21
🔥ZINARE🔥
NAFISA ALIYU SASAAL
Page 21
Sufyan kansa ya sunkuyar ƙasa, raɗaɗin yankar da Mahaifinsa ya yi mai a kunci da yankar da Kabeer ya yi mai a zuci na naiman zautar da shi. Shi da kansa kunyar kansa yake ji, baƙin ciki mai girma na da ɗa mamaye zuciyarsa.
Ɗayyib da ya juya ya kalli irin gyaran da Masautar Yankin ya samu da dukiyar da kai tsaye za'a kirasa da na Kabeer da irin manyan mutanen da ya ɓata dukiya ya gayyata, sai ya ƙara juyowa. Da wani irin fushin mai girma yake yankar Sufyan ta ko ina yana maimaita
"Ko Abdulyasar Dhahab zai dawo duniya a raye ba zan yimasa irin wannan hidimar ba na rantse da Sarki Allah! Sufyan ka cuceni! Ka cuceni!!"
Daƙyar aka ƙwace Sufyan da ya yi kacha-kacha da jini a hannun Ɗayyib da ya zama kamar Mahaukaci.
Mutanen Jalal ne suka ja ĆŠayyib cikin Gida, shi kuma Sufyan aka wuce da shi Asibiti yana ihun azaba kafin ya sume.
Sarki Hammam a take ya bayarda umarnin a rufe iyakar Yankin Tudu, kuma a turo masa Kabeer cikin Iyayensa da gaggawa.
Da ƙananun gulmammaki taron shagalin bikin Sufyan ya watse maimakon yabo da ya ci burin yasamu a wajen Mutane.
Kamar yadda Sarki Hammam ya bada umarni haka akayi sai dai babu Kabeer babu Iyayensa. Da gaggawa Sarki Hammam ya ƙara bayarda umarnin abi duk Yankin da yayyen Kabeer mata suke aure a kamo su. Sai dai suma duk basanan acewar Surukansu sun bar Gida da sunan zuwa shagalin bikin Ɗan shugaban kasuwar zinaren Yankinsu tare da rakiyar Mazajen su da Ƴaƴan su.
Babu inda ba su bincika ba amma babu Kabeer babu ahalinsa. Dagaske dai Kabeer ya gudu da dukka ahalinsa.
Ɗayyib da labarin ɓacewar Kabeer da ahalinsa ya riskesa Ihu ya kurma haɗe da ɗaura ɗamarar binciko Kabeer da ahalinsa a duk inda suke. Fadawan Sarki Hammam majiya ƙarfi Jalal ya bawa umarnin tare Ɗayyib daga barin Masarautar, ya na fizgewa suna tarosa, daƙyar suka danneshi aka nemo likita ya yi mai allurar barci.
NAILA; ɗaukemin waya da Bayin Gidan Sarki Hammam sukayi ya zama iyaka tsakanina da Yasar, saboda tanan kawai yake iya sanin halin da nake ciki. Lamarin ya sosa zuciyata tare da ɗaga hankali na sama da Sakin da Sufyan ya yi min, domin ko bai sakeni ba, bazan ƙara iya rayuwar auren rashin ƴanci da shi ba.
Damuwar da na shiga akan hanyar da zan ƙara samun Yasar ba ƙaramin tashin hankalin Kaka ya yi ba, cikin ƙarfin halin ɓoye ta ta damuwar take jaddadmin ko da karo-karon zasu haɗamin kuɗi na koma Makaranta ita da ƴan uwan Mahaifina dana Mahaifiyata har ma da mutanen Yankinmu. Wannan ƙarfin gwiwa da Kaka ta bani sai ya gusar da duk wani damuwa da fargaba dake danƙare a cikin zuciyata na fara walwala kamar kowa.
A haka muka kwashe kwanaki uku a cikin gidajenmu, ba tare da dogon zirga-zirga ba, abisa umarnin Sarki Hammam.
SUFYAN; yasha azaba irin azabar da bai san akwai irinsa ba, kullum cikin kuka yake tunda ya farfaÉ—o daga duniyar azabar da Mahaifinsa ya kaisa.
Sumaya ta na gefe itama tasha kuka idanuwanta duk sun koɗe, wahalar da bata taɓa tunanin zatasha ba har su gama rayuwar Aurensu da Sufyan shi take sha, idan zai yi fitsari da Toilet duk ita take taimaka mai gashi da raki kuma ita dama can ba saba aikin wahala ta yi ba. Ga shi
Bayin ma da aka bari Maza ne masu gadinsu balle su taimaka mata.
Ćłan uwanta suma gaba É—aya sun matsu su koma Birnin Abyad, danasanin rako Sumaya Yankin Tudu na damun zuciyarsu.
A ɓangaren Hindu bayan barinta Yankin Tudu zuwa Yankinsu, kai tsaye wajen Malaman dubanta ta wuce.
Tabbacin nasarar Sufyan na isar tsakiyar Babban Birnin Abyad tare da É—aukaka mai girman gaske na tare da Naila, babu abinda ya sauya.
Amma su da Sufyan sun karya dokar da aka shimfiɗa musu tun farko. Na farko zaman Sufyan a Birnin Abyad saɓanin Babban Birnin Abyad da aka sharɗan ta musu, na biyu gaggawar Sufyan na yin Soyayya da Sumaya har da aurenta. Na uku sakin Naila da ya yi, shi ya ƙara wargaza komai.
Da rawar murya kuka Hindu take roƙon asama mata wata mafitar tun da wannan ya lalace.
Sihirin da za'a shayar da Naila ya bata na tsahon kwanaki uku ba tare da rarrabewar kwanaki ba. Zata dawwama a ciwon da babu magani, bayan tasha wahala Sufyan zai je da sunan taimakonta.
Idan har Iyayenta sun amincewa Sufyan ya samu damar ɗaukarta zuwa Masarautar su to ta dawo za'a bata maganin da zai karyar sihirin da sukayimata ta samu sauƙi, daga nan sabon shirin tunkurarsu Babban Birnin Abyad zai kankama da zafin da dole nasara ta tabbata. (Anya wannan nasarar zata tabbata🤔)
Da wannan ƙwarin gwiwar Hindu ta fara shirye-shiryen dawowa Yankin Tudu, bayan tayi kwanakin da ta ɗibarwa kanta.
*************************
Har sati ɗaya ya shuɗe idanuwan Ɗayyib ba su washe ba, baya iya magana saboda baƙin cikin da suka yi mai karo. Ko Asibiti yakasa zuwa duba Sufyan, itama Hindu tattare lamarinta ya yi ya watsar, burinsa ya samo ina Kabeer da Malik su ke, su bashi labarin wanene Uban gidansu.
Babban Malamin duba Jalal ya gayyato tun daga wata ƙasar domin fayyace musu abinda Ubangiji ne Masani akai.
Ina su Malik da Kabeer suke? A wacce duniya suke rayuwa? Shin dagaske Kabeer shine Uban gidan Sufyan. Wanene ko wacece asalin Uban gidansu? WaÉ—annan tambayoyin shi su ĆŠayyib suke neman haske a kansu ido rufe.
Ukun bayyanannu ne inda Malik da Kabeer suke da duniyar da suke rayuwa, da kuma shin dagaske Kabeer shine Uban gidan Sufyan, amma sanin asalin Uban gidan su, abune ɓoyayyen da Malamin da suka gayyato ya kasa ganewa.
Ya bayyana musu Kabeer da Malik suna wani gari Daf da shiga Babban Birnin Abyad, kuma suna rayuwa ne kusa da Company da Sufyan yake aiki ba a cikin asalin ƙwaryar Babban Birnin Abyad ba.
Kabeer kuma ba shine Uban gidan Sufyan ba, a yadda dubansa ya nunamai Kabeer ba shi da alaƙa ma da Ma'akatar su Sufyan kawai rufa ido ya yi musu. Asalin Ubangidan su kuma Macece wacce ta taɓa zama a nan Yankin Tudu amma yakasa gano asalin wacece.
Da sauri Ɗayyib ya miƙe yana dariya, cikin yaƙini ya ce idan ba Faɗima ba ( kakar Sulaim matar Ubaidu) to Aysha ce( matar Abduh Dhahab Mahaifiyar Sulaim). Da sauri malamin duba ya gyaɗa kai alamar gaskiya ne.
Kuɗi masu nauyin dake bayyana jindaɗinsu suka sauke mai. Da murmushin samun nasarar duƙunƙune sun da ya yi, ya saɓa jakarsa ta zallar fata ya yi musu sallama. A zahirin gaskiya Kabeer da Malik tabbas a kusa da Company Dhahab suke rayuwa, amma da gaske Kabeer shine Uban gidan Sufyan yasan idan ya faɗi gaskiya a matsayinsa na babban malamin duban da suka ɗauko tun daga wata nahiyar ba zai samu kuɗi mai tsoka ba, batun Macece ko Namiji ne asalin Uban gidan su Malik ba shi da sanin komai akai, shima ya faɗa ne don ya faranta musu shima su faranta mai. Da mugun murmushi malamin duba ya hau motar da zai sadashi da iyakar Yankin Tudu da tumulin kuɗinsa a jaka.
Da gaggawa Ɗayyib da bai taɓa zuwa duba Sufyan ba ya ɗauki hanyar Asibiti, ɗauke da wayar Sufyan da ya jima a kashe.
Bai damu da halin da Sufyan yake ciki ba, ko yaya yanayin jikinsa yake ya naimi waje ya zauna.
Cikin sanyi murya Sufyan ya gaisheshi. Da sakin fuska ya amsa yana yi mai yaya jiki, ko kallon inda Sumaya take baiyi ba, balle ya yi mata godiyar hidimar da takeyi da É—ansu, sai ta basu guri zasuyi magana da ya faÉ—a a kausashe.
Jiki a sanyaye Sumaya ta bar Ɗakin nadamar auren Sufyan na mamaye ruhinta, tausayin Naila da ta fita shaƙar takaici da rashin samun rayuwar Ƴanci na tsarga mata, "ashe haka Naila take ji? Wallah na cuci kaina kaicona!" Ta faɗa ƙasa-ƙasa cikin kuka.
Bayan fitar Sumaya Ɗayyib ya mayar da kansa kan Sufyan. Ya ya jiki ya ƙara yimai yana miƙamai wayarsa. Babu wasa a fuskar Ɗayyib kamar ba Mahaifinsa daya sani a baya ba ya miƙamai wayar.
Jiki a sanyaye Sufyan ya kunna ya ajjiye yana jiran umarnin da zai biyo baya.
"A baya ina lallashinka domin ka yi min biyayya akan abinda kai ne zaka samu cigaba ba ni ba, amma ka bijiremin, to a wannan karon ba cigabanka bane kai kaɗai cigabanmu baki ɗaya, mun gayyato malami daga wani Birni, ya kuma shaida mana Kabeer ba shine Uban gidan ka ba, rufa ido ya yi mana, ba wai don ban yarda da shi ba, sai don na ƙara tabbatarwa nakeson ka kira wanda ya miƙa katin gayyatar bikinka wajen GM ɗinku ka ji dagaske ne ko a'a"
Sufyan yaso ya musa, amma tuna irin yankar da ya sha yasa ya fara lalubo number jikinsa yana rawa.
Bugun farko aka ɗaga da Muryar jimamin da ya nuna andaɗe ana naiman mutum ba'a samesa ba. Bayan sun gaisa da hanzari Baturen yake tambayar lafiya, bai dawo aiki ba ko fushi yake yi GM bai samu halartar taron shagalin bikinsa ba, ya yi haƙuri uzuri ne ya tareshi, ga ayyuka ta ko ina a office amma ba bu shi, don Allah ya dawo.
Daga Sufyan har Ɗayyib ajiyar zuciya suka sauke mai ƙarfi kafin Ɗayyib ya tashi ya rungume Sufyan cikin kukan farin ciki ya ce;
"Ya ɗana Sufyan ina mai neman afuwarka, sai dai banason wannan damar ya zama abin sakankacewa garemu, inaso ya zama fitilar haska mana asalin wacece ta ƙara dawo da Dhahab a tsakanin Faɗima da Aysha" Sufyan da yake son tambayar su wanene Faɗima da Aysha shiru ya yi tuna Mahaifinsa zai iya tuhumar mai yasa bai sansu ba.
A haka ĆŠayyib ya share hours ya bar Sumaya zaune a waje ba tare da damuwar komai ba. A wannan yanayin Hindu ta iso Asibitin kallon inda Sumaya take batayi ba balle ta amsa gaisuwarta.
A wannan karon ma É—ari bisa É—ari ĆŠayyib ya amince da batun da Hindu ta zo dashi, tare da bawa Sufyan umarnin sakin Sumaya da zarar sun koma Birnin Abyad ya ajjiye maganar Soyayya ya fuskanci gobensa. Sai dai dole sai sunyi taro na musamman a kan yadda za'a shayar da Naila sihirin da Hindu ta zo da shi.
Shi dai Sufyan kai kawai yake É—aga musu saboda tsoron yin magana yake yi.
Tun a baya kowa yasan mutanen Yankin Tudu da son kansu da tsananin butulci, sai dai talauci da tsananin rayuwa ya sa suka sauya zuwa mutanen ƙwarai, amma duk da haka ba'a rasa nono a ruga kuma baza'a taɓa taruwa a zama ɗaya.
NAILA
Sartaj ya na ɗaya daga cikin matasan da suke yawan shigowa Gidan Kaka, kuma yana daga cikin waɗanda suka dinga bani kariya, yawan shigowarsa ya haifar da shaƙuwa a tsakaninmu har yakan ci abinci Gidanmu.
Da ƙwaɗayin asalin jinin Yankin Tudu da butulcinsu da bai gama barin jinin Sartaj ba su Ɗayyib su ka samu dama sukayi amfani da shi. Sai dai shure-shure baya hana mutuwa....✍🏻
Na gode da Addu'o'inku Allah Ya bar mu tare Ya kuma bar zumunci.