ZINARE🔥

11

by @nafisatusasaal01

.🔥ZINARE🔥

    

      SASAAL


     11

Duk kukan da na ke yi, Sufyan ya na jina amma bai ce kanzil ba. Sai da ya fuskanci ba kukan ganin ido ba ne na gaske ne, sannan cikin isa da izzar fitarshi zakka a kaf faɗin ahalinshi saboda samun nasarar tafiya Babban Birnin Abyad ya ce;
"Kukan na menene? Kinsan ina zakije kuwa? Dan Allah karki ɓatamin farin cikina, ke da ma baki da Iyaye, ko ni da na ke da Iyaye a raye bandamu sai ke. Kar ki bari tun kafin tafiyarmu ta yi nisa ki fara saɓawa umarni na kinji na gayamiki" da ga haka ya ɗora farin yatsun hannunsa da ba su san wahalar komai ba a saman nawa dogayen yatsun. Maganganunshi sun sokeni irin sukar da Marainiya ƴar uwa ta ce kawai za ta san zafin su, saboda ƙara jaddada min da ya yi da gaske bani da Iyaye don haka bani da abin yiwa kuka. Ban ƙara ko tari ba sai idanuwana da na lumshe ina jin yadda Drivern Motar mu ya ke gudu.

A tashar da zamu hau Motar da zai yi tafiyar kwanaki kafin isar Babban Birnin Abyad Drivern da ya ɗaukomu mu kaɗai da ga Yankin Tudu ya sauke mu. Hannun Sufyan maƙale da nawa muka shiga ƙaton Motar mai ɗaukar fasinja da da yawa.

Ba mu jima a ciki ba bayan munci abinci, aka fara sanarwa tashin motar da komai na cikinshi ya ke kamar na jirgin Sama. 

A gefen Sufyan na ke zauna, kamar zai sumbaceni haka ya sunkuyo da sunan ɗauramin belt. Bayan ya ɗauramin ya ƙara kamo hannuna ya na sarƙewa da na shi.

Murmushi mai ciwo na yi a cikin zuciyata domin duk da ba ni ilimin sanin yanayin Maza ma su son kasancewa da mace zan iya cewa Sufyan ba lallai ya cika alƙawarin da na ji ance ya ɗaukarwa Mahaifiyarsa ba.

Tafiyar mu bana yini da kwana ba ne tafiyar kwanaki ne, saboda da su Sufyan hamshaƙan ma su arziƙine da jirgin sama za su  biya mana na ba mota ba. Duk inda zamu tsaya ba bu magana a tsakanina da Sufyan sai kayan guzurin da Mahaifiyarsa ta zubamai a ƙaramin Akwati mu ke ci akai-akai.

 ```BIRNIN ABYAD```

Lokacin da Motarmu ta iso Birnin Abyad, yanayin sanyin ƙasar, hasken Mutanen ciki, gina-ginensu, da wasu irin motoci ma su kyan gani a ido da kwaɗayin son shigarsu ne su ka haskemin idanuwa.
Idanuwana da na ke jinsu kamar madara saboda haske a Yankinmu sai na ke jin su kamar sun koma jajaye saboda kyawun mutanen Birnin Abyad da nake gani da gine-ginen su. Sai na ke hasaso Yankinmu kamar wani kusurgumin daji mai duhu da ya ke da ƙaracin kayan more rayuwa. Fatarmu da na ke ganinshi mai haske da kyau a Yankinmu a take ya dusashe a idanuwana ya koma sak na ƴan karkara, ƴan karkarar ma su ƙarancin komai na cigaban rayuwa. 

A maganganun su na fuskanci ba sa kai ƙarshen zance sai sun haɗa da harshen nasarar da Malaminmu yake ta kwaɗaitar da mu, mu koya.

 Wa sun su kuma nasarar kawai su ke yi babu sirki. 

Tunano yadda Mutanen Yankin Tudu su ka dinga ɗaga  mana hannu lokacin tahowarmu sai tausayin su ya ƙara tsargamin musamman Kakata da Mahaifana. Mahaifina ya ƙare rayuwarsa a dinki ƙarshe rashin gatan Asibiti ya yi sanadiyar ajalinsa, haka Mahaifiyata. Kakata ce dai ban cire rai tare da Yaƙini haɗe da fatan wata rana ta zo taga duniyar Birnin Abyad.

A ɓangaren Sufyan shima ji ya yi duk ya muzanta, wannan jiji da kan da sumarshi da ya tara duk domin ya zo ya Yaƙi Ƴammatan Babban Birnin Abyad sai ya bi ruwa, ya na jin inama da yana da hula a kusa ya lulluɓe gashin saboda Kunya. Farin fatar da ya ke yiwa Mutanen Yankin Tudu yanga da shi sai ya ga ashe da sauran shi. Kananun kayan da idan ya sa a Yankinmu maza da mata su ke bi su na kallo har da tuntuɓe sai ya tashi kamar na ƴan Karkara.

Lambar wayar wanda zai kai mu gidan da Iyayen Sufyan su ka kama Sufyan ya zaro a ƴar ƙaramar jakar da ya ɗauko ya na yanga da shi a Yankin Tudu saɓanin zuwan mu Birnin Abyad da ya ke ɓoyeshi a hammata. 

Cikin ƙarfin hali ya tambaya aka nunamai wajen kira. Shi kanshi sakayayyen wajen kiran da aka sakaye da gilashi abin a yaba ne. Nutsuwata ne ya ta taimaka wajen sakaya gidadancina, saɓanin Sufyan da dama can ba wani cikakken nutsuwa ne da shi ba, dan dole ya ƙaƙabawa kanshi nutsuwar dole kamar ba Sufyan Ɗan gidan Ɗayyib shugaban kasuwar Tukwanen Zinare ba😂. 

Ba mu wani jima ba, Uban gidan Ɗayyib mazaunin Birnin Abyad ya zo ɗaukarmu. 

Sai da muka tashi hawa Motar inda zamu je na fahimci ABYAD sunan ƙasar ne Birnin Abyad kuma shine inda aka sauke mu kuma anan Mahaifan Sufyan su ka kama Gida, BABBAN BIRNIN ABYAD kuma shine asalin Babban Birnin da kaf faɗin ƙasar ba bu kamar shi. 

To idan har Babban Birnin Abyad da nake ji a bakin Mutanen Yankin Tudu ya fi inda muke ciki kyau da tsari to ya ya kyanshi da mutanen cikin shi za su kasance???

Lokacin da muka shiga motar da za ta kai mu Gida idanuwana su ka faɗa kan Motocin da akace su ne masu shiga Babban Birnin Abyad, ko da banyi karatu mai zurfi ba, ban kuma saba riƙe kuɗi ma su nauyi ba nasan ba motocin shigar mutane bane irin mu. Tafiyarsu na ke kallo inajin kamar na fito na bi su. Sai na ke jin kamar ina ƙewar abinda ni kaina bansan menene a inda za su je ba, ina kallon tafiyar motocin wani yanayi na tsarga zuciyata, haka na yi taji har Motocin suka ɓacewa ganina.

Kasa jurewa na yi na tambayi wanda ya zo ɗaukarmu; " hour nawa ne tsakaninmu da Babban Birnin Abyad"
Amsar "hour biyar" ya bani tare da shaidamin zamu iya zuwa a ranar mu dawo a ranar. Sufyan da ya ke tunanin  na yi tambayar ne domin na nuna Iyayensa ƙarya suke yi, da su ka ce sun kama mai Gida a Babban Birnin Abyad harara ya watsomin ya na cije baki.

Unguwar mu da Gidan da aka kama mana abun a yaba ne, duk da ba na jin komai akan Sufyan na soyayya ko makamancin haka sai da na ji ya ɗan birgeni, saboda gida ne da ban taɓa mafarkin zan kwana a cikin irinsa ba har ƙarshen rayuwata.

SUFYAN;
Da Sufyan ya yi tozali da living room da two Bedrooms ɗin da su ka sha kayan ado dai-dai misali a matsayin hidimar da Mahaifan shi su ka yi mai sai ya ji kwaɗayin son kasantuwa da Naila na bin iska daga gangar jikinshi. 

Da farko kafin tahowar su ya yi zargin ashe dukiyar da ake zuzutawa Kakanshi na wajen Uwa ya mutu ya bari duk ƙaryane, banda ƙarya ne tayaya za'ace da dukka wannan dukiyar da wanda Mahaifinsa ya samo akayi hidimar kamamai Gida ba ma Siyamai ba a Birnin Abyad? sai kuɗin Makaranta da suka biya mai. Sai da ya gani da idonsa sannan ya tabbatar da dagaske ba ƙananun dukiya ba ne za su zaunar da mutum a unguwar da aka kama mu su Gida ba. 
Idan kuwa har Mahaifiyarsa za ta yi irin wannan sadaukarwa saboda ɗaukakarshi ba tare da damuwar komai ba, to ba bu abinda zai hana shima ya sadaukar mata da na shi farin cikin.

Amma duk da haka dole ya rage zafi, domin ba  zai iya kwana ɗaki ɗaya da Naila ya tashi da ita ba tare da ya kwashi rabonsa ba.

Gidan ba su su ƙadai ba ne, mutum huɗu ne a Gidan amma kowa rayuwarsa yake yi, ba tare da damuwa da rayuwar Ɗan uwansa ba.

NAILA;

wanka na yi na ƙimtsa jikina. Sai a lokacin naga kamar na ɗanyi kyan gani, saboda dattin Motar da na wanke daga jikina. Ɗakin da Sufyan ya bani a matsayin nawa nake ƙarewa kallo, nutsuwa na saukarmin.

Cikin baƙaƙen Abayoyin da na taho da su masu adon saƙi na shirya na tayar da Sallah ta inda na ga an shimfiɗa abun Sallah alamun nan ne gabas.

Uban gidan Ɗayyib ya hidimtamana ƙwarai da jikinsa da lokacinsa har ma da kuɗin aljihunsa. Abinci mai daɗin da bamu taɓa ci ba ya siyomana Da Suturar sawa kala biyu da ya siyo Sufyan don fara zuwa Makaranta sai wayar hannu da layi a ciki shima mai kyau dai-dai misali.

 A kunyace Sufyan ya sa hannu ya karɓa ya na ƙara tabbatar da ashe ba shi kaɗai bane ya raina kayan jikinsa ba dagaske kyan ne ba su da shi.

Da yake saukar Safiya muka yi bayan munci abinci, Uban gidan Ɗayyib ya yi mana Sallama da sunan washe gari zai dawo  barci ya kwashe kowannenmu a ɗakin da ya ke.

Ba mu farka ba sai azahar shima babu wanda ya fito a cikin mu tunda kowanne abinci da zai ci ya na dakinsa. Sai wajen ƙarfe 9 da ƴan mintina na dare Sufyan ya shigo ɗaki na. 

Gaisheshi na yi ina ƙara gyara lulluɓin kaina. 

Wayo da kuma shekarun da Sufyan ya fini yasa ya fara goge maganganun ƴan matan da na ji a Masarsutar Yankin Tudu. Da farko kusa da ni ya matso ya zauna saboda ya lura kamar inada sani ko hasashe a kan abinda ya ke ranshi. Cikin taushin lafazin da lumshe idanuwansa da su ke tsaye ƙyam a kan fuskata ya ce;

"Na san surutai da yawa za su yi ta zuwa kunnenki Naila, amma iyakacin wannan Gidan da kuɗin motar da Iyayena suka kashe mana ya kamata ace kin watsar da surutun auren manufa akayimana da ke, Mahaifiyata Mace ce mafaɗaciya kuma tana tsananin so na wannan dalilin yasa ta kuɗiri niyyar auramin matar da zata bauta min kamar Sarki da Baiwarsa, amma kisani Naila har cikin raina ban zaɓe ki domin kisha wahala a Gidana ba, sai domin muyi zaman aure ki bani goyon baya ɗari bisa ɗari akan karatu na. Ga shi kuma kuɗin Mahaifana ya ƙare a wannan hidimar da suka yimana, kuma a halin yanzu ina buƙatar suturun sawa kuɗin hidindimun makaranta da kuma abinda zamu ci Naila." 

Naila da batasan sanda ta ɗago kanta ba, idanu ta zubamai domin sam bata fahimci ina ya dosa ba.

Fahimtar hakan ya sa ya cigaba da magana cikin ƙaramin sauti.
"Naila da Baiwarki zaki taimakamin Ni kuma na yi alƙawarin mayar da ke mace ƴar gata a cikin ƴan uwanki Mata." 

Still Naila bata fahimci ina ya dosa ba don haka ta ƙara gyara zama.
Da kame-kame ya ce "ina so ki bi dukka Gidajen Unguwarnan ki sanar da su kina kitso, a kwai ma su ra'ayin kitso a cikin su, da wannan kaɗai zaki taimakamin Naila na roƙeki" 

Dan jim Naila ta yi maganganun Kaka na dawo mata "ki mayar da hankali kan sana'arki saboda sana'ar kitso baiwane mai girma a Babban Birnin Abyad."

Cikin yarda da rauni irina ƴa mace Naila ta ɗaga kai alamar ta gamsu ko dan Kaka tayi alfahari da ita. 

Da sauri Sufyan ya rungumeta kafin ya yi dabarar ragewa kanshi pressure ta hanyar sumbatarta da tattaɓa wa su gurare na jikinta sannan ya tattara ya bar ɗakin.

NAILA;
Da murmushin raɗaɗin da marata yakemin na mirgina na kwanta, abinda Sufyan bai sani ba zuciyata Macacciyace  ba bu rai balle a yaudareta, da sha'awa yana da yare da ko ya taɓani bazanji komai ba sai dai bani da ikon hakan.
Idan ƙarya yakemin domin ya zalunci ne Allah Shi ne gatana, daga wannan hirar zucin Barci mai nauyi ya ɗaukeni...✍🏻