Chapter 14
by @khairatup01
SHINGEN ƘAUNA.
Khairat.
Wattpad:khairi_muhd.
Paid book #500
free page 14.
Kafin safiya na fita daga hayyacina an kai ni asibiti.
Kwana na biyu a can. Na riga na ɗauki dangana na ɗauke kai daga lamarin.
Ana ta zuwa dubiya ko nace gulma tuni ana ta yayatawa a unguwa Abeed na da cutar ƙanjamau ƙila nima ita nake da ita shi yasa na kwanta ciwo kowa kun san da abinda zai faɗa. Kowa da abinda yake tunani a kai na. To yaya zan yi ta ina ma zan fara kare kaina. Wannan shi ne taƙaicina daman an sa min ido ana ganin akwai abinda nake yi a ɓoye to ga shi yau an fasa aurena a ranar aurena.
Nabeel.
Tunda na dawo ban samu na huta ba. Ogana baya nan matarsa ba lafiya ya koma gida ni ne mataimakinsa dole ni zan yi aiki.
Ina ta son na kira Hajiya amma babu lokaci. Hanan ma ba wayar kirki muka yi ba tana ta complain. Ni damuwata ɗaya da ita bata uzuri ko yaya in ban kirata ba sai ta ɗau fushi tace na manta ta ko wata na kula. Na lura tana da kishi sosai.
Wayata na ɗauka na duba agogo dare yayi amman ba sosai ba zan iya kiran ta.
Na kira layin sau biyu amma ba a ɗaga wayar ba. Duk da haka na tura mata saƙo.
"Fatan kina Lafiya Hajiya?"
Ban sani ba ko zata bani amsa a yanzu ko ba zata bani ba na dai tura mata na damu na san a wane hali take ciki gaskiya. Saboda yadda na tafi na bar ta sai kuka take yi hakan ya taɓani ba kaɗan ba.
Da na ji ƙarar shigowar saƙo ɗin sai na ɗauki waya amma sai in ga ba ita ba ce sai na yi tsaki na maida wayar. Wai ni kaina mamakin yadda na damu da ita nake yi.
Har bacci ya soma fizgata na ji shigowar waya. Da sauri na diro na ɗauki wayar Wallahi ban san lokacin da na yi tsaki ba kawai sai na maida wayar na dangwarar da ita gefe ina tsaki.
Bana buƙatar ɗaga wayar kowa a wannan lokain bayan ta Hajiya. Sai na ji ma duk haushinsu nake ji masu kiran nawa. A jirgi na saka ma na sa a caji na koma na kwanta,har da ɗora fillo a kan fuskata.
*
Washegari.
Hanan.
Saffiya ba za ki gane ba Wallahi. Ku kawai kuna hangen bai da kuɗi ne ni kuma kun san ina son abu mai kyau. Anya kuwa kin taɓa ganin Nabeel kuwa? Kyau , ilimi, gayu duk ya haɗa babban abin ma akwai shi da iya soyayya mai nake buƙata ne in ba soyayyar ba?
Ke dalla matsa can tun yaushe aka wani daina wani soyayya. Hajiya in kina da buƙatar capacity dole ne ki samu ki auri mai kuɗi ko da yake ba za ki damu ba tunda a gidanku akwai kuɗi. Ke kina son ki ce min ƴan gidanku sun yarda da hakan?
Ya ba zasu yarda ba? Kin san Abba babu ruwansa in dai kin kawo mai kina so zai miki bare ma Nabeel yanzu ya samu aiki mai gwaɓi kin manta ya koma Lagos.
Ni dai ki kula da kyau. Kar ya zama kina nan kina kula masa da so yana can yana kula wata . Kin san mazan Hausawan nan musamman ma marasa kuɗi sai kiga sun auri mata sama da biyu a zo ana Wallahi tallahi ko a damu jama'a da yen yen ga ƴan duguwi-duguwi su ishe ka da kuka.
Hanan tayi dariya. Kar ki wani damu duk abinda zai yi sai ya gaya min ke ko be gayan a lokacin ba zai gaya min daga baya. Wallahi ina son sa. Na gaya mai ma ya turo.
Kya bari ya samu muhalli dai ko?
kuma fa haka ne.
Amma kin san meye matsalar?
Sai kin faɗa.
Abba ba zai bari ba son samu ma kawai ya turo iyayensa sa a san da shi a gida.
Na san dai Mamaa ba zata bari ba. Kin san ta da son mai ɗan maiƙo-maiƙo.
Na sani amma na san yadda zan gyarota ta hanyar Abba zan bi ai. Shi ai in ya faɗa bata musawa.
To haka ne. Allah Ya nuna mana.
Amin.
*
Abeed.
Kunya dai ta duniya na sha ta har bana son fita zaman ɗaki ya aure ni. Alhaji duka ne kawai bai min ba amma tabbas ya ɗauki fushi da ni sosai. Ban taɓa sanin haka abin kunya yake ba sai bayan faruwar wannan lamarin da ya ruguza min duk wani tanadi. Na rasa Nadeeya na rasa mutuncina a idon duniya ma gabaɗaya. Ita kan ta Yayar ba wani nema na take ba kawai an bar ni daga ni sai halina.
Sau ba adadi ina gwada kiran layin Nadeeya amma bana samun ƙwarin guiwar kiran ta, sai na ajiye wayar. Yanzu ina ji ina gani sai dai na sauya sheƙa dole zan bar garin Kano na wani lokaci amma na sani ko kusa Abba ba zai bani izinin barin garin Kano ba tare da na yi aure ba. Don na soma jin ƙishin-ƙishin yana neman Aliya. Aliyar ce ta saka min ita ce kuma zamu lallaɓa tare. Haka ya saka na gwammaci na auri Aliyar da Abba ya cire ni daga cikin ƴa'ƴansa magada na rasa madogara. Na fawallawa Allah komai zan ci gaba da zuwa ganin likita ina karɓar magani ko don na yi kyan gani.
*
Nadeeya.
Sai da na ƙara kwana biyu a asibiti na dawo gida.
Na gamsu da irin kulawar da na samu daga wurin ahalina.
Bayan amsar wayata ne na ga kiran mutane rututu da sakonin waya. Ba zan iya bin su na amsa ba hakan ya saka na ajiye wayar kawai na saka ta a jirgi nayi wanka da ruwa masu ɗumi na sauya kaya zuwa masu kauri na shafa humra na kwanta a kan gadona.
Gabaɗaya jin duniyar nake yi babu daɗi don sam komai baya min daɗi.
Bani na yi abin kunyar ba amma ina jin kunyar haɗa ido da mutane ina kuma jin kunya da tsoron yadda zan amsa tambayoyin mutane. Na sani suna nan da yawa da suke son su ga durƙushewata su ga gazawata su yi mini dariya ko su yaɗa sharri a kaina na sani wannan dole ne daman jama'a sun saka min ido sosai.
Haka na janyo wayar na kunna data ai kuwa saƙonin kawai ke shigowa ɗaya na dukan ɗaya sai ajiye wayar ma na yi a gefe suka gama hantsilowa ciki.
Group ɗin mu na fara shiga nan na dinga cin karo da sakonin jama'a wasu na min jaje wasu kuma dariya suke yi min wasu kuma ba jajen ba kuma dariyar sai dai reacting. Dama na kwana da sanin Shamsiya ba zata ƙaunace ni ba tana ɗaya daga cikin waɗanda suka yaɗa batun an fasa aurena ranar auren ance ina da wata cutar ango ya gudu yace bai aurena an neme ni ma an rasa sai tafiya suka yi basu gan ni ba.
Ban yi mamakin hakan ba. Sai group ɗin ya kasu kashi biyu da masu goyon bayan Shamsiya da masu kuma jajanta min suna kare ni. Gishiri-gishiri na ji a cikin bakina ashe hawaye nake yi.
Da kaina na tambayi kaina "Why me?" Sai kuma na yi sauri na ce "Astagfirullah."
Kiran Summaya ne ya shigo wayata ta watsapp ɗin na ɗauka.
"Baby fatan dai jikin da sauƙi?"
"Da sauƙi fa Baby. Na gode."
"Kin tabbata?"
Na lumshe ido kamar tana gani na nace "Wallahi."
"Alhamdulillahi! Don Allah kar ki maida kai ga zantukan da ake yi a group kin san mutane da son yi wa mutum hisabi. Ki ɗauke kai ai mu mun san ba haka ba ne kaddara ce kawai. Kuma Abeed ba mijinki ba ne."
"Baby me ya sa ya min irin wannan yaudarar? Ya san ba zai zauna da ni ba ya saba min da son sa? Ya san ba mutumin kirki ba ne ya sa son sa ya shiga raina? Ya tozarta ni a idon duniya yanzu ki gaya min mutum nawa ne suka yarda da nima ina da cutar? Ba ki ji me suke cewa ba?"
"Haba mana Nady! Ke fa musulma ce, ki sani dole ne ki yarda da kaddara. Dole ne ki yarda da cewa akwai mai kyau akwai mai marar kyau. Wannan wani mataki ne na rayuwa wanda zai wuce da yardar Allah. Kowa zai manta. Mutane kamar yadda na gaya miki they always talk. Shamsiya kuma ya kamata ki saba da halinta. Hassada take miki tun fil'azal. Ki je ki kwanta ki huta. Rest ki manta ba ke ce ya kamata ki tsangwami kan ki ba Abeed ne, ba ke ce za ki ɓuya ba Abeed ne. So ki manta ki warware ki dawo mana yadda kike asalin Nadeeya."
"In sha Allah!"
"Yauwa off the data. Sai anjima."
"Tam."
Muka ajiye waya na ji daɗin wayar da muka yi da Summaya na samu sauƙi a raina sosai.
Saƙo ne ya shigo min na ga lamabar Yakasai ce.
"Ina ta kiran ki ba kya ɗauka.Allah sa ba laifi na yi miki ba. I was just trying to help."
Maida masa nayi nace:
"Na gode Yakasai haƙiƙa ka cece ni kuma ba zan manta ba. Ka bi ni bashi wata rana zan rama taimakon da ka yi min. Na gode ƙwarai da ceton rayuwata da ka yi. Ban ɗaga wayar ka ba saboda bana nan ina asibiti yau aka salamo ni."
Can naji ɗin saƙo ya shigo.
"In kira ki?"
Na kalli screen ɗin da rubutun ciki kamar ba zan ba shi amsa ba sai kuma nace;
"Zaka iya."
Cikin sakanin da basu gaza biyar ba kiransa ya shigo wayata.
Asalamau alaikum.
Wa'alaikum salam.
Barka Hajiya yaya jikin? Ban san baki da lafiya ba."
"Da sauƙi ai Alhamdulillahi."
"Ba dai saboda wancan mutumin kika kwanta ba? In saboda shi ne na janye dubiyata."
Murmushi kawai na yi masa.
Har cikin kunnensa ya ji sautin murmushin.
"Saboda shi ne?"
"Uhm'uhm kawai damuwa ce ta yi min yawa."
"To ki daina ki share ki manta."
"Sai a hankali ba abu ne mai sauƙi ba."
" Bai cancanci ki damu a kan sa ba ne."
"Na sani."
"To ki manta shi kamar wani mummunan mafarki ki ci gaba da tafiya kina addu'a shi kenan."
"In sha Allah! Na gode sosai."
"Ba komai."
"Yaya aiki ,ina Hanan kuma?"
Murmushin yay min shi ma ɗin yace "Aiki mun gode Allah ga mu cikinsa dumu-dumu. Hanan kuma tana lafiya yau ba mu yi waya ba."
"Ayya! Allah Ya taimaka."
"Amin."
"Sai anjima."
"Tam ki huta ki manta da wanacn banzan kar ki ce za ki matsawa kan ki."
"In sha Allahu Yakasai."
"Sai anjima."
Ya ajiye wayar. Atleast na sauke wasu daga cikin damuwoyi na.
Bature yace "Life must go on" haka ne dole ne a ci gaba da rayuwa babu abinda za a fasa saboda rashin wani ko wata rayuwar dai dole a ci gaba da ita one way or the other.
Na manta Abeed na goge lambarsa a wayata. Ba a manta ba kuma ba za a manta nan kusa ba duk da an kai wattani kusan bakwai ma da faruwar lamarin amma wasu basu manta ba kuma basu fasa jifana da munanan kalamai ba ko a gabana ko a bayana nima na saba kuma na daina damuwa.
Bayan Abeed akwai wani Aminu da ya zo shi ma ƴan zuga suka saita mai hanya an fasa aure na ina da cuta sida (HIV) Sai ya tsorata ya fasa.
Wani ma ya zo Hashim shi ma ban san waya gaya masa ba sai ga shi ya daina zuwa ya daina ma kirana da na kira shi kuma yace min ba komai ba ne kawai na fi ƙarfinsa ne nace mai da baka san na fi ƙarfin ka ba ka zo? Na dai rabu da shi. Cikin shekara guda nayi samari kusan biyar sun guduwa abin ya fara damuna sabod yanzu shekaruna sun fara tafiya, nima ina son na yi auren na tara zuri'a kamar kowa kamar su Yaya Muhmmad.
Zan iya cewa a shekara ɗayar nan mutum guda ne na kasa manta shi a raina Yakasai. Tun bayan wancan lokacin ban ƙara ganinsa ba kuma bana ma ganinsa a watsaap ko dan nima jefi-jefi nake shiga oho.
Mafarin sauyawar rayuwata.