18
🔥ZINARE🔥
SASAAL
18
Duk number wanda ya kira ba ya samu hatta number Bushra da bai ƙara gani ba a kashe yake. A take nadamar rashin siyawa Naila waya ya lulluɓesa, da yanzu ita zai kira yayiwa barazana tunda yasan matsoraciyace.
Fatar hannunsa, takalmin ƙafarsa da kayan jikinsa ya kalla, ya ƙara kallon ofishin bai san sanda ya fashe da kuka ba. Sam Chemistry bai haɗu ba dole akwai manufa. Cikin kuka yake ƙara zagaye ofishin har da Bedroom da washroom.
Lokacin da ya gama ƙarewa komai na ofishin kallo sai ya ƙara sakin kuka, hannunsa na tsuma ya ƙara lalubo wayarsa a karo na biyu ya dannawa mahaifinsa kira, saboda daa baiyi niyyar kiransu ba kar ya ɗaga musu hankali.
Duk son duniyar Sufyan a bayan Hindu Mahaifiyarsa yake haka itama duk son duniyarta a bayan Ɗayyib suke, domin shi bashi da tsoro akan duk wani abu daya kafawa ƙahon zuƙa.
Sufyan cikin kuka yake bawa Ɗayyib labari. Maimakon ya ji tashin hankali a muryarsa sai ya ji ya saki ƙaramin dariya.
Da ƙwarin gwiwa ya ce;
"Naila bata da muguwar zuciyar sayar da kurwarka Sufyan"
Kai Sufyan ya girgiza idanuwansa ƙyam akan kujerar alfarmar da yake a matsayin mazauninsa.
"Baaba bazaka fahimta ba, ba su kirani interview ba balle na tantance ƙwarewa ta ce yasa suka bani wannan ofishin, babu wani abu daga neman aiki sai shiga ofishi, tun daga ranar da na sauka ko Bushra banƙara gani ba, Baaba ni dai kawai haƙura zanyi da aikin nan"
Da zafin muryar da zai nutsar da Sufyan kar yaja musu asara Ɗayyib ya ce;
"Bushra ba ɓoyayyiba ce, duk na sa Ubangidana ya bincikamin, kana tunanin rayuwar kara zube kakeyi a Birnin Abyad? Har soyayyarku da Sumaya na sani, da bushashar da kakeyi da Kuɗin sana'ar Naila, dama abinda muka turaka kayi kenan?
To ka buɗe kunnuwanka dakyau ka saurareni. Ka mayar da hankali kan aikinka domin fansar dukiyar da Mahaifiyarka da ni kaina muka sadaukar akanka ba ka zauna yin shirme ba. Inaso ka tara kuɗi Ubangida yaƙara bincikamin komai a kan ma'aikatarku domin sanin muhimman abubuwa akan mai kuɗi sai da kuɗi.
Yaya ma sunan ma'aikatar taku ka ce?"
Kafin Sufyan ya ɓude bakinsa da ya yimai nauyi saboda kalaman Mahaifinsa da suka sanyaya mai jiki, an buɗe ƙofar ba tare da naiman izini ba. A gigice ya katse kiran.
Rashin nutsuwar da yake ciki da kuma rashin sanin matsayin da aka bashi yasa bai tuhumi wanda ya shigo maiyasa bai naimi izini ba.
Ɗayyib bai haƙura ba ya cigaba da kira Sufyan a ɗan gajarce ya ɗaga ya ce ya bari idan yaje Gida zasuyi waya.
Cikin ƙwarewa wanda ya shigo yake koyawa Sufyan yadda zai gudanar da aikinsa.
Fara'ar fuskar Baturen da yadda yake nunamai yadda zai gudanar da aikinsa ne yasa Sufyan ya ɗan saki jiki.
Ko da Baturen ya fita sai da ya ƙara ƙarewa komai kallo yanajin alfahari da girman kansa na ƙaruwa a hankali. Murmushi ne ya kufcemai bayan ya sauke ajiyar zuciya wawtar dayaso aikatawa na dawomai.
Bayan Sufyan ya isa Gida ko cikakken hutun minti biyu bai yi ba, aka aiko mai da lafiyayyun kayan fita Office. Cikin isa yake gwada kowanne kanshi na ƙara girma.
Da yake Sufyan sha-sha-sha ne ko da ya nutsu maimakon ya kira Mahaifinsa sai ya kira Sumayya suka yi ta waya har barci ya ɗaukesa.
★sai washe gari da safe ya tuna da kiran Mahaifinsa, a gurguje ya kirasa suka gaisa sama-sama.
Irin motar da aka zo ɗaukarsa zuwa office ne yasa ya ji daɗi kamar ya kashe shi, cikin isa ya gyara kwalar rigarsa haɗe da motsa kafaɗunsa kafin ya shige.
Daga wannan rana aikin Sufyan da ya mayar da kai ya miƙa, cikin kwanaki ya ƙara gogewa ya fara ɗaukar hanyar zama Sufyan Dhahab ɗin da yake fata.
A computer yake ganin irin Tukwanen da Company Dhahab yake ƙerawa amma bai taɓa ganinsu ido da ido ba, domin ma'aikar da ake ƙera Tukwanen daban yake da na sarrafa shinkafa da yake aiki. Sai dai labarin Tukunyar da ya ke datsa jefi-jefi a wajen Abokanan aikinsa.
Hankalin Sufyan ya ƙara tsayuwa waje ɗaya bayan samun tabbacin Turawane manyan Company ƴan asalin ƙasar Abyad tsirrai ne a ciki.
Cikin ɗumbin narasa, kwanciyar hankali, ƙaruwar soyayyarsa da Sumaya, manta Naila gaba ɗayanta, rayuwar Sufyan ya miƙa.
BUSHRA; tun ranar da ta sauka a Babban Birnin Abyad bata samu nutsuwa ba sai da ta tattara ta bar ƙasar gaba ɗaya. Saboda har lokacin bata cire ran samun kira daga saman Dhahab ba. Lokacin da taje Dhahab ma a tsaitsaye suka gaisa da Simbi Uzair ya dawo da ita Gida. Daga wannan rana ta ƙauracewa ƙasar Abyad gaba ɗaya, sai saƙon kuɗi da take aikawa Yasar ya bawa Naila.
NAILA; Duk da na saki jikina a wasu lokutan inajin raina babu daɗi, inason magana da Kaaka amma bani da hanyar samunta.
Ina cikin wannan yanayin na zana jarabawar share fagen shiga jami'a ni da ƙanwar Yasar. Har lokacin babu kira daga Sufyan, kuma bai zoba, ko Yasar ya daina kira a waya. Kwanaki biyu da gama zana jarabawar mu aka kira Sufyan Interview a Dhahab Babban Birnin Abyad.
Rai babu daɗi Yasar ya fara shirin tafiya Babban Birnin Abyad. Bazan taɓa manta alkhairin da ya yimin ba, da abubuwa dayawa da bazan taɓa iya mantawa da su ba, ya yi min alƙawarin zaman ƙanwarsa a tare da ni. Sai dai da yaje yiwa Iyayensa sallama ƙememe suka nuna ba su amince ƴar su ta zauna a inda babu mafaɗi ba, da yake na rakashi domin dawowa tare da ƙanwarsa tasa a gabana suka dinga sakin maganganu marasa daɗi da nuna ni ɗin ba wata abar aji tausayi ba ce. Ban yi kuka ba, ban kuma ga laifinsu ba amma na ɗan ji haushinsu tunda ko ba komai ai sai su yi tunanin suma tasu ɗiyar zata iya tsintar rayuwarta a kwatankwacin irin yadda na riski nawa.
Har muka dawo Gida haƙuri Yasar yake bani ina nunamai babu komai.
A washe garin ranar da ya rage saura kwana ɗaya ya tafi Babban Birnin Abyad ya kaini ya buɗemin asusun ajiyar kuɗi a Babban bankin Birnin Abyad, tare da siyayyan kayan abinci da kayan maƙulashe kala-kala.
★washe gari da sassafe Yasar ya fito. Na yi kuka irin kukan da ban san iyakarsa ba, sai nake ji kamar ni kaɗaice a duniyata, sai na ke jin kamar na bishi naga inane wannan Dhabah ɗin, su waye a ciki, inaji a jikina kamar na san su, kamar ina da alaƙa da su. Cikin kuka na ce idan ya je ya gaishemin da mutanen cikin Dhahab. Duk yadda Yasar yaso ya jure kasawa ya yi yasa kuka da haka muka rabu da shi ba tare da sanin ranar da zamu ƙara ganin juna ba.
Ban taɓajin kaɗaicin da na ji ba a kaf rayuwata irin ranar da Yasar ya bar Birnin Abyad. Ko ina yayimin shiru wa su lokutan sai na ji kamar motsi a bayana wa su lokutan kuma sai na ji kamar ana kiran sunana. A wannan dare na gane girman rahamar zama da mutum a waje ɗaya.
A haka wahalallen barci ya ɗaukeni cike da mafarkai ma su ban tsoro.
A haka na shafe kwana uku cikin kaɗaici duk da muna waya da Yasar jefi-jefi a rana.
Tun ina jin tsoro har na haƙura na sanyawa zuciyata dakiya.
Da sannu zuciyata ta ƙeƙashe na daina jin tsoron komai. Zan tashi da safe na yi Breakfast na ci na ƙoshi idan rana tayi na tafi Gidan Customers ɗina wa su kuma su biyoni Gida. Idan Dare ya yi na ɗauki kuɗi a cikin kuɗin sana'ata na je nasha Ice cream a wajen da Yasar ya nunamin.
A haka rayuwata ta miƙa, jarabawata ta fito tayi kyau. Da taimakon Abokin Yasar na samu gurbi a jami'a mai zaman kanta na Birnin Abyad duk Bushra ce ta biya ta hanyar Yasar, shi kuma ya turawa amininsa.
Kuɗin siyayyar kayan abinci da abubuwan amfani Yasar ya turomin. Da na rasa kalar godiyar da zanyi musu shi da Bushra kuka na sanya.
Duk da Bushra ta ƙauracewa waya dani ta ƙauracewa zuwa inda nake domin ta jima da dawowa Babban Birnin Abyad amma saboda tana tsoron kar abibiyi kiranta ya sa ta daina kirana ta daina zuwa wajena kar ta ƙarasani a cikin matsala.
Da taimakon Abokin Yasar na kammala komai na fara attending lectures
A ranar da na fara zuwa Makaranta da yamma bayan sallar la'asar na fita siyayyar abinda zanyi amfani dashi tunda a Hostel zan zauna saboda tazarar Makarantar da Gidanmu.
Doguwar Riga mai taushi da faɗi na sa na naɗa mayafin da ya yiwa fuskata da ya rage rama kyan gaske. Waya da card ɗin da zanyi siyayya dashi kawai na ɗauka.
Wajen siyayya mafi girma a Birnin Abyad na nufa saboda a can zan samu duk abinda nake so.
Tun shigowata na hango Sufyan hannunsa sarƙafe da na Macen da ban sani ba (Sumaya).
Ya yi kyau irin kyan da yake buri, ya ƙara haske da ƙiba kamar ba Sufyan ba. Macen ce ta fara hangoni kamar ta Sanni sai ta ƙara ƙanƙame hannunsa cikin kishin da ya bayyana a saman fuskarta. Ban nuna na gansu ba, na fara ɗaukar abinda ya kawoni.
Duk yadda ta so janye hankalin Sufyan daga ɓangaren da nake sai da ya waiwayo.
Da farko bai ganeni ba sai daga baya. Hannunta ya saki da sauri ransa na suya hassadar yadda na canza har na samun ƴanci da kuɗin yin siyayya a wajen da ya kawo Budurwarsa na cin zuciyarsa. Ina sane da tahowarsa kafin ya ƙaraso na yi wuf na nufi wajen biya. A kwai mutane a wajen don haka ya juya ya na ɗaukar komai a hanzarce don suyi su gama, bai damu da yadda Budurwartasa take ƙunci ba.
Lokacin da ya iso da jibgin kayan siyayyarsu lokacin na nufi ƙofar fita.
Yaso jirkintawa su gama biya amma ganin kamar hakan zai ɗauki lokaci har na ɓacemai yasa ya miƙa mata card ya bi bayana da sauri ba tare da tsayawa kallon ƙuntatacciyar fuskarta ba.
Ya na fitowa ina shiga Taxi kafin ya shiga Mota tuni mai Taxi ya bar wajen.
Lafiyayyen motar da Company Dhahab suka siyamai ya shige a hanzarce. Da speed ya bi bayanmu kar mu tsere mai, ganin mun ɗauki wani hanyar daban ba na gidan daya sani ba sai ya ji hassada na naiman kassarashi zuciyarsa na tiriri.
Da ɗan hanzari na sauka a Taxi dama tun a ciki na sallamesa.
Gate ɗin Makarantarmu na nufa hankalina a kwance duk da na hango motar da na ke kyautata zaton na Sufyan ne. ID na nuna na wuce. A take na ƙara shiga Motar da zai kaini har bakin Hostel ɗinmu. Sai a lokacin na saki ɗan dariyar da ya ƙaramin kyau ina hasaso irin ƙuncin da Sufyan zaiji domin nasan ko shi yafi kowa kuɗi baza'a barshi ya shigo ba, tunda bashi da Numbern wayar kowa kuma bai san kowa ba a Makarantar.
Sai ta nutsuwarsa ya yi bayan ya yi parking domin kai tsaye suka hanashi shiga kamar yadda ya so.
Ba irin bayanin da bai yi ba, babu kuma irin rantsuwar da baiyi ba shi Mijinane amma suka nuna su sam basu sanni ba, shin yamasan a gaban wani University yake tsaye kuwa? Securities suka tambayeshi.
Sai a lokacin ya ɗaga kai yana kallon sunan da yake jiki saman Dogon Ginin ɓaro-ɓaro a take ya ji hassada na naiman kasheshi jirin baƙin ciki na naiman kai shi ƙasa. Sum-sum ya fito yana jin muzanta a karon farko tun bayan tafiyarsa Babban Birnin Abyad.
Da ya shiga Mota kasa jurewa ya yi, ya fara dukan kujerun motar ya na surutai "Ni Naila zata yiwa taurin kai, har ta yarda su kawota jami'a irin wannan, wallahi! Wallahi!!! Wallahi!!! Sai nayi sanadiyyar barinta Birnin Abyad wayyo zuciyata zata fashe" ya ƙasara faɗa ya na dukan saitin zuciyarsa....✍🏻