ZINARE🔥

Chapter 2: page 10

by @nafisatusasaal01

🔥ZINARE🔥

    

  NAFISA ALIYU SASAAL



   *CHAPTER 2*

*TAFIYAR NAILA DA SUFYAN  BABBAN BIRNIN ABYAD*
            

     
   Pg 10

A dai-dai lokacin da mutanen Yankin su ke ji inama da su ne zasu tafi Babban Birnin Abyad Naila na maÆ™ale da Kakarta ranta ba daÉ—i. 

Gabannin sallar magrib Malamin da ya ke yiwa Kaka rubutu ya aiko da shi.

Kaka da ke cikin matsanancin damuwa saboda abubuwa ma su muhimmancin da takeson sanarwa Naila amma babu hali laƙwas tayi idonta ƙyam a kan dogayen yatsun Naila da ke juyemata rubutu a kofi.
Kanta Naila ta kamo bata saketa ba har sai da ta gama sha. Yunƙurawa tayi ta miƙe, sai dai ko taku ɗaya ba ta yi ba ta ji Muryar Kaka na ambaton sunanta
"Naila" 
Da sauri Naila ta juyo cikin mamaki kafin ta rungumeta da ƙarfi haɗe da kai mata sumba a gefe da gefe ƙuncinta. Da tsananin farin ciki ta ce; " na ji daɗi sosai Kaka fargaba da komai ya gushe da ga gareni, Allah Ya cigaba da karemin ke" Kaka da tsananin farin ciki ta amsa da "Amin" sai dai bayan amsawarta ƙwallane ya cika idanuwanta da su ƙyam a kan Naila.
 Ta yunÆ™ura zatayi magana Naila ta dakatar da ita, ta hanyar girgiza mata kai. Amma duk da haka bayan wasu daÆ™iÆ™u sai da ta numfasa cikin karyewar zuciya ta fara magana;
"Kafiyata da nuna ikona ba za su yi tasiri a garemu ba, tunda tun kafin muje ko ina Hindu ta fito mana da manufarta ƙarara. Amma Allah Ba ya barci Naila, da ƙarfin mulkinSa zuwanki Babban Birnin Abyad babban nasara ne a gareki, makircinsu shine matakin nasararki In Shaa Allah."
 maganganun Kaka sun Æ™arawa Naila Æ™warin gwiwa a kan wanda take da shi, har tanajin zata jurewa duk wasu Æ™alubale da zasu biyo bayan zaman auren su da Sufyan.

A haka suka raba wannan dare su na hira saboda washe gari Naila za ta bar Gidan, mafi rinjayen hirar ta su a kan Tufar da Hindu ta ciyar da Kaka ne da kuma shawarwari da dabarun zaman Gidan Miji.

★washe gari da sassafe Dangin Mahaifin Naila su ka zo É—aukarta, saboda sunfi son a zo É—aukarta a inda su ka tsara. Kaka bata tanka ba sai rungume Naila da ta yi bayan ta sumbaci goshinta. Cikin Æ™arfin halin danne kukan da ta ke yi ta ce;  "Ki kula Naila, inanan ina jiran dawowarki wata rana da dumbin nasarar da zaki zamemin abin alfahari da Mutanen Yankinki gaba É—aya, ki mayar da hankali kan sana'arki saboda sana'ar kitso baiwane mai girma a Babban Birnin Abyad. Daga Æ™arshe ki tuna da shawarwarina, haÆ™uri, juriya da biyayya sune matakan nasararki" daga haka Kaka ta saki hannun Naila da ke kuka kamar zata shiÉ—e.

NAILA;

Barin Gidan Kakanta zuwa Gidan ƙannen Mahaifina ya tabbatarmin da na bar Gidan Kaka kenan sai kuma wata rana idan da rai da lafiya. Bayan na kai can zagaye ni su ka yi kowannen su na faɗar albarkacin bakinsa da sunan nasiha.

Ba bu nisihar su É—aya da ya shigeni saboda kallon maÆ™iya na ke yi mu su, kamar yadda su ka nunamin Æ™iyayya a zahiri. 

Ban tabbatar da ni cikakkiyar Marainiya ba ce, sai da dangin Mahaifina su ka miÆ™ani Masarautar Yankin Tudu. Sufyan ya na zaune a tsakankanin Iyayensa, wannan ya tunamin da nawa Iyayen dalilin haka sai kukana ya Æ™aru, takaicin yadda Æ´an uwan Mahaifina su ka dinga Æ™asÆ™antar da kansu duk don samun wajen zama a wajen ÆŠayyib kamar ya kasheni. 

A ranar na zagaya Masarautar Yankin Tudu na kuma tabbatar da kyansa da mutane su ke zuzutawa, har gaban Sarki Hammam sai da na kai gaisuwa. Bayannan aka miÆ™ani É“angaren da zan kwana. 

Ban shafe hour biyu da kwanciya ba Matasan mata ma su kusan shekaruna su ka shigo, da alama turosu akayi don tayani kwana. Ba su san ba barci na ke yi ba su ka fara hira. 

Cikin jimami É—aya ta ce;
"Ai ni na jiyo abinda yafi Æ™arfina, ni dama na yi zargin Uwar gida Hindu bazata taÉ“a yarda wannan makirin É—an nata ya auri Æ´ar Æ™aramin Gidan da su ke talakawan fitik ba sai da wata manufa" 

Cikin rashin yarda ɗayar ta ce "Ni kam sam na kasa yarda da zancenki Ƙawata, ta ya ya zata sadaukar da dukiyarsu da ake zuzutawa a kan abinda ba ta da tabbaci a kai, anya kuwa kin jiyota da dakyau?"

"Wallahi tsaf na jiyota, ke harda sharaɗi ta ce ta kafamai, karya kuskura ya kusanci Matar kar a haifo mu su ƙasƙantaccen jika, ya bari su ga kalar ɗaukakar da zai samu."

 inajin su suka kwashe da dariya haÉ—e da tafawa, kafin É—ayar ta ce 

"To wallahi ki adana wannan dogon bakin naki idan ba haka ba shi zai kai ki ya baro ki, kin ji na gayamiki."

Da sauri ta damƙi bakin na ta kafin ta saki su ƙara kwashewa da dariya.

Daga kwancen da na ke jikina ya fara rawa, gumi da zazzaÉ“i su ka lulluÉ“eni lokaci É—aya. Kuka mara sauti mai fitowa tun daga Æ™asar zuciya na zuwar min, Æ™warin gwiwata na bin iska. Na É—auki lokaci ina kuka mara sauti kafin wahalallen barci ya fara É—aukata, har barci ya  É—aukeni ba su daina tattaunawa É“oyayyun sirrinkan da su  ka shafi Masarautar ba.

★washe gari da na farka da su nayi tozali su na barcinsu hankali kwance, daga yanayin suturun jikinsu na gane ba Bayi bane Ƴaƴan Gida ne.

Shagali na musamman aka ƙara shiryawa kafin tafiyarmu Babban Birnin Abyad.

FaÉ—a sosai Jalal kakan Sufyan da Mahaifinsa ÆŠayyib su ka yimin. A É“angaren Mahaifiyar Sufyan Hindu faÉ—ar hannunka mai sanda tayimin mai surke da baÆ™aÆ™en maganganun da ke nuna ba Mata ta aurawa Sufyan ba Baiwa ta auramai. A gabana ta Æ™ara jaddadawa Sufyan Umarninta, wanda bana raba É—ayan biyu akan hirar da naji Æ´ammatan jiya su na yi ne. Ba bu wani mai faÉ—a aji a Masarautar Yankin Tudu da baiyimin nasiha ba, wa su na su nasihar ta lallami suka yimin wa su kuma gori da nuna iyaka ne kai tsaye. 

Daga haka Drivern da zai kaimu Babban Birnin Abyad ya ƙaraso. Sufyan da ke sanye cikin tsadadden farin yadi mai taushi, malalacin murmushin da ke nuna jin kanshi ya saki haɗe da ɗagawa Mutanen Yankin da su ka yi kirco-kirco su na washe baki haɗe hannu. Idanuwansa a kan Mahaifiyarsa suka tsaya daga ƙarshe, alamar jinjina ya yi mata kafin ya shigo Mota ya na gyara zamanshi a gefen da na ke.

Da sannu da sannu motarmu ta fara motsawa har lokacin mutanen Yankin na É—aga mana hannu, kukan da na ke É“oyewa ne ya bayyana saboda tuna Mahaifana da Kakata da na san tana can tana kuka. 

Na bar Yankin Tudu da tarin rauni da tabo a cikin zuciyata, ko yaya zamana a Babban Birnin Abyad zai kasance??

Kuyi manage