CHAPTER 2
by @khairatup01
SHINGEN ƘAUNA
khairat.
Wattpad:khairi_Muhd
arewabooks:Khairatup01
Paid book.
Free page 2.
Tare muka ci abinci. Bayan mun gama mun nutsa sai Baba ya kalli Umma ya kalle ni yace magana ce ya zo da ita. Duka hankalinmu muka ba shi.
Dazu bayan na dawo wani yaro matashi ya zo ya same ni da wata magana. Maganar kuma ta Nadeeya ce. Tsakani da Allah hankalina ya kwanta da nutsuwa da kamalar yaron. Ya burge ni abinda ya saka nace ya burge ni bai zo ya hurewa Nadeeya kunne da ƙarairaki ba. Be buɗe mata ido da dukiya ba. Sai ya zaɓi ya fara zuwa ya same ni ya nemi izinin fara zuwa taɗi gun ta. Hakan ya burge ni sosai duk da na ba shi dama ba don arzƙinsa ko na mahaifinsa ba sai dan nutsuwa da kamalar sa. Amma ba na son ke ma na tauye ki ke yaya kike gani kin yadda ya dinga zuwa za ki ba shi dama?
Rasa ma me zance na yi tuni na harbo wa ake nufi. JJ ne. Amma ban ɗauka da gaske yake ba. Nima ya kwanta min sai na ji zuciyata zata iya buɗe masa shafin soyayya zan iya ba shi damar mulkar zuciyata ba don kuɗi ko kyau ba sai don na ji ina son sa a cikin raina.
A hankali na tashi da kunya na shige ɗakina.
Ina jin Baba yana hamdala. Nan ya kuma labartawa Umma yadda abubuwan suka wakana kuma waye JJ.
Daga wannan lokacin ni da JJ muka ƙulla ƙarfafar alaƙa irin alakar nan mai wuyar lallacewa. Na yi jarabawar fita daga sakandiri na yi jamb kuma duk JJ ne ya shigar mini gaba. Tuni ya zama ɗan gida don Umma ba ka ce ma ba ita ta haife shi ba. Ina jindaɗin yadda yake nuna min kulawa da soyayya da yadda yake kula da iyayena yake girmama su. Ban taɓa tambayarsa abu ba hakan kuma yana masa daɗi sai dai ya kintata ya min shi ma ba mai tsada ba daidai da rayuwata haka yake yi min. Iphone ya yi niyar siya min amma na nuna mai bana so Baba zai min faɗa Umma zata ce me yasa na karɓa ya sani haka ya saka da kan sa ya kai wa Baba wayar yace ya bani. Ina mamakin saukin kan JJ sabanin sauran masu kuɗi da suke da jiji da kai da ɗagawa yadda ƴan gidanmu suka san ni nima haka ahalin JJ suka san ni. Hakan nan ma sai ya kawaso min ƙannensa wai su zo su gaishe ni.
Jarabawata ta jamb ta fito kuma Alhamdullilahi na samu abinda nake so Bayaro na cike da taimakon JJ. A lokacin shekarar mu ɗaya da rabi muna soyayya.
Ban fara zuwa jami'a ba sai da aka yi baikon mu ni da shi an saka biki wattani sha biyu cif ma'ana shekara guda kuma an sa hakan ne
saboda Baba.
Idan nace bana son JJ na zuba zuƙi-tamalle. Hasalima yadda nake son sa sai nake ganin kamar ba haka yake sona ba. Bayan na san ba haka ba ne yana mugun ƙaunata.
Bana mantawa akwai wata rana ana biki ƙawata Sayyada da farko shi ya kai ni rijiyar zaki yace kuma na jira shi zai dawo ya ɗauko ni kar na sake na tafi na amsa masa da to.
Biki ya yi biki har na manta da wata waya ina can ina cashewa filin rawa ina tsaka da rawar ne wani ya zo ya soma yi mini liƙi ganin haka ya saka na fita da sauri. Ashe bai bar bina ba. Wurin zamana na koma na zauna na ɗauko wayata na duba adadin missed call goma sha na gani duk na JJ na ji babu daɗi ba mamaki ma ya dawo ne don bakwai ta wuce. Haka na ɗauki wayar na kira shi sau biyu bai ɗaga ba sai daga baya ya kira ni.
"Idan kin gama rawar sai ki fito mu tafi." Kit ya kashe wayar bai bani damar yi masa bayani ba haka na fita ko sauran ban yi wa sallama ba.
Daga gefe na hango motarsa. Hular nan facing cap ya saka ya rufe fuskar sa ya saka baƙin gilashi. Dama yace min zai je aski da alamu an yi askin don na ga an gyara mai fuska an rage gashin na sa.
Ban yi tunain wani yana bi na ba Wallahi. Sai da na ji JJ yace "Kai waye haka kake bin matar mutane haka? Liƙin da ka yi ma bai ishe ka ba har sai ka biyo ta ɗan iskan banza da wofi." Ya faɗa a hasale daga cikin motar yana ƙoƙarin fitowa nayi wuff na tsaya a gaban ƙofar na sani in ya fito sai ya yi masa rauni don baya wasa da lamarin sam.
"Ki matsa min."
"Aa Masoyina ka yi haƙuri bai san matar ka ba ce ni."
Ganin da gaske JJ zai iya kilarsa kawai sai ya karya kwana ya bar wurin.
Shi kuma sai huci yake yi min ban sare ba na yi sauri na zagaya na zauna a wurina. Kujerar baya na dauko ruwan roba na ba shi ya sha tas sai da ya shaye ruwan nan ko kaɗan bai bari a cikin robar ba.
Wullar da robar ruwan yayi waje. "Ashe ban ce ki riƙe wayar ki a kusa ba? Ban gaya miki ban da rawa ba? Raina ni kika yi saboda kin ga ina son ki da yawa ko? Kin shiga kina rawa ana miki liƙi haba Nady haba don Allah zuciyata zata yi bindiga Wallahi."
"Don Allah ka yi haƙuri ban san za a shigo ba. Na yarda na yi laifi na yi kuskure amma ba zan kuma ba don Allah ka daina fushi da ni."
Ganin na dabarbarce ya saka ya sassauta min ya yi wa mota key kawai muka tafi.
Har muka isa gida bai ce komai ba ana ta kiransa ma bai ɗaga wayar ba sai tsaki yake kawai ban taɓa ganin wannan fuskar ta sa ba sai yau kuma na ɗauki aniyar kiyayewa.
Zan mai magana yace "Je ki,sai da safe."
Na san bai sauka ba kuma ba zai kula ni yanzu ba dole na tafi na bar shi bai bar wurin ba sai da ya daina gani na wannan sabon shi ne ko da can ko rako shi na yi baya tafiya sai na shige.
Daren ranar bacci ɓarawo ne kawai ya sace ni.
*
Washegari kuwa na shirya zan tafi na yi sallama da Umma da Baba. Na fita ma muka haɗu da Yaya Muhammad za shi cikin gida muka gaisa ya ƙara min ɗari biyar kan wanda Baba ya bani.
Wallahi JJ masoyine na da Allah Ya kadarra mini haɗuwa da shi bayan abinda ya faru jiya ban ɗauka zai sauko nan kusa ba ina fitowa daidai santar layin mu na gan shi amma a mashin yau ya ajiye motar ne.
Sai na yi kamar ban gan shi ba na zumburi bakina gaba na yi gaba. Ya ja mashin ɗin ya kuma matso kusa dani ,ni ma na ƙara yin gaba haka ya dinga bi na ina yin gaba in na tari adaidaita yace "Jeka matata ce faɗa muke shi yasa taƙi hawa mashin ɗin." Haka ya yi ta yi wasa-wasa sai ga shi mun yi nisa da unguwarmu a haka yana korar min masu adaidaita sahu.
A shagwaɓe na juya ina kallonsa idanuwana suka ciciko da hawaye ina son na yi kuka amma fa na shaƙiyanci da kashe jiki.
Yana ko ganin haka ya sauko ya matso sosai kusa da ni kamar zai kamo ni ya ce "Mene ne Nady? Ni ne ko? Kiyi haƙuri jiya kishi ne ya rufe min ido amma ke kin san ba haka nake ba bana son na ga ana kallon ki ne. Bana son na ga kina kula kowa sai ni kaɗai am sorry." Ya faɗa yana kama kunnensa.
Na murguɗa masa baki na kuma ɗauke kaina gefe sai gani na yi ya tsugunna kan guiwowinsa ƙasa bai damu da inda muke ba, bai damu da kayan jikinsa ba, bai damu da ana kallonsa ko ba a kallonsa ba kawai burinsa ya lallabani ya bani haƙuri bayan ni ce na yi masa laifin.
Tuni aka soma tururuwar kallonmu aka kewaye mu wasu na cewa ni ko na haƙura mana wannan ai masoyina ne na gaske . Agogo na duba na yi mugun latti.
"JJ ka tashi gaskiya mu tafi na makara. Ji yadda ka zo ka tara min al'umma."
"Gwara su shaida yadda nake son ki."
"Allah sa sun maka bidiyo."
"Sai me in sun yi? Kina ganin zan ji wani ɗar ne? Lallai baki da wayo har yanzu kina tantama a kan son da nake miki ko?"
"Uhm'uhm bana yi JJ."
"Good! Zauna muje."
Ni na fara hawa na zauna ya gyara min rigata ya ja ta ƙasa shi ma ya hau muka tafi muna hira an manta da faɗan jiya."
Har inda zamu yi lectures ya je ya sauke ni ya ƙara mini dubu ɗaya. Ana ta kallonmu musamman ma ƴan matan wurin hakan na saka ni kishi sosai musamman in naga ana kallon mini masoyi sai dai na kan manta na ji sanyi a raina in na tuna cewa ni kuma duk faɗin birnin zuciyarsa ni ya fi so ni ce kuma a kwance ciki na yi bake-bake na kanainaye ko ina har babu sauran wurin zaman wata bayan ni a ciki.
Ƙawata Summaya Kabir ce ta dafa ni ta baya na juya ina mata murmushi nace "Ashe kina bayana?"
"Ina nan fa muna ganin lovayya. Yaushe za a kira mu wannan lamari ne?"
"An kusa da izinin Allah. Ki kwantar da hankalinki Hajiyata."
"Wallahi kuna burge ni ke ba ma ni kaɗai ba kuna burge mu da yawan mu. Gaskiya ki ƙara godewa Allah da Ya ba ki nagartacce kamar JJ."
Dariya na yi mata kawai na ja hannunta muka wuce cikin hall ɗin da zamu yi lecture ɗin.
*
Soyayya ta da ta JJ abar kwatance ce kuma abar bada misali har ta kai yanzu kowa na layin mu da kewaye yana da labain Nadeeya da JJ. A maimakon bikina ni kaɗai sai aka haɗa da na Yaya Imam.
JJ ya lissafa mini adadin abubuwan da za ayi na bikin kuma su ne za su yi. Duk da haka ni na so ace nima na yi wani abin amma ba zan ɗorawa Baba nauyin komai ba ga kayan ɗaki ga na kitchen ga gara da za ayi sai na ƙi yin wani abun kayan da zan saka ma yayar shi Aunty Ramlat ita ta zo har gida muka tafi kasuwa ni da ita da kanta ta zaɓa min komai da zai dace da ni har su takalma da sarƙoƙi daga nan muka tafi wurin tela aka auna ni. Ta ce "Ke fa ƴar gatan Mama ce komai nan Mama ce tayi ruwa tayi tsaki ta kuma ce na gaya miki kar ki kusura ki ce mata kin gode kuma kar ki kusura ki sa a ranki an yi ɗawainiya da ke don a nuna miki gazawar komai ba sai don ita tana son ki saboda kina son Jabiru babanta."
Kamar ko ta san ina jin wani irin don abubuwan da ni ya kamata nayi ita tayi min su har ƙwalla sai da na yi kuwa. Auntu Ramlat tace "Kina da aiki. Saurara min yanzu zamu je booking ɗin gyaran jiki wannan kuma Aunty Sakina ce ta ɗauki nauyin hakan."
"Me zan ce da ku ni kuwa Nadeeya? Gaskiya kar ku saka na soma jin ni wata ce a rayuwa na soma yi muku shagwaɓa. Na gode kuma da yardar Allah sai kun yi alfahari da kasancewata ɗaya daga cikinku. Kuna da bambanci da sauran masu kuɗin da suke musgunawa talakawa ko suke ganin arziƙinsu bai kai a tara da irin mu ba."
"To me karatu na gaba." Ta faɗa tana dariya. Nima dariyar na yi. Ita ke tuƙin dama muna tafe muna hira. Tuni na sake da dangin mijina. Dangin mijin da suke da sauƙin kai da kamala da daraja ɗan'adam dole in jinjinawa iyayensu da suka koya musu yadda ake mu'amala a rayuwa. Ba zan basu kunya ba da yardar Allah!.
Yini muka yi muna yawo kai kace ya da ƙanwa ce yayar amarya ba yayar ango ba.
Shi kuwa ya kirani sau ba adadi yana tambayar ko mun dawo, ina muka je ne? Shi fa in dawo da wuri ya zo ya gan ni ya tafi don ni ɗin ni ce cikon numfashinsa.
Kodayaushe in na juya na ga irin lullubin da Allah Ya yi min da mayafin alkairi da mutane nagari da ya bani sai na ce Alhamdulillahi! Kawai na wuce wurin.Na kan nanatawa kaina "Na yi dace."
A bakin layinmu ta sauke ni da kayan kwalam tayi gaba da sauran. Hatta wurin kwalliya duk ta yi min booking ranar kawai ake jira ta zo.
Na nunawa Umma komai na kuma labarta mata abinda yake faruwa ta dinga yi mini nasiha tana maimaita min in daraja waɗanan bayin Allahn in bisu yadda ya kamata sannan in kama mutuncin kai na da na su.
Cikin raina kuwa nace "Ba sai an gaya min ba."