ZINARE🔥

12

by @nafisatusasaal01

🔥ZINARE🔥

    

      SASAAL


     12

★washe gari bayan na yi sallar Asubahi ban koma barci ba, har sai da gari ya yi haske. 
Barcina bai yi nisa ba, Sufyan ya tasheni. Da kayan da aka siyomai jiya ya yi ado, ya yi kyau dai-dai misali domin bazan ce sosai ba, a matsayinsa na Mazaunin Birnin Abyad. Bayan na gaisheshi ya ji banƙara da komai ba sai ya haɗe rai ya na ƙara shafa wuyar Rigarshi. Sam ban fahimci ina ya dosa ba, sai da ya yi tsaki haɗe da faɗin; 
" Anya kuwa Naila ki na da lafiyar ido, na san babu Macen da za ta ce banyimata ba, amma ke kullum sai ki dinga nuna kamar Ni ɗin ba wani mai kyau ba ne, ko Hassada ki ke yimin?" ya tambaya da iya gaskiyarshi haɗe da murza zoben silver da ya ke matuƙar ji da shi.

Dariya ƙeta musamman a kan mugunta ba halina ba ne, amma da na ƙaremai kallo na tuna irin siffar Mutanen da muka riska a lokacin da muka iso Birnin Abyad sai da na murmusa har jerarrun haƙwarana su ka bayyana. Tunda na ke ban taɓa ganin Namiji mai son ace mai ya na da kyau ba irin Sufyan domin ko Mace albarka, "shi kuma kalar jarabawarsa kenan." Na faɗa a cikin raina amma a zahiri miƙewa na yi kafaɗunmu na gogar na juna na ce;
"Kai kyakkyawane ko ba ka yi kwalliya ba, balle yanzu da kayi ado da kayan da aka siya a Birnin Abyad, Godiya ta tabbata ga Ubangijin halittun da ya halicci Namiji kyakkyawa irinka Mijina."

 Dariya da ban taɓa gani ya yi irinsa ba ya saki, ya na kamo fuskata sumba ya saukemin a goshina tsabar daɗin da yake ji har wani lumshe ido yake yi yana bina da kallo kamar zai lasheni. 
Sallama ya yi min haɗe da sumbatar laɓɓana. Har ya fita ya ƙara dawowa ya na jaddadamin alƙawarin da na yi mai. 

Bayanshi na bi da kallo maganar Kaka na faɗomin; " ko wani Namiji da kalar halinsa, halin Mijin wata ba zai taɓa zama irin naki halin Mijin ba, dole a samu banbanci duk ƙanƙantarshi, don haka ki karanci halayyar Mijinki saboda samun sauƙin zama da shi." Na gazgata zancen Kaka a kan Sufyan saboda duk daɗin soyayya ko  kwalliyar da Mace za tayi  domin ta ja ra'ayinshi ba ya ɗaɗashi da ƙasa a kan ta zauna ta na zuzuta kyanshi da yaba kwalliyarsa sama da kyan da ya yi.

Kamar yadda na alƙawartawa Sufyan da maƙotana da mu ke cikin gida ɗaya na fara, ba na jin turancin arziƙi amma kuma hakan bazai daƙusar da ƙudirina ba. Ko da kwatacce ne da haɗe-haɗen iya wanda na iya zanyi mu su bayani har su fahimta.

Biyun dukka Mata ne kuma nayi sa'a dukkansu gashinsu na kitsawa ne amma ɗaya kai tsaye ta shaidamin bata da ra'ayin yin kitso saboda zafi ya ke mata. Cikin ƙanƙan da kai kamar na saba da ita na kwantantamata ta zo na gwada yimata hannuna ba shi da zafi. Ga mamakina cikin raha ta ce to na je around 2:00pm na dawo.

 Abinda Ruwaida Maƙociyata ta yi min ya ƙaramin ƙarfin gwiwar tunkarar ko ina domin tallata sana'ata. Mutum na ƙarshe a gidanmu Namijine ɗan asalin ƙasar Abyad fatarsa fari fat. Da sauri na fito duk kiran da ya ke ƙwalamin ban juyo ba, ina jiyoshi ya na dariya da alamun mamakin Gidadanci na ya ke yi.

Duk Gidan da zan shiga Daƙyar ake barina wasu su yimin tarba mai kyau wasu kuma su wulaƙantani. Gida na ƙarshe kuma mafi kyau a layin shi na tunkara sai dai kai tsaye dakarun da su ke gadin Gidan su ka hanani Shiga. 

A gajiye na dawo ɓangarenmu, saboda ba laifi na yawatu, ba kuma komai yasa na dage ba, sai don sauya tunanin Sufyan daga wanda Mahaifiyarsa ta ɗorashi a kai.

Kamar yadda Ruwaida ta ce na dawo ƙarfe biyu haka na koma. 

Yanayin ɗiban kitson da yadda ya kwanta a saman farin tafin kan Ruwaida ya matuƙar ƙayatar da ita ga shi sam ba zafi, godiya tayimin da tsananin farin ciki a saman fuskarta. 

Da Ruwaida ta tashi sallamata, ta yimin bayani iya adadin kuɗin da ta bani kamar yadda ake biyan makitsa a Birnin Abyad nutsuwata ce kawai ta riƙeni. Ba irin yawan kuɗin da Iyalan Sarki Hammam da ake matuƙar ji da su, suke bani ba ta bani kuɗine ma su ƙauri. Ƙwalla ƙwance a ƙasan idanuwana na ke yi mata godiya. Dariya ta saki cikin mamakin yadda na damu ta tambayeni daga ina nake?

 Saboda ta ƙara tausayamin ta naimomin customers, na ba ta labarin ni da Mijina ne mu ka zo, ya zo Karatu ne kuma kuɗin iyayenmu sun ƙare shine muke neman kuɗin cin abinci da sauran buƙatun rayuwa. Dafani tayi cikin tausayawa tare da yimin alƙawarin zata naimo min mutanen da zan dinga samun kuɗi amma na tambayi Mijina shin zai banni zuwa Gida-gida yin kitso?
Ban zaɓi yanke hukunci ba tare da na tambayi Sufyan ba, don haka na ce ta bari na yi shawara da shi idan ya dawo.

Daga haka mukayi sallama kuɗina ƙam a hannuna.

SUFYAN;

Lokacin da su ka isa Jami'ar Birnin Abyad da Ubangidan Ɗayyib ya yi cuku-cukun samo mai scholarship ya yi mamaki tare da ƙaƙabawa zuciyarshi cika alƙawarin Mahaifiyarsa babu gudu babu ja da baya.

Bayan sun gama yin komai. A ranar ƙarfe 12:00pm Sufyan ya fara ɗaukar lectures saboda tuni su ka fara ba bu shi.

Bayan sun gama lecture Harabar Makarantar ya fito ya naimi wajen zama, tunanin kuɗi da yadda zai yi kalar rayuwar da zai samu Mace wayayyiya ƴar Birnin Abyad ɗin da zai yaƙi mutanen Yankin Tudu da ita na addabar zuciyarsa. Ya na cikin wannan yanayin wata matashiya mai kyan gaske ta raɓa gefenshi ta zauna. Sanye take cikin ƙaƙanun kayan Saint Laurent riga da wandon da suka amshi farin fatarta sai lulluɓin da ya lulluɓe iyakacin wuyarta bai sauko kafaɗunta ba. 
"Barka dai kyakkyawan Matashi, sunana Sumaya, kai fa?" Ta faɗa da harshen nasara mai ɗauke da wani irin sanyi murya tana miƙamai hannu. "Kyakkyawan Matashi" da ta faɗa ya fi bugar da kan Sufyan a kan kyawun fuskarta. A ƙiyastin da ya yi cikin daƙiƙu zata yi sa'ar shekaru da shi, babu wani abu mai kyau a saman fuskarta da gangar jikinta da Naila da take cikin talauci bata da shi currently. sai wayewar da ta fi Naila da kuma hasken fatarta mai tsananin haske sosai. Cikin wani irin salon yadda ta birgeshi har cikin ranshi da jin nan take ya samu Abokiyar rayuwa ta zahiri matsawar ba ta fi ƙarfinsa ba ya ce;

 " Barka dai ya ke kyakkyawa Sunana Sufyan na ji daɗin haɗuwa da ke" ya ƙarasa faɗa yana damƙar hannunta.
 Daga haka kamar wasa hira mai cike da aji da zuzutawa kyanshi irin yadda ya ke buri da ga Naila ya ɓarke a tsakaninsu, har da musayar lambar waya. 

Kan Sufyan bai ƙara ɗaukar zafi da kwaɗayin mallakar dukiya ba sai da yaga Sumaya har ɗan ƙaramin mashin mai kyau take da shi, ba irin na shi na Yankin Tudu ba. Da sakin fuska ta yi mishi tayin hawa, ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗane.

A hirarrakin su kafin su isa Gida Sufyan ya fuskanci Sumaya ba wata ƴar ma su kuɗi ba ce ba a Birnin Abyad, naiman kuɗi ne ya kawo Mahaifanta har su ka haifeta a nan ta kuma yi dacen samun scholarship a Makarantar da shima ya samu. 

Ran Sufyan fari fes Sumaya ta saukeshi a street ɗin Gidan su, kamar kar su rabu haka su ka yi sallama Sufyan ya nufi hanyar Gate ɗinsu da ƙayataccen murmushi a saman fuskarsa.

NAILA;
Wanka na yi naƙara shirya kaina cikin abaya ta dai mai adon saƙi, sai dai ba baƙi ba ne kamar ragowar. Ina ƙoƙarin shiga kitchen don duba abinda zan iya dafawa daga Abinci da Ubangidan Ɗayyib ya kawo mana, na ji ana knocking. Ruwaida ce kanta ba bu kallabi da alama bata da mu dashi ba duk da kasantuwarta cikakkiyar Musulma. Mazubin abinci mai kyau na gani a hannunta. Cikin gwari-gwarin Turanci da zan fahimta ta shaidamin Abinci ta kawomin sannan gobe idan Mijina ya amince na shirya zata kaine wani Gida a ƙarshen layinmu da zanyi kitso. Godiya mai tarin yawa nayi mata kafin mu yi sallama.

Kasa taɓa abincin na yi, na zauna dakon jiran dawowar Sufyan mu ci tare. 
Da murmushi a saman fuskarshi ya shigo, sai dai yana ganina ya kalli Abayar jikina sai ya sauya fuska. Har cikin raina ban kawo komai ba, sai ɗaukar da na yi mishi a matsayin bauɗaɗɗen mutum mai saurin fushi.

Fuska ba walwala ya amsa gaisuwata haɗe da sumbatar ƙuncina kamar yadda al'adar Yankinmu ya ke.

Ruwan wanka na tashi domin haɗa mai ya dakatar da ni, duk ban damu ba ina dai zaune ina jiran shi. 

Bayan ya fito na gabatar mishi da Abincin da Ruwaida ta kawo mana, ba bu tambayar ina na samo? Na ci ko ban ci ba? Ya zauna ya take cikinshi sai kaɗan da ya ragemin. Jiki a sanyaye na ɗauka na ci raina ba daɗi. Fuskantar sauyi a fuskata yasa ya fara ƙorafin ai bai san banci ba, kuma maiyasa ma bansa hannu munci tare ba? Bance komai ba amma na ɗan ji sanyi a raina.

Bayan na gama na fito da kuɗin da Ruwaida ta bani da kuma Gidan da ta ce zata kaini, ga mamakina Sufyan ƙanƙameni ya yi yana dariyar nishaɗi, ba tare da wani jinkiri ba ya fara kasafta kuɗin.

"Naila kuɗinnan kawai abinda ya kamata shine na ƙara riga ko kala ɗayane ragowar kuma na samu na cin abinci a Makaranta Kinga yau ma da yunwa na wuni. Allah Ya yi miki albarka Naila" ya ƙarasa faɗa yana shafa duk inda hannunsa ya kai. 

Tambayar izinin fita ta gobe da na tambayeshi da Gudu ya amince ya na ƙara samun albarka. 

Cikin dabara da girman zaluncin rashin tunanin halin da zan faɗa idan tasa buƙatar ta biya ya fara ragewa kanshi zafi, har sai da yaji ya gamsu dai-dai misali sannan ya tattara ya barni a wajen. 

SUFYAN;

Wanka ya ƙarayi fuskar Sumaya da ya ke maƙale a cikin zuciyarsa na wasa da nutsuwarsa, sai ya ke ganin anya batafi Naila kyau ba? Dariya ya saki ya na lalabo wayarsa. Ba shi da kati kamar yadda ya sanar da Sumaya don haka ya zauna zaman jiran kiranta.

Da kiranta ya shigo sun sha hira. 

Sumaya da Sufyan soyayyar da zai kai su ga aure sukewa junansu, duk da yinin su ɗaya da haɗuwa.

 Sumaya tana ganin ta samu Talaka irinta tunda Sufyan ya gayamata Karatu ya zo yi da Yariyar da Mahaifansa su ka dage sai sun aura mai kar ya zo Birnin Abyad ya na neman Mata, idan ya so duk ranar da ya gama Karatu ya saketa idan kuma ya ji yana sonta to su cigaba da zamansu, shi kuma baya sonta ba kuma zai iya rayuwa da ita bayan ya gama Karatu ba. Ɗari bisa Ɗari Sumaya ta yarda da zancen Sufyan.

Shima Sufyan gani ya ke yi Sumaya itace Macen nunawa. Mace ƴar Birnin Abyad mai kyan sifa da tarin ilimi kuma ba ƴar talakawan fitik irin Naila ba.

Tabbas! Mahaifinsa Ɗayyib zai yi alfahari da shi Kuma Tarihi zai maimaita kansa domin kamar yadda Marigayi Ubaidullahi Dhahab ya dawo Yankin Tudu da tarin dukiya da kuma zankaɗeɗiyar Matar Aure haka shima zai koma Yankin Tudu da tarin Dukiya da kuma Sumaya a matsayin Matarsa..✍🏻