19
🔥ZINARE🔥
SASAAL
19
Sufyan ba wannan ne zuwansa Birnin Abyad na farko ba. Tun lokacin da aikinsa ya miƙa komai ya yi mai yadda yake so ya fara kawowa Sumaya ziyara.
Sumaya macece tasan kuma abinda Sufyan yake yiwa Iyalinsa ba daidai ba ne, a addini har ma da al'ada amma son kai da tsanin son zuciyar kusa kai cikin abinda batasan mafarinsa ba yasa take ganin kamar Sufyan ma son Iyalinsa ya ke yi banda haka ya saketa mana kawai ita ya gabatar da ita a wajen Iyayensa suyi aurensu.
Son zuciyar Sumaya kaɗan ne akan na Mahaifanta, domin su cewa su kayi bazasu ba shi Sumaya ba har sai ya saki Naila.
Da Sufyan ya dammaƙa mata Card zuciyarta ce kawai bata haɗiya ba, kishi ya toshe komai nata gani take yi duk kuɗin da Sufyan yake ikirarin ba shi da shi Ita yake kashewa ba Iyayensa yake turawa ba kamar yadda ya faɗa. Saboda tun fara aikin Sufyan ranar ne kawai tasan ya yi mata siyayya ma su nauyin kuɗi, duk zuwa idan ya yi ƴan kuɗine yake rabawa Mahaifanta. Amma ga Matarsa nan tayi kyau tasa sutura na alfarma, saboda kishin ma kar wani ya ganta har rufa mata baya ya yi yana muzurai sai ka ce wani sakarai. To kenan yaudararta ya ke yi da ya ce ba ya zuwa wajen Naila?
Da kuka shaɓe-shaɓe ta tari Taxi ta nufi Gida.
SUFYAN; bayan ya gama bige-bige da ayyana irin ramuwar gayyar da zai yi akan abinda Naila ta yi mai sai ya ɗauki hanyar Gidan su Sumaya.
Kukan da take yi da irin maganganun da take saki Iyayenta na ƙara tunzura ta ne su ka ƙara harzuƙa Sufyan, cikin tsananin fushi ya buge kofin tangaran ɗin da su ka zuba masa lemo a ciki, a take ya fashe. Sumaya tana yunƙurin zaginsa ya zuba mata marin da ya taɓa zuciyar Iyayenta, Babanta ma na yunƙurin kwasamai mari ya riƙemai hannu, kafin ya jefar da hannun da iya ƙarfinsa. Cikin isa da takaici ya ce;
"ki je mun rabu! kuma karki ƙara nemana tunda har yau baki fuskanci Naila itace mukullin ƙofar nasarata ba" yana gama faɗa ya bar madaidacin living room ɗin da aka ƙawata da kuɗin Naila.
Da sakakken baki ya bar su, sukar kalmarsa na "sun rabu" na cakar zuƙatansu sama da raɗaɗi marin da ya saukewa Sumaya da hannun Mahaifinta da ya jefar, saboda Sufyan da shi suke taƙama domin sanadiyyar haɗuwarsa da Sumaya rayuwarsu ta sauya ba kaɗan ba. Sumaya kuka take yi har da birgima danasanin abinda ta aikata na mamaye zuciyarta. Sufyan baya ɓoyemata tasan da kuɗin kitson Naila suke ci suke sha a makarantar kuma sanadiyyar Naila ya samu aikin da ya ke yi, amma ita ta rasa dalilin da ya sa ta tsani Naila.
Daga wannan rana Sufyan ya ƙauracewa kiran Sumaya. Ga hotuna da ya ke saki masu kyan gaske a shafukansa, duk domin Sumaya tasan ko a jikinsa. Ya yi narasa kuwa domin Sumaya ƙara gigicewa tayi. Ba dare ba rana kullum sai ta turamai saƙo.
Rasa yadda zata shawo kanshi yasa ta turamai saƙon tayasa fakon Naila, har ya samu damar mayar da ita Yankin Tudu kamar yadda yake yawan faɗe tun kafin ya tafi Babban Birnin Abyad.
cikin jimami ta zauna zaman jiran amsar da zai bata.
NAILA; cikin nasara da wadatacciyar nutsuwa na fara gudanar da karatuna.
A ɓangaren sana'ata kuɗi na ke samu ba kaɗan ba, saboda ƴaƴan manyan mutane da suke Campus ɗin mu waɗanda kansu ya ke kitsuwa a waje na suke yin kitso.
Cikin watanni na ƙara zama wayayyiyar mace sai sanyin kyau da ɗabi'a. Ba na shiga sabgar da bai shafeni ba ina kuma tsayawa a iya matsayina.
Ina zuwa Gida jefi-jefi musamman ranar sati. Batun Sufyan kuwa tuni na share shi a raina, na mayar da hankali kan abinda ya kaini Makaranta. Yasar kullum shi yake ba ni ƙarfin gwiwar yin karatu, domin shine matakin zamana a Birnin Abyad na din-din har na kawo Kaaka mu ƙarasa rayuwarmu. Wannan ƙwarin gwiwar da Yasar yake bani ba ƙaramin dadinsa na ke ji ba.
A hankali komai ya yi ta sauyawa watanni na shuɗewa, shauƙin son zuwa Yankin Tudu domin ganin Kaaka na ƙara mamaye rai na, a haka muka fara shirye-shiryen zana jarabawar da zamu yi hutu mai ɗan tsahon da zan iya zuwa Yankin Tudu na taho da Kaaka. Kamar yadda Yasar ya shawarceni tunda ina samun kuɗi.
SUFYAN; bai daina son Sumaya ba amma yanason ta gane shi ɗin Namijin da za'a lallaɓa ne ba wanda za'ayiwa hargagi ko rashin kunya ba. Ko da yaga saƙonta fuska ya yi, domin yasan ba ta da wani abun tsinanawa, kawai don ya kulata ne.
Magiya da nacinta ba dare ba rana ne ya dawo da soyayyarsu har ya fara yunƙurin tarar Mahaifansa da batun ta, tare da shawarar da ya yanke na sawwaƙewa Naila kafin ya aiwatar da ƙudirinsa a kanta.
Cikar Sufyan shekara ɗaya a ma'aikatar Dhahab yasa sukayi mai kyautar da ya hanasa runtsawa. Waya kuwa kwana sukayi suna yi da Ɗayyib, cikin isa Sufyan yake bada umarnin abinda za'ayi da kuɗin. Ba bu lissafin yinƙurin yin wani abu na cigaban Yankinsu a kason kuɗin da duk wani kuɗi da yake turawa sai Gidan Sarautar su da aka ƙara ƙawatawa, musamman ɓangaren Mahaifansa.
Ba bu wani tsarin tallafi da suka tsiro da shi a matsayinsa na Ɗan Yankin da ya samu cigaba a Babban Birnin Abyad sai dai mutanen gari su gani a jikin Iyayensa, ƴan Masarautar su da Gidajensu, duk da mummunar talaucin da suke fama da shi. Har lafiyayyen titi aka shimfiɗa daga farkon shigowa Yankin Tudu har ƙofar Masarautar su.
A ɓangaren Ɗayyib Gidan Game ya buɗe ƙato matasa su samu kuɗi suyi ta bugawa Yara kuma su sato kuɗin Mahaifansu. Abun takaicin sai Matasa da Iyayensu sun sha wahala sun ƙera Tukwane sai sun samu an siya daƙyar sai Ƴaƴan su kwashe kuɗin su gudu gidan Game ɗin Ɗayyib.
Cikin ƙanƙani lokaci shima ya fara zama hamshaƙi.
Dukka wannan facakar sai dai ƴan uwan Naila da Kaakarta su ji labari kamar dai gama garin mutane ba surukansu ba.
Ɓullowar batun auren Sumaya da Sufyan, ya tayar da ƙura a tsakanin Hindu da Ɗayyib don sai da sukayi faɗan da ya kaita ga tafiya Gidansu. Ta kafe bata yarda da auren ba matsawar ita ta haifi Sufyan domin malaman tsibbunta sun sanar da ita sakin Naila zai rusa komai, haƙurin mutanen da suka zuba masa ido ya na zaluntar ta zai ƙare daganan suyi masa ɗaurin talalar da zai mutu a ɗaure.
Sam Ɗayyib bai yarda da batun Hindu ba, acewarsa ɗaukakar Sufyan daga Allah ne, babu wata Naila don haka dole su bar Sufyan ya rayu da abinda yake so.
Ankai ruwa a tsakanin su har sai da Jalal Mahaifin Ɗayyib ya shiga faɗan da suke yi a sirrince don bakowa ba ne yasan Hindu bata gidan.
Da saka bakin Iyaye Hindu ta yarda da auren amma da sharaɗin ko zai saki Naila sai lokacin da ta yarjemai. A kan haka suka bar zancen.
Da tsananin rawar kai Sufyan yake rabon katin aurensa ga Manyan ma'aikatarsu. A cewarsa ma bai taɓa Aure ba.
Labarin auren Sumaya da Sufyan sai da yaje har kunnen Bushra, ba tare da ɓata lokacin ba ta naimi Yasar ya toshe duk wani hanya da Naila za ta iya jin labari, saboda kar hakan ya kawomata tsaiko a jarabawar da take zanawa. Kuma da zarar ta gama ya shirya mata tafiya Yankin Tudu.
A rabon Invitation card da Sufyan yake yi ne, Baturen da yake sama da shi ya bashi shawarar ya shirya katin gayyata na musamman ga GM wataƙila ya samu alheri mai yawan gaske.
Da yake Sufyan ɗan son banza ne a daren ya biya kuɗi mai yawa aka shiryamai katin gayyata na musamman. Washe gari kafin ya shiga office ya miƙawa oganshi ya bawa GM. Ba tare da nutsuwa ya yi tunanin maiyasa tunda ya ke aiki a Dhahab bau taɓa ganin GM ba.
Gaba ɗaya sai Sufyan ya matsu ranar Aurensa ya zo, irin shagalin da ya tanadi maƙudan kuɗi za'ayi a Yankin Tudu na sanyashi jin alfaharin da bai taɓa jiba.
Ɗayyib da su Sarki Hammam ne su suka zo Gidansu Sumaya naimawa Sufyan aure. A take Iyayen Sumaya da suka matsu da komai suka ce sun bashi sati mai zuwa a ɗaura aure su tafi da Ita Yankin Tudu su je can suyi Biki, a maimakon wata ɗaya da suka tsara da Sufyan tun kafin zuwan Iyayensa ya yi rawar kan buga katin gayyata.
Sun ce su basu da wani shagali da zasu yi bayan ɗaurin Aure.
Abin takaici daga kan Sarki Hammam da Ɗayyib da muƙarabansu da suka zo Birnin Abyad tare ba bu wanda ya tambayi ina ƴarsu Ƴar Yankin su take? a wani yanayi take ciki?. Kowannen su fuska ya yi yana dirzar duniyar da ya samu.
Da rawar jiki Sufyan yake ƙara bawa mayansa haƙurin matso da lokaci kusa an samu akasi. Wa su sun nuna zasu je wasu kuma tambayarsa suka yi babu wani shagali da za'ayi ranakun da zasu biyo bayan ɗaurin auren da zasu iya zuwa? Da sanyin jiki ya sanar da su na Yankin Tudu tunda yasan ba lallai su je ba.
Ga ɗumbin mamakinsa washe gari ya samu saƙon GM ya ce ya amsa gayyata amma ba zai samu zuwa ɗaurin aure ba, sai dai na Yankinsa da za'ayi In Shaa Allahu. Sufyan ihu yasa ya na tsalle, har ya fara hango irin ƙafafa da zafin kan da zai yi, inama da Naila tana wajen ya nunamata ko babu ita shi ya zama kafin Allah a Dhahab sai dai ta mutu da baƙin ciki.
Cikin walwala da son Daular da ya ke iya canza tunanin ɗan Adam lokaci ƙanƙani su Sarki Hammam suka cika sati guda.
Irin fareren Turawan da suka zo ɗaurin auren Sufyan da Sumaya a Birnin Abyad ne yasa bakin Ɗayyib yaƙi rufuwa. Bayan komai ya lafa sun keɓe Ɗayyib ya murmusa cikin alfahari ya ce
"Sufyan ina alfahari da kai akanka na fara samun cikar burina na tsayin shekaru, kaga Ubangidana ko sam bai halarci ɗaurin aure nan ba kuma nasan yana gari, dama ina sane da shi, tun daga kan takardun da na ce ya samar maka ya ƙauracewa waya dani, to dama haka rayuwa take, yau ina jina na daban ya ya ma kace sunan wannan Ma'aikata taku mai albarka." Ya ƙarasa faɗa yana kafa lemo mai tsada a baki.
Sufyan da ke murmushin isa ɗan dariya ya yi kafin ya ce "DHAHAB"
Azababben tari ne ya rasƙe Ɗayyib lemon da ya kurɓa ya soma biyomai ta hanci da baki...
NAILA; A dai-dai lokacin da Tari ya sarƙe Ɗayyib Naila ta kammala haɗa kayan tafiya Yankin Tudu....✍🏻
Wanene General manager company sarrafa shinkafar Dhahab da Sufyan yake aiki a ƙarƙashin shi?😄
Maiyasa ya zaɓi zuwa wata ƙasar shagalin ta ya murnar ma'aikacin da ya ke ƙasan-ƙasansa duk da girman matsayinsa.
Yaya zaman Naila a Yankin Tudu zai kasance shin zata dawo ko bazata dawo ba? Kaaka tana raye ko bata raye?
Wani 🔥🔥 ne zai kama a Yankin Tudu?
Next page In Shaa Allah