CHAPTER 1
by @khairatup01
SHINGEN ƘAUNA
Khairatup.
Wattpad:khari_Muhd.
arewabooks:khairatup.
01.
Paid Book.
A hankali nake tuƙi babban burina a halin yanzu na kai unguwar da aka kwatanta mini don kai ɗinki. Na gaji da rainin hankalin da telolina suke yi mini na saɓa alƙawari. Haka ya saka na tambayi wata ƙawata ta lambar telan ta don na ga ya iya ɗinki in na gani a jikinta yana burge ni. Na kira shi ya zo gida ya ƙarba ya ce min yana da ayyuka da yawa sai dai na kai mai can shagon na sa.
Yakasai na nufa wurin shekara. Nan na ga shagunan masu ɗinki kala-kala. Na rasa ma wanne shago ya faɗa min. Tsaki na yi na gyara faking ɗin mota ta.
Wayata ƙirar iphone na ɗauka na soma kiran layin na sa. Ni a yadda ta turon lambar a haka na yi saving. "N.Yakasai.
Kamar ba za a ɗaga ba sai kuma aka ɗaga kiran da sallama ya fara.
Na amsa masa a gajarce.
"Na iso ina daidai shekara."
"Gani nan zuwa." Ya ce da ni ya kashe wayar. Na kwantar da kaina a kujerar ina jiran ya ƙaraso.
Wayar tayi ƙara na duba na ga shi ne. Ɗaga kiran na yi ina sauraronsa.
"Ban gan ki ba.kina daidai ina ne?"
Tagar na buɗe na leƙa na kuma kiran sa nace "Kai kana ina? Ni gani a cikin mota."
Juye-juye ya soma da waya a hannuns hakan ya saka na gane shi ne nake jira. Gajeran wando ne a jikinsa da riga t-shirt.
"Na gan ka ma bara na fito."
Ina fita yana juyowa ,kallo ɗaya nayi masa na kawar da kaina gefe.
Shi ya zo inda nake.
"Salamu alaikum Hajiya."
A hankali na juya na kalle shi sai na ji wani irin banbarakwai wai Hajiya ko da yake da dama haka suke kira na da shi Hajiya. Duk da shekaruna ba su kai ba amma a haka suke kirana Hajiya saboda dalili ɗaya dukiyar da na ke da ita.
"Wa'alaikum salam. Barkanmu ya aiki?"
"Alhamdullilahi Ya faɗa. Ke ce za ayi wa ɗin ki?"
"Ni ce."
"Ina kayan? Ko za ki ƙarasa shagon ɗinkin?"
Na yamutsa mai fuska nace "Aa kalle ni a nan kawai. Gashi nan ayi min ɗinki mai kyau dogwayen riguna nake so masu kyau. Sannan don Allah ka cika alƙawari."
"Ba ki da damuwa in sha Allah!."
"Advance zan baka ?"
"Aa zan kira ki in buƙatar hakan ta taso. Na gode sai anjima."
"To." Ya faɗa.
Na shige cikin mota na yi gaba.
*
Nadeeya suna na.Nadeeya Nazif ni ƴar asalin jihar Kano ce. Mahaifina ba Alhaji Kabir ba ne sannan mahaifiyata ba Hajiya Saffiya ba ce mu ɗin ƴan cikin gari ne. Mahaifina na da shagi a kwari amaa ba babban shago ba ne ba amma ba a taɓa ƙin ɗora tukunya a gidanmu ba.
Yayyuna maza biyu Yaya Muhammad sai Yaya Imam sai kuma ni Nadeeya sai autan Umma Jameel. Gidanmu ɗan matsakaici ne ɗakuna uku da shago a waje. Yaya Muhammad aiki yake a banki yana da mata nan bayan mu gidansa yake. Sai Yaya Imam da yake masters a Abu Zaria fannin education G&C lecturer ne ma ,be yi aure ba shi amma ana sa ran auren na sa.
Na yi makarantar mata ta jar ƙasa ina aji uku na haɗu da JJ (Jabir Jamil) matashin saurayi mashahurin ɗan kasuwa gidansu baban gida ne kowa ya san arziƙin mahaifinsu ainihin gidansu a makwarari ne. Babban gida ne mai sassa da dama babansu ɗan gargajiya ne shi yasa bai bar unguwarsu ba.
Allah Ya haɗa ni da shi wata rana bayan mun dawo daga makaranta shi kuma ya yo titin asiya bayero nan tudun wuzurci ni kuma zan tsallaka ina ta aikin surutu ya kusan buge ni na saki jakata na sa ihu na runste idanuwana biyu saboda firigita na sadakar ya taɓa ni.
Fitowa ya yi cikin kaya ƴan ubansu shadda ce mai sunan shadda a lokacin ban san kuɗinta ba amma na san an zuba mata dukiya.
Maganar sa na ji a kai na yace "Hey beautiful haka ake tsallaka titi a garin ku?"
A hankali na buɗe idanuwana bakin tsiwa ya buɗe min na murguɗa masa bakina nace "Kai haka ake tuƙa mota a garinku? Baka ga ƴan mata sun fito ba zasu tsallaka titi ba?" Na faɗa ina tsatsare shi da ido.
"Hah! Wai ma kina da bakin magana?" Zan maida masa martani muka soma jin horn ɗin motoci.
Maimakon ya koma ya shiga motar ya tafi, sai na ga ya gyara fakin ya kuma fitowa ya kalle ni cikina kuwa ya ɗuri ruwa na ɗauka duka zai min ko ya sa a kama ni mai rashin kunya.
"Yaya sunan ki? " tambayar da ya fara yi min kenan.
Na buɗe bakina nace "Ina ruwan ka?" Na ce da shi tare da murguɗa masa baki.
"Kin burge ni kina da confidence. Sunana JJ."
"JJ? Me kuma JJ?"
"Suna na ne. Jabir Jameel."
"Ni kuma ba zan faɗa ba." Na yi gaba. Na ɗauka zai tafi ne sai na ga yana ta bi na a mota har na shiga adaidaita sahu bai bar bi na ba. Cikina ya ɗuri ruwa na tsorata na san Baba ba zai ba ri ba. Yana ganin layinmu ya faka da ƙafa ya shiga ya dinga bina har ƙofar gidanmu yana gani ya ce a hankali " Zan zo zance anjima yanzu biki za ni."
Na ko kwalalo masa idanuwa na waje. Da gudu na shige cikin gidanmu.
Sai na maƙale a bayan ƙyaure ina kallonsa ya tambayi wani yaro a layinmu Inga wai ya sunana. Yaron ya ce da shi "Nadeeya"
"Kai waye a jikin ƙyauren nan ne?"
"Ni ce Umma".
Ke yau na ga shegantaka yau kuma da haka kika shigo?
Aa abu na ne ya faɗi shi ya tsaya ɗauka.
To maza shige lokacin sallah ya kusa ki yi ki zo ki siyo mana garin masara yau baban ku tuwon masara zai ci.
To Umma.
Ruwa na ɗiba a buta na shiga banɗaki na kama ruwa nayi alwala. Ina komawa ɗaki na sauya kaya na ɗaura zani na saka hijabi. Ana kiran sallah na bi liman don massalacin a bayan gidanmu yake. Ina idarwa na yi addu'a na shafa.
Ko abincin rana ban ci ba na tafi aike Umma. Hijabi na har ƙasa na saka na fita. Zan je makarantar dare ma sauri kawai nake yi don na kai wa Umma na tafi.
Ina karya kwanar layinmu na ga bawan Allahn nan a tsaye jikin motarsa yana waya. Sai kuwa na yi maza na saka hijab ɗina na rufe fuskata.
"Kin ɓoye a banda Nady. Na gan ki ai. Dawo muyi magana don Allah."
"Aike na Umma tayi za a yi wa Baba girki."
"To je ki dawo zan jira ki a nan."
"Ba kusa ba ne ba yanzu zan dawo ba."na ce da shi ina son ya tafi.
"Zan zauna duk da haka. Kin manta in da mota?"
Na rasa ma me zan ce masa gudun kar na ɓatawa Umma rai ya saka na yi sauri na tafi. Ban jima ba na siyo na koma gida na kai ma Umma lokacin ma Baba ya dawo da Jameel suna zaune a tsakar gida suna hira.
"Nadeeya ba ki tafi islamiyar ba?"
"Yanzu zan tafi Baba.Gari na siyowa Umma."
"Hanzarta ki wuce kin ji?"
"To Baba." Na kai mata na yi musu sallama na tafi. Tsoro nake ni sosai bana son a gan ni da JJ.
Amma sai na kasa tafiya. Sai naga kamar in na tafi ba zai tafi ba zai tsaya jirana ne kuma ni ba zuwa zan ba. Dole ƙanwar naƙi haka na juya na koma bakin layinmu.
Wannan karon a cikin mota na same shi ya koma yana dadana waya .
Sallama na yi masa ya juyo da fara'a a saman fuskar sa. Daga ɗazu zuwa yanzu na lura shi mutum ne mai yawan fara'a.
"Na ɗauka ba za ki dawo ba.Na gama tsara nan da mintuna talatin zan tafi in ba ki zo tunda na ga dare ya soma yi."
"Islamiya dare zan tafi. Me ya sa ka dawo?"
"Saboda ina son na yi magana da ke."
"Maganar me?"
"Tambayoyi zan miki tukunna."
"To."
A wanne aji kike? Sannan ki kalle ni da kyau za ki iya aure na?
Na rasa ma meye auren kai na ya ƙulle nayi tsile-tsili da idanuwana waje.
Yatsunsa biyu ya murza suka bada sautin "Dal." Na yi firgit na dawo cikin hayyacina.
"Ban gane abinda kake nufi ba."
"Kin gane. Sarai kin gane amma tunda so kike ki gane ina nufin ina son ki. Kuma so nake ki aure ni."
"Ba zan iya auren ka ba."
"Me yasa?"
"Haka kawai."
"Aa ba haka ba ne dole akwai dalili. Ko dai ban miki kyau ba?"
Na yi murmushi a karo na farko tun haɗuwar mu da shi. Cikin raina nace wai bai min ba. Saurayi santalele da shi fari dogo ga saje baƙiƙirin ya kwanta kamar balarabe haka yake.
"Hey! Kin kuma komawa wata duniyar ne?"
"Uhm'uhm".
"Zan tafi amma gobe zan dawo sai muyi magana. In kuma tsoro kike ji zan zo wurin Baba da kaina zan gaya masa ina neman izini."
"Innalillahi aa kar ka je in ka zo zan gan ka kawai."
"Ki gan ni a ina?"
"A nan mana." Na faɗa mai da sauri.
Dariya yayi ya koma cikin motar ya ce "Zan dawo gobe sai anjima."
Karo na farko a rayuwata da na yi bunking ɗin makaranta. Amma ba san me yasa ban ji komai ba sai ma tunanin JJ da zuciyata ta faɗa.
Mafarin komai.
*
Kamar yadda ya faɗa washegari ina dawowa daga makaranta na kuma ganin sa a bakin layinmu yayi fakin. Ni kuma na yi sauri na ja facemask ɗina na yi luuu zan wuce.
"Haba ƴan mata an gaya miki ba zan gane ki ba?"
Tsayawa nayi na kasa tafiya.
"Nadeeya ba da wasa na zo ba , ban kuma ce miki ke na fara so ba, kuma ban ce miki ina son ki don yaudare ki ba. Hakan nan soyayyar ki ta kwace mini duk wani sukuni da nutsuwa na zuciya. Ban taɓa jin son wata ƴa mace a raina kamar yadda soyayyar ki ta kama ni ba. Ban yi baccin kirki ba , a kasuwa ma yayyuna sai da suka ce bani da lafiya nan ko basu san cewa ciwon so ne ya kama ni yayi min tarko ya yi min ɗaurin talala. Kawai amsa ɗaya zuwa biyu za ki bani ita ma da a ko aa."
Za ki iya ƙarbar soyayyata?
Na rasa me zance a ko aa.
Ya kara maimaita min tambayar ban san yadda aka yi ba kawai sai na amsa masa da A.
Kin bani izini na nemi izinin zuwa wurinki a gun Baba?
Na gyaɗa masa kai na kawai.
Ma sha Allah! An gama gimbiyar mata.
Kafin nan ni ne mai kamfanin JJ & Brothers investments. Mahaifina sunan sa Jameel Yusuf Mai taya.
Na san sunayen da ya ambata amma ban san wani kololuwarsu ko iyakarsu ba.
Yanzu Baban yana nan?
Aa sai anjima zai dawo.
To zan je na dawo ayi a wuce wurin.
Toh sai ka dawo.
Ki kula mini da kan ki kuma kar ki manta akwai wani bawan Allah JJ yana son ki yana ƙaunar ki yana kuma kewar ki a kowacce daƙiƙa.
Ina shiga gida kamar koyaushe buta na ɗauka na shiga bayi na kama ruwa na yi alwala. Nan na tallafa wa Umma muka soma kacaniyar aikin ɗora abincin dare kafin dawowar Baba.
Sai da na yi sallar magariba na saka kayana don tafiya islamiyar dare kuma har lokacin Baba bai shigo ciki ba, na ji dai maganar Jamilu.
Ina fitowa na ga har da Baba ashe a ƙofar gida da Yaya Muhammad ma suna tattaunawa. Ƙasa na tsugunna na gaishe su tare da yi musu barka da lokaci.
Na tashi zan tafi Baba yace "Zo Nadeeya, dawo zamu yi wata magana da ke."
"To Baba."
Haka na tafi ina jinjina maganar da Baba zai min ko a kan meye ma Allah ma sani. Ana tashi kuwa muka yi sallar isha kaitsaye gida na tafi.
A tsakar gida na gansu dukka har Yaya Muhammad. "Yaya baka tafi ba dama?"
"Ban tafi ba Nady. Ina nan ina kwasar garar Umma yau."
"Aa sai na gayawa Aunty nan ka ke gudowa ka ke cin abinci."