ZINARE🔥

16

by @nafisatusasaal01

🔥ZINARE🔥

     

        SASAAL


          16

"Yankin Tudu Daular Sarki Hammam, Naila ƴar gidan Mahmoud madinki, Aminin Abduh Dhahab." Yasar ya ƙarasa faɗa zuciyarsa na bugawa da sauri.

Dukan mai laifi kai tsaye ba tare da gudanar da ƙwaƙwaran bincike ba laifi ne mai girman gaske a ƙasar Abyad. Wannan dalilin yasa ko da jami'ai masu tsaron lafiyar Simbi suka cimma Yasar ba su taɓasa ba sun dai yi mai katanga tsakaninsa da ita. 
SIMBI; Designer jakar hannunta mai tsananin nauyin kuɗin da ya dace da arziƙinsu ta ƙanƙame da fararen hannunta ma su sanyi kyau ga mai Kallonsu, kafin ta juyo da kyakkyawar fuskarta. Idanuwanta da suke farare ƙal ta zubawa fuskar Yasar, batason dogon magana da shi, saboda doguwar magana a tsakanin su tamkar karya alƙwarin Alhalinta ne, don haka ta ce;
 "A ina kasan dukka wannan?."

Jira take yi ya saki layi ta sa akamashi saboda gudun shigarta matsala amma da yake Yasar wayayyene akan aikinsa da kuma fahimtar inda ta dosa kai tsaye ya ce;

"Gidan naiman taimakon ƙarshe, hannun hangu makitsiya mai ƙaracin shekaru." 

Jami'an tsaronta shirme suka ɗauki kalaman Yasar saboda ba su fuskanci ina kalamansa su ka dosa ba tunda ba su ji abinda ya faɗa lokacin da ya risketa ba. Umarnin barin wajen suka ba shi, bayan Simba ta shiga Mota.
Yasar bai musa ba ya juya ya bar wajen, maimakon ya koma Gidansa sai ya wuce na Iyayensa saboda yasan dole abi bayansa, domin ko shakka ba ya yi labarin tare Simbi da ya yi da tsayawarta ya isa Babban Birnin Abyad. 

SIMBI; bata manta fuskar Yasar ba, saboda tun ranar da ta gansa ta ji ya birgeta a ƙofar Gidan da ya faɗa, kuma a wannan ƙofar Gidan ya naimi taimakon aiki da gareta gaba da gaba na ƙarshe  saboda ta fito workout, gudun matsala da sanin abun da take saƙawa zuciyarta ba zai taɓa tabbataba yasa tasa a wulaƙantashi saboda ya yi zuciya kar ya ƙara bibiyarta.

Bata manta Naila ba, ba kuma zata mantata ba har abada,  saboda ƙawarta ce kuma maƙiyiyar Ƴar uwarta Barirah.

Waiwaye; lokacin wasannin ƙarshe mako a Daular Sarki Hammam akwai wata matashiya mai kusan Shekarun Sulaim da ta kwashewa Naila ƙafafu saboda ta matso kusa da wasa, har Naila ta kawo ƙararta wajen Sulaim. Ƙanwar Malik ce Uba ɗaya Sunanta Barirah.

 Mahaifinsu Malik, ya auri Mata biyu matarsa ta farko ita ce Mahaifiyarsu Malik, tun da suka haifi Malik ba su ƙara samun wani ba har Malik ya kai shekaru biyar, gajen haƙuri ya sa shi ƙara aure, ya auri Mahaifiyar Barirah. Bayan wani lokaci ta haifin Barirah sa'ar Sulaim daganan itama ba ta ƙara ba, sai Mahifiyar Malik da ta yi ta haihuwa, baƙin kishi da rashin son zaman lafiya ya sa Mahaifin Malik  sauwwaƙemata ya kuma karɓi ƴarsa Barirah. 

Barirah muguwar gaske ce musamman idan taga ta fika ƙarfi, ba ta baro komai na halin Mahaifiyarta ba. Da farko bata tsani Naila ba tana dai cin zalinta matsawar sun haɗu, amma daga lokacin da Sulaim da take son ya kulata ya riƙe Naila a matsayin ƙawa ta tsaneta ko aikota akayi Gidansu sai ta ranƙwasheta.

Wannan tsanar bai sauya zani ba duk tsayin shekarun da su Barirah suka kwashe a cikin daula, har gobe Naila itace kukan Barirah ita ce ta hana zuciyar Barirah sakat, ko menene dalili?

Wannan dalilin ya sa har gaban abadan Simbi bazata manta fuskar Naila ba, amma mai ya kawo Naila Birnin Abyad? Allah Ya sa ba wani Yaƙinne yake shirin tunkaro su ba.

 Saboda ta tabbatar da ainihin abinda yasa Yasar ya iya yin kasadar tararta kai tsaye saboda matsalar Naila kawai da kuma abinda ya kawo Nailan Birnin Abyad ta shirya tunkarar lamarin ita kaɗai kafin komai ya lalace.

A take ta soke tafiyarta da taimakon aminiyarta, ƴa ga Aminin mahaifinta Bushra.

NAILA ; kamar kullum da sassafe na yi ayyukana ban wahalar da kaina wajen girkawa Sufyan Breakfast ba saboda ba ci zaiyi ba, idan na yi a wajen yake barmin kayana.

Wanka na yi na ɗauko Abayar da ta zamemin tamkar na gado na saka, saboda ina jin tsoron saka wanda Yasar ya aikomin da su gudun duka da ga Sufyan, domin wanda Sufyan ya siyomin masu sauƙin kuɗine marasa quality duk sun zaizaye wa su guraren ma duk sun yage. Turare na fesa saboda customers kamar yadda Rufaida ta ɗorani a kai domin a wasu lokutan jikin mutum ya kan ɗanyi tsami wanda hakan ya ke takurawa ma su zuwa kitso musamman idan suka ɗora kansu a tsakanin ciyoyi. 

Sana'ar da ya zamemin jiki ko da yaushe shi na zauna yi( tunani) wa ni lokacin na saki kuka wa ni lokacin kuma na yi dariya. Ina cikin tunani na ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. Da hanzari na miƙe na nufi ƙofar.

Bantaɓa ganin fuskarta ba, don haka nayi mata tarba na musamman ina washe haƙoran da suke ƙara bayyana ramata. Ƴar gayu ce kuma da alama daga Gidan arziƙi ta fito.

A lokutan baya bani da surutu ba ni da yawan dariya irinna rashin kamun kai, amma tunani da ƙunci rayuwa suka sa na zama mai tsananin surutun da ni kaina bansan inayi ba, ga dariya da nake yawan yi na rashin dalili wanda ya zarta a kirashi fara'a. 

Ba mai yawa ta ce ta na so ba, don haka na yi mata irin yadda take buƙata.

Da ta tashi tafiya kuɗi mai yawan da daa  abayane ta bani su ihun murna zansa saboda ina da yaƙinin zan iya gina Gobena da su. 

Rashin fara'ata da yadda na yi ƙasa da kaina yasa ta magantu;

"Baiwar Allah ko kuɗin ne ba su yi miki ba, na ga kamar ranki a ɓace" ta ƙasara faɗa tana karantar yanayina.

A hankali na ɗago idanuwana da ƙwalla yasa na ke ganinta dishi-dishi sannan na ce;

"Na gode! na gode!! Allah Ya biyaki, amma dan Allah daga ina kike na baki kuɗin ki taramin?" Na ƙarasa faɗa kamar wacce batasan me take yi ba.

Idanu ta zaro kafin ta ce; "ta yaya ba ki Sanni ba zaki bani ijjiyar kuɗi bakya tsoron na gudu da su? saboda me ke bazaki ɓoye a ɗakinki ba ko ɓarayi su na damunku na sanar da jami'ai?" 

Kai na girgiza kuka da bana iya yiwa idanuwana shamaki da su na tahomin. 
Idanuwa ta ƙara zarowa wannan karan da mamakin  bayyane a saman fuskarta, cikin tashin hankali ta ce;

"Menene matsalar Baiwar Allah?" 
Cikin kuka na ce
"Inaso na koma Yankina amma bana iya tara kuɗi Mijina kwashewa ya ke yi domin gina gobensa, ya na dukana kullum, ki taimakamin kinji Don Allah nasan kinfi ƙarfin su bazaki Gudu da shi ba" 

kamoni ta yi zuwa jikinta tana shafa bayana kafin ta ce;

" Ya ya sunanki kuma ina ne Yankin ku? Ko zan iya taimakawa" 
Da sauri na ce ; " sunana Naila, yankin mu shine Yankin Tudu" 
inajin lokacin da zuciyarta ya buga da sauri, kafin ta ƙarawa cewa;
" Maiyasa ba zaki bawa Mijinki kuɗinki ya gina gobensa ba, gina gobensa ai tamkar gina na ki ne" 
Kuka nasa ina roƙonta ganin kamar ba ta fuskanceni ba. 

"Zan karɓa amma sai kin sanar da ni dalilin dayasa baƙyason mijinki ya mori kuɗinki alhali kuna tare bai sake ki ba" 

Kamar wacce take jira haka na soma sako mata zance da wanda ta tambaya da wanda bata tambaya ba. 
Ba ta ce min komai sai sallama da ta yimin ta karɓi kuɗin. 

SIMBI; Recording ɗin da Bushra ƙawar ta yi ta kunna mata, a tare suka sha kuka. Daga wannan ranar kullum sai Simbi ta tura Bushra Gidan Naila da sunan tayata hira a haka suka samu dukka bayanan da suke so, amma har lokacin Simbi ba ta fahimci waye Sufyan ba tunda sun bar Yankin Tudu ya na yaro. 

Lokacin tafiyar Simbi Gida ya yi, ba tare da sun samu damar bincikar Sufyan ba, don haka ta bar ragowar aikin a hannun Bushra ta tattauna da Yasar a sirrince domin ya sanar da su wanene Sufyan.

Dalili yawan tambayoyin Bushra da yadda ta saki jiki da ni duk da kasancewarta ƴar masu hali yasa na fara zargin ko Sufyan ne ya turota, da na fara zargin haka sai na daina bata kuɗina na nuna mata na sauko na fison Mijina ya gina gobensa domin mu mora tare.

 Babu kalar tambayar da batayimin ba, Sufyan Ɗan wanene a Yankinmu amma naƙi faɗa saboda tsoro.

YASAR; kamar yadda ya yi zargi an bibiyi bayansa, a sirrince suka bincika babu makitsiya a gidan, daga haka suka ɗora mizanin maganganunsa akan shirme kamar yadda sukayi zargi tun farko.

 Da sunan Ganin likita Bushra ta samu keɓewa da Yasar daya koma gaban Mahaifansa da zama saboda tsaro. 

Alƙawarin naimarmasa aiki ta yi matsawar ya gayamata Ɗan gidan wanene Sufyan a Yankin Tudu. 

Ko batayi alƙawarin cikamai burinsa na samun aiki a Dhahab ba ya yi alƙawarin taimakon Naila ta koma Yankin su ta kowacce fuska.

Bai ɓoyewa Bushra komai ba, ya kuma roƙeta ta riƙe amana, kuma a shirye yake domin ba da gudunmawa idan hakan ta taso.

A wannan rana kwanan tunani Bushra ta yi. Matsawar Simbi tasan Sufyan jinin masarautar Yankin Tudu ne, to ba shakka ba za ta taimaki Naila ba, dama kuma can ba tana son taimakon Naila ta wata fuska ba bane daban sai na mayar da ita Yankinsu. Amma ga Bushra ba irin wannan taimakon takeson yi wa Naila ba wanda zatayi farin ciki har abada takeson yi mata.

Ko da sukayi waya da Simbi kai tsaye ta sanar mata bata gama bincike ba.

A cikin kwana biyu Bushra ta binciko Sufyan ciki da wajensa har da soyayyarsa da Sumaya da abinda yakeyi da kuɗin Naila saboda ta samu tabbacin baya sana'ar komai.

Ta na son Naila taje Dhahab amma ta yaya? 
Ta na kuma son Sufyan ya ɗanɗani azaba ƙiri-ƙiri irin  ɗanɗanar da zai gusar da nutsuwar zuciyarsa yana ji yana gani, amma dole sai ya riski Dhabah, to amma ta yaya riskarsa Dhahab zai yiwu? 

Tsakiyar Dare ta naimi layin Mahaifanta, sunyi magana ya fi na hour huɗu, kafin ta katse ba tare da jira ba, ta dannawa Yasar kira.

★washe gari Bushra da ke lulluɓe cikin shigar larabawa ita da Yasar suka kaiwa Sufyan ziyara Makaranta. Sufyan tsaf ya gane Yasar, wannan dalilin yasa ya tsamke fuskarsa ya na bawa Sumaya umarnin ta jirasa yana zuwa.

Labarin haɗuwar takardunsa daga kan na primary har na secondary suke so da kuma shaidar takardun jami'ar da ya ke zuwa zasu samar masa aiki a Dhabah amma sai takardun Makarantarsa sun kasance na Birnin Abyad, za kuma a samar mishi sabon jami'a a can. 

Kwaɗayin da burin duniya su suka taru suka lulluɓewa Sufyan ido ya kasa tantace cuta da so da kuma tantance ina ne Dhabah maiyasa suka zaɓi naima mai aiki. Jikinsa na rawa ya tashi gefe ya kira Mahaifinsa.

Ɗayyib ihun murna yasa ba tare da tsayawa saurarar sunan Ma'aikatarba ya kira amininsa. 

Kai tsaye amininsa ya sanar da shi bashi da hanyar da zai samarwa Sufyan takardun bogi. A take Sufyan da jikinsa yake rawar murna ya yi sanyi laƙwas.

Jiki a sanyaye ya dawo wajensu Yasar.  Bushra da ke tantance son banza irin na Sufyan kai tsaye ta ce zata samar mai amma sai ya yi mata alƙawarin barin matarsa ta naimi jami'a ya kuma daina karɓe mata kuɗin sana'arta.

Son banza bai sa Sufyan ya tambayi kanshi ina Bushra ta samu labari ba, ya ce ya amince amma a iya bakinsa ya tsaya, domin har cikin ransa ya yi alƙawarin jami'a sai dai Naila ta ga anayi....

A cikin kwana biyu Bushra da ƙarfin ikon Mahaifinta a ƙasar Abyad suka samarwa Sufyan takardun bogi. 

Tare da Takardun Yasar Bushra ta shigar ta hanyar yanar Gizo tare da addu'ar dacewa.

Duk wannan wainar da ake toyawa Naila batasan ana yiba, sai shige da ficen Sufyan da take gani a ruɗe. 

★washe gari abinda ya shigar da Bushara Toilet ya fi sau uku shine Ɗaukar Sufyan aiki tare da wani irin albashin da ya tsoratata. Ba ita kaɗaiba dai-dai da Mahaifinta ya shiga zullumi ya kuma gano akwai babban Yaƙi domin ko rantsuwa ya yi bazai yi kaffara ba sun gano wanene SUFYAN.....✍🏻