ZINARE🔥

26

by @nafisatusasaal01

🔥ZINARE🔥




  SASAAL




Page 26


Har muka gama Exams ban daina tunanin tattaunawarmu na zuwa Babban Birnin Abyad ba. Amma na sawa raina amincewar Kaka shi ne nawa.

Da murna Kaka ta tarbeni bayan girki-girke ma su daÉ—i da ta shiryamin. Bayan na huta na ci abinci, na so sakomata zancen zuwana Babban Birnin Abyad amma tsoron yadda zata fassara zancen ya sa na kasa. 

★har washe gari na kasa yi mata zancen tafiyar, Sai ita da kanta ta kalleni cikin dariyar da ya haɗe da mamaki tana cewa;
"Me kikeson faÉ—a kika kasa Naila? Tun jiya ina ankare da ke, karki  ji nauyi ki faÉ—amin zan fahimceki kinji"
Murmushi na yi ina murza goshina, cikin kame-kame na ke bata labari. 
Kaka kallona takeyi maganganu Sarki tsafin Yankin Tudu na amsa kuwa a cikin kunnenta "Naila zata warke amma akwai jarabawar da ya fi wannan raɗaɗi a gaba, domin zata isa Babban Birnin Abyad, da ƙarfin ikon Allah! Amma daga lokacin ƙullin shekarun da aka kasa warwaresa zai fara warwarewa da kansa, arziƙin da Sufyan ya yi gajen haƙurin ya riskesa zai bayyana, wannan yana ɗaya daga cikin abinda Mahaifiyarsa take kwaɗaitar masa ya gaza fahimtarta, da ya yi haƙuri da zai zama wankakke abisa laifin da Kakannin-kakanninsa suka jima su na aikatawa aban ƙasa, ko da Naila ta warke ta koma Birnin Abyad, Birnin Abyad ba mazaunin Naila ba ne. Ba lallai ki yarda da maganganuna ba, amma daga ranar da sanadi ya kai Naila Babban Birnin Abyad, zaki gasgata batuna" furucin Sarkin Tsafin Yankin Tudu kenan lokacin da ya zo duba Naila, amma Kaka taƙi basa damar yiwa Naila magani acewarta Boka Ɗan uwan shaɗai ne, ita kuma magani mai tsarki take nemawa jikarta.

"Wallahi ban amince ba Naila, kinsan abinda kike faɗa kuwa? Babban Birnin Abyad har abada ba wajen zuwanki ba ne, karma ki ƙara tambayata don bazan lamince ba na gayamiki" Kaka ta faɗa cikin masifa! Tsabar masifa har rufe idanuwanta take yi.

Birkicewar Kaka lokaci ɗaya da yadda take magana har da su fashewa da kuka ba ƙaramin tsoron abin ya bani ba, cikin haushin yadda ta hantare ni har da su kuka na ce;

"Kaka kukan me kike yi, ni fa kawai shawararki na nema, bance dole sai na je ba, sannan ke kika ce na gayamiki kar na ji nauyin komai zaki fahimce ni, amma gashi akan kawai na faÉ—a miki gaskiya shine kike masifa har da su kuka, dama can dai haushina kike ji, daga dawowata zaki sanyani cikin damuwa, na fara ciwo kuma kiyimin sharrin Yankin Tudu nake son komawa, gaba É—aya kin canza Kaka."  Tsit ta yi tana kamo hannuna. ÆŠan fizgewa na yi ina cewa " ki Æ™yale ni Kaka, tunda kin fara jin haushina a É“oye bansani ba, ni ma daga yau babu ruwana da ke"

Hawayenta ta share still ba ta saki hannuna ba, da sanyi jiki ta ce 
" to zauna na faÉ—a miki gaskiya ina fatan kema za ki fahimceni, ki janye batun zuwanki Babban Birnin Abyad"

Son labari irin nawa yasa na zauna da sauri jikin mu na gogar na juna.

Abinda Sarkin tsafin Yankin Tudu ya faÉ—a ta maimatamin sannan ta É—ora da;
" Naila bawai na gazgata maganganun sa bane ɗari bisa ɗari, amma a yanzu a jikina nake jin ko dukka maganganunsa ba su zama Gaskiya ba, to baza'a rasa gaskiya ko da yaya bane ciki, duba da yadda su Hindu suke fafutukar dole sai kin koma cikin rayuwar ɗansu, Naila inajin tsoron matsalar da zai ƙara kunnowa rayuwarmu kai a yanzu, ki gafarceni"

"Saboda iya wannan dalilin zaki haramtamin samun kuɗin da zai sauya rayuwar Yankina? Kinsan nawa za'a biyani Kaka?. Rayuwarmu bazai taɓa cigaba da tafiya a haka ba, dole sai da gwagwarmaya tare da ƙalubale Kaka, baƙin ciki da farin ciki basa dawwama a rayuwar Bawa, idan warware ƙullin ne zai zama cigaban Yankinmu mai zai hana mu tunkari warwareshi ko da hakan zaisa mu rasa rayukanmu, tun da dai dole zamu mutu wata rana. Kaka kiyi tunani tunda na ki tunanin yafi nawa zurfi, ba kuma zanyi yin kaina ba dole zan jira umarnin ki, amma Kaka ki tuna gina kanmu da Yankinmu wajibunne, saboda Yasar shine ƙarfin gwiwar zamanmu a Birnin Abyad, to idan ya mutu fa? ko ya gaji damu fa? Jira zamu yi tayi sai dai wani yayimana gwagwarmaya muji daɗi mu ba za muyi da Kanmu ba? Saboda muna tsoron mutuwa?
Kaka kiyi tunani a nutse, kuma karki ji shakkar sanar da ni duk abinda kika yanke, In Shaa Allah zan yi miki biyayya kin ji." 
na ƙarasa faɗa ina rungumeta bayan na sumbaci goshinta.

Tun a lokacin bugun zuciyata ya sauya daga tsoro zuwa ƙarfin gwiwa.


SUFYAN
Da ya farka ya ganshi a gadon Asibiti baiyi mamaki ba.
 Sumaya tana ganin ya farka ta ajjiye wayar hannunta tana matsowa kusa da shi, sannu take ta maimatamai tana kamo hannunsa. LaÆ™was Sufyan ya yi. A hankali ya buÉ—e bakinsa ya zaro harshensa. 

"Sumaya kina ganin harshena, yana cikin bakina?" Ya yi tambayar yana karkaÉ—a harshensa.

Da mamaki Sumaya ta ce; "gashinan kana karkaɗawa, maiyasa zaka yimin irin wannan tambayar Baby, relax har yanzu zafin ciwon bai gama sakinka ba, bari na kira Doctor" ta ƙarasa faɗa tana sakin hannunsa haɗe miƙewa ta bar ɗakin.
Ajiyar zuciya Sufyan ya sauke, sai dai kafin ya yi relax ɗin da Sumaya ta ce, asalin fuskar Malik da babu Tabarau babu komai sai ƙasumbar da shima an ragesa sosai saɓanin jiya da ya cikemai rabin fuska ya bayyana a ɗakin, mai kamannin Salman sak na biye da shi a baya.
 
Jikin Sufyan ne ya saki, tabon tsoron Malik da ya kwana da shi washe gari ya ɓace na dawowa sabo fil, idanuwansa ya kulle gam kamar mai barci.

Ido Malik ya lumshe kafin ya saki murmushin da sam bai masa kyau ba saboda bai saba ba, da iya ganin fuskarsa kaɗai zai iya kawar da Sufyan a doron ƙasa ta hanyar bugawar zuciyarsa. Amma Yaron tausayi yake bashi bai san komai ba sai abinda suka ɗorasa akai, ya jima da karantar Sufyan shi ba faɗan kawar da wani ne a gabansa ba, shi dai burinsa ya zama kyakkyawa ya tara kuɗi shima ya zama Dhahab ɗin kansa kamar yadda suke sauraran duk wa su hirarrakinsa ta offishinsa har ma da Gidan da yake kwana.

Da buɗaɗɗen muryarsa mai nauyin dake amsa amo da ya dace da kalar siffarsa Malik ya ce "sannu da Jiki Sufyan Ɗayyib Jalal, Allah Ya ƙara afuwa, ga colleague ɗina Uzair ku gaisa" ya ƙarasa faɗa yana nuna Uzair.

Sufyan daya kasa gaishesu da sunan ya na barci, kuka ya fasa idanuwansa a kulle, kansa a can gefe. Hannuwansa biyu ya haÉ—a waje É—aya ya É—agashi can sama dai-dai saitin su alamar roÆ™o. Tsabar kukan da yakeyi kafaÉ—unsa da ko ina nasa rawa yakeyi. 
Malik miƙewa yayi zai fita saɓanin Uzair da ya tsaya kallon Sufyan da mamaki. Ds taushin Muryar da sam baya kama da na Salman yake tambayarsa da yaren Abyad

 "maiyasa kake kuka?"

 Damacan Sufyan ba wani sanin Murya Salman ya yi ba balle ya tantance.
Sufyan bai amsa ba still yaÆ™i kallon gefen da Malik ya bar Uzair a tsaye. 

Sufyan na jin Muryar likita ya ɗan saki ajjiyar zuciya sai dai ƙara jin Muryar Malik a bayansa ya sa ya sume kansa ya karyo kamar zai faɗo daga kan gadon.

Hannun Malik Uzair ya ja suka fito waje. 

Da fuskar tausayi Uzair yake tambayar Malik wanene Sufyan? Maiyasa yake jin tsoron da ya ke sashi sumewa idan ya gansu?

"Yankin Tudu, Babban ÆŠa namijin ÆŠayyib Jalal" Malik ya faÉ—a yana kallon diamond wristlet É—in hannunsa.
Wayar Uzair ne ya faÉ—i kasa a take gilashin baya da na gaba yayi kwatsa-kwatsa.

Dariyar muguntar da ba kasafai Malik ya fiye yi ba yasa ya na kama hannun Uzair da ya sanƙame a tsaye. Wayarsa ya sunkuya ya ɗaukarmai suka bar wajen.

Sufyan sai da ya yi kwana biyu yana fama da zazzafan zazzaɓi jininsa har hawa ya yi, baya iya ɗaga kiran kowa, da zarar ya ji motsin ƙofa gabansa yake faɗuwa, hankalisa baya dawowa jikinsa har sai yaga wanda zai shigo.

Likita ne ya zaunar da shi yayi mai faÉ—an yana so ne ya kashe kanshi? Ko wani abun ake yi mai a Asibitin da yake sashi yawan fargaba?

Hannu likita Sufyan ya kamo yana kuka yana bashi labarin su Malik ne suke basa tsoro. A wannan ranar daƙyar Sufyan ya nutsu ya kwantar da hankalinsa tunda likita ya yi masa alƙawarin su Malik ba zasu ƙara dawowa ba.

Da yammaci ya dannawa Mahaifiyarsa kira, bayan Sumaya ta tafi Gida ta É—an huta.
Kamar tayi shekaru tana jinya haka Sufyan ya tsinkayi Muryar Mahaifiyarsa. Saitin zuciyarsa da bugunsa yake fita da ƙarfi ya dafe kafin ya ce;
"Menene yake damunki Ummeena? Kwanana biyar bani da lafiya babu wanda ya nemeni a cikinku, ashe idan ba buƙatar kuɗi ba, ba ni da wani amfani a gareku"
Murmushi tayi kafin ta ce;
"Sufyan É—ana na fika shiga halin jinya, domin ciwona ba irin naka bane" gyara zama Sufyan ya yi yana yi mata sannu cikin tausayawa. Kamar daga sama ya ji tace;
"Ina ka jefar da makarin sirihin jikin Naila Sufyan?" Kame-kame ya farayi, sauƙin dole na zuwarmai lokaci ɗaya.

"Sufyan!  Malik zai iya riskarka a koda yaushe, amma kafin na baka labari, inaso duk halin da kake ciki karka É—ara kwana biyu baka isa Birnin Abyad wajen Naila ba, duk iya yadda za kayi karka bar Naila ta isa Babban Birnin Abyad ba tare da ta amincewa komen aurenku ba, ko kwanciya ne kayi a Æ™asa ka roÆ™i yafiyarsu, domin Naila itace Makamin tsirarka daga su Malik Sufyan albarkacin matsayin da take da shi a Dhabah. Karkayi watsi da umarnina kamar yadda kayi watsi da shi ka cigaba da zama da Sumaya, idan ka isa Birnin Abyad duk abinda ka riska ka yi gaggawar kirana domin na baka wasiyyata ta Æ™arshe." Tana gama faÉ—a ta datse kiranta.

Shi dai Sufyan bai san abinda ya samesa bayan katse wayar Mahaifiyarsa  ba, sai da ya wayi gari yaga Sumaya tsaye a kansa tana kuka.. 

Daƙyar Sufyan ya daure ya ƙara kwana ɗaya a Asibiti. A gaggauce ya sanar da Sumaya ta shirya kayanta, a kwai aikin da zaiyi a Birnin Abyad.

NAILA
Muna zaune da Kaka kiran Customernta ya shigo wayata. Domin Kaka taji komai a sarari na saka wayar.

 Da zumuÉ—i take sanar dani kitsona ya yi matuÆ™ar jan ra'ayinsu kuma sunyi alÆ™awarin biyana kuÉ—i masu nauyin gaske. Zanzo nayi kwana biyu sannan tayi musu bayanin ina da Kaka sun ce zasu turo tikiti da komai mu taho tare. Kallon Kaka nayi ina jiran umarninta.

A hankali ta ɗaga kai alamun ta amince!!!!.....😄

Shin Sufyan zai riski Naila.???