ZINARE🔥

23

by @nafisatusasaal01

🔥ZINARE🔥


 NAFISA ALIYU SASAAL




Page 23


Da hanzari Kaka ta É—auke Æ™ullin maganin ta wurgashi  kwanon gefenta. 

Yayyan Mahaifin Naila ne suke yunƙurin fitowa. Sallama su kayi mata, tare da alƙawarin kawo wani malamin ya ƙara duba jikin Naila. Su na fita Kaka ta sauke ajiyar zuciya, ba ta koma ɗakin ba tasa mayafi ta lalluɓe jikinta sai gidan Mallam.

Juya maganin yake yi a hannunsa fuskarsa da yalwataccen murmushi "Tabbas! Allah ba Ya barci, sun biyota har gida sun shayar da ita sihiri, Allah kuma Ya Æ™addara su zasu Æ™ara biyota gida da makarin sihirin." Kaka da ke ta zare ido alamun bata fahimta ba domin ta É—auka wani bala'in Sufyan ya Æ™ara kawo musu. Dalla-dalla Mallam ya yi mata bayani. 

Cikin kuka Kaka takai goshinta Æ™asa tana yiwa  Allah godiya. 

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, shayar da Naila maganin a Yankin Tudu zai dawo da hannun agogo baya, domin da zarar sun ga ta warke zasu É“ullo ta wata hanyar, mai zai hana tunda Naila tana da matsugunin haya a Birnin Abyad da kuÉ—insa bai Æ™areba tunda Bushra kuÉ—in shekaru uku ta biya kamar yadda Naila ta faÉ—a, Kaka ta bi can  suyi jinya. 

Kaka wani irin kallo take yiwa Mallam fuskarta ɗauke da murmushi, kafin ta fashe da kuka domin ta rasa abun faɗa, bata taɓa kawo irin wannan shawarar a cikin zuciyarta ba balle ta samu mafitarsa a zahiri sai gashi Mallam ya haska mata hanya. Ta na godiya tana kuka.

 Bayan tasha kuka sai ta Æ™ara naiman shawararsa akan yadda zasu tara kuÉ—in motar zuwa Birnin Abyad. 

Kaka da murnar da ta danne a cikin zuciyarta ta dawo Gida, cikin jakar da take adana muhimman abubuwa ta anada maganin makarin sihirin jikin Naila.

Kaka har Yankinsu Mahaifiyar Naila ta yi tattaki ta kai mu su koken ance akwai malami a Birnin Abyad da zaiyiwa Naila magani ta warke kuma ita bata da halin da zasu iya tafiya tare, su taimaka mata da abinda suke da shi.

Kakan Naila mutum ne mai jama'a, don haka kafin tafiyar Kaka ya shiga layi-layi yana roƙon a taimaka mai za'a kai jikarsa ƴar gidan marigayiya Birnin Abyad neman magani kuma basu da hali a taimaka. Kafin rufuwar hour uku sai ga kuɗi masu yawa sun taru. Kakannin Naila ba su cire ko sisi ba suka bawa Kaka kuɗin tare da alƙawarin kowawa Naila ziyara kafin su wuce.

Kaka É“oye kuÉ—in ta yi ta tunkarin yayyan Mahaifin Naila, suma É—ari bisa É—ari suka bayarda da goyon bayansu, saboda samun lafiyar Naila ta koma bakin karatunta shine burinsu domin daga gareta suke sa ran samun canji. Suma layi-layi suka bi suna shela. 

A ranar dai ba'a samu waÉ—anda suka bayar da kuÉ—i ba, amma washe gari bayan sun ci Kasuwar Tukwanen Zinare suka dinga kawo kuÉ—i, kafin kace me kuÉ—in zuwa Birnin Abyad har da na cin abinci da extra sun haÉ—u. 

Su ma Yayyen Mahaifin Naila tasu gudummawar suka kawo, tare da tattaunawa sirri da Kaka, akan idan Naila ta warke kar su dawo, su yi zamansu a can ta dinga kula da Naila, tunda ta iya riƙe Sufyan har da taimakon Mahaifansa da sana'ar kitsonta to suma zasu samu ingantacciyar rayuwa a chan, za su ƙara taro wasu kuɗin da zasu dinga cin abinci kafin jikin Naila ya ƙarasa warwarewa.

Kaka tana kuka tana godiya suma kukan suke yi suna nuna mata cigaban Naila shine burinsu.

Bayan komai ya lafa Kaka ta koma gidan Mallam domin yimasa godiya akan shawarar da ya ba ta. Wa su addu'o'in yaƙara bata, domin yasan duk daran daɗewa za su samu labari warkewar Naila, duk da ba lallai Sufyan ya ba su labarin yardar da maganin da ya yi ba.

SUFYAN; bayan ya fito daga gidan Kaka daidaita tafiyarsa ya yi kamar komai bai faru ba. Bayan ya kai gida ɓangarensa ya wuce ya yi wanka ya yi Breakfast dukka ransa ba daɗi da abinda Kaka tayi mai lokaci zuwa lokaci sai ya saki tsaki, a haka ya koma barci Bayan ya yi wayar sirri da Sumaya.

Sufyan lokacin da ya isa Birnin Abyad kai tsaye masauki ya wuce da Sumaya Æ´an uwanta kuma suka wuce Gida. Maganganu ma su daÉ—i yake ta lallashinta da su tare da shaidamata duk wasu abubuwa da suke faruwa ta hanyar wanke Mahaifansa har da ce mata;

"Mahaifina mutumin Æ™warai ne mai sauÆ™in kai, amma rashin fahimta da butulcin mutanen Yankina yasa suke ganin mahaifina kamar azzalumin da ya hana Yankinsu cigaba. Mahaifiyata Macece mafaÉ—aciya amma da zarar kun saba ta sauko daga fushin sakin Naila da na yi zata fara sonki, fushinta na wani lokaci ne, kuma Ni bazan taÉ“a son Naila ba, saboda  mutumin da na fi tsana a rayuwarta take so har yanzu, da hotonsa take yawo, kuma akansa ta zaÉ“i bijiremin. Saboda haka nake roÆ™onki Sumaya ki kwantar da hankalinki ki bani haÉ—in kai" 

A kaf maganganunsa ba bu wanda ta fahimta tunda ya ambaci ba ya son Naila ne saboda tana yawo da hoton maƙiyinsa. Cikin kasa danne kishin Naila da ya yunƙuromata ta ce;
"Kenan da ba don tanason wanda ka tsana ba, ka na sonta kenan? Dama can itace bata sonka kakeyimin Æ™arya? Sufyan banajin aurenmu zai kai labari saboda kowa naka ba ya sona, hatta Mahaifinka Æ™iri-Æ™iri na hango tsanata a cikin idanuwansa. Tun kafin komai na mu yayi nisa kawai ka sauwaÆ™emin." 

Sufyan murmushi ya saki yana kallonta, tayaya zai sha dukka wannan Yankar daga mahaifinsa kuma ya ɓata shekaru yana kashe mata kuɗinsa da na Naila ta ce haka kawai zata suɓucemai shi ba zai moreta ba? Su kansu Mahaifansa da zai bayyana musu bautar da ya yi mata da basu ba shi umarnin sakinta ba. Sai da ya numfasa sannan ya fara yaudararta da yaudararrun kalamansa da rabi da kwantansa duk ƙaryane, saboda yasan har abada Iyayensa ba za su taɓa sonta ba, amma shi kam bazai yi gangancin sakinta da wuri ba sai ya samu wacce ta kwanmai ko Naila ta dawo hannunsa kamar yadda suka tsara.

Sumaya da yake gwanace wajen son duniya tana ganin Sufyan ya lodo musu Siyayya tare da cewa ta biyosa zuwa Babban Birnin Abyad idan taji batason zama da shi yayimata alƙawarin sakinta sai ta amince.

★washe gari suka je har Gidan Iyayenta ta yi musu bankwana.

 Muguntar Sufyan yasa ya biya tsohon Gidan su ko zai samu mukullin sashen Naila, ga mamakinsa hanasa shiga Gidan akayi gaba É—aya, haka suka dawo suka É—auki hanyar Babban Birnin Abyad ransa a Æ™untace. 

Kyan matsugunin  Sufyan na Babban Birnin Abyad ba Æ™aramin tafiya da imanin Sumaya ya yi ba, a take ta manta irin Æ™iyayya da wahalar da ta sha a Yankin Tudu. Tana jin ko Iyayen Sufyan ba su isa su rabasu ba. 

A zahirin gaskiya yanayin yadda yake iya juya Naila da yi mata abinda yaga dama wajen sauke buÆ™atarsa sam ba iri É—aya bane da na Sumaya, Æ™iri-Æ™iri take nuna ita batason wannan ita bazata iya wannan ba. 

Wannan dalilin yasa ya ƙara karɓar shawarar Iyayensa hannu bibbiyu, Naila tamkar baiwa take sai yadda ya ga dama zai yi da ita, ta ƙiyi kuma jikinta ya gayamata tunda bata da gatan kowa dalilin dawowarsa Yankin Tudu kenan.

★washe gari Ɗayyib ya tura wakilansa kan komen Naila ta hanyar Yayyan Mahaifinta da suka yaudara da kuɗi a baya.

Da ƙarfin gwiwarsu dukkansu suka haɗa bakin ba su yarda Naila ta komawa auren Sufyan ba har sai ta samu sauƙi, kuma ko ta samu sauƙi sai sun ji ta bakinta idan ta amince. Idan kuma har da gaske Sufyan magani zai nema mata to yafara naima mata kafin ta koma Gidansa.

Martanin Yayyan Mahaifin Naila akan komenta gidan Sufyan mummunar labari ne a wajen ÆŠayyib, Jalal, Hindu da Sufyan kanshi. 
A wannan dare dukkasu sukayi tafiyar Sirri zuwa Yankinsu Hindu, suka bawa  Malamin duban Hindu kuÉ—i maiyawa ya Æ™ara tura mugayen aljanun da zasu addabi Naila ta ji kamar zata mutu har sai ahalinta sun sallama sun amince da komenta.

Fitar su da rashin dawowarsu sai tsakiyar dare yasa Sartaj da ya kawo musu gulmar tafiyar Naila da sassafe Birnin Abyad kasa samun su. Don haka a daren ya haƙura ya juyo domin dawowa Gida.

Ya na É—anyi nesa da Masarautar Sarki Hammam, MALIK da ya sauko daga mota ya bayyana a gabansa gaba É—ayanshi....

NAILA; A wannan dare nasha azaba irin wanda bantaÉ“a ji ba, Kaka tana kaina, da Æ™arfin gwiwa tare yaÆ™inin samun sauÆ™i daga wajen Ubangiji take tofamin addu'o'i wasu ta tofa a ruwa ta watsamin. Bayan wani lokaci barci ya É—aukeni. 

Hannunta ta É—aga sama tana ce wa;

"Ya Ubangiji!   da wanda ya ke zuwa ya biya kuÉ—i a sanyawa Naila ciwo, da wanda yake turo ciwon, da shi kanshi jinnun da yake assasa ciwon duk Kaine Ubangijinsu Ya Allah! Ya Allah kayimin maganinsu da gaggawa Don Æ™arfin Mulkinka, Ka sauÆ™aÆ™amin tafiya da ita Ya Allah.

★ washe gari da asuba Driver ya iso ƙofar Gidanmu, kafatanin mutanen Yankin da suka san da tafiyar duk sun hallara a ƙofar Gidanmu, duk suna kuka da addu'o'i kala-kala ɗauke a bakunansu.

ÆŠaya bayan É—aya suka dinga rungumeni, suna sumbatar Æ™uncina, Ni dai nayi laÆ™was Hannuna a cikin na Kaka, Yayyan Mahaifina suna kuka suma suka rungumeni, Ni dai bana iya kuka sai kai da nake É—aga musu. 

Muna yunƙurin shiga Mota Kakannina na wajen uwa suka iso da mutanensu, kalaman su gareni na ƙarfin gwiwa ne, tare da tarin yaƙini a kaina.

Da haka muka shiga Mota kaka tana kuka nima sai a lokacin hawaye ya zubomin ina É—agamusu kai, Mutanen Yankin Tudu suna kuka muna kuka muka rabu.

Misalin ƙarfe Takwas na safiya muka isa Iyakar Yankin Tudu da wajen hawa motar Birnin Abyad.

 Driver shi ya taimaka mana har motar mu ta tashi, shima da yaga Motarmu ta fara tafiya hawayensa ya sharce yana É—ago mana hannu...🥹