24
🔥ZINARE🔥
N. A. S
Page 24
Bayyanar fuskar Malik ga duk wani ɗan Yankin Tudu, babban abun fargaba ne. Saboda ba ya zuwa ya tafi bai bar shaida ba.
Sartaj mummunar gani ya yiwa Malik saboda bai sakaya fuskarsa da hutu ya yi kamu mai kyau ba, a zallarsa ya fitomai.
Fararen idanuwansa masu tsananin haske da girma Malik ya zubawa ƙafafuwan Sartaj da suketa rawa kamar an jona mu su shocking.
Da zafin takunsa ya ke tunkaro Sartaj da gumi ke tsiyayowa tun daga cikin gashin kaa, har cikin suɗaɗɗen takalminsa.
Da sauri Sartaj ya yunƙura zai gudu, fitsari da bayan gida na zuwarmai lokaci ɗaya.
Munfashi Malik ya sauke kafin ya taka sawun da ya basa damar cafkar Sartaj.
Guri ɗaya ya tsayar da fuskar Sartaj yana kallonsa shima ya na kallonsa. A hankali Malik ya ɗage girarsa ɗaya sannan ya ce
"kasanni?"
"Ni dai ina neman afuwa, wallahi na daina" Sartaj ya faɗa daƙyar muryarsa na karkarwa.
"Na ce kasanni?" Malik ya ƙara tambayarsa kamar bai ji abinda ya ce ba.
"Na sanka! Au wallahi bansan ka ba" Sartaj ya faɗa a ruɗe.
"Tabbas ba ka sanni ba, domin da ka sanni da bakayi abinda ka yi ba" Malik yaƙarasa faɗa yana kai hannunsa bayan wandonsa.
"Au na tuna, na sanka wallahi! kuskure ne daga yau na daina, na daina kai gulmar kowa kuma ba zan ƙara cutar da kowa ba, Dan Allah ka yafemin wallahi sharrin shaiɗan ne."
Yana ƙoƙarin ƙarayin magana Malik ya kwantar da shi ƙasa ya na cewa;
"Bayyanata a Yankin Tudu na mutane ne ma su kafiya irinka, ba na zuwarwa laifi ɗaya sai sun taru. Idan na barka gobe sharrin shaiɗan zai sa ka ƙara kai musu wani rahoton, ba tare ka tuna da kashedina ba amma idan na bar maka shaida Fa??"
Azabar ficewar ƙafar Sartaj ɗaya ne yasa ya sakin ihun da ya karaɗe Yankin.
Kafin fitowar Fadawan Sarki Hammam babu Malik, sai Sartaj da ke kwance cikin jini da ƙafarsa ɗaya da aka yanke rungume a hannunsa, kamar yadda Malik ya maƙalamai a tsakanin Hannuwansa.
Ihu su ma suka kurma.
Tuni mutane suka fara firfito daga Gidajensu.
Duk da Sartaj ya ba wa Mutanen Yankin Tudu tausayi hakan bai hanasu murmusa a ɓoye ba, acewar su sakayyar abinda ya yiwa Naila ne.
★washe gari yana farfaɗowa daga dogon sumar azabar da ya yi da ihun kiran Malik yafara yana roƙo da magiya.
A surutan Sartaj da aka sanarwa su Ɗayyib da su kayi dawowar cikin dare suka fuskanci Malik yana bibiyarsu, irin bibiyar da basu san ta hanyar da zasu toshesa ba.
Mutanen Yankin da suka ji ai aikin Malik ne, tsoron gulmar kowa da cin amanar junansu ne ya ƙara shigarsu. Tunda ga shi an yankewa Sartaj ƙafar da yake zaryar kaiwa su Ɗayyib gulma dashi.
Amma mai yasa Malik bai taimaki Naila ba, ko bai san halin da take ciki ba ne?????? Tambayoyin da suke ta yiwa junansu kenan.
Duk nacin da akayi Sartaj ya buɗe baki ya faɗi ina yaga Malik har ya yanke mai ƙafa, ƙin yin magana ya yi.
Washe gari da su Ɗayyib suka zo dubasa ihu ya kurma yana rufe fuskarsa, alamun bayason ganinsu. Har suka bar ɗakin bai buɗe fuskarsa ba.
Har Sartaj ya warke ba ya iya yin gulmar kowa, balle ya ambaci sunan Malik, gani yake yi kamar idan ya ambaci sunansa zai bayyana a gabansa.
Ranar da su Ɗayyib suka yanke shawarar mafita akan Sartaj gudun tonuwar asirinsu washe gari aka nemesa aka rasa shi da tsohuwar Mahaifiyarsa.
Ɓatan Sartaj da mahaifiyarsa ya yi matuƙar tayar da hankali Mutanen Daular Sarki Hammam, sama da yadda labarin tafiyar Naila da Kakarta Birnin Abyad ya tashi hankalin su, domin sun san ko sunje dole su dawo, saboda maganin matsalarta ya na wajensu. Saɓanin talakawan Yankin da suke ganin Sartaj ya gudune saboda abun kunyar da ya aikata.
A karon farko aka fara saka jami'ai a duk wani hanyar da zai kai mutum cikin Yankin Tudu domin kawo ƙarshen Malik, shima Sufyan cikin gaggawa ya shirya komawa, saboda ɓacewar maganin da yasan dole idan ya cigaba da zama a tambayesa ya na ina? da kuma gudun kar ɓarna Malik ta ratsa da shi, domin zuwa lokacin ya fuskanci a kwai wasu manyan sirrikan da bai san da su ba...
NAILA
Allah Ya amsa addu'ar Kaka. A tafiyar kwanakin da muka yi, ciwona ya na yawan tashi, amma da zarar ya tashi za ta rungumeni ta yi ta tofamin addu'o'i har sai jikina ya yi yaushi barci mai nauyi ya ɗaukeni.
BIRNIN ABYAD
Da taimakon Allah muka isa Birnin Abyad. Kaka ta zuba ƙauyanci wasu lokutan garin Kallon Mutane har tuntuɓe takeyi.
Da ɗan ƙarfin da nake ji, nake yi mata raɗar motar da zamu hau a kunne. Da hannu kaka take kwatanta mu su komai tunda batajin turanci, kuma batajin asalin yaren ƙasar. Kamar ko da yaushe idanuwana na maƙale a hanyar Babban Birnin Abyad, ƙewar Bushra da Yasar na bijiromin.
Gidanmu ba ƙaramin burge Kaka ya yi ba.
Ba ta hutu ba bayan munyi salla ta fara gyara ko ina na sashen.
Da taimakonta bayan ta gama nayi wanka. A ranar Kaka ta farayimin amfani da maganin su Sufyan kamar yadda Mallam ya koya mata. Bayan wannan ta haɗa har addu'o'in da ya bata.
Da guzurin kayan abincin da muka taho da shi daga Yankin Tudu muka fara amfani, kafin na ji sauƙi mu siyo wasu. A cikin kwana uku sauƙi ya fara samuwa, ina iyayin komai da kaina, har nayi Sallah a tsaye a kan ƙafafuwana.
Kwana biyu bayan nan na shirya Ni da Kaka muka tafi Gidan Iyayen Yasar domin jin halin da yake ciki.
Yasar ya na kwance babu lafiya tsohon watanni biyar kamar yadda Mahaifiyarsa ta faɗa. Accident ya yi a kan hanyarsa ta dawowa daga Babban Birnin Abyad. Ya na barci muka je, bai farka ba har sai da muka fara haramar tafiya.
Da mamaki yake kallonmu kamar bai ganemu ba, har sai da na gaisheshi na faɗamai sunana sannan ya fahimci ni ce. Da zafin naman ɗan ƙarfin da yake ji ya gyara zamansa ya na faɗin
"Naila! Maiyasameki kika koma haka? Ciwo kakayi? Maiyasa baki dawo Makaranta ba? Na so zuwa har Yankin Tudu cigiyarki wannan tsautayin ya faɗamin ki gafarceni."
Kaina na sunkuyar ƙasa ina Kuka.
Kaka ce ta basu labarin jinyar da na yi. Dukkansu sun tausayamin har Iyayensa da a baya suke guduna. Mun ɗan jima a Gidan kafin mu dawo Gida.
★washe gari sai ga siyayyar kayan abinci da kayan motsa baki kala-kala har da kayan sawar Kaka, da wayar amsa kira duk daga Gidansu Yasar. Munyi farin ciki matuƙa tare da godiya mai tarin yawa.
A hankali a hankali jikina ya fara murjewa saboda canjin cima, muhallahi da kuma lafiyar da nake ƙara samu. Itama Kaka tsaf ta yi kyau, su na waya da mutanen Yankin Tudu lokaci zuwa lokaci da number da suka rubuto mata a jikin takarda.
Bayan na samu sauƙi, Yasar da kansa ya jagoranceni har Makarantamu duk da baya iya tafiya sosai saboda karayar ƙafarsa da bai gama warkewa ba.
Ban samu matsalaba albarcin Yasar da kuma shaidun da suka gani da ido, saboda har lokacin akwai banbanci da yadda nake a baya kafin na bar Birnin Abyad.
Da farin ciki na dawo Gida, itama Kaka daɗi ne ya kamata, tayi ta yiwa Yasar godiya tana samai albarka.
A cikin watanni biyun da Makarantarmu suka ƙaramin a matsayin hutu, jikina ya yi kyau kamar ban taɓa jinya ba. Da kaina na kai Kaka mukayi siyayya kafin mu wuce Gidansu Yasar.
Irin motocin da muka gani a harabar gidanne yasa na cewa Kaka mu juya, domin jikina ya na bani wakilai ne daga wajen aikinsa na Babban Birnin Abyad. Sam Kaka ta nuna bata san zanceba ba, a cewar ta "mu ina ruwanmu da su? mu da ba wajensu muka zo ba."
A living room ɗin farko idanuwana suka sauka a kan mutumin da na ke gani tamkar Malik, duk da ya sanya tabaran rage hasken ranar da ya sakaye idanuwansa, ga kuma tarin ƙasumbar da ya bari a fuskarsa. Sai mace ɗaya da take zaune a kujera daban itama na kasa gane ina na santa ina na taɓa ganinta. Kamar yadda nake Kallonsu bayan na gaishesu haka Macen da shekarunta suka ɗan ja ta ƙuramin ido.
Kaka tunda ta gaishesu ta nufi cikin Gidan wajen ƙannen Yasar da suke wasa da dariya.
Namijin ne ya fara miƙewa gaba ɗayansa yana miƙawa Yasar hannu. Miƙewarsa ya sa ya fito sak a Malik ɗin da nake zargi, kallon da na yi mai shekarun baya a gidan Abduh Dhahab yana shara da safiya na ƙara dawowa idanuwana. Zumbur na miƙe ina kallonsa kamar zan cinyesa, kafin na ambaci sunansa mahaifiyar Yasar da take ganin girmansu a matsayin su na Manyan Iyayen Gidan ɗanta ta ja hannuna ta zaunar da ni a gefenta, a tunaninta ciwon jinnun da Kaka tace inayi ne ya ƙara dawowa. Da harshen ƙasar Abyad take ba su haƙurin ba ni da lafiya ne.
Macen ce ta amsa mata amma Namijin fita ya yi. Itama miƙewa tayi Zinaren da ta yi ado da shi na walwali a kunnenta da wuyarta.
Har mota Mahaifiyar Yasar da Yasar suka yi musu rakiya, har lokacin ina zaune kamar an dasani.
Bayan sun dawo Yasar yake tambayata na san su ne? Nasan ko nayi mai bayani ba lallai ya yarda da ni ba don haka na ce mai "a'a." Har muka bar gidan ban saki jikina ba, duk Yasar yana ankare da ni.
Rashin walwala da yadda nake haɗe rai yasa Kaka ta ce na zo na rakata mu siyo abu, Yasar ya bata kuɗi. Waccen wajen da na taɓa haɗuwa da Sufyan na ce muje. Ƙananun kayan CK da Yasar yake yawan siyomin na sanya sai scarf mai girman da na nannaɗe har rabin fuskata da shi gudun haɗuwa da Sufyan, ko Sumaya.
Muna cikin siyayya idanuwana suka faɗa kansa da jami'ai biyu a bayansa, same mutumin da na gani a Gidan su Yasar da rana.
Ya na fita na rufamai baya da hanzari ba tare da na saurari Kaka da ke tambayar "Naila ina zaki je?"
Yana ƙoƙarin zura gangar jikinsa a Mota na ƙaraso da Gudu, cikin ɗan ɗaga murya na ce "Malik, dan Allah idan kaine ka tsaya na roƙeƙa"...✍🏻
Duk mai son Ɗaukar Malik haya a Yankinsu tayimin DM saboda irin su Sartaj😂😂 I came in peace ☹️