ZINARE🔥

9

by @nafisatusasaal01

🔥ZINARE🔥

    

      SASAAL


     09

Abduh ya tuntuɓi Abokanansa su Ɗayyib, Mahmoud( Mahaifin Naila), Mallam da Mahaifin Malik su fito da Kayan sana'ar su idan da rabo sai su sayar batare da sunyi wahalar bin Kasuwanni da suka saba ba. Ga mamakin Abduh babu wanda ya yi yunƙurin tankamai, kamar ma ba su san abinda ya ke faɗa ba. Kunya suke ji su fitar da Kayansu azo ba'a siya ba ayi mu su dariya. Mahmoud Madinki ne, kayan yara da na manya dinkakku yake bi Kasuwanni yana siyarwa, Mallam kuma Qur'ani da littafan addinin musulunci yake fansarwa, Mahaifin Malik kuma maganin gargajiya yake siyarwa. Ɗayyib ne kawai baya sana'ar hannu taƙamaimai sai abinda ba'a rasa ba. Da Abduh ya fuskanci inda suka dosa sai ya nuna kamar bai damu ba, amma har cikin zuciyarsa baiji daɗi ba.
Da yaƙini Abduh ya share ƙaton filin Ubaidu Mahaifinsa da shi kaɗai ya Gada duk sun wawashe ragowar, ya jere Tukwanen da ya ƙera. A gefe ya shimfiɗa buhu shi da Sulaim suka zauna bakinshi bai gajiya ba da ambaton Sunan Allah. Har lokaci ya fara tafiya babu wanda ya zo daga waɗanda sukayi alƙawarin zuwa, mutanen Yankin sai suka fara leƙoshi su na dariya, bai nuna ya gansu ba, balle su gane abinda suke yi mai yana sukar zuciyarsa. Yunwa da ƙishi ne yasa Abduh Dhahab yunƙurin miƙewa tunda yasan ko yunwa zai kashe Sulaim ba zai yi magana ba. Har ya miƙe hayaniyar mutane daga nesa ya dakatar da shi. Fuskokin mutane ƙalilan ya gane a cikinsu amma ragowar duk yawon kasuwannin da ya gamayi bai taɓa ganin su ba. Waɗanda sukayi alƙawarin zuwa siyan Tukwanensa ne, bakin Abduh kamar zai yage wajen tarbar su, kafin shuɗewar hour ɗaya sun yi ciniki sun siye Tukwanensa gaba ɗaya. Mutum ɗaya a cikin su ne ya tambayi ina zai samu fansar Qur'anin da zai siyar?. Abduh Dhahab manta abinda suka yimasa ya yi, ya nufi hanyar Gidajensu da sauri kamar zai tashi sama, batare da tunanin za'a iya sace mai Ɗa ko dukka kuɗin cinikin da ya yi ya zuba a ƙarƙashin buhu ba, shi dai burinsa ya kira Abokansa ayi musu ciniki. 

Jiki na rawa, Mahmoud da Mallam da Mahaifin Malik suka nufo Kasuwar Tukwanen Zinare da Kayansu. Da rububi akan siye kayan har sai da suka ƙara komawa Gida suka ɗebo wasu. Mahaifin Malik ne kawai maganin gargajiyarsa ta ɗan yi ragowa.

 Bayan kowa ya adana kuɗinsa bakin kowannen su a washe, sai suka ɗaga Abduh Dhahab sama suna dariya jindaɗi da waƙeshi da waƙe kala-kalan da ya ke nuna jarumtarsa da dagiyarsa. 

Daga wannan rana Abduh Dhahab ya kafa Kasuwar Tukwanen ZINAREN da kafatanin mutanen Yankin su ke amfana da shi.

Bayan komai ya dai-daita Abduh Dhahab ya fita wani Yankin ya auro Mairam. A dalilin Mairam Mahmoud ya ga Mahaifiyar Naila ya aura saboda yawan zuwa Gidan da takeyi, kafin daga baya Abduh Dhahab ya haramtawa Mairam shiga ko ina, don dalilin shigarta Gidan Mahmoud ne aka fara samun masu zugata.

Halaccin Abduh Dhahab yasa Mahaifin Malik ba shi Malik ya dinga yi mai hidima, tunda lokacin Sulaim ba shi da ƙarfin da zai taimakawa Abduh da wasu hidindimun.

A sirrince ba tare da sanin kowa ba Abduh Dhahab ya ƙirƙiri Makarantun boko da na Islama da Asibitoci a Yankin da taimakon abokanan kasuwancinsa na Babban Birnin Abyad. Ya danƙa amanar komai a hannun Mallam ne saboda shi kaɗai ne mai ƴan uwa masu ƙarfin arziƙi a Babban Birnin Abyad da Sarki Hammam da mutanen gari zasu gamsu taimakon daga garesu yake, amma a baɗini Mallam ko ƙofar Gidajen Ƴan uwan nasa bashi da matsayin zuwa. 

Abduh Dhahab ya yi hakane don kawar da idon mutanen Masarautarsu akan lamuransa duk da sun san yana samun kuɗi amma ba su isa su ƙiyasta iya adadin abinda yake samu ba.

Abin mamakin duk da wannan girman halaccin na Abduh Dhahab ga mutanen Yankinsa bai sa sun ɗagamai ƙafa ba, a wasu lokutan sai su ce 

"ai Mahaukaci ne, banda Mahaukaci wanene zai zaɓi sadaukar da iya Gadon da Mahaifinsa ya barmai domin ya yi suna ya burge mutanen gari?" Babu wasu kalmomin su na ɓatanci da baya dawomai amma bai taɓa damuwa ba domin yasan a sannu zasu gane ranarsa.

Mutanen Yankin Tudu a ɓangaren halayya mutane ne ma su son kansu, butulci da rashin damuwa da damuwar Ɗan uwansu.

 A ɓangaren siffa kuma suna da kyan fuska da haske fata, manyan idanuwa buɗaɗɗu, yalwataccen kashin kaa da kaurin jiki, mafi akasarinsu ba su da tsaho daga gajeru masu faɗi da jiki sai masu matsakaicin tsaho da kaurin jiki, idan kaga mutum da siffa saɓanin wannan to Mahaifiyarsa ko Mahaifinsa ba asalin ɗan Yankin Tudu bane. Kamar Naila bata da irin siffarsu sai irin gashin kansu haka Sufyan shima ba laifin yana da tsaho da ginannan jiki amma duk da haka ya sirko da irin ƙibarsu da idanuwansu, dukkansu saɓanin Sulaim suke domin Sulaim ba shi da siffa ɗaya na mutane Yankin tudu kalar fatarsa idanuwansa, tsayuwar ginannen jikinsa tun yana yaro dukka ba irin nasu bane, shi yasa suke  ganin a kaf faɗin Yankin babu Matashin da daya girma a raye zai shafe Tarihin duk wani Matashi ɗan ƙwalisa a Yankin Tudu kamar Shi. Sai Malik mai irin hasken fatarsu da idanuwansu amma sam siffar tsayuwarsa kamar sun aroshi daga Mahaifiyar Abduh da Sulaim yake kama da ita. Wannan dalilin yasa Abduh ya ke son Malik har ranar da sukayi nasarar kaishi ƙasa.

 ```DOWAWAR LABARI```

Idanuwan Naila da suka ɗanyi jaa ta lumshe tana ƙara ƙanƙame hannun Kakarta, itama Kaka ƙara ƙanƙame hannun Naila tayi cikin kuka ta cigaba da magana;
"Su na kashe junansu abisa son zuciyarsu, ba tare da wani haƙƙi ba. Ba su taɓa nuna ƙin bare ya shigo cikinsu kai tsaye ba sai a kanki Naila, saboda talaucinmu. Shiyasa nakejin tsoro da fargabar kar kema su kashemin ke a banza, domin bani da dukiyar da zan jaa da su."

Da ƙarfin gwiwa Naila ta girgiza mata kai tana rungumeta cikin taushin lafazi ta ce "bazan mutu ba har sai lokacina ya yi, idan kuma lokacina ya yi ko ba na cikin Masarautar Yankin Tudu Allah zai ɗauki raina Kaka, batun cewa a'a ko ki kai kanki gaban Sarki Hammam abisa ƙin amincewarki duk mu haƙura mu gayawa Allah, In Shaa Allahu zai sauƙaƙa mana."  Da haka sukayi barci hannunsu ƙanƙame da na juna.

★washe gari Kakar Naila ta tattauna da Ƴan uwan Mahaifin Naila kan su bawa Iyayen Sufyan haƙuri Naila ta kammala Makarantar sakandare tunda saura wata bakwai. Da yake babu Allah a lamuransu sai suka taso mata bakinsu a haɗe, acewarsu  su kansu basu da tacewa duk abinda Shugaba Ɗayyib ya yanke dole shi zasu haƙura su bi.

Zuciyar Kakar Naila na tafasa ta nufi Gidan su Sufyan kai tsaye. 
Wani irin kallo Hindu take yimata da soyayyan idanuwanta da suke ƙananu a tsaitsaye farare ƙal. Murmushi ta yi kafin ta ce;
"Haba Ummu Habeebah ai da baki zo da kanki ba, Ni dai ina neman afuwarki akan abinda ya faru shekarun baya, sannan na fuskaceki amma bazan iya yanke hukunciba tunda Maigida Jalal( Mahaifin Ɗayyib) shi ya tura mutane da kanshi nemarwa Sufyan auren Naila. Ki bari Mahaifin Sufyan ya dawo In Shaa Allahu zan isar da saƙonki" godiya Kakar Naila tayi tana yunƙurin miƙewa. Da sauri Hindu ta dakatar da ita ta hanyar faɗin; 
"Bari na kawo miki abun motsa baki mana" kai Kaka ta girgiza haɗe da cewa; "bakomai Hindu, fuskantata da kikayi yafi komai yimin daɗi, Allah Ya ƙara arziƙi" duk da haka Hindu bata bar Kaka tabar Gidan batare da abinda tayi niyyar bata ba. Dama kuma tuntuni ta tanadeshi domin tasan har gaban abadan Mahaifiyar Habeebah bazata taɓa ƙaunarta ba.

Ko zancen Hindu bata yiwa Ɗayyib ba da ya dawo Gida, sai shirye-shiryen tafiya Babban Birnin Abyad da suke yi domin duba Gidan da Sufyan zai zauna da Naila saboda a gaggauce takeson ayi komai duniya tasan tasan da zaman ɗanta.

A ɓangaren Kakar Naila bayan ta koma Gida ajjiye Tufar da Hindu ta bata tayi a gefe, ta na bawa Naila labarin abinda ya faru. Murmushi mai tsayawa a iya saman laɓɓa Naila ta saki zuciyarta a raunane. 
Da nishaɗi Kaka ta ce "kinji daɗi ko ba ki ji ba Naila?" 

Naila sai da haɗiye abinda take ji sannan ta ce "na ji daɗi Kaka Allah Ya biyaki da Alkhairin Sa" Kaka ɗauke kanta tayi tana amsawa da "Amin".

Da yammaci aka turo ana sallama da Naila, ba ta tsaya ɓatawa kanta lokaci ta zura doguwar rigar da aka yiwa ado da saki baƙi da malulluɓinsa. A tsaye ta hango Sufyan, ya yi ado cikin ƙananun kayan da suka dace da siffarsa, fuskarsa ta maza masu raina mutane na tsaye ƙyam akan ƙofar Gidan su. Mutanen Yankin kowa ya wuce sai ya waiwayo ya ƙara kallonsa shi kuma yana ƙara hura siririn hancinsa. 

Tsaf yake ƙarewa Naila kallo haɗe da wassafa yadda zamansu zai kasance, tana da komai da yakeso dangane da Ƴa mace abu ɗayane kawai ya yi mata cikas a wajenshi shine rashin zamantowarta ƴar hamshaƙai ko wayayyiyar Babban Birni. Ya na son ƴar masu kuɗin ba irin Naila ƴar Madinka jikar Madinka ba.

Ƙarasowarta ne ya dawo dashi hayyacina, da girmamawa ta gaishe shi, ya amsa yana tattare girarsa, har ya fara hura hanci sai ya tuna da hudubar Mahaifiyarsa, a take ya saki ranshi yana janta da hira cikin aji da kamewa. Daga eh, a'a, uhm sune amsoshin Naila. Sufyan kamar ya shaƙeta maiyasa bazata ɗago ta kalleshi kamar zata lashe shi ba, ko dai itama har yanzu fuskar Matacce Sulaim bai bar zuciyarta ba? Tuna wannan kaɗai sai da zuciyarsa tayi bugawar daya ɗan dafe ƙirjinshi, jin kanshi da ƙarin tsanar Sulaim na dirarmai lokaci ɗaya. Tarin sumar kanshi ya shafo cikin isa da ɗacin dayake ji a cikin zuciyarsa ya ce " ki shiga Gida, ba ni da wani shagali da zanyi kamar yadda bani da lokacin ƙara dawowa gareki, ina fatan zakiyimin kyakkyawar fahimta" ya yi tunanin zata ji ba daɗi tayi magiya da nuna zumuɗin son dawowar kyakkyawan Matashi irinshi wajenta amma sai ya ga ta ɗaga kai alamar da gamsu. Kafin ta kai ga barin wajen tuni ya tashi lafiyayyen mashin ɗinshi ya baɗeta da ƙura. Kai Naila ta girgiza mamakin abinda ya tunzurashi na kama zuciyarta.

Kaka bayan fitar Naila ta janyo Tufar da Hindu ta bata kamar ana fizgarta ta ɗauko ta wanke ta soma ci, har Naila ta shigo tana gutsirar Tufar suna hira a hankali. Tana  gama ci barci ya ɗauketa. Da mamaki Naila take kallon yadda ta kwanta a jirkice kafin ta gyara mata har lokacin ranta cike da mamaki.

★washe gari Ɗayyib da Hindu suka ɗauki hanyar Babban Birnin Abyad.
Su da suka tafi da sunan kama hayar shekaru uku daƙyar suka samu mai sauƙi shima ba akusa da asalin tsakiyar Babban Birnin Abyad yake ba suka kama na shekara biyu. Sai guntun kuɗin da suka adana don biyan kuɗin Makaranta Sufyan idan sun samu sun haɗa da wani. Saboda Hindu shawarar siyar da ragowar kadararsu ta yanke idan ta koma.

 Har suka iso Gida labarin kyan Babban Birnin Abyad bai bar bakinsu ba, shima Sufyan tuni ya fara tada kafaɗa zuciyarshi da kanshi tsabar yanda yakejin girmansu gani yakeyi kamar gangar jikinsa ba zai iya ɗaukar su ba. Domin shi a yanzu yafi ƙarfin duk wani Matashi a Masarsutar su bama Yankinsu kaɗai ba tunda ko Ƴaƴan Sarki Hammam mace ɗayace ta taɓa Aure a can shima bawai cikin Babban Birnin Abyad ɗin bane daf da shine.

Har gari ya yi haske Kaka bata motsa ba wannan dalilin yasa Naila ta birkitota da ƙarfi, idanuwanta ta gani a kakkafe. Cikin yanayinta na nutsuwa ta fara ambaton Allah kafin ta nufi Gidan Yayyan Mahaifinta. 

Kwanan su biyu a Asibiti kaka taji sauƙi amma magana kam sai a hankali, sai ta wuni batace komai ba ko baifi tayi sau ɗaya ba, tanason bawa Naila labari da yunƙurin daƙile Hindu. Saboda kai tsaye ta fuskanci Hindu ce ta bata Tufa mai ɗauke da sirihin da zai duƙufar da ita ayi komai batare da ta iya yin yunƙurin komai ba, amma ba hali. Sai dai tayi ta hira da zuciyarta. Naila tayi kuka musamman da zancen zaman Aurenta a Babban Birnin Abyad ya cika lungu da saƙon Yankin. Har shishigi Ƴammatan Yankin suka fara yimata da fadanci kullum suna Gidan. 

Daga wannan lokacin Naila ta fuskanci labarin Yankin Tudu da abubuwan da suka faru a baya dole su zama Tarihi a rayuwarta, musamman idan tanaso ta tsira da lafiyar Kakarta domin itama ta gane Tufar da Hindu Mahaifiyar Sufyan ta bawa Kakartane ya mayar da ita haka.

Kakarta tana cikin wannan yanayin Masarautar Yankin Tudu suka fara gudanar da shagalin gagarumin bikin da ya tashi kan mutanen Yankin, har ma da maƙotan Yankunansu.

Da ido Naila take magana da Kakarta kuma harta fahimceta, duk wannan shagulgulan ɗaya aka gayyaci Naila da ƙawayenta ƴan shishigi. Sufyan ya yi kyau kamar ka sace ce shi ka gudu murnar tafiya Babban Birnin Abyad na ƙara haukata kanshi yanajin inama da Kabeer yana nan ya nuna mai shi ba'asan yinsa bane, kuma ba da iya Shugabancin Kasuwar Tukwanen Zinare suka dogara ba.

Wani irin kyau Babban Birni Abyad yake da shi har Sufyan da bai taɓa zuwa ba yakewa zumuɗi???...✍🏻