ZINARE🔥

14

by @nafisatusasaal01

***

🔥ZINARE🔥

( ```The Gripping family saga with high Caliber) 
     
``` 
        SASAAL


          14

Sufyan bai ce min komai ba har na ɓacewa ganinsa. 
A ganinsa mai zai jiyewa takaici? kuɗi ne dai dole ya karɓesu saboda da su ya dogara.

★washe gari as usual ban koma barci ba, sai da na gama Breakfast.

 Ko da na farka misalin tara na safe, a yadda na jera abincin haka na samesa Sufyan bai ci ba. Nasan ya yi hakane saboda kuɗaɗena da ya karɓe, a karon farko hawayen takaicinsa su ka zubomin, ban tsawaita zubda hawaye na ba, ban kuma hana cikina abinci ba. Bayan na ci na ƙoshi na fito harabar Gidan ina shan iska.

Yasar na hango ya na yunƙurin fitowa, da farko na yi niyyar guduwa saboda ba na son haɗuwarmu, amma da na tuna taimakon da ya yi min ranar da accident ɗin sashen Ruwaida ya faru sai na jirkirta.

Yasar manazarcin halayyar Ɗan adam ne, kuma likita a babban Asibitin Birnin Abyad. Gaishesa kawai na yi ina matsar da kaina gefe ina ƙananun maganganun da suke fita a hankali.

Matsowarsa kusa da ni ya sa na juyo ina zare ido a tunani na ya ɗauka zaginsa na ke yi. 

Yadda na zare ido na ne ya sa ya saki dariya ya na shafa tarin sumar kanshi da ya tattara wajen ɗaya ya ɗaure kamar Mace.

Ba bu zato na ji ya ce;

"Maimakon zama haka mai zai hana Mijinki ya naima miki gurbin karatu a jami'ar su, idan ma ba shi da hali ki naimi izininsa ni zan biya miki Fisabilillah." 

kalamansa sun wanke dattin da ya jima danƙare a cikin ƙwaƙwalwa na tsahon lokaci, maganarsa abun dubawa ne a gareni, kuma shawara ne mai kyau amma tuna Sufyan ya sa na furta; 

"mijina ba zai yarjemin ba" na faɗa muryata na bayyana rauni na

Yasar ya kai wa su daƙiƙu ya na kallona kafin ya murmusa da cewa; 

"idan Mijinki ya na da sauƙin kishin da zai barki zuwa Gidajen da maza da mata su ke rayuwa, kamar Campus ɗin su Ruwaida yi wa Ɗalibai kitso, to babu dalilin da zai sa ya hanaki naiman ilimi. Menene amfanin neman da ba zamu gina gobenmu ba?"

 Kamar talabijin haka na zubawa fuskar Yasar mai tsananin haske da kyau ido, ba haskensa da kyansa na ke kallo ba, gaskiyar da ya faɗa nake gani a saman fuskarsa. Duk na san ya gamsu ɗari bisa ɗari na yarda da maganarsa amma ina kwakwanton naiman mafita sai ya ƙara ce min;

 "ga hanya mafi sauƙin warwarewa kanki komai, ki fara naiman izininsa a kan na ce zan biyaki kuɗi mai yawa ki kitsamin kaina, ki ji mai zai ce, idan ya ce a'a sai ki san dabarabar da za kiyi ki tambayeshi izinin naimar miki jami'a, idan kuma ya ce eh, kin samu hanyar da zaki tafi Jami'a cikin sauƙi, ki nutsu ki warware komai dalla-dalla za ki fahimce ni da kyau".

Cikin nauyin baki na yi mai godia. Har ya ɓacewa ganina ban daina kallon hanyar da yabi ba. 

Yinin ranar a tunani na ƙaresa domin na kasa yarda Sufyan ba ya kishina, shi da ya ce kishina ne ya ke hanashi siyamin kaya kar nasa wa su, su ga kyawuna, duk da nasan ba ya sona sosai kamar kuɗin da na ke samu. 
Kusantowar lokacin dawowar Sufyan ya sa na miƙe na ƙarayin wanka, kayan dai da na taho da su daga Yankinmu na saka, duk sun ƙode sun jeme.

SUFYAN; Sufyan kayan ciye-ciye da ice cream kala-kala ya siya mu su shi da Sumaya, har sun dawo sunyi lecture ya tuna rashin siyawa Naila kaya zai ƙara tunzura ta, har ta ɓullo da wata dabarar tara kuɗin a inda ba zai gani ba balle ya ƙwata, musamman wajen Ruwaida, kuma siya mata kayan zai kawar da tunanin ba ya sonta ba ya son farin cikinta a ranta. Bai naimi rakiyar Sumaya ba ya tafi, kusan rabin kuɗin ya siyamata kaya da su ba dan ransa ya so ba. Ƙiri-ƙiri Sumaya ta nuna ƙishinta, ranar ko ƴar hirar da su ke yi a kan hanya ba su yi ba, bakinta a gaba take tuƙi takaici da kishi na nuƙurƙusarta. Ko da ta sauke Sufyan kafin ya yi mata sallama ta figi mashin ɗin ta.
Jiki a sanyaye Sufyan ya shigo gida. 

NAILA;
Sufyan bai bani kayan da ya siyo ba, ɗakinsa ya wuce da kayan ransa fal kokwanton ko dai gobe ya kaiwa Sumaya, saboda bai ji daɗin yadda su ka rabu ba.

Jikinsa ba kuzari ya tsakuri abincin da na girka, nima tawa fuskar sam ba fara'a. Bayan na tabbatar ya huta na sako masa hirar neman izininsa zan yiwa Yasar moƙocina kitso tare da bayyana masa irin kuɗin da ya ce zai ba ni. Ga mamakina Sufyan ko alamar banbanci tsakanin jinsi Namiji da na Mace bai nuna ba yace ai neman kuɗi ne babu Matsala. Zuciyata da jinina na gudana da sauri-da sauri ta tambayeshi izinin komawa Makaranta, kai tsaye ya ce min "ba ni da kuɗi, ko kuɗin da kike ba ni kike yiwa baƙin ciki Naila?" Muryarta ta na rawar kukan da ya tahomin ina ƙoƙarin dannewa na ce;

"ance ba sai ka biya ba za'a samomin Scholarship" kamar an tsikaresa haka ya miƙe ya na masifa kamar zai taune harshensa. Sai da na bari ya gama kumfar bakinsa, sannan na miƙe haɗe da cewa;

"zuwa Makaranta, da sunan naiman ilimi, da zama aji ɗaya da Maza, amma kowa da Mazauninsa, ba bu kuma tilas ɗin mu'amalantar juna, iskanci ne. Amma zuwa Gidan da Maza su ke da sunan sana'a haɗe da kama kansu na kitsa saboda za su bani kuɗi mai yawa shi ba Iskanci ba ne Sana'a ne ko? Idan ka rayu a matsayin miji a gareni sannan ka zaɓi zaluntata da duƙushemin rayuwa wacce riba za ka samu Sufyan?" 
Ƙasa ya yi da kansa, ganin ba shi da mafita sai ya fara lallashina haɗe da garzayawa ɗakinsa a hanzarce ya kwaso kayan da ya siyo min. Kamar zai yi kuka haka yake magiyar gwadani ya ke yi kamar yadda akasarin Maza suke yaudarar Mata da sunan gwaji, idan banda haka ta ya ya zai yadda na yiwa Yasar kitso sai ka ce ba Musulmi ba, shi kanshi Yasar ɗin ai ba mutumin ƙwarai ba ne, idan ban da haka ta yaya zai ce Matar aure ta yi mai kitso. Da ire-iren waɗannan kalaman ya so yaudarata.

Ba bu daɗin bakinsa ɗaya da ya samu gurbi a cikin zuciyata, amma na ji daɗin kayan da ya siyomin. Kamar komai ya wuce haka na nunamai, domin ya ƙara shashantar da ni sai ya fara ragewa kanshi zafi kamar yadda ya saba. 

Bayan na koma daƙina kuka da ya sanyamin ciwon kai na yi, ba ni da wanda zan buɗewa zuciyata na zazzage dukka damuwata na gayamai sai dai nasha kuka na ni ɗaya a ɗaki.

★washe gari da Sufyan zai fita Makaranta Cikin dabara ya ke jamin kunnen rage mu'amalantar Ruwaida idan ba haka ba zata kai ni ta baro.
Abinda bai sani ba 
Kalaman Ruwaida a gareni ma su taushi ne haka zuciyarta da niyyar ta dukkan ma su kyau ne a kaina, idan ma cuta ce ta rasa wacce zata cuta sai irina. Ban ce mai kanzil ba har ya bar Gidan.

Da ga ranar na ƙauracewa zaman harabar Gidan, idan ka ganni a waje to Ruwaida ce ta haɗani da customer, ko kitso idan aka biyoni Gida a living room na ke zama mu yi.

A hankali a hankali na fara rama mai busar da Mutum tambayar duniya idan Ruwaida ta yi sai na ce mata"ba komai".
Sufyan ya haramtamin gaisawa da Kaka kullum sai ya ce ya kira Ɗayyib Mahaifinsa ba ya samu.

A kwana a tashi cikin hikimar Ubangiji muka shekara ɗaya da rabi a Birnin Abyad.

 A ɓangaren Sufyan ya canza ya ƙara haske ya yi kyau sak mazaunin Birnin Abyad, saɓanin Ni da na bushe na rame idan na yi dariya sai haƙora su cikamin fuska. Na ƙara samun customers wa su na je Gida wa su kuma su biyoni Gida, duk tarin kuɗin da nake samu Sufyan ne yake kwashewa domin akwai ranar da na ɓoye kuɗina a wajen Ruwaida, har ya titsiyeni da tambaya ban ɓoye mai su na wajen Ruwaida ba, a ranar sai da ya yi min dukkan da ya hanani motsi. Bayan ya fita Makaranta ya kira Mahaifinsa ya yi mai bayani. A take shima ya sanar da Uban Gidansa, washe gari jami'an tsaro mata suka zo har Gidan su ka jawa Ruwaida kunne haɗe da karɓe kuɗin da na ke tarawa, bayannan su ka yi mata tsakani da ni.

Ruwaida ta na tsoron abinda zai taɓa karatunta. Ba tare da ta nemi ƙara gani na ko tambaya ta ina sane ko ba na sane da  wulaƙancin da aka yi mata  ba ta tattara ta bar Gidan, sai ma su kwashe kayanta kawai na gani.

Tun da ga lokacin sai na zama kamar sha-sha-sha. Ga shi Yasar tun da ya ga ya bani shawara na yi watsi da shi har ina gudun haɗuwa da shi ya tattara lamarina ya watsar ko gaishesa na yi daƙyar ya ke amsawa. Yasar bai ƙara tsanata ba sai da ya ji labarin abin da ya faru tsakanin Mijina da Ruwaida. Daga wannan ranar ko gaishesa na yi baya amsawa.

Abubuwan da su ka faru da ni sun sa na yi losing hope, sai na ke ganin sakarwa Sufyan komai ya yi iyakacin zaluncin da Allah Ya ƙaddara a cikin rayuwata shi kawai ya  kwai  fiyemin sauƙi.

Da ga wannan dukan Sufyan ya mayar da ni kamar jaka, akan abu ƙalilan sai ya zane ni. ɗai-ɗaikun ranaku ne baya kai hannunsa jikina, ga dabaru da ya ɓullo da shi, haka zai sakamin videon tsaraicin wa su ya ce na nutsu na kalla irinsa zanyi mai. Da farko gardamar bazan yi ba na yi mai, ai kuwa ya kamani ya yi min dukan tsiya, abisa tilas ɗin rashin zaɓi na fara bin umarnin Sufyan. 

A haka mu ka ƙara shafe shekara ɗaya cikin uƙuba da tsanani, ba na gaisawa da Kaka, ba ni da abokin hira, domin wacce ta tare a ɓangaren Ruwaida sai da Yasar ya ja mata kunnen kar  ta kuskura ta kulani idan ba haka ba zan ƙulla mata sharrin da Allah ne Kaɗai zai wanke ta. 

Da kuɗin gumina Sufyan ya ke rayuwa, da  kuɗin gumina ya ke tari a Bankin da Ubangidan mahaifinsa ya yi mai jagora ya buɗe, da kuma kuɗin gumina ya ke yiwa budurwasa Sumaya siyayya. Ni kuma ko cikakken Suturar sawa ba ni da shi, idan na yi dariya tsananin munin na sai ya bayyana saboda rashin namar fuskata har wani yamushewa fatata ta yi. Sufyan ma ya kance ba ni da abinda zai mora a jikina duk na rame sai ƙasusuwan da zasu jimai ciwo, da wannan yake fakewa sai dai ya tuɓe ya yi ta umartata ina yimai abinda zai gamsar da shi.

A ɓangaren Sumaya da Sufyan soyayyar su kullum ƙara armashi ya ke yi saboda basa ɓoyewa junansu komai sai na ɓangaren da ya shafi sirrin su, Sumaya ko sunana bata son ji a bakin Sufyan wannan dalilin ya sa baya yi mata hira ta.

A yammacin wata asabar na shirya zuwa Gidan ƙawayen Ruwaida da ta taɓa kaini, domin ba ta muzantani a wajen kowa ba, dukka ƙawayenta waɗanda su ke kirana na yi musu kitso ba su daina ba ita ce dai kawai ta ƙauracewa haɗuwa da ni.
Ina fitowa na haɗu da Yasar, da na gaishesa daƙyar ya amsa yana gyara zamansa a han ɗan tudun da ya ke zaune.

Ban yi nisa da Gidan mu ba,  na hango lafiyayyen mota mai farin gilashin da mutum zai iya ganin na ciki, fuskar Salman na gani kamar dai yadda na gani a farkon zuwana Birnin Abyad. Da gudu na tunkari mota da ya ke tafiya a hankali ina kuka haɗe da magana da iyakacin ƙarfin muryata;

"Salman na san kai ne ka tsaya ka cikamin alƙawarina na roƙeka, ina shan wahala ka taimakeni ba ni da kowa a Birnin Abyad ka ji ƙaina ka faɗamin ina SULAIM da gaske ya ƙone ya mutu?" kamar yadda na yi tsammani bai tsaya ba ina ji ina gani mu ka haɗa ido cikin ido da mutumin da na ke ganin sak Salman shima nasa idanuwan kamar da ƙwalla kwance a ciki sannan yaƙarawa Motarsa gudu ya barni a wajen. Ƙasa na zube ina kuka. 

Yasar da ya ga komai kuma ya kasa jurewa nufo inda na ke ya yi, ya kamo hannuna ya kawoni har harabar gidan mu. Cikin taushin murya ya ce;

 "Naila menene ya ke damunki daga ina ki ke(ma'ana Yankina) " 

kasa magana na yi saboda shesheƙa. Na ɗauki mintina a haka kafin na daki  ƙirjina saitin inda zuciyata da na ke ji kamar zai fashe ya ke, sannan na fara magana sheshekar kuka na tare ni

 " ina shan wahala🥹, ina so na koma Yankina, ina ji kamar zan mutu...✍🏻