ZINARE🔥

22

by @nafisatusasaal01

🔥ZINARE🔥




 NAFISA ALIYU SASAAL




Page 22

Kuɗi masu nauyi a hannu da rashin albarka wajen sauke buƙatu Jalal da kansa ya biya Sartaj, bayan ya siyar da yardar da amince dake tsakaninsa da su Naila.

Da tattacen kayan marmari Sartaj ya fara amfani. Ya na zaune suna hira da Naila har ta shanye. A kwana na biyu da yankakkun kayan marmari ma su kyan gani a ido ya yi amfani. A kwana na ukun da ya kasance na ƙarshe da abincin Gidan Kaka ya yi amfani.

SUFYAN; Sufyan bai ƙarasa warkewa ba suka tattara suka koma Birnin Abyad da sunan idan sun isa ya miƙawa Sumaya takardar ta kafin ya wuce Babban Birnin Abyad bakin aikinsa.

NAILA; 
Labarin tafiyar Sufyan bai zama abin damuwa a gareni ba, domin abinda kake so shi kakeyiwa kishi.

A hankali na fara ramewa ƙasusuwan jikina suka fara bayyana kansu kamar ba na cin abinci, kasalar rashin son yin Sallah a kan lokaci da ƙinyi azkhar na neman zamemen jiki.
A cikin kwana biyar nayi wani irin ramar da ya tsoratar da kowa.
Kaka bata wahalar da kanta wajen kaini Asibiti ba, tunda tasan su wanene Iyayen Sufyan. Malamin da ya taimaka mata a waccen lokacin da Hindu ta ciyar da ita Tufa mai ɗauke da sihiri ta nufa. 

Bai buƙaci a kawoni ba da kansa ya zo. Ya na ganina ya tabbatarwa da Kaka abinda take zargi, sai dai nawa sihirin ba irin nata bane, samun maganinsa abune mai matuƙar wahala domin a wajen wani Malami da ke gabashin Yankin Tudu za'a iya samu maganin karya Sihirin. 

Cikin kuka Kaka take faɗin; "wanene ya zaɓi Duniya akan lahira?, wanene ya zaɓi shayar da marainiyar Allah sihiri irin wannan, Allah bamu da kowa sai Kai!" Babu wanda bai tausaya mana ba.

Cikin fusata matasan Yankin suka nufi Gidan Sarkin tsafin Yankin Tudu ya  duba musu wanene ya shayar da Naila Sihiri?.. 

Gangamin Matasan Yankin Tudu ne sukayiwa Gidansu Sartaj zobe, Sartaj ba shi da Uba sai Uwa itama ta fara tsufa.
 Cikin alhini da fargaba take sanar da su yanzunan Sartaj ya ce mata zaije Fadar Sarki Hammam Mai girma Jalal na naimansa.

 Bayaninta ya ƙara fusatar da Matasan tare da ƙara tabbatar da maganar Sarkin Tsafi, don haka suka koma Gidajensu kowa ya ɗebo  makamai sai fadar Sarki Hammam.
A fito musu da Sartaj su yankemai hukunci dai-dai da abinda da ya aikata.

Ihun su da maganganunsu ma su khaushi ne yasa Sarki Hammam umartar fadawansa su lallashesu su kuma sanar da su Sarkin Tsafin Yankin Tudu ba gaskiya ya faɗa ba, so yakeyi ya hanasu zaman lafiya tunda ya ci amanar Masarautarsu ta koresa shiyasa su ma yake so ya tunzura su. Kuma lallai ya na bada umarnin kar wanda ya taɓa lafiyar Sartaj idan ba haka ba zai fuskanci hukunci mai tsanani. 

Duk da an sanar da Matasan Yankin Tudu wannan jawabi na Sarki Hammam  basu motsa ba, har sai da Sarki Hammam ya fito da kanshi ya taushesu da kalamai ma su taushi tare da tabbatar musu da ƙarya Sarkin Tsafin Yankin Tudu yake yi, Sartaj da ya ke na hannun damar Naila tayaya zai shayar da ita sihiri? 

Ba don sun gamsu ba sai don bin umarnin Sarki Hammam wajibi ne a garesu suka tattara suka dawo Gida. 

Da labarin abinda ya faru ya isa wajen Kaka ba tace komai ba sai kuka da takeyi tsoron mutane da rashin yarda da su na ƙara kamata.

★washe gari Matasan Yankin suka yanke shawarar fita naimo Malamin da zai yi min magani a Yankin gabashin da ake ce yake ko kuma ya basu maganin su kawomin. 

Da Kaka tana dama da ta hanasu domin ko sun karɓo bazata iya yimin amfani da shi ba, saboda bata yarda da kowa ba.

Matasan Yankin mu su Goma sha uku, sun kwashe kwanaki huɗu a gabashin Yankin Tudu amma ba su samesa ba, sai maganin da suka ƙarbo daga takwarorinsa. 

Da hannu bibbiyu Kaka ta karɓi maganin su, tare da tarin godiya mai yawa. Sai dai tana karɓa ta zubashi a shara.

Sartaj ya fito yana rayuwarsa kamar kowa amma bayayin nisa da Gida a wayonsa kar wani ya yi mai wani mugun abun. Hanyar Gidan Kaka tuni ya zama haramiya a garesa.

Cikin watanni biyu na ƙanƙance na tsotse na dawo kamar ba ni ba idan Kaka ta kalleni sai ta fashe da Kuka tana cewa;
"Ba sai mun nemo mai warware mana sihiri ba, mai warware mana yana tare da mu, kuma In Shaa Allahu da ƙarfin mulkinsa sai kinga har jikokinki Naila" idan ta faɗi haka fuskata da ta dawo ƴar ƙarama ta yamushe nake kawarwa gefe nayi kukan da ban iyakarsa ba. 

Kaka bata gajiyawa wajen kaiwa Allah kukanmu, dare da rana, Safiya da yammaci. Jinkirin samun sauƙina bai sa Kaka ta karaya ba.

Taimako da ake bamu  ne ya farayin ƙasa, abincin ci ya fara gagararmu, yunwar da ya yi sauƙi a Yankin Tudu ya dawo sabo fil, amma duk da haka da zarar sun ci kasuwar Tukwanen Zinare Matasan Yankin zasu haɗowa Kaka kuɗi, haka ƴan uwan Mahaifina, a wasu lokutan har da Kakannina na wajen uwa.

Shawarar dawo da sana'ar Mahaifiyata na yin kayan wasan Yara na lakar ƙasa Kaka ta yanke. Drivern da yake fita iyakar Yankin Tudu ta roƙi alfarma ya dinga kaita bakin tasha tana siyarwa idan tayi ciniki ta biyashi, tunda kullum sai yaje. 

Kai tsaye ya nuna mata kyauta zai dinga kaita ya dawo da ita amma tana ganin barin Naila a gida ba zai zama matsala ba, mai zai hana ta dinga lulluɓeni muna tafiya tare? Da sauri Kaka ta amince domin itama fargabarta kenan yadda zata barni ni kaɗai.

Ba ta naimi shawarar kowa ba, kwana biyu bayannan muka fara bin Driver zuwa Iyakar Yankin Tudu. 

A gefe nake rakuɓewa, Kaka kuma matafiya take bi tana tallata musu su zo su siya kayan lakar da ta ƙera Fisabilillah. Cikin hukuncin Ubangiji, sai tausayin Kaka da tausayin yadda na koma ya sa mutane suka yi ta siya har da masu ba mu kyautar kuɗi. kullum ba ma dawowa Gida da rogawa sai ya ƙare. kuma Driver bai taɓa karɓar ko sisinmu ba. 
Duk wannan wahalar da Kaka take sha haka take ƙara raba dare a zaune tana kaiwa Allah kuka, domin bata iya tsayuwa saboda shekaru da wahalar da take sha. 

Ƴan uwan Mahaifina sun kawo ƙorafin ta dinga barina a Gida, amma ta nuna sam bata yarda ba, tunda suma ba zama sukeyi ba kowa nema yake fita, matansu kuma ba lallai su kula da ni ba.

A lokacin da muka cika sati shida da fara fita Iyakar Yankin Tudu, jirginsu Sufyan ya sauka. Motocin fadar Sarki Hammam ne suka zo tarbarsa amma da yake gulmar halin da muke ciki ya je mai tun kafin ya iso, sai ya gwada zuwa inda muke don kawai yayimana izgilanci kafin ya wuce.

Lokacin da ya iso ɗan rumfar da muke zama Kaka na can tallatawa matafiya kayanmu Ni kuma ina rakuɓe da ruwan shan da Kaka ta bani a gefena. Dariyarsa kawai na tsinta a kaina.
Kafin ya fara magana Cikin izgilanci;

"Naila korarriyar Ɗalibar da talauci ya hana iyayenta naima mata magani ta warke ta koma Makaranta, ba kina ganin zaluntarki mukayi ba, lokacin da muka yi miki gata muka kaiki Birnin Abyad muka baki makwanci. Amma saboda butulci don kawai ina karɓar kuɗin kitson da kike yi kika zaɓi tozartani, yanzu gashi Ni da ke waye yake ji a jikinsa, kalleki domin Allah." 
Ban ɗago ba sai yawun da nake ta tofawa ruwan hannuna kamar zautacciya.

Farar fuskarsa da ya ke matuƙar ji dashi ya shafa dai-dai satin Yankar da Ɗayyib ya yi mai da bai gama bajewa ba kafin ya ƙara ce wa;
"Banso haukarki tasa bakya gane maganganuna ba, amma wannan yawun da kike tofarwa da adanawa kikayi wataƙila kya rage wannan yamutsewar da kikay..." Saukar ruwan har cikin bakinsa yasa ya kurma ihu haɗe da tsalle kamar ƙaramin Yaro kafin ka ce kwabo tuni Matafiya sun cika wajen, suna kallon Sufyan da yake ihun "Saliva! Saliva!!" Haɗe da waftar ruwan hannun mutane yana wanke fuskarsa da bakinsa. Gudun abun kunya ba tare da bin ba'asi ba Fadawan Sarki Hammam suka jashi Mota. Abinda Sufyan bai sani ba maganata ta koma kamar ta ƴan yara ba kowane yake fuskanta ba, ko azabar ciwon ya tashi sai dai na yi ta kuka bana iya bayani yadda za'a fuskanceni. Kaka bata wahalar da kanta wajen tambayar abinda ya faru ba ta koma wajen tallarta, suma mutanen da suka taru kowa ya kama gabansa.

A hanyar mu ta dawowa nake yiwa Kaka kwatancen abinda ya faru. Dariyar da rabonta da yin irinsa har ta manta ta ƙyalƙyale da shi, har muka isa gida lokaci zuwa lokaci sai ta saki dariya.

A wannan dare nasha azaba irin azabar da bansan yadda zan misaltashi ba, da taimakon addu'o'in da Kaka take tofamin barcin ya ɗaukeni. Kafin wayewar gari na ƙara fita hayyacina, babu wanda hankalinsa bai tashi ba.

SUFYAN; har ya suka isa gida bai sanar da Fadawa abinda ya faru ba suma kuma ba su tambayesa ba sai sannu da suke ta jeromai.

Ya yi wanka ya fi sau biyar haka bakinsa ya wanke yafi a ƙirga. Da daddare bayan Sallar isha suka ɗauki hanyar Yankinsu Hindu shi da da ita.

 A daren Suka turo jinnun da zasu matsamin da zarar Sufyan ya zo da buƙatar komawata tare da albishir ɗin samo Malamin gabashin da suke nema Su Kaka za su amince a mayar da aurenmu.

 Sufyan aka bawa maganin da zansha sihirin ya karye ya zura a aljihun bayan wandonsa.

Gaba ɗaya sai ya matsu gari ya yi haske domin a daren suka ƙara dawowa Yankin Tudu.

Da Safe ko wanka bai yi ba balle ya karyawa ya nufo Gidan Kaka da sunan duba jikina kamar yadda suka tsara kafin zuwan su Ɗayyib. Babu wanda ya rakosa, fuskarsa a tsamke alamun dai ba'a son ransa zai zo ba.

A tsakar gida ya samu Kaka ƙannen Mahaifina na ɗaki tare da ni kowa ya na tofamin duk addu'ar da ta zo bakinsa.

Kaka tana ganinsa ta dakata daga hura wutar da takeyi. Cikin ladabi kamar gaske ya tsugunna yana gaisheta. Kafin ya ɗago Kaka ta rarumo ƙaton iccen da ya ke ci da wuta ta nufesa. Sufyan ya na hangota ya yunƙura ya miƙe a guje, garin wannan yunƙurawa Maganin bayan aljihunsa da bawani zurfi ne da shi ba ya faɗo ƙasa ba tare da ya ankara ba. 

Ƙur Kaka take kallon magananin, kafin ta yi Bismillah ta na yunƙurin kai hannunta.

 Muryar mutum taji a bayanta.....✍🏻