MATAR COLONEL : A Sex Therapist

Chater eight

by @rularnt

✈️ Two Weeks Later – Arrival in Nigeria

Wani gagarumin convoy ya tashi daga Yola International Airport, motocin sirika masu glass tinted da tsaro a gaba da baya. Jami’an DSS da ‘yan sanda sun jagoranci su, suna bubbuga siren yadda mutane ke waige-waige. Ambassador Umar Balarabe da iyalinsa sun dawo gida — forever, ba ziyara ba.

Binta, zaune a cikin black Prado jeep, ta duba window tana kallon tafkin Daji da bishiyoyin palmatta da ke gefen titi. Iskarta daban ce — wacce ke  shiga har cikin zuciya.

"Gida... finally." Ta furta a hankali, tana murmushi.

Umma (mahaifiyarta) kuwa ta dafa hannunta gently, "Ya a kayi Binta, kin ji dadin da na ke ji? Allah ya sa dawowar nan ta zama alheri."
Binta ta gyada kai, "Amin Umma, I can't wait to settle in and start something impactful."



Da suka iso, gidan ya cika da mutane — danginsu, abokai, masu ruwa da tsaki. Manyan inflatable canopies sun cika harabar gidan.

Anty Amina ce ta fito da sauri daga cikin gidan, tana sanye da atamfa peach da head tie mai dinki na zamani.
“oyoyo! Baby London! Come here!”
Ta rungume binta sosai, suna dariya, tana hawaye.

"Wallahi kin zama budurwa sosai, kamar ba ke ba! Kai na rasa bakin magana."

Firdausi da Bello, ‘yan uwan Binta..yaran  Anty, suka rungumeta da murna.

"Yanzu haka zamu dinga kasancewa,there is no going back!" Bello yace yana dariya.

After some hours, Baki yan uwa da abokan arziki suka tattafi ya rage yan gida.

Gidan ya sha gyara — sabbin furniture, wallpapers, chandeliers da English–Hausa fusion aesthetics.
An ware daki daya musamman domin Binta, an yi shi ne a matsayin office dinta inda za ta dinga gudanar da therapy session dinta.

Binta da iyayenta sun shiga cikin sabuwar rayuwarsu.

Sun watsa ruwa, sun sauya kaya, suka zauna cikin VIP sitting room.
Umma ta gyara zani tana kallon mijinta, "Alhaji, Allah ya dawo da mu lafiya. May Nigeria treat us well."

Ambassador Umar ya dafe hannun kujera yana kallon su Binta da mahaifiyarta,
 "This is our home. We will contribute. And our daughter will shine here too, In shaa Allah."

Can da daddare a daki,Binta cikin dogon peach gown da white chiffon veil, ta duba kewayen dakinta mai tsari sannan tace,

"Gaskiya I feel this is where I truly belong. In shaa Allah this relocation is for something bigger."

Tana kallon waje daga cikin glass window, “home sweet home.” 
Tace yayinda ta ke gyara kwanciyar ta a kan gadon ta. Ta kashe bedside lamp dinta, tayi adhkar sai bacci.