nailan akai-akai ta ce

" karki kiyi kukan zuci ke kaÉ—ai Naila ki fito da shi sarari muyi tare"

Naila tanajin haka ta saki Kukan daya maƙalemata tuntuni. Sun kai minti Talatin a haka kafin Kakarta ta jata Ɗaki. Manne da juna suka zauna kan Naila kwance a samar Kafaɗarta.

"Ba na jin tsanar Sufyan a raina duk da labarin É—abi'unshi marasa kyau da nake ji a bakin mabanbanta Mutune, sai dai ina tsoron wani irin Æ™ulli Hindu ta Æ™ulla da har zaisa ta amince ki auri ÆŠanta. Hindu Ƴar masu rufin asirce a Yankinsu, dalilin haka ta Æ™ulla makircin da ya haramtawa Habeebah yayar Mahaifinki auren Yayaanta saboda talaucinmu, domin sana'ar ÆŠinki muka gada daga Iyaye da kakanni, dalilin wannan baÆ™in cikin Habeebah ta rasa ranta. Babban burin Hindu a waccen lokacin shine ta auri ÆŠan babban Gida, Allah Kuma ya cika mata burinta. Babban ÆŠa ga Ƙanin Sarki Yankin Tudu na wacce lokacin ÆŠayyib ya nuna yana sonta, har sukayi aure. Abinda yake bani mamaki da tsoro shine idan har Hindu zata guji ÆŠan uwanta ya auri Habeebah saboda Talaucin mu tun a waccen zamanin, wani dalili ne zaisa yanzu ta bari ÆŠan da ta haifa a cikinta jinin Sarautar Yankin Tudu a wannan zamanin da burika suka yi yawa  ya aure ki duk da Æ™in amincewar da mutanen Masarautar suka nu na?"

Naila ba tace komai ba sai ƙara ƙanƙameta da tayi da dukka hannayenta, a haka barci ya fara ɗaukarta.

Sai da aka kira Sallar la'asar sannan suka miƙe, kowannen su zuciyarsa ba daɗi.

Har dare ya raba Kakar Naila ta kasa runtsawa, sai kai da take girgizawa lokaci zuwa lokaci saboda zuciyarta dake hasaso mata ai gara Halayyar Hindu da Halayyar mutanen cikin Masarautar Yankin Tudu.

Miƙewa tayi tana sarƙe hannuwanta waje ɗaya, Allah Ya ɗauki ran Mahmoud da Mahaifiyar Naila a tsakankanin Shekaru kaɗan kuma Allah ya jarabceta da mugayen Ƴan uwan uwa da na Uba gaba ɗaya idan aka cireta ita kaɗai ba bu wanda ya ke son Naila ko ya raɓeta sai domin buƙatar kanshi. Idan har ta zuba Ido Naila ta auri Sufyan to tabbas taci amanar Naila ba kuma zata yafewa Kanta ba, dole ta samo mafita ko da kuwa zai kaita ga gaban Sarki Hammam ne don Masarautar Yankin Tudu tamkar Masarautar Uƙubane ga baren cikinta har ma da Ƴaƴan cikinta.

Naila shafa gefenta ta yi taji ba bu Kakarta. A hankali ta miƙe, a tsakar gidansu ta hangota ta na zarya. Da sanyin tafiyarta ta ƙarasa bayanta. Cikin taushin harshe ta fara magana;
"Lokacin da na wayi gari ba bu Sulaim ya Æ™one, na ji raÉ—aÉ—i a raina, da na zo na rasa Mahaifi sai na Æ™arajin raÉ—aÉ—i amma ba irin wanda naji lokacin da na rasa Sulaim ba. Da rasa Mahaifiya sai na Æ™arajin raÉ—aÉ—in da sam ba shi da haÉ—i da irin waÉ—anda na ji a baya. Abin nufi zafin rasa abu a zuÆ™atan mu na da alaÆ™a ne da yanda matsayin abun yake a wajen mu, saboda haka nasan abinda kike ji Kaaka, amma karki bari hukuncin Ubangiji ya hanaki barci wajen tunani har ki kasa neman mafita a Gareshi.  Zuciyata mai kaushi ce akan abinda ba na so Kaaka. Auren Sufyan ba ya nufin komai gareni balle har ya hanani barci, abu É—aya na sani, idan abu mara daÉ—i ya sameni kuma na jure na yi haÆ™uri to tabbas Ubangiji Zai musanyamini da mafi alkhairinsa."
Naila ta ƙarasa faɗa da siririn kuka tana ƙanƙame Kakarta.
Itama Kakaa da rawar murya ta ce.
"Hakane Naila, amma ki sani zanyi iya yina don samar miki mafita domin nasan Hindu dole ta na da wata manufa, Naila ba na son rasaki, ke kaɗai nake gani na ji daɗi" dukkansu kuka suka sa, su na ƙara ƙanƙame juna a haka Naila ta jata suka koma ɗaki.

Sun É—auki tsahon mintina a haka kafin Naila ta ce;
" Maiyasa ki ke tsoron Masarautar Yankin Tudu,  ko saboda kashe-kashen da akayi shekarun baya ne?"

Kai Kaaka ta girgiza tana lumshe idanuwanta labarin asalin Masarautar kamar yadda Marigayi Mijinta babansu Mahmoud ya bata labari na dawo mata

```MASARAUTAR YANKIN TUDU```

Sarki Musa shine Sarki na farko da ya kawo sauyi mai girma a Yankin Tudu lokacin Mulkinsa. Daga wannan lokacin mutanen Yankin suka samu ƴanci da sauƙin abubuwa da dama, da shigowar gwamnatin cikin lamuransu. Sarki Musaa yana da ƴaƴa da yawa Maza da Mata daga Uwaye daban-daban amma wanda ya yi zarra a cikin su kuma ya fi ƙarfin arziƙi shine ABDULYASAR MUSA DHAHAB, Abdulyasar su biyu Mahaifiyarsu ta haifa, kafin Allah Ya ɗauki ranta. Matsi daga Kishiyoyi da asirce-asirce kala-kala da Abdulyasar ya fara fuskanta da ga ɓangaren kishiyoyin Mahaifiyar su bayan ranta ne ya sa Mahaifinshi Musaa ɗaukeshi daga cikin Ƴan uwansa zuwa Babban Birnin Abyad wajen Abokanan Kasuwancinshi don yin ilimin zamani dana Addini.

Anan Babban Birnin Abyad Abdulyasar Dhahab ya yazama Babban ÆŠan kasuwa.

Kasuwanci Zinare yakeyi da taimakon Bature Francis ÆŠan Aminin Mahaifinshi da ya É—orashi a  hanya har yazama hamshaÆ™in mai ArziÆ™i.
Dalilin wannan Kasuwanci na Zinare da ya ɗauka da matuƙar muhimmanci sama da Abokanan Kasuwancinshi ya sa suka sauya mai Suna daga Abdulyasar Musaa zuwa Abdulyasar Dhahab.

Bayyanar Abdulyasar Dhahab a Yankin Tudu a matsayin hamshaƙin ɗan Kasuwa babban abin alfahari ne a wajen Mahaifinsa Sarki Musa. Abdulyasar bai jima da dawowa ba Allah Ya amshi ran Mahaifinsa Sarki Musa. A waccen lokacin anso naɗa Abdulyasar a matsayin magajin Mahaifinsa ko dan ƙarfin arziƙinsa amma ya nuna bayaso da suka takura ya tattara ya gudu na ɗan lokaci. Dole aka naɗa Yaya ga Sarki Musaa Mahaifin Sarki Hammam.
Ƙarfin arziƙin Abdulyasar Dhahab da taimakon shi ga Talakawa Yankin sai ya shafe sunan kowa a Masarautar su kamar shine Sarkin Yankin. Lamarin ya na sosa ransu matuƙa, wannan dalilin yasa suka fara kaiwa dukiyarshi hari ta kowacce siga tare da alƙawarin kaishi ƙasa ko ta halin ƙaƙa.

Su na cikin wannan yanayin matar Abdulyasar Dhahab ta haifa ɗa Namiji Ubaidullah. Da taimakon Iyalinshi bayan ta haihu saboda kwaɗayin abin duniyar da sukayi alƙawarin za su ba ta kaso maiyawa, ta taimaka musu suka kai Abdulyasar ƙasa, duk da haka Abdulyasar Dhahab bai bar rayuwar Ɗanshi Ubaidu ya lalace kamar yanda suka so ba, ya miƙa amanarshi hannunshi abokannan kasuwancinshi suka tafi da shi can wata nahiyar, shi kuma ya cigaba da gwagwarmaya da azzaluman Masarautar su.

Ubaidu bai tashi dawowa Yankin Tudu ba sai da kowa ya fara mantawa da shi, domin da kyakkyawar Matarshi da Ɗanshi mai kama da shi Abdullah(Abduh) daya zama ƙaton saurayi ya dawo sai ƴar Yayar Matarshi da Mahaifiyarta ta mutu. Ga dukiya mai tarin yawa da Ubaidu Dhahab ya dawo da shi.

Dawowar Ubaidu Dhahab da dukiya da kuma zankaɗeɗiyar Matar da babu ma su irin siffarta a Yankin Tudu ya yi matuƙar sosa ran maƙiya Masarautar. Maimakon su yaba sai suka hau kushewa da aibata Ubaidu Dhahab ya auro bare mai kyan da zata kashe shi ta kwashe dukiyar da ya tara. Duk Abdulyasar na sane da su sai dai bai ce komai ba, sai jikanshi Abdullah da yaja a jiki.
Sanin matsawar Abdulyasar ya na raye ba zai barsu su kai Ubaidu ƙasa kamar yadda su ka kaishi ba, ya sa suka fara shayar da shi guba a sirrince ta hanyar amintacciyar hadimarshi. Cikin ruwan sanyi suka kashe Abdulyasar ba tare da kowa ya ankara ba.

Mutuwar Abdulyasar ba iya Ubaidu da Iyalanshi kawai ya taɓa ba har da mutanen gari, saboda alkhairinsa.

Bayan wani lokaci suka dawo kan Ubaidu. Duk da sun kashe Abdulyasar sun kasa kai Ubaidu ƙasa ta cikin ruwan sanyi kamar Mahaifinsa, sun tusawa ɗanshi Abdullah ƴaƴansu yaƙi yarda, saboda alƙawarin auren da ke tsakanin Abdullah da ƴar Yayar Mahaifiyarsa da suka taho tare da ita. Babu yadda su ka iya, haka suka haƙura Abdullah ya auri Aysha. Daga wannan lokacin ne suka ƙara duƙufa wajen ganin bayan Ubaidu ko ta halin ƙaƙa, da suka ga sun kasa, sai suka bishi har Gida suka yi mai kisan gillar da ya tashi hankalin mutanen Yankin.

A lokacin Iyalinshi Mahaifiyar Abduh Dhahab tayi Æ™ururuwar abi mata haƙƙinta amma babu wanda ya saurareta sai É—anta Abduh shima kuma alokacin shima ba shi Æ™arfin yin komai. BaÆ™in cikin hakan yasa ta tattara kayanta ta gudu aka neme ta aka rasa. Shima Abduh tattara komai nashi ya yi ya bar masaurata zuwa Gidan da Mahaifinsa ya gada a wajen Abdulyasar Dhahab. Daga wannan lokaci Abduh Dhahab ya barrata kanshi da masaraurar Yankin Tudu, ya dawo kamar kowanni É—an gari. Ba bu tsinke daga dukiyar  Ubaidu da ba su ga bayanshi ba.

Abduh ya na da buri mai zurfi, da kuma kishin Yankinshi, ya na son ya kawowa Yankinshi cigaba, kamar yadda Kakanshi da Mahaifinshi sukayi yunƙuri Allah bai ƙaddara ba. Wannan dalilin yasa ya fara tunanin mai zai ƙirƙiro sabo da zai kawowa Yankinshi cigaban da kowa zai amfana???

Abduh ya share sama da wata ya na tunanin abinda zai ƙirƙiro amma ya kasa samun mafita. A wani dare Ubangiji ya sanya masa tunanin ƙirƙirar Tukwane. To amma ai akwai mutane ma su ƙera Tukwane da yawa, ƙirƙirarsu kaɗai ba zai zama wani sabon abu da zai ja hankalin mutane ba, dole sai ya haɗa da wani sabon abinda mutane ba su san da shi ba. Har ya gama saƙe-saƙensa a wannan rana bai samu mafita ba.
★washe gari har Iyalinshi Aysha da ke ɗauke da tsohon ciki ya tuntuɓa itama ba bu wani basirar da ya zo mata.

A haka Abduh ya Æ™ara shafe wata ya na tunanin abinda zai sa Tukwanenshi su zama ma su jan ra'ayi da kwaÉ—ayin mallakar su a wajen Mutane. Ya na  cikin wannan tunanin  sana'ar Kakanshi na Zinare ya faÉ—o mai. Mai zai hana ya yi wa nashi Tukwanen laÆ™abi da Tukwanen Zinare, hakan zai zama sabon abu a wajen mutane, kuma abin rububi domin ko da mutum ba shi da niyyar siya zai so ya ga yaya Tukwanen Zinaren su ke, daganan wataÆ™ila yaji sun yi mai ya siya.

Da ya yi shawara da iyalinsa ɗari bisa ɗari ta amince, amma daga baya da ta fuskanci ɗan abinda ya rage mu su suke samu su ci, su sha Abduh yakeson kwashewa ya kafa sana'ar Tukwane sai ta nuna sam bata yarda ba, dama can lallaɓawa takeyi ta gaji da talaucin da suke ciki shine yanzu zai ƙara kwashe abinda ya rage ya yi jarin Tukwane da shi. Da lallaɓawa da kuma nuna mata gagarumin nasarar da zasu samu, cike da yaƙini Aysha ta amincewa Abduh.

Da zallar basirar ƙere-ƙeren da ya koya a wajen a Abokansa na bakin Kasuwa, Abduh ya ƙera Tukwanen da ya yiwa laƙabi da Tukwanen ZINARE zuciyarsa cike da ƙwarin gwiwa da kuma yaƙinin ko bai siyar ba a take wata rana zai siyar.

Lokacin da mutanen Yankin suka ga Tukwanen da Abduh ya ƙera dariya suka bushe da shi haɗe da faɗin " Abduh ya zo da abinda ba shi da wani amfani zai zallar yaudara, shikenan dan Kakansa da mahaifinsa sunyi kasuwancin ZINARE sunyi arziƙi, sai ya ce shima sai ya yi, to ai zasu ga waɗanda za su siyi waɗannan ruɓaɓɓun Tukwanen na sa, wai Tukwanen ZINARE tunda ya ɗauka kowa Mahaukaci ne irinsa."

Tsaf surutansu yake dawowa kunnen Abduh, ya na kuma sukarsa, sai dai ba shi zaisa ya ja da baya ba, sana'ar Tukwanen Zinare ba gudu ba ja da baya.

A ranar ta farko da Abduh Dhahab ya fita da Tukwanen Zinare Kasuwar maƙotan Yankinsu ba bu wanda ya siya, da ya tarkatosu ya dawo Gida sai mutanen Yankin suka dinga yi mai dariya. Matarshi Aysha da baƙin ciki ta kwana, dalilin haka ta tashi da naƙuda washe gari.

A babban Asibitin Yankin Aysha ta haifi Sulaim. Kallon fuskar jaririn kaɗai ƙarfin gwiwa yake ƙarawa Abduh Dhahab haka Aysha domin bai bar komai na Kakarshi Mahaifiyar Abduh da basusan inda take ba, kamar ita ta haifeshi.
Da yawa idan suka shigo Barka da hassadar kyan jaririn suke barin Gidan.

Abduh Dhahab ya cigaba da gwagwarmayar fita da Tukwanenshi Kasuwanni ba tare da gajiyawa ko ƙosawaba. A haka ya shafe shekaru biyu ya na wannan bautar babu wani cinikin arziƙi. Matarshi Aysha ta sha yunƙurin guduwa saboda talauci ya na lallaɓata ta haƙura.

A cikon shekaru na biyar ɗin da ya yi yana bautar bin Kasuwanni Allah Ya amshi roƙonsa aka siye Tukwanensa tsaf, har da neman ƙari. Addireshin Yankin Tudu yake ta basu tare da yi musu alƙawarin ƙera wasu Tukwanen ma su yawa ga waɗanda suka nuna su na son sari domin siyarwa. Lokaci da rana Abduh Dhahab ya tsayar mu su, tare da alƙawarin ba za su bar Yankin Tudu ba tare da iya adadin Tukwanen Zinaren da suka buƙata ba.

Da tsananin farin ciki ya nufo Gida, sai dai ya na zuwa ya tarar Aysha ta gudu, sai Sulaim da ya tarar da takarda a hannu. Abduh ya yi kuka shi da Ɗanshi kafin su haƙura su fuskanci rayuwarsu da sam babu walwala a ciki.

Ba ji ba gani Abduh ya ke ƙera Tukwane.

Ranar da ya rage saura kwana biyu ranar da ya yi alƙawarin kafa Kasuwar Tukwanen Zinare ya cika bai runtsa ba kwana ya yi kaiwa Allah kukanshi....

Wane fata kuke yiwa Abduh Dhahab da masu irin zuciyarsa???