17
🔥ZINARE🔥
SASAAL
17
Har yamma ta yi liƙis nutsuwar Bushra bai dawo jikinta gaba ɗaya ba. Idan wayarta ta yi vibrating har firgita takeyi.
Dole zancen Mahaifinta ya zama gaskiya banda haka Sufyan bai cancanci ya samu aiki lokaci ɗaya haka ba, dama dai Yasar ne da takaddunsa suke nunawa gogewarsa.
Har dare Mahaifinta bai kirata ya samu kira daga saman Dhahab ba wanna dalilin yasa ta ɗan samu nutsuwa a ranta, amma duk da haka sai da ta kira Simbi.
Yanayin muryar Simbi da shawarar da take bata na ta dawo ta ƙyale Naila domin ita ta fasa taimakonta ne yasa ta ɗan sanyi a ranta har ta samu sukunin kiran Yasar tayimai bayani.
Shawarar su haɗu washe gari a Gidansu Naila suka yanke.
NAILA; tunda na ɗauke yardata a kan Bushra na miƙawa Allah komai tare da alƙawarin ba zan ƙara naiman taimako a wajen kowa ba.
A tsakanin kwana da wuni Sufyan sam bai tambayeni kuɗi ba, kuma a kan idonsa na kitsa kan mutum biyu.
Ban yi mamaki ba, domin ga dukkan alamu akwai gagarumin al'amarin da ya tisosa a gaba.
A daren cikon kwana na huɗun da ya yi da daina tambayata kuɗi, kuma nima ban ba shi ba, ya kirani ɗakinsa.
Cikin muzurai yake sanar da ni samun aikinsa dalilin tonon Asirin da na yi mai a wajen Bushra, to ga kuɗina ya barmin amma na jira hukuncin da zai biyo baya.
Har ya gama kumfar bakinsa da maganganun izgilancinsa bance mai komai ba.
Daga ƙarshe ya jamin kunnen karna kuskura Bushra da Yasar su naima min jami'a na yarda na je. Idan kuma na saɓawa umarninsa wallahi sai ya hukuntani da hukuncin da har na mutu bazan manta da shi ba.
Babu abinda ya motsa daga jikina balle ya gane na fahimta ko ban fahimta ba, takaicin hakan yasa ya haureni da ƙafa ya na faɗin;
"Fice min daga ɗaki, sha-sha-sha kawai ai gashi garin ki tonamin asiri kin janyomin daukaka, kuma wallah na rantse bazaki ci ko sisi daga arziƙina ba"
Sam surutansa ba su dameni ba, tunda zai bari na tara kuɗina. Kuma ko su Bushra sun tambayeni inason zuwa jami'a da babban murya zan amsa "eh".
SUFYAN; ranshi fari fes yake ji, sunan ma'aikatar da za'a samarmai aiki na kai kawo a cikin zuciyarsa, anya babu wani sirri a cikin wanda ya kara DHAHAB(ZINARE) a cikin sunansa, Abdulyasar Dhahab Ubaidullahi Dhahab, Abduh Dhahab, duk ba su bar duniya ba sai da suka zama ababen koyi, ga shi ya kuma samun wani mai arziƙin a Babban Birnin Abyad shima Dhahab. Tabbas! A kwai wani ɓoyayyen abu a cikin wannan sunan tunda shi kanshi asalin DHAHAB(zinare) ba abun yadawa bane abune da ake kokawa a kansa. Kakanninsa da suka ƙi kwantar da kai subi Abdulyasar Dhahab tun farko ai gashi za su mutu babu wanda ya sansu sai ƙananun muƙamin Sarautar da suke taƙama da ita. Anya bazai koma Sufyan Dhahab ba kuwa? Dariya ya bawa kanshi yana shafa sumar kanshi, tare da ayyanawa ransa irin girman kuɗin da zai dinga kashewa sumarsa, duk da dai bai san iyakacin albashin da za'a biyasa ba. Yanzu matsalarsa ita ce Naila, hanyar da zai rabu da ita ya korata Yankin Tudu kawai yake nema ba tare da su Bushra da Yasar sun ga baƙinsa ko butulcewarsa ba, tunda ko yana so ko baya so Naila ce sanadi. Da Sumaya yake son su tare a Babban Birnin Abyad idan komai ya yi masa yadda yake so.
Tuna irin abubuwan da zai yi idan ya fara aiki yasa ya tashi yana taka rawa.
NAILA; bayan na koma ɗaki kuɗina na ƙara adanawa ina lissafa irin kayan da zan siyawa Kaaka duk ranar da Allah ya ƙaddara tafiyata, godiya nayiwa Allah sannan na godewa Bushra tare da alƙawarin naiman yafiyarta duk ranar da Allah Ya haɗani da ita abisa munana mata zato da nayi.
Raina babu damuwar komai sai godiyar sauyin da na fara samu nayi alwalar kwanciya barci, cikin abinda bai gaza minti biyu ba, bayan nayi addu'o'i barci mai nauyi ya ɗaukeni.
★washe gari iyakacin abincin cikina na girka. Sufyan fita ya yi ya jubgowa kanshi siyayyar lafiyayyen Breakfast daga kuɗina da yake tarawa a Banki.
Ko kallonsa banyi ba na tattara na bar living room ɗin. Hakan da nayi ba ƙaramin haushi ya bashi ba, don haka ya hau zage-zage da gorin ai na kusa daina ganinsa sai na dafa gidan na cinye ni kaɗai idan na samu kuɗin biyan haya, domin wallahi shi bazai biya ko sisi ba, ko na tattara na koma Yankin Tudu tunda bani da kunya na fara rainashi bazan roƙeshi ya sammin abinda ya siyoba na sawa kaina girman kai alhali Ni ba ƴar kowa ba ce face ƴar Madinkin da ya ke talakan fitik da sanadiyyar rashin kuɗin zuwa Babban Asibiti ciwon ciki ya kasheshi.
Kamar babu mutum a gidan haka nayimai shiru, amma a ɗaki kuka nakeyi zuciyata na suya.
Bai daɗe da gama Breakfast ba su Yasar suka iso Gidan.
Jiki na rawa ya shigo da su Living room yana baza kunnuwar jin dalilin zuwansu har Gida. Ba su fara bayani ba sai dai suka bashi umarnin kirana.
Jan kunnen karna kuskura na saɓawa abinda zai faɗa ya yimin sannan ya kamo hannuna muka fito tare.
Ina hangosu na ƙwace hannuna na nufi Bushra, ƙam na rungumeta ina nanata kalmar ta yafemin na zargeta da cin amanata ashe tanadin da ban taɓa tunani ba tayimin.
Sufyan harara yake watsomin ta ƙasan ido saboda ya matsu ya ji dalilin da ya kawo su. Sai da na nutsu tukunna sannan Bushra ta fara yi mai bayanin samun aikinsa da kuma irin albashin da za'a dinga biyansa duk wata.
Duk yadda Sufyan ya so yaja aji ko ya kame kansa kasawa ya yi ya miƙe zurbur yana zaro idanunsa, kafin ya fashe da kuka yana yi musu godiya. Kai suka girgiza a tare suna haɗa bakin faɗin;
"Naila zaka yiwa godiya dalilin gwagwarmayarta kakai matsayin da kake kai a yau, don haka karka manta alkhairinta domin shine tsanin nasararka" da gigin farin ciki ya fara nanata "Naila na gode! na gode!! na gode!!!" A tunanina Sufyan ya sauya kenan don haka na taso na ƙanƙamesa ina yiwa su Bushra godiya, suma murmushine kwance a saman fuskokinsu.
Bushra bata nanata naimar min jami'a ba tunda sun riga sun yi maganar da Sufyan tun farko kuma ya nuna ya amincewarsa. Bayan wani lokaci Yasar yayimana sallama Bushra kuma ta zauna na kitsa mata kanta. Shima Sufyan barin Gidan ya yi da sunan zuwa Makaranta, zuciyar Bushra na suya tabi bayansa da kallo saboda ko shakka batayi wajen Sumaya zaije. Kenan Sufyan ba zai taɓa sauyawa ba.
Ni da ban fahimci komai ba bakina a washe nake yimata kitso Ina janta da hira.
A hankali a hankali hirarmu ta faɗo kan Sulaim da yadda muka haɗu da sanadiyyar mutuwar Mahaifiyata da ko Yasar ban faɗawa ba, na dai ce mai ta mutu.
Bushra tari ne ya sarƙeta ta hau yi babu kakkautawa, sannu na fara yimata kafin na wuce kitchen na ɗauko mata ruwa.
Bayan tarin ya tsagaita sai ta yimin murmushi kafin ta ce; "idan har kin aminta dani inaso ki ɗaukomin hoton Sulaim na gani."
Da hanzari na miƙe ina dariya na nufi Ɗakina.
Bushra ta ɗebi mintina tana kallon hoton, sannan ta miƙamin tana janyo gilashinta mai ɗan duhun da nake iya ganin idanuwanta amma ba sosai ba ta manna. Ban kawo komai ba a raina na hau yaba gilashin da ƙoda irin kyan da ya yi mata. Ba tacemin komai sai ɗan danne-dannen da takeyi a waya.
Tambayar Bushra ne ya tsayar da ni daga surutun da nake yi.
"Idan yau ace Mairam Matar Mahaifin Sulaim kuma ƴar Uwar mahaifiyarki da Mahaifiyarki ta rasa ranta wajen hidimtamata amma tabi umarnin iyayenta ta gudu ta barki duk da tasan zakisha wahala, kika ganta cikin ƙarfin daular da take da damar nemanki ta taimaka miki amma batayi ba yaya zaki ji?"
Kaina na ɗago dakyau hawayen tuna irin mutuwar azabar da Mahaifiyata tayi na zubowa ƙuncina, cikin dakiya da kyakkyawan fata ga kowa na ce; "wata ƙila tana da dalili ina kyautatamata zato a duk inda take, idan da rai da rabo wata rana Allah zai ƙaddara saduwarmu, amma gareni na yafe mata duniya da Lahira." Na ƙarasa faɗa ina kuka.
Rungumeni Bushra ta yi cikin ƙosawa ta ce;
"Yaushe zaki daina barin hawayenki suna zuba Naila? dole duk wani matakin nasara na tare da ƙalubale, Karki bari yawan kukanki yazama lagonki a wajen maƙiyanki"
Kai nake girgizawa. A haka Bushra tayi ta lallashina har na yi shiru. Kafin ta bar Gidan sai da ta bani kuɗi masu yawa tace na ɓoye zata ƙara dawowa kafin ta wuce Babban Birnin Abyad.
SUFYAN; Kuɗina da yake tarawa kaf ya kwashe sukayi ƙwarya-ƙwaryar walima shida iyayen Sumaya da ƙawayenta, tare da alƙawarin da zarar yaje Babban Birnin Abyad ya samu yadda yake so shirye-shiryen auren su da Sumaya zai kankama.
Sai dare sosai ya dawo Gida.
★washe gari ma da sassafe ya bar gida. Duk ban damu ba na barshi a matsayin shirye-shiryen tafiya Babban Birnin Abyad.
Ranar da jirginsu zai tashi a bakin Bushra nake ji, sai dai ban nunamata bansaniba. Tayimin kyautar kuɗi masu yawan gaske ta kuma yimin alƙawarin zan zana jarabawar share fagen shiga jami'a da taimakon Yasar. Da ta tashi tafiya waya mai kyau da tsada ta bani ta ce na ɓoye kar na bari Sufyan ya gani.
Ban fahimci tsanata ya yi nisa a zuciyar Sufyan kuma har gaban abadan bazai taɓa ƙaunata ba, sai da naga dare ya yi babu Sufyan ko da na kira Yasar da wayar da Bushra ta bani a nan nakejin ashe Sufyan tun da yamma jirginsu ya tashi. Na yi kuka mai raɗaɗi da ciwon da bansan iyakarsa ba, kafin na haƙura na kulle kaina a ɗaki.
Tafiyar Bushra da Sufyan ne yasa Yasar dawowa ɓangarensa tare da ƙaramar ƙanwarsu da zamu zana jarabawa tare sai dai na girmeta amma ta fini girman jiki.
Naji daɗin dawowar Yasar da ƙanwarsa, da kai tsaye ɓangarena ya turota. A take na saki raina domin fuskantar sabuwar rayuwata.
SUFYAN; tunda sassafe Naila tana barci ya ɗauki iya ƴan kayan da zai ɗauka ya bar gidan, a Makarantar suka wuni da Sumaya tana kukan zatayi ƙewarsa. Gudun lalacewar komai yasa bai barta ta rakasa airport ba kamar yadda ta buƙata.
Kamfanin Dhahab bai ƙarasa cikin garin Babban Birnin Abyad ba kuma anan inda Company ya ke anan staff quarters ɗinsu yake.
Bayan sun isa filin jirgin Babban Birnin Abyad mota daban-daban suka hau da Bushra baima ƙara ganinta ba, kamar ba tare suka taho ba. Ma'akacin Company ya kira kamar yadda Yasar da ya kira ya yi mai bayani haɗe da turomai Number.
Apartment ɗin da yasa Sufyan zubewa ƙasa yana yiwa Allah godiya aka kaishi. Ranar kwana ya yi bawa Sumaya labari haka su Ɗayyib da ya kira. Sam ya manta da Naila.
Kan Sufyan bai ƙara kwancewa ba sai da aka kaishi Office ɗin da ake ce nashi ne.
Duk da Sufyan yana da son banza da kwaɗayin son tara abin duniya sai da ya tsorata ba kaɗan ba. Tayaya ya samu matsayin da ko da dukka karatunsa ya kammala ba zai samu ba? anya Bushra da Yasar da Naila ba haɗa baki sukayi domin a siyar dashi ba tunda yana cinyemata kuɗin kitso? Hannunsa na karkarwa ya lalubo wayarsa😂....✍🏻