15
***
🔥ZINARE🔥
SASAAL
15
Bayan na gama furta ciwo da raɗaɗin da na ke ji a cikin zuciyata, sai na ƙasa magana saboda kukan da ya ci ƙarfina.
Kamar talabijin haka Yasar ya zubamin fararen idanuwansa ma su haske.
Na kai wa su daƙiƙu ina kuka, kafin na cigaba da magana;
"Sufyan ya na ganamin azaba, ya na dukana, ba ya barina na mori kuɗin da na ke samu. Ruwaida ita ce take taimakamin kuma ya yi mata sharri saboda ina tara kuɗi a wajenta ta bar gidan nan. Ni marainiya ce, ba ni gata kuma ba ni da ƙarfin yin komai ka taimakamin na koma Yankina"
"Ina ne Yankin ku Naila? Kuma maiyasa ƴan uwanki tunda sun san ba su da halin da za su iya taimaka miki a ko wani lokaci su ka ba wa Sufyan ya taho da ke har Birnin Abyad? Wannan gangancine mai girman gaske" Yasar ya faɗa da takaici kwance a cikin muryarsa.
Ba bu ƙarya a maganarsa amma ƙaddara ta riga fata. Cikin sanyin yanayin da ya ɗan fara shigata na ba shi labarin Yankin da na fito. Amma ban ba shi labarin dalilin da yasa na ke bibiyar mutumin da na ke zargin Salman ba ne.
Yasar ya gamsu da bayani na, amma sai ya jefomin tambayar "maiyasa ki ke kiran Mutumin da ya wuce ɗazun har ki ke cewa ya taimaka miki? Wanene kuma Sulaim ɗan uwanki ne? Ki faɗamin gaskiya idan da hali zan iya taimakawa."
Ƙur na yiwa Yasar da ido, tarihin abinda ya faru na kusantowa ganina kamar a lokacin su ke faruwa.
Waje na samu na zauna Yasar ya biyo bayana. A baya Yankina da mahaifana sun mutu kawai na faɗamai da rashin adalcin dangina na ɓangaren Uwa da na ɓangaren Uba, amma tunda ya nuna zai taimakeni na koma Yankina to dole ya ya san asalin inane Yankin Tudu da kuma surƙullen da ya ke cikinsa.
Kamar Yasar ya na ganin komai haka na ke ba shi labari tun da ga lokacin da na yi wayo har zuwa mutuwar Salman da abubuwan da suka faru bayan nan har aurena da Sufyan da kuma manufar Mahaifansa a kaina.
Mamaki ne zalla a saman fuskar Yasar, banda yana da ilimin nazatar Ɗan adam da kai tsaye zai ƙaryata Naila, wani irin Yanki ne wannan? Wani irin mutanene ma su ƙaracin basira ne a Yankin?
Kusantowar lokacin dawowar Sufyan ya sa Yasar gajarta tunaninsa. Cikin alhini ya ce;
"Tabbas! Naila akwai DHAHAB CITY a Babban Birnin Abyad, Unguwar da wani mashahurin mai arziƙi ya gina, Shekaru goma sha biyar baya. Ahalina ne ma su tsauri da tsantseni domin dai-dai ma su gadin alƙaryar Dhahab ababen tsoro ne, sai dai shi ba sunanshi Abduh ba sunansa Muhammad Dhahab kuma a zahirin da mu mutanen gari mu ka sani Ɗan asalin Birnin Abyad ne, amma wa su na cewa ba shi da asali babu wanda yasan asalinsa. Duk wani mai hidima da ma'aikatan Company's ɗin su, su na da record ɗin komai na sa, rayuwar su ba bu sakewa sam duniyar su tamkar daban ya ke da namu, ba bu wanda yasan sirrinsu sai makusantan su, Tun shekarun baya na naimi aikin tsaron sashen Babban Ɗan Muhammad Dhahab a yanar Gizo kamar yadda na ga an wallafa saboda ma su irin ilimina ake nema, amma saboda sun kasa samun cikakken bayani asalin ni ɗan inane da kuma inda Mahaifana su ke zaune, sai su ka fasa ɗaukata duk da cancanta, na yi kuka a waccen lokacin saboda albashin aikin ninkin wanda na ke samu a yanzu sau huɗu ne. Gane rashin samun cikakken asalina ya sa suka hanani aikin sai na tattaro Mahaifana na tara kuɗi na siya mu su Gida a Birnin Abyad, saɓanin daa da su ke a bayan gari. Sai dai duk da na yi haka samun aikin sai ya gagareni haka na gaji na haƙura.
Bayyanar Simbi ahalin Gidan Muhammad Dhahab a Asibitin mu sai ya dawomin da burina na baya, wannan dalilin yasa na fara bibiyarta ta taimakamin saboda zan ƙara samun sakewa wajen taimakawa mahaifana har na samu na yi aure, amma sai Simbi ta wulaƙantani dalilin da ya sa nayi zuciya kenan na haƙura da aikin.
Amma Naila dole yanzu zan ƙara zage damtse har Simbi ta saurareni, saboda shigata Dhahab zai bayyanarmin alaƙar tarihin Yankin Tudu da rayuwar su, fatana ki tayani da addu'a."
Baki, hanci, da ido dukka na saki ina kallon Yasar, cikin kokwanto na ce "menene sunan wanda aka ce shine Mijin Simbi mutumin da ya ke yimin kama da Salman?"
Ɗan dariya Yasar ya yi kafin ya ce;
"A binciken da na yi Simbi sam ba ta da Miji, kuma wanda ki ke gani sunansa Uzair, ba shi cikakken lafiya sosai saboda ya taɓa ciwon da ya yi shekara shida a kwance kafin ya warke, bansan wani ciwo ba ne, amma na samu bayanin ne da ga Yayan Ruwaida amintaccen ma'akaci a Companyn su, shima a sirrince ya faɗamin don haka ki kiyaye" kafin ya ƙarasa tuni na ɗora hannuwana dukka biyu a kan bakina alamun ba bu wanda zai ji.
Dariya Yasar ya yi kafin ya ɗoramin da nasihar na kwantar da hankali da ƙarfin mulkin Allah sai munyi nasarar shiga Dhahab ko a masu goge-goge ne.
Tuni na ji dukka ƙuncina ya yaye sai na ke ganin kamar komai ya zo ƙarshe, da wannan farin cikin na yi wanka na ci abinci. Gidan kitson da banje ba kenan na kwanta barci.
Daga wannan ranar ban ƙara ji daga Yasar ba gaba ɗaya ma sai na daina ganinsa. Da farko na ɗan damu sai da ya ba da gajeran saƙo a kawomin haɗe da suturar sawa ma su kyau da kayan ciye-ciye.
Babban akwatina na sauko da shi, na ɗura kayan gudun kar Sufyan ya gani saboda ya kusa dawowa. Ina kici-kicin mayar da akwatin hotona da na Sulaim ya faɗo, da sauri na ɗauke saboda har ga Allah bansan ya na cikin aljihun bayan Akwatin na da taho da shi ba, kuma nasha zuba kuɗi a ciki na kwashe amma hoton bai taɓa bayyana kansa ba. Da wani irin farin ciki na ke kallon hoton. Bansan na ɗauki lokaci a haka ba sai da naji Muryar Sufyan a baya na, dama ya na da key.
Firgitarwar da bayyanar sa yasa ni ne yasa na saki ƙara haɗe sakin ƙaramin hoton ƙasa, sai dai kafin ya cimma hoton tuni na yi hanzari ɗaukewa.
Fes Sufyan ya ga abinda nake kallo, ciwon da ya jima da shafesa a tarihin rayuwarsa ne ya yunƙuromai, cikin ɗacin zuciya ya fara dukana ya na ƙwallo da ni, haɗe da faɗin; "ba ni hoton wato amanata ki ke ci ko? Shi yasa kullum bakya ganin kyawuna, kina maƙale da wannan hoton shaiɗanin da ya addabi mutane duk da ba ya raye, wallahi idan baki bani ba sai na kusa kashe ki" maganganun sa ba su ƙaramin komai ba sai ƙaimin ƙara dunƙulewa da na yi da hoton waje ɗaya, idan ya kasheni ma ai na huta da uƙubarsa.
Har ya gama dukana ban warware daga ɗunƙulewar da na yi ba, cikin azabar kishi ya sa mukulli ya kulloni.
Kuma ya yi rantsuwar ba zai buɗeni ba har sai na bubbuga da kaina na yarda zan bayar da hoton ya ƙona kuma na ba shi haƙuri.
Haka na kwana na wuni inda Allah Ya taimakeni akwai kayan ciye-ciyen da Yasar ya aikomin da su, idan na ɗanci sai na kora da ruwan banɗaki na ɗoro alwala na kaiwa Ubangiji kukana.
A haka na shafe kwana uku ina manejin abinda Yasar ya bani ina korawa da ruwa kuma cikin hukuncin Ubangiji sai na ji na ƙoshi.
Banda shirmen Sufyan idan har shi da ya ke a iya haka yana ganin yafi ƙarfina to ina ga SULAIM da ya fishi komai ya na raye mai zai yi da ni? Sulaim tamkar Aboki ya ke a gareni, har ya bar duniya, ba bu soyayya balle alƙawarin aure a tsakaninmu. Dalilin da ya soyayyarsa ya ƙara samun matsuguni a cikin zuciyata shine barinsa duniya ne, ta hanyar da dole na tausayamai na kuma kasa mantawa da shi. Amma ko a raye ko a Mace bazan taɓa sawa raina lallai Sulaim sai ya soni ko ya aureni ba, matsawar ba ƙasƙancin da Sufyan yake nunamin dama nake so na fuskanta ba.
SUFYAN; A kwana na biyu da kulle Naila a ɗaki kafatanin kuɗin da ya ɗan rage a Bankinsa saboda ya turawa Gida kuɗi a rabawa Danginsa har da Dangin Naila da Kakarta da sukai ta samai albarka tare da farin cikin Naila tana cikin daula, su ka ƙare, ga shi ya saba siyawa Sumaya kaza, da su ice cream da sauransu har Gida ya ke siyamata ta kaiwa Iyayenta.
Tun washe garin da ya kulle Naila yake sa ran yunwa zai ci ƙaniyarta ta buga ƙofar ta ba shi haƙuri haɗe da ba shi hoton, amma ya ji shiru.
Daƙyar ya kalato canjin aljihunsa ya taho Makaranta. Ranar ba su ci abincin arziƙi ba don haka ya keɓe ya kira wayar da ya tura kuɗi aka siyawa Mahaifiyarsa .
Masifa kamar zata cijeshi ta waya,
"yanzu kai saboda ba ka san ciwon kanka ba shine zaka kulleta ka janyowa kanka asarar kuɗi ma su yawa, a kwana ukun nan banda kulletan da kayi da nawa zata samo maka? Amma wallahi Sufyan sam ba bu basira a cikin kanka, har yanzu ba zaka daina kishi da Sulaim da yake matacce ka gina rayuwarka ba, Yankin Tudu kowa ya na samaka albarka, kai kana can kana shirme? To idan bata so Sulaim ba a matsayinsa na mutumin da su ke tafiya Makaranta tare su dawo tare su je wasa tare kuma ya ƙone lokaci ɗaya ba wa kake so ta so eh? dabba mara tunani!"
Saukar kalamanta sai da ya sauya kalar fararen idanuwansa, ya na jin kamar ana barbaɗa mai yaji, zagin da Ɗayyib Mahaifinsa ya ɗoramai da shi ne yaƙarasa birkitasa, cikin rawar murya ya ke ba su haƙuri amma still Ɗayyib faɗi ya ke
" to yanzu haka Kasuwar Tukwanen Zinare ya mutu miɗis, sabuwar yunwa ta kunnowa Yankin mu kai, saboda an samu hamshaƙin mai arziƙin da ya saci fasaharmu ya mayar da su Tukwane na alfarma a kaf faɗin duniya ba bu inda ba'a siya, mu kuma an watsar da namu saboda ya zama tsohon yayi. Shine kai mun samu ka tsira zaka dawo damu baya, Allah Ya wadaran wannan son kyau na ka Sufyan! kai kullum ba ka da zance sai zancen Mutumin da tuni ya ruɓe a ƙarƙashin ƙasa, idan ka dama ka gyara to idan kuma baka dama ba kai sani. Kasan da abinda zaka biya kuɗin hayar ku idan ya ƙare"
Sufyan kanshi ne ya ɗauki zafi a take yafasa kuka yana ba su haƙuri. Shi gaba ɗaya ya manta da kusantowar biyan kuɗin hayar su.
Tahowar Sumaya inda ya ke ne yasa ya yi mu su sallama haɗe da yi mu su alƙawarin komai ya wuce, In Shaa Allahu zai gyara.
Kayan ciye-ciyen da Yasar ya aikomin da shi ba laifin ya na da yawa, amma ba irin sosai ɗinnan ba, rashin sanin ranar da Sufyan zai buɗeni yasa nake cancanensa kar ya ƙare na rasa abin ci, saboda ko zai mutu bazan ba shi Hotona da Sulaim ya ƙona ba.
Da yammaci ina zaune a inda na yi sallar la'asar na ji ya buɗe kofar, fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bai ce min komai ya juya ya fice.
★washe gari saboda rashin kuɗi ko Makaranta bai je ba. Ya na ɗaki ma su zuwa tambayar kitso su ka zo har mutum uku, ɗam jim na yi kamar na ce mu su ba ni da lafiya, amma yadda su ka nuna su na son kitson ya sa na amince. Sufyan dake laɓe yana kallonmu ajiyar zuciya ya sauke bayan amincewata.
Bayan na gama su na fita ya yi zumbur ya fito ya ƙwace kuɗin fuskarsa ƙunshe da dariya.
YASAR; duk wata hanya da zai bi ya samu ganin Simbi abin ya ci tura, abinda ma ya lura da shi kamar ba'iya son haɗuwa da shi ne ba ta yi ba, gaba ɗaya gudun mutane ta ke yi. Ranar da ya ji labarin saura kwana ɗaya ta gama abinda ya kawota ta koma Daular su, a bakin ofishinta ya wuni.
Ta na fitowa ma su gadin lafiyarta su ka rufa mata baya, kai tsaye tasa a hana Yasar bin bayanta. Sai dai kafin su kaiga riƙeshi ya taka da gudu zuwa inda motarta ya ke dai-dai inda ta ke tsaye yadda za ta jiyosa cikin yanayin maganar da matsawar tasan Naila zata fahimcesa a hankali da kuma sauri ya ce;
"Yankin Tudu, Daular Sarki Hammam Naila ƴar Gidan Mahmoud madinki, Aminin Abduh Dhahab....✍🏻