20
🔥ZINARE🔥
NAFISA ALIYU SASAAL
*CHAPTER 3*
*YANKIN TUDU🔥*
Page 20
NAILA; da ƙananun kayan Calvin Klein na yi sauƙaƙaƙiyar adon da ya dace da siffata ya kuma haska kyawuna.
Fuskata ƙunshe da murmushi nake kallon mutanen Birnin Abyad, farkon zuwanmu Birnin ni da Sufyan na dawomin. Rashin banbancin da ke tsakanin fatarmu ta ɓangaren murjewa a yanzu yasa na ɗan faɗaɗa murmushina. Ashe komai zai sauya, ashe nima zan zama ƴar gayu kyakkyawar Macen da zatayi alfahari da kanta wata rana.
Dogon mota mai kyau na hau, idona tsaye ƙyam a kan hanyar Babban Birnin Abyad.
A wannan karon ina alaƙanta kallon hanyar da Yasar da Bushra da suke can tare da Sufyan da Mutanen Yankina irinsu Sarki Hammam suka zaɓi Duniya akan lahira, kar su faɗi gaskiya ko su marawa gaskiya baya su rasa ransa. Domin duk da Bushra tasa Yasar ya ɓoyemin sai da naga komai a shafin Sufyan kamar yadda nake bibiya lokaci zuwa lokaci.
Babban sauyin da na samu a komawata Yankin Tudu shine jirgin da na bi a maimakon Mota da taimakon mutumin Bushra. Cikin ɗan tsoron da ya mamaye raina saboda hawana jirgi a karon farkon jirgin mu ya ɗaga zuwa Iyakar Yankin Tudu da Babbar tashar da filin saukarsa ya ke.
SUFYAN; Da hanzari ya nemo ruwa ya miƙawa Ɗayyib, haɗe da nanata kalmar "sannu" da yake tayi ba ƙaƙƙautawa.
Ɗayyib ya ɗauki tsahon mintuna ya na tari, fararen idanuwansa da suka ƙara haske saboda daular da ya samu na kwana biyu na juyewa zuwa jajaye marasa kyan gani.
Da salon murya da Sufyan bai san Mahaifin nasa da shi ba ya ce;
"Kasan menene DHAHAB" cikin rashin fahimtar ina ya dosa Sufyan ya ce; "Zinare Baaba"
"Sufyan ina nufin kasan mafarin ƙirƙirar Dhahab, tunda kake a duniyarka ka taɓajin mai inkiyar banda Ahalin Abdulyasar" cikin rashin fahimtar abu da wuri Sufyan ya ce;
"Waccen Dhabah ɗin ai zuri'arsu ta mutu Baaba, waɗannan turawa ne ba ma ƴan asalin ƙasar Abyad ba ne, kusan dukka manyan da suke samana Turawa ne."
Ɗayyib cikin rashin gamsuwa ya ce;
" Wanene mamallakin ma'aikatar ba ina nufin GM ɗin da zai zo shagalin bikinka ba, tunda ance suna da reshe da yawa, asalin mamallakin Dhahab ɗin nake nufi gaba ɗaya, kasan sunansa da inda yake da zama"
Sufyan ido ya zaro cikin mamaki ya ce; " Babaa ba ni da issue da duka waɗannan abubuwan da ka lissafo burina kawai na samu kuɗi, Ni ma na zama Dhahab ɗin kaina, tunda na lura sunan ya na da wani ɓoyayyen sirri, shine kawai."
Kamar talabijin haka Ɗayyib ya zubawa bakin Sufyan ido, zuciyarsa kuwa Allah Ne kaɗai yasan faɗinta da sirrikan data ƙunsa.
Da kaushin murya ya ce;
"Daga ranar irin ta yau kafara saka lissafin abinda na tambayeka a cikin ƙwanyarka, domin ba ra'ayi ba ne ko ganin dama ba, tilas ne musan su wanene Dhahabs, aikinka zai fara daga yau Sufyan!"
Ɗayyib yana gama faɗa ya miƙe jiri na ɗibansa sama-sama.
Kafaɗa Sufyan ya ɗaga alamun ko a jikinsa, shi ba shi da wannan ra'ayin da dai maganar kuɗi ne da kyau to da sai iya inda ƙarfinsa ya ƙare, amma ace duk Kuɗin da ya tare sai ya je yana binciken abubuwan da basu shafesa ba, why not ya ba shi shawarar ƙirƙirar wani hanyar da zai ƙara tara dukiya shima ya zama Dhahab ɗin da'akewa kokawa shekara da shekaru har ake salwantar da rayuka duk domin a kawar da su.
Amarya Sumaya tasha gyara kyanta da farin fatarta sun ƙara fasowa. Sufyan kamar ya siɗeta bini-bini ya kirata a waya su share mintina suna hira.
Kayan alfarmar da zai fitar da Sumaya ta zama ta musamman sama da yadda Ubaidullah ya kawo Kakar Sulaim Yankin Tudu aka tanadarwa Sumaya da taimakon Ɗayyib da kansa aka fitar da adon kayan da ya dace da Masarautarsu.
Bayan komai ya kammala tsirran ƴan uwan Sumaya da kansu yake rawar Ƴar uwarsu tayi dacen gidan kuɗi da Sarauta suka fara shirye-shiryen tafiya Yankin Tudu.
Ranar Alhamis da ya rage saura kwana biyu shagin Yankin Tudu suka ɗugunzuma dukkansu, abin birgiyar daga Company su Sufyan aka turo da motoci na alfarmar da zai kaisu Airport.
Sarki Hammam da ya jima da watsar da gaskiya saboda ya tsiratar da rayuwarsa murmushi yake saki cikin ransa ya na sambarka, ba tare tuna jinin mutanen Yankinsa da aka salwartar wajen kafuwar Yankin da ya ke shugabanta ba.
*YANKIN TUDU*
NAILA; lokacin da jirgin mu ya sauka a iyakar mafarin shiga Yankunan mu, murmushi na saki, zuciyata na azalzalata inajin ƙarfin gwiwar da ban taɓa jiba. Cikin kasuwar chanjin wajen na shiga aka canza min kuɗin Birnin Abyad zuwa na ƙasarmu, ban rage ko sisi ba. Kuɗine masu yawan gaske don haka na zuba su a cikin jakar da na tanada domin su. Masauƙin baƙi na nufa na canza Suturar jikina zuwa Abayar da muka fi amfani da shi a Yankin Tudu duk da nawa da ɗan bambanci.
Drivern da ya ɗaukomu Ni da Sufyan shekarun baya shi ya ƙara ɗaukata. Da shi da Motar tasa duk sun tsufa sun jeme.
Gudu yake yi amma sai nake ganin kamar baya sauri saboda yadda na matsu na riski Kaka na ga ko ita yaya ta koma?
Hirar yadda Yankinmu ya koma yake yimin muryarsa a raunane da yadda Sufyan ya ke kashe Kuɗi a iya Masarautarsu da mutanen cikinta.
Ban tsawaita magana da shi ba, saboda yadda zuciyata take suya.
Lokacin da muka shigo Yankin Tudu bansan sanda dariyar da ya bayyana jerarrun haƙwarana ya kufcemun ba, da zumuɗi na buɗe murfin motar, kuma nayi sa'ar babu mutane. Duk suna cikin Gidajen su sai tsirran da ba'a rasa ba. Da taimakon shi na sauko da kayan tsarabar da na jibgo. Kuɗi ma su nauyi na ɗauko na bashi da sunan kuɗin da ya ɗaukoni. Ƙasa ya zube yana kuka cikin shesheƙa ya ce;
"Allah Ya aramin ranar da zan saka miki da abinda kikayimin Allah Ya haska gabanki Ya haska bayanki, Na gode! Na gode!!!" Kai na girgiza mai haɗe da kutsawa Gidan Kaaka.
Murna tace ta koma ciki sanda nayi ido biyu da yadda Kaaka ta rame ta lalace fatarta ta yamushe kamar babu ruwa a jikinta.
Da farko bata ganeni ba, sai daga baya, da gudu ta taso garin ta iso inda na ƙame a tsaye ta zube ƙasa saboda tuntuɓen da ta yi. Da sauri na ƙarasa muka ƙanƙame juna, ina kuka tana kuka.
A haka Drivern ya gama shigo min da kayana. Kaka kallona tayi ta shafa fatata sai ta fashe da kuka, ta yi haka ya kai sau uku, kafin ta miƙe tayi hanyar waje. Jakar kuɗina na adana kafin na saki dariya.
Layi-layi Kaaka take bi tana kuka haɗe da cewa;
"Ya ku ƴan uwana mutanen Yankin Tudu ku fito ga jikata Naila ta dawo daga Babban Birnin Abyad, ku fito ku ganta Mutanen Yankin Tudu"
Kafin ka ce me, dangin Mahaifina, mutanen gari daga kowani ɓangare sun cika Gidan. Kowannensu idan ya yi dariya sai dai kaga haƙoransa a waje saboda rama. Maza da mata haka suka cika Gidan.
Da na kalli fuskokinsu da yadda suke dariyar da yake nuna irin farin cikin da suke ji sai na fashe da Kuka.
Suma da yawansu sai suka saka kuka suna zayyanomin irin talaucin da suke ciki.
Tsabar da na taho da shi a take ya ƙare wa su ma basu samu ba. Bayan kowa ya watse Mahaifiyar Kabeer da ta kasa tafiya ta matso kusa da Kaka, da ƙaramin murya take roƙon ita bata samu ba mu taimaka mata, da na kalleta na tuna da ɗanta Kabeer mai zafin naima sai na fashe da kuka, da sauri na shiga Ɗakin Kaaka na ɗauko kuɗi na bata.
A wannan dare kwanan labari mukayi da Kaka cikin kuka mai taɓa zuciya.
Da ƙarfin gwiwar Kaaka dana Yasar na yanke shawarar ƙin zuwa Gidan su Sufyan idan ya ji haushi ya bani takardarta ta.
★washe gari labarin dawowata da shirye-shiryen shagalin bikin Sufyan da ƙin zuwa gaishe da Mutanen Masarautar Yankin Tudu ya bazu ko ina, har kunnen Hindu mahaifiyarsa da Kakansa Jalal.
Ƙura bai ƙara tashi ba, sai da na ɗebi dubban mutane Yankinmu muka shiga Kasuwar Maƙotan Yankinmu abisa shawarar Kaaka muka siyo ɗayyan abinci a farashi mai rahusa.
A wannan rana sai da hankalin duk wani mai faɗa aji a Masarautar Yankin Tudu ya tashi, domin ɗabi'ar da na tsiro da shi ɗabi'un Zuri'ar Abdulyasar Dhahab ne. Labari bai tsaya a iya Yakin Tudu ba har kunnen Sarki Hammam, Sufyan da Ɗayyib.
Sufyan kishine ya kamashi, shi kuma Ɗayyib da yake komai nasa a lissafe yake tafiya, a take ya alaƙanta kalan taimakon da nayi da mamallakin Companyn Dhahab da ɗansa yake aiki, domin ko maƙaho a Yankin Tudu yasan irin taimakon da na yi irin na jinin Abdulyasar Musa Dhahab ne. Domin su ne suke taimako da gumin su, su kuma kawowa mutanen Yankin su cigaba da ƙwaƙwalwar su.
Lokacin da labari ya riskesu su na Airport, don haka suka matsu su iso ayi shagalin biki agama su kawo ƙarshen komai.
Ba bu tsangwama babu nuna wane na wane, wane ba nawa bane, na basu umarnin kasafta abincin a tsakaninsu.
kuka da addu'o'in Tsofaffi, Maza da mata, Matasa, da Yara ne yake ta tashi tare da kabbarorin su ta ko ina.
Maimakon sanya idon da bindiddigin auren Sufyan sai Mutanen Yankin suka mayar da hankali wajen yimin addu'o'i da fatan nasara mai ɗorewa.
A wannan rana na wuni cikin jindaɗi da soyayya daga ɓangaren Mahaifi harma da ɓangaren Mahaifiyata da suka samu labari, duk da kaf kuɗin da na ɗau shekaru ina bautar yin kitso da wanda Bushra da Yasar suka bani na tattara na bayar sai abinda ba'a rasa ba daya ragemin. Barci mai cike da nutsuwa muka yi ni da Kakaa.
Ranar da su Ɗayyib suka sauka wanda ya yi dai-dai da ranar cin kasuwar Zinare mukayi shawara da Mutanen Yankin da suma ƙiris suke jira har da matasan da abincin dana raba ya ɗarsa musu tsanar Ɗayyib a ransu, muka taru muka rushe ƙaton wajen da Ɗayyib ya kewaye da lallaga Mazanmu da Matanmu kuma mukayi tattaki har ƙofar Gidan Sarki Hammam da saukarsu kenan muna ƙorafin bamason Gidan Game da Gidan Rawa lalata mana Yanki yake yi!. Kayan Game ɗin ciki babu wanda ya taɓa Matasa majiya ƙarfi suka Tattaro suka zuɓe a ƙofar Gidan Sarki Hammam.
Da yake bikin Sufyan suke burin suyi hankali kwance sai Sarki Hammam ya fito ya bamu haƙuri.
Ɗayyib mutuwa ne kawai baiyi ba. Jalal Mahaifinsa da muƙarabansa a ranar suka shirya taro a kaina tare da bawa Sufyan umarnin sakina da gaggawa, don shawarar kamani da Kakata suka fara yankewa sai dai hakan zai tunzura mutanen Yankin da dama can a gajiye suke.
Hukuncin su Jalal gagarumin rigima ya tayar domin Hindu a take ta nuna Sumaya ba ta yimata ba idan kuma Sufyan ya sakeni sai ta tsinemai.
Sumaya dake lulluɓe cikin mayafi bata fuskanci duk abinda yake faruwa ba, ita da ƴan uwanta sai zare ido sukeyi.
Jalal ne ya daki ƙasa kai tsaye ya ce ƙaryar Hindu ya na so kafin rufuwar mintuna Talatin takarkar Sakin Naila ya isa ga ahalinta.
Maza majiya ƙarfi masu ƙarfin tsafi a Jikinsu Sarki Tsafi na Yankin Tudu da Masautar Yankin Tudu ta butulcewa ya turo su yi gadin kaf faɗin kewayen Gidanmu.
A ɓangaren Matasan Yankin suma ƙofar Gidan Kaka suka mayar majalisar su har da abin shiffiɗar kwanciyar su saboda tsaron kar a biyoni cikin dare, Ni ma kuma ban gajiyaba wajen ambaton Ubangijin halittu.
Bayan na huta muka ƙarayin waya da Yasar ya kuma ƙaramin ƙarfin gwiwar kar na gajiya nasara na tafe In sha Allahu kafin na dawowata.
Da bayin Gidan Sarki Hammam ta ɓangaren Jalal suka isar da saƙon Jalal, da rufa ido ɗaya da dama don abinda aka aikota kenan ta ɗauke wayata. Ba mu ankara ba sai bayan tafiyarsu.
A daren Ɗayyib ya yi duk wani bincike shida Sufyan da ƙwararren masanin na'ura mai ƙwaƙwalwa a Masarautar amma basu ga alama ɗaya daya haɗani da Ma'aikatar su Sufyan ba. Cikin ɗacin hali Sufyan ya farfasa wayar ya cire layin ya karya.
★washe gari layi-layi fadawan Sarki Hammam suka bi suna gayyatar mutanen Yankin filin wasannin ƙarshen mako don gudanar da shagalin bikin Sufyan.
★
Ranar da ya kama shagalin bikin Sufyan da Sumaya. Sufyan ya yi ado na kece raini duk da ba haka yaso ba Naila ta ɓatamai komai.
Sarakuna daga Yanki-Yanki ƴan kasuwa da ƴan siyasa, su aka warewa waje na alfarma har da wajen da GM ɗin Sufyan da sukayi waya suna kan hanya zai zauna.
A cikin Dattawan da suka je gudun abinda zai baya har da Mahaifin Kabeer da ya tsufa ya yanƙwane saboda wahala.
Lokacin da taro ya yi taro motocin fadar Sarki Hammam da Sufyan ya sake sababbi suka tafi taro GM ɗin Companyn sarrafa shinkafa na Dhabah.
Isowarsa da saukarsa duk akan idanuwan Mahaifin Kabeer.
Dark blue suit mai nauyin kuɗin gasken daya kwantawa farin fatarsa da kakkaurar jikinsa ya sanya. Gashin kansa dake amsar gyara na kwance luf. Lokacin da ya fara takawa, Mahaifin Kabeer da yunwa tasa ya ranƙwafa ya yanko wajen da aka hanasu ƙetarawa saboda su talakawa ne da gudu. Cikin ihun da ya haɗe da kuka ya ke faɗin;
"Ashe Malik zai cikamin alƙawarin da ya ɗaukarmin! sai dai ya shammceni, da na san irin wannan alfaharin yake nufi da na tattara masa dukks Ƴayana ya tafi da su.
Ya kabeer Ɗana ashe da gaske zaka dawo garemu bayan mun cire rai, lallai Allah Abun godiya ne."
Cak matashin ya tsaya haɗe da buɗe dukka hannayensa da ke fitar da wani irin ƙamshi. Cikin soyayyar Uba da Ɗa kabeer ya rungume Mahaifinsa.
Babu wanda bai miƙe ba, babu kuma wanda bai razana ba daga waɗanda suka san Kabeer har waɗan da basu sanshi ba.
Da wani irin fushi Ɗayyib yake taka ƙasa kamar zai hudasa, gaban Sufyan da shi ma yake tsaye kamar mutum mutumi ya tsaya ya na kai hannunsa saitin ƙugun wandonsa.
Da zafin zuciyar azabar dake neman halakasa tashi ɗaya ya ce;
" Lallai ban haifo ɗa ba sai soko kaicona!
Idan har Malik zai mallaki dukiyar da zai sauya rayuwar Kabeer, Kabeer kuma ya sauya taka kai kuma ka sauya namu to tabbas su na da Ubangida, Uban gidan da ya kamata ace kasani tuntuni, amma sai gashi ko Kabeer ɗin ma baka sani ba Balle kuma Ubangidan su, daga yanzu har zuwa ajalinka ba zan taɓa yafe maka ba har sai ka gano min wanene DHAHAB 🔥?????
Ɗayyib ya ƙarasa faɗa yana yankar ƙuncin Sufyan da wuƙar da ya zaro a ƙugunsa, a take jinin kumatun Sufyan ya yi tsartuwar da ya fallatsa har saman fuskar Ɗayyib....✍🏻
Barka da Jumu'a.