08
🔥ZINARE🔥
SASAAL
13
★washe gari bayan Sallar Asubahi ban koma barci ba kamar jiya.
Bayan na gama azkar na tashi na ƙimtsa ko ina. Abinci mara nauyi na yi mana, na jere a kan teburin cin abinci. Da na tabbatar komai ya kammala sai na koma ɗakina domin yin wanka.
Sufyan ranshi fari fes ya tashi, saboda mafarkin ya zama hamshaƙin mai Dukiya sanadiyyar Sumaya. Bai koma barci ba, sai dai ba zama Karatun Alkur'ani ko azkar ya yi ba, wanka ya shiga. Har Naila ta kammala girki Sufyan na washroom ya na kallon mudubi, fatarshi kuwa tsabar dirza da soso a tunaninsa hakan zai sa ya ƙara haske, har zafi ya ke mai. Duk motsin Naila ya na jinta har ta kammala ta wuce daƙi.
Da sauri ya fito ya cinye kusan abinci dukka yanajin alamun fitowarta ya tattara ya fita da sauri.
NAILA;
Lokacin da na fito na ga son zuciyar da Sufyan ya aikata banyi mamaki ba, saboda na san zai iya sama da haka matsawar hudubar Mahaifiyarsa bai bar zuciyarsa ba.
Ragowar na ƙarasa cinyewa, bayan abincin ya ɗan sauka na nemi waje na kwanta ina jiran zuwan Ruwaida.
Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana Ruwaida ta ƙwanƙwasa ƙofar sashena. Da hanzari na lulluɓe sumar kaina har zuwa ƙasan kafaɗuna da yalwataccen malulluɓi. Da fara'a sosai na tarbeta. Kamar jiya ba bu lulluɓi a ƙanta sai ƙaramin scarf ɗin data nannaɗe kanta da shi. Ba ta karɓi tayin shigowarta Sashena ba ta ce na taho mu tafi.
Mu na tafe mu ɗan hira har mu ka kusa ƙofar Gidan da dakarun Gidan su ka hanani Shiga. Nunawa Ruwaida gidan nayi haɗe da yimata bayanin abinda ya faru. Da farko dariyar da ya sa ta ɗan ranƙwafawa ta yi kafin ta ƙara kallona ta kuma sakin murmushi, da sauƙin turancin da ta san zan fahimta ta ce "Karki ƙara zuwa saboda ba wajen zuwanki ba ne"
"Saboda me?" na tambayeta da mamaki a saman fuskata.
"Gidan Simbi ne, Matar Uzair. Ahalin Shahararren ɗan kasuwa a Babban Birnin Abyad, ta zo gudanar da wani bincike ne a Asibitin jami'ar mu. Rayuwata ba bu sakewa sam, yawan zuwanki da sunan makitsiya zai iya janyomiki matsala don haka ki kula." Ruwaida ta ƙarasa faɗa ba bu wasa a muryarta.
Mutum ɗaya na taɓa ji da irin sunan a Yankinmu, kuma itace ƴar autarsu Malik uwa ɗaya uba ɗaya. Don haka faɗar sunan sai ya dawomin da tunanin abinda su ka faru shekarun baya. Simbi sun bar Yankin Tudu ta na yarinya ƙarama na girmemata da Shekara ɗaya.
Nasan ma ba ita ba ce domin babu yadda za'ayi ko Malik da ya ke Babban yayansu ya mallaki irin wannan Gidan a Birnin Abyad balle ita. Ban ƙara cewa Ruwaida komai ba har muka zo giftawa ta dai-dai saitin Gidan.
Ba ni da ciwon ido balle na ce shi ya haddasamin ƙarancin gani, fitowar Mota mai ɓakin gilashin da akayi ƙasa da shi kaɗan saboda ɗagawa dakarun da su ke gadin gidan hannu ne yasa nayi baya kafin na saki ƙarar da ya ja hankalin har na cikin motar ya ɗago kai saitin da muke kafin ya zuge gilashi gaba ɗaya ya fice daga layin.
SALMAN! Salman to ai ya mutu, tun shekarun baya, to idan ba Salman ba ne wanene wannan ko ƙaninshi ne?
Da hanzari Ruwaida ta taroni ta na faɗin "Naila! Menene ya sameki, kinsan shi ne? Ko bakyajin daɗi ne mu koma gida?"
Razanata na shanye na miƙe tsaye ba tare da bin bayan Motar da kallo ba na ce;
"Na shiga razani ne sai na ke ganin kamar na sanshi"
Ajiyar zuciya Ruwaida ta sauke kafin ta ce "ohh Allah! Naila kin bani tsoro to ai mutane ma su kamaceceniya su na da yawa a duniyar nan ki kwantar da hankalinki kinji?" Kaina na ɗaga mata alamun na gamsu.
Gidan da muka je dukka su ƴammatane su biyar kuma abokanan karatun Ruwaida. da alama Makarantarsu na kusa da nan.
Jarumta da son na tara kuɗi domin cikawa Kaka burinta yasa na yi juriya kitsa mu su gashin kansu dukka irin na Ruwaida na yi mu su. Waje ɗaya suka haɗamin kuɗin da ya sanyaya raina na ji zazzaɓin da ya ke shirin rufeni na sauka. Ba mu wani jimaba bayan na gama yi mu su muka bar Gidan. Yanayin shiru-shirun da na koma lokaci ɗaya ya sa Ruwaida cikin damuwa, dalilin da ya sa ta jani ɓangaren kenan kafin Mijina ya dawo.
A kan kurajerun living room ɗinta ma su taushi na lafe ina kallon shige da ficenta. Cikin yanayinta na barkwanci ta ce na taso na tayata girki. Ina shiga idanuwana suka sauka a kan Tukunyar girkinta, sunan jiki ne yasa na ƙarasa kusa da Tukunyar da sauri, "DHAHAB" ne rubuce a jikin Tukunyar kuma tare da sunan a ka ƙera shi ba sticker aka manna ba. A take zuciyata ta yi bugawar da ya sa na jingina da bango ƙwaƙwalwata na tariyo baya.
Ruwaida da raha ta ce " kema Tukunyar ya birgeki ko?, ai Kamfanin ahalin su Simbi ne, Yayana a can ya ke aiki shi ya yi min kyautarshi ranar murnar zagayowar haihuwa ta, kinsan kuwa nawa ake siyar da Tukunyan nan, Tukunya ne mai matuƙar tsadar, Ni kaɗai ce mai shi a cikin ƙawaye na, Tukunya ne da Sarakuna da ma su dukiya su ke girki da shi, shi kanshi Yayana da yake aiki a can da albashi shi muke rayuwa da ahalina a wadace, kinga kuwa ai ba ƙananun kuɗi ba n.." zubewa ta ƙasa kamar gini ne ya dawo da hankalin Ruwaida da ke surutun Tukunyar Dhahab kaina. Hankali a tashe ta jani da ƙyar zuwa living room.
Sashen Dr. Yasar moƙocinmu da na gudarwa ta nufa.
Da taimakon Yasar na dawo hayyacina, ko da su ka tambayeni ban ɓoye mu su abinda ya rikita ni ba. Ajiyar zuciya dukkan su, su ka sauke domin Ruwaida ta yadda da gaske kamanceceniyar Mutumin da na gani sak Salman da Tukunya mai irin sunan Abduh Dhahab ne kawai su ka rikitani a matsayinsu na mutanen Yankina ba tare da wani alaƙa ba, saɓanin Yasar da ya kasa yarda ba ni da haɗin komai da abinda ya rikitar dani sai alaƙar Yanki kawai.
Sai gabannin la'asar Ruwaida ta taimakamin na koma sashena.
SUFYAN; Bayan sun fito daga lecture Sumaya rakasa ta yi ya zaɓo kalar rigar da take so. Sauƙin kayan sawarsu da abincin cin su, yasa itama ya siya mata irin rigarsa su yi anko, ragowar kuɗin kuma abinci ya siya mu su mai lafiya suka ci suka ƙoshi, ɗan canjin da ya rage ya loda kati saboda kiran Ɗayyib.
Ɗayyib da Hindu sun sawa Sufyan albarka tare da nu na tsananin jin daɗin yadda Naila ta fara samun kuɗin da zai yi karatunsa hankali kwance, saboda Ɗayyib ya shaidamai bayan tafiyarsu da kwana ɗaya akaci Kasuwa bai san dalili ba sam babu cikini.
Bayanin Mahaifinsa sam bai ɗaga mai hankalin ba, tunda ya samu Naila ta fara sana'ar da su ke samun kuɗin shiga. Bai ba su labarin haɗuwar sa da Sumaya ba saboda ya san bazasu ba shi goyan baya ba, za su ce yayi wuri ya ɗakata shi kuma abinda ba ya son ji kenan.
A wannan yini da Sufyan da Sumaya su ka ƙarayi a Makaranta, shaƙuwa mai ƙarfin gaske ya ƙara shiga tsakaninsu. Kowannen su ya na jin ya yi dace da Abokin rayuwa dai-dai burinsa.
Kamar jiya ita ta koshi har bakin Street.
NAILA; Bayan na dawo ban iya aikata komai ba, barcin ma da ya ɗaukeni a zabure na miƙe saboda mummunar mafarkin da na yi, ga Salman ya biyoni zai ciremin harshe. A take wani irin tsoro da kaɗaici ya soma tsargani, a haka Sufyan ya shigo ya same ni. Bai tantace muryata da kuka ya dusasar ba, balle kayan jikina da banyi wanka balle na sauya su, kuɗin da'aka biyani a wajen kitso ya tambaya bayan ya zauna. Dama su na gefena, don haka na ɗauko na miƙamai.
Da ƙarfi ya ce "Allah! Naila sannu da aiki, Naila idan na gama Karatu na samu aiki sai kinfi kowa jindaɗi, kuɗin da kika ba ni yau ma riga ɗaya kawai na siya da shi, haka na wuni da yunwa. Yanzu kinsan mai za'ayi zan ɗauki kuɗinnan na ƙarasa siyen kayan sawa kinga mun gama da wannan, ɗan abin ya rage kuma na riƙe kuɗin makaranta ko ya ya kika gani, ko da yake bari na tashi na je yanzu saboda gobe lecture 7:00am zan shiga." Ya ƙarasa faɗa ya na miƙewa.
Kafin na haɗiye hawaye na tuni Sufyan ya fice, ko tambayar dalilin da ya sa banyi girki ba baiyi ba.
Sufyan ya zaɓi tafiya shi shi kaɗai ba tare da jiran gari ya waye ba saboda Sumaya karta sa ran zai kuma siyamata wa su kayan.
Sufyan ko tsinke baiyi hikimar siyawa Naila ba tunda itama kayanta duk Abaya ne ma su arahar gaske ga adon da aka yi mai na saƙi sak na ƴan karkara. Chocolate kawai ya iya siya da Naila shima kuma sai da ya haɗa da na Sumaya.
Daɗin samun komai da sauƙi yasa yake ta murmushi shi kaɗai har ya dawo Gida.
Lokacin da Sufyan ya dawo na ga bai siyomin ko tsinke ba kasa shiru na yi na ce;
"Ba ka kyauta ba, tayaya zaka siyo kaya iya kai kaɗai bandani? " Da farko da zafinsa ya ɗago amma kome ya tuna sai ya fasa ya fara lallashina haɗe da tambayar abinda ya ke damuna. Da salon dabaru Sufyan ya kalamanceni har ya yi nasarar tserewa daƙinshi bayan ya bani abinda ya siyomin. Na so ba shi labarin abinda na gani amma gudun kar ya kira ya fesawa Mahaifiyarshi ya sa naja bakina na yi shiru.
Daga wannan ranar Sufyan ya ƙara zage damtse wajen yin ado da kaya kala-kala, da zarar na samu kuɗi zai siyeni da daɗin baki ya karɓe, har Mahaifinsa ya sa ya tura Yaro a kaiwa Kaka waya muka gaisa.
Ranar da na gaisa da ita ban runtsaba, saboda inaso na bata labarin abinda na gani da wanda Sufyan yakemin amma ba hali domin zama yakeyi gadina idan muna waya da sunan kallon talabijin.
A haka rayuwar ta miƙa da Sufyan, da kuɗin sana'ar kitsona ya ke komai na Makaranta har ya yi wa Budurwarshi Sumaya duk ban sani ba, da shi ya ƙara ƙawata living room ɗin mu har da ɗakin kwananshi. A ɓangarena Suturar sawa na arziƙi ba ni da shi, idan nayi ƙorafi sai ya ce mezanyi da sutura ni da ba fita na ke yi ba, shi dama kuma ba ya son idan zan je yiwa Mutane kitso na yi kwalliya kar wani ya ƙwacemasa ni, shi ya ma fi son ya ganni na yi ado da kayan da na taho da shi saboda hakan na tunamai da Yankinmu.
A kwana a tashi Ruwaida ta fuskanci Sufyan cutata yake yi duk na rame nayi duhu saboda ƙewa da damuwa. Shawarar na fara ɓoye kuɗina ta bani, za ta rakani na siyi suturun sawa, idan ya tambaya na ce ita ta siyamin da kuɗinta.
Sufyan ya jera kwanaki uku ya na tambayata kuɗi sai na ce babu, da ya ga dai dagaske na ce babu kuma aljihunsa ya yi ƙasa sai titsiyeni da tambayoyi, ƙarshe ina kitchen ina girki ya shiga ɗakina ya bincike har sai da ya samu kuɗin da nake ɓoyewa. Ina tsaye ya shigo kitchen da kuɗin a hannunshi kafin na yi magana ya kwasheni da mari cikin zafin rai yake masifar yasan Ruwaida ce take zugani, wallahi ta ci darajar itace ta naimomin customers da sai ya ci mutuncinta ya wulaƙantata.
Sufyan ya yi tunanin ganin sauyi ko wani gagarumin ɓaci rai a saman fuskanta amma sai ya ga akasin haka kamar baiyimin komai ba, cikin neman magana ya ce "gaba zakiyi da ni saboda nayi miki faɗa ko,? to wai Naila saboda wa nakeyin karatunnan? Saboda ke nake da ƴaƴan da zamu haifa, Naila saboda tsoron kar mu zo mu tara ƴaƴa babu kuɗin kula da su yasa kikaga na daure har yau ban kusanceki ba, duk wannan bai sa ki tausayamin ba haba Naila sai a fara zugaki ki na ɓoyemin samunki."
Murmushin mai ciwo na yi kafin na kalli fuskarshi na ce;
"matacce ai ba shi da ran yin rigima da rayayye, idan kuma kasan yau ai ba kasan gobe ba, dalilin baiwata yasa ku ka kawoni Birnin Abyad, ga shi kana mora har ka na da ƙarfin halin yin iko da shi. Ba ni da ƙarfin yi ma iyaka amma lokaci zai yi maka a yanayin da baka taɓa tsammani ba"....✍🏻