25
🔥ZINARE🔥
NAFISA ALIYU SASAAL
Page 25
A kaikace yake kallona, irin kallon da bansan yadda zan fassarashi ba.
A kan idanuwana ya shige mota still yana kallona kamar wanda bai Sanni ba amma yake tunanin a ina ya taɓa ganina.
Ina ji ina gani Malik ya yi tafiyarsa.
Tafiyarsa ba tare da ya buɗe baki ya cemin komai ba ya yi matuƙar sosa zuciyata, har ya sani fara tunanin to maiyasa nake bibiyar duk wanda abu ya taɓa haɗa shi da Sulaim? mai nake so su sanar da ni? Kenan banyi imani da ƙaddara ba. Ko so nake yi su cemin Sulaim yana raye? To idan ma Sulaim ɗin ya na raye cewa ya yi damacan ya na so na, ko zai iya aurena? Maiyasa bazan rungumi maraicina na rufawa kaina asiri ba kamar yadda Allah Ya rufamin. Domin abinda ya yi Sufyan shi ya yi Sulaim saboda daga tsatso ɗaya suka fito sai dai banbancin ra'ayi da ɗabi'a.
Jikina a sanyaya na koma wajen Kaka, har muka dawo Gida ban saki raina ba. Tun tana lallashina da tambayar abinda ya ke damuna har ta gaji ta shareni.
Sanyawa zuciyata lallai sai na manta Sulaim da duk wani abu daya dangaceshi na fuskanci rayuwar da zai kawowa Yankin cigaba ne ya sanyamin zazzaɓi mai zafin gaske.
★Da Asubahi ta yi ko miƙewa da kyau bana iya yi saboda ciwon kai.
Kaka hankalinta ne ya tashi, cikin kuka takeyimin faɗar idan zaman Birnin Abyad ɗin ne banaso to na tattara mu koma Yankin Tudu, su ƙarasa kasheni tunda ba zan kwantar da hankalina ba.
Da sassafe ta kira Yasar tana mitar ƙuncin da na kwana da shi, yanzu gashi na tashi da zazzaɓi. Inajin Yasar ya na tausarta tana ƙara haƙiƙancewa ya zo ya tambaye ni idan zaman Birnin Abyad ɗin ne banaso sai mu tattara mu koma Yankin Tudu.
Ba su yi hour biyu da yin waya ba, sabon Drivern da'aka ajjiyewa Yasar ya kawo shi. Kaka ta na ganinsa ta miƙe zubur tana cewa;
"Ni bani da zaɓi, tunda bata tausayin kanta, tafison na mutu ina ƙunsar baƙin ciki, kuma daga yau Ni dai ba bu ruwana da ita" murmushi Yasar ya yi yana gaisheta, daƙyar ta haƙura da mitarta ta amsa gaisuwarsa kafin ta bar ɗakin.
Kafin na gaishe da Yasar ya katseni da ambaton sunana
"Naila"
A hankali na ce "na'am"
"Menene alaƙarki da su Malik Dhahab? domin tun jiya ina sane da sauyin yanayinki, baki taɓa ɓoyemin komai ba amma jiya kin ɓoyemin Naila, menene gaskiya? " Yasar ya ƙarasa faɗa yana kallona.
Haɗin sunan Malik da Dhahab shine abinda ya ƙara tsananta ciwon kaina, kenan dai da gaske Malik ɗin Yankin Tudu mai gutsirewa mutane harshe shi na gani, to ko dai da harshen mutanen dayake gutsirewa ya yi kuɗi har ya koma Malik Dhahab? Tunda a sanin da na yi musu a shekarun baya talakawa ne fitik.
"Naila kinyi shiru, ko dai da gaske Yankin Tudu kikeson ku koma kamar yadda Kaka ta faÉ—a?" Yasar da ya gaji da dakon jiran amsata ya tambaya.
Kaina na girgiza kafin na fara magana muryata a sanyaye;
"Nasan Malik a Yankina, shekarun masu yawa baya, ina bibiyarsa ne domin na tambayesa ina Sulaim da gaske wuta ta ƙoneshi ya mutu, sai dai ƙiri-ƙiri Malik ya nuna bai Sanni ba bai ma taɓa gani na ba, wannan ne ya yi min ciwo har tashi da zazzaɓi."
Da mamaki Yasar ya ce;
"Anya kuwa Naila kinsan wanene Malik? Su Malik fa asalin ƴan ƙasar Abyad ne, domin da harshen da mafi rinjaye kuma mafi wahala na ƙasar Abyad dukka ahalin Gidan su ke amfani, yare ne mai wuyar koya a wajen bare, ko dai kama yake yi miki da waccen Malik ɗin?"
Nasan dama ba lallai ya yarda da ni ba, don haka kai tsaye na karɓi yardar Malik kama yake yimin da waccen Malik ɗin.
Nasiha Yasar ya yimin tare da tunamin yaƙinin da mutanen Yankina suke da shi a kaina, don haka na mayar da kai nayi karatu bakin iyawata.
Kamar zan iya cire komai a raina na amsawa Yasar zan cire tunanin komai nayi karatu.
Ya na É—an jima a Gidanmu kafin ya tafi.
Bayan tafiyarsa dalla-dalla na zauna na warwarewa Kaka komai. Kaka tsohuwace mai saurin fahimta da sauƙin hali bata da birkicewar wa su tsofaffin.
Cikin hikima ta nusantar da ni, ko da ace Sulaim yana raye ba Mijin aurena ba ne, na tsaya a iya matsayina na kuma tsaya tsayin daka wajen manta baya na fuskanci gaba, kar kuma na manta haɗakar kuɗin Mutanen Yankin Kakana, da na Mutanen Yankin Tudu ne ya kawomu Birnin Abyad ba domin komai ba sai don na yi karatu saboda gareni suke sakaran samun canji, kar na bari tunanin wanda da zai samu damar ƙara dawowa duniya ban kai matsayin da zai soni ba ya lalatamin Gobena. Har na kasa zama abinda mutanen Yankina suke yi min fata.
Sufyan da bai gaji arziƙiba bai kuma gaji sarauta ba ya gujeni balle wanda ya gaji Sarauta gaba da baya tare da tarin arziƙine zai so ni, Karki kuma wahalar da kanki wajen tunanin Sulaim yana raye ko baya raye, ki ƙaddarawa ranki ya mutu, ba kuma zai ƙara dawowa ba har gaban abadan!
Maganganun Kaka gaskiya ne, amma É—aukarsu gareni a lokaci É—aya abune mai kamar wuya, amma zanyi iyakar iyawata don ganin na fidda mutanen Yankina kunya.
Kwanaki bayannan, na fara bin gidan Customers ɗina, hannu bibbiyu suka karɓeni. A ranar da kuɗi masu nauyi na dawo gida.
Daga wannan rana na ƙara himma akan sana'ata, har zuwa lokacin da ranar komawata Makaranta ya yi.
Yasar ne yayimin siyayyar komai. Shi da Kaka da ƙannensa ne sukayi min rakiya.
Kasantuwata a Makarantar ƴaƴan masu wadatar Birnin Abyad bai sa na kai matsayina dai-dai da nasu ba, kitsona nakeyi ido rufe, kuɗi kuwa kamar anayimin yayyafin su, domin wasunsu biyan fariya da isa sukeyimin Ni kuma na karɓa ina godiya.
Watana É—aya a Makaranta na dawo nayi weekend tare da Kaka tare da bata ajjiyar kuÉ—in da na tara.
SUFYAN.
Babu abinda ya sauya tsakaninsa da Sumaya, yawan ƙorafi, batason wannan, ita wannan take so da dai sauransu. Rashin mafita yasa Sufyan yake lallaɓawa, kuɗi kuma idan ya samu na su Ɗayyib ne. Sumaya sai dai ta samu ɗan abinda ba'a rasa ba.
Wata rana taro ya kai Sufyan Companyn Dhahab da suke ƙera Tukwane. Lafiya qalau suka gama taro ya fito, a hanyarsa ta fitowa ya ga mutumin da ya zo Yankinsu a matsayin Kabeer saboda shi dai ya kasa yarda da gaske Kabeer ne. Basarwa ya yi, ya nufi Motarsa. Har ya shiga Mota ya tuna ya manta tabaransa a teburin da ya zauna. Da ɗan zafin nama ya juya saboda aikin dayake jiransa a office.
Baya ya dawo yana matse idanuwansa da suka farayimai yaji. Masu tsananin kamanceceniya da Malik, Salman, Kabeer ya gani a waje ɗaya. Ƙara buɗe idanuwansa ya yi gaba ɗaya yana zaresu. Babu wanda ya kallesa a cikinsu har su gama gaisawa suka tafi sai wanda yake tsananin kama da Malik ne ya rage a tsaye yana duba wayarsa.
Sufyan bai motsa ba sai gumin dayake tsiyayomai, yana cikin wannan halin Maigidanshi Baturen da suka zo tare ya fito daga ɗakin taron, da sauri ya ƙaraso kusa da Sufyan yaja hannunsa har gaban wanda yake kallo.
A gabatarwa da Baturen yake yi Sufyan ya ji ya ambaci Malik Dhahab shugaban Companyn Tukunyar Dhahab na ƙasar Abyad. Malik baya kallon fuskar mutum sai cikin idanuwansa, kamar yadda ya koya daga iyayen Gidansa, don haka kai tsaye cikin idanuwan Sufyan da suka fara canza kala yake kallo
Tafin hannun Malik mai girma da faɗi ya miƙawa Sufyan, shima Sufyan ƙasa ya yi da kansa kafin ya ɗago hannunsa da ya jiƙe da gumi tare da yimai nauyi ya miƙawa Malik bayan ya laso laɓbansa don ya tabbatar da harshesa ya na bakinsa bai fita ba.
Haɗuwar tafukan hannuwansu waje ɗaya yasa Sufyan ya ɗan ɗago kansa a hankali don satar kallon fuskar Malik, charaf idanuwansa suka faɗa cikin nashi, kafin ya sunkuyar da kansa ƙasa Malik ya ce; "Sufyan Ɗayyib Jalal right?"
Ambaton sunansa da salon da yasan dole sai wanda ya sanshi a Yankin Tudu ne zai iya faÉ—a da kuma Muryar da ya tabbatar masa da dagaske Malik ne a gabansa yasa idanuwansa juyewa numfashinshi ya É—auke É—if.
NAILA.
A makaranta na haɗu da ƙawa ƴar masu arziƙin da take biyana kuɗin kitso mai nauyi, da style kala-kala take zuwa a wayarta na yi mata sak irin wanda ta kawo. wannan dalilin yasa muke ɗasawa da ita har mukan yi hirar da ya shafi Kaka da Yankinmu da ita, musamman da nake nuna mata ni ɗin ba kowa ba ce, na riƙe matsayin na ƴar Talaka jikar Talaka.
Sun rigamu gama Exams. Ana saura kwana ɗaya zata tafi Gida ta zo da wani style ta ce nayi mata. Bayan mun gama take shaidamin Babban Birnin Abyad zataje shirye-shiryen Biki, wataƙila idan kitson ya yiwa ƙawayenta su zaɓeni na zo nayi mu su, domin dalilin da yasa tace nayi mata kenan. Ko Kakata ba zata amince ba? Tuna muradina na son zuwa Babban Birnin Abyad yasa na ji kamar na amsata mata amma da na tuna faɗan da Kaka tayimin, sai na ce mata bansani ba idan zata amince....
Shin Kaka zata amince kuwa??😄